← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 130

Sashe 73

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mata da suke ganin su ba kyawawa bane ma ni kuna bani mamaki wlh, na taɓa jin wata da kanta tana zagin kanta wai ita mummuna ce, for what reason? Kina hauka ne? Angaya maki ALLAH ya taɓa yin abin da babu kyau ne, sannan dik cikin abin da ALLAH ya halitta babu abin da ya karrama sama da halittar ɗan adam, amma har kina da bakin da zakice baki da kyau ko ki ce wata bata da kyau? Billahillazi babu ɗan adam ɗin da bashi da kyau, domin kuwa dik abin da ALLAH ya halitta mai kyau ne, bari in baki misali, ALLAH ya yi ki da bakar fata, kice bari ki canza zuwa fara, wlh ba karamin muni masu canza halitta suke yi ba, to tin daga nan zaki gane dik abin da ALLAH ya ajiye a wajen bashi da muhallin da ya wuce wannan waje, uhm ALLAH yana bawa bayinsa abubuwa da dama a time da ya so, ya halicci fara, ya hanata sura da diri, dan basu dace da ita ba, ya halicci baka, ya bata kaifin ƙwaƙwalwa da ilimin da duniya zata yi alfahari da ita, zata taka in da farar bata taka ba. Amma mu duba me ALLAH ya ce. Allah ya bayyana cewa duk abin da ya halitta yana da kyau, yana da hikima, kuma babu rashin adalci ko kuskure cikin halittarsa. Wannan ya haɗa da kyawawan mutane da waɗanda ba su da kyau a bayyane, domin dukkanin su suna da wani sirri da amfani a cikin tsarin halitta. Cikin Suratul As-Sajdah sura ta 32 aya ta 7 zuwa ta 9. Wannan aya tana tabbatar da cewa kowane abu da ALLAH ya halitta yana da kyau cikin tsarin da ya so. Kazalika cikin Suratul At-Tin sura ta 95 ayata 4. Wannan ayar na nuna cewa a cikin asali da tsarin halitta, mutum yana da kyakkyawan sura da daraja. Suratul Ghafir sura ta 40 aya ta 64. Ayar nan na nuna cewa ALLAH ne ya halitta mu cikin sura mai kyau wanda yake bisa kyakkyawan nufi da tsarin hikima.

Dan haka babu halittar da ba ta da amfani. Suratul Ali Imran sura ta 3 ayata 191. Rabbana ma khalaqta hadha batilan..............Abin da ke nuni da cewa kowane abu da ALLAH ya halitta yana da hikima da ma'ana ba kawai kyakkyawa a bayyane ba, akwai ta sirrance da ALLAH ya yita. Idan na ce zan tsaya zayyana maku ayoyi a kan halittar ɗan adam sai mu kare page ɗin nan, dan haka ku daina raina halittar ALLAH, babban kuskure ne. Dik yadda Manzon ALLAH ya kai ga son Nana A'isha sai da ranan ya tsawatar mata da ta ce wa wani yana da katon kai, iya abin da ta faɗa kenan, amma manzon ALLAH ya ce mata wannan magana da kika faɗa A'isha, muninta ya kai ta iya lalata ruwan teku, to ke waya aikeki ki ce da wata mummuna ko ki cewa kanki Mummuna?. Ki ji da kanki, ki ji a ranki kin fi kowa kyau, ki ce babu biyunki a kyau, kada ki kuskura ki taɓa haɗa kanki da wata, dan ke tadabance, na jima ina son yin magana a kan halittar nan wlh lokacin ab-ban samu, yau dai nace bari in daure in yi, kada karatun littafai ko kallon fina-finai yasa ki ji ke ba kyakkyawa bace, ina karya ne wlh, kyanki sirri ne, ki natsu zaki gano hakan. A dai hasken fata na Nigeria ni ba baka bace, ni fara ce, amma ina balain kaunar bakake sosai, shiyasa bana taɓa yin rubutu babu bakaken fata ko ban daraja fatar ba, saboda me? Saboda wasu Annabawa bakaken fata ne, sannan tushen kowani ɗan adam baki ne tin da Annabi Adam (As) baki ne!!. Kada ki raina halittarki ko na wata, baki san sirrin da ALLAH ya ɓoye a wajen ba!!!.

---------------------🔥

Ganin ta shagaltu da kallonsa ba tare da tasan tana kallon nasa bane yasa ya ɗage mata gera guda yana cigaba da ƙayataccen murmushinsa. "Yah how far? Nai maki kyau ne?". Ya faɗa yana kai hannun saman waist ɗinsa, ya riko kugun nasa yana ɗan jujjuyawa kaɗan-kaɗan.

"Kai É—in ne kyakkyawa? Tab ka cuci kyawawa, yo ai nina ma fika kyau". Ta faÉ—a tana harararsa. "For sure kin fini kyau, amma ke kaÉ—ai ce kika fini, ni dai kawai cewa na yi shin nai maki kyau ne? Ban ce na fikiba chocolatyna mai É—an karamin baki sai faÉ—a da masifa". Cikin zolaya ya yi maganar.

Tana cigaba da harararsa ta ce. "To ai na fika baki nesa ba kusa ba, kai ba dan ALLAH ya ceceka bakin naka pink color sosai bane da ai bama za'a san kana da shi ba saboda ƙanƙanta"........... Shiru bai yi magana ba yana cigaba da murmushi.

"Ni ka fita mun a É—aki na ce". Ta faÉ—a tana dirowa kasan bed É—in kamar wata renon Chinawa. Yana tsaye bai motsa ba har ta kariso gabansa, a karo na biyu tasa hannu zata cakumesa ta kaishi waje, sai dai a wannan karo hannayenta dikka biyu ya damko da hannunsa É—aya, ya mai da hannayen nata ta bayanta.

Ƙoƙarin kwacewa ta fara yi amma ta kasa, hakan yasa ta hakura ta fara faɗin. "Ni ka sakeni bana so". Gera guda ya ɗage mata. "Ki kwaci kanki tin da kina da karfi". Turo mashi baki ta yi. "In baka sakeni ba sai na ja maka ALLAH ya isa".

Wani irin kallon kurilla yake binta da shi, showly ya É—an rankwafo kanta kaÉ—an, hakan yasa ta yi gaggawar ja da baya, matsawa ya yi dab da ita, da sauri ta sake ja da baya. Haka suka yi har suka kurewa wall É—in wajen. A hankali ta juya ta ga sun kure bango, da sauri ta juyo da kallonta a kansa, ai wani irin razana ta yi na ganin ya matso da face É—insa dab da tata.

Zazzaro mashi idanu waje ta yi, da sauri ta sake cewa. "Ni ka sakeni bana so"...... Shiru bai yi magana ba, yana dai cigaba da kallonta. Cikin faÉ—a ta ce. "Na ce ka sakeni ko?".

"Shiiiiiiiii, ki daina magana mana, ki tsaya shiru". Ya faÉ—a cikin wata iriyar murya tamkar yana a cikin maye. Kirjinta ne ya yi wani irin bugawa na jin yadda voice É—insa ta rikiÉ—e, shi kansa ya rikiÉ—e mata, idanunsa sun canza kala, yanayin fuskarsa gabaÉ—aya ta sauya, hannunsa da ya riketa sai kakkarwa yake yi tamkar yana jin sanyi.

"Ba zan daina yin magana ba tin da ba bakinka bane nawa ne, ni ka sake ni, dama kullum ina faÉ—a cewa kai É—an iska ne, to ni ina da mutumcina, ka sakeni"........ Kashe mata ido É—aya ya yi, in a low voice sosai ya ce. "Ai ban ga mutumcin naki ba, kuma wlh in kika sake yin magana a nan zaki sha mamakina". Ya yi maganar kallonsa a kan É—an siririn dogon wuyanta.

"Magana fa saina yi tin da ba da bakinka nike yi ba, kuma sai ka sakeni in ba haka ba in gantsara maka cizo a hannun naka sai an kaika asibiti..........". Ai bata kai karshen maganar ba ta É—auke wuta diff sakamakon matsawa da ya yi ya haÉ—e bakinsu waje guda.

Da karfi ta fara kokarin kwace hannunta dan ta turesa, sai dai kuma ina, bazata iya ba, ta yi iya kokarinta ta kwaci bakinta daga nasa, nan ma ta gagara. Shi kuwa ai É—ayan hannunsa ma yasa ya mannata da jikinsa sosai, ya rikota ta baya, ga É—ayan hannun nasa kuma ya rike hannayenta da shi.

Hot kiss ya bata mai rai da lafiya for almost 5 mins kafin slowly ya zame É—an bakinsa daga nata yana lumshe idanunsa tamkar mai jin barci. To É—azun da ya ce kada ta sake yin magana bata yarda ba da ta sake, yanzu kuma sai ga shi bai ce kada ta sake yin magana ba ta yi shiru diff tamkar an É—auke wutar nepa, ta kafe shi da ido tamkar wacce ta sume mashi, ko motsi bata yi.

Da kyar ya iya waro idanunsa gabaÉ—aya a kanta, saboda tsabar neman tsokana irin nasa shi ma sai cewa ya yi. "You're over, in kara kaÉ—an?". Yadda ya yi maganar tamkar irin wanda kwaya ta buga É—in nan. Shiru bata amsa mashi ba, hakan yasa ya É—an saki hannayenta tare da É—aukarta cak sai saman bed É—inta, yana jin tana breathing, hakan yasa ya fahimci ba suma ta yi ba, kawai ta tafi hutu ne na wuccin gadi, zata dawo daidai idan ta É—an huta, yau dai babu bakin rashin kunya. NI KUWA NA CE AKWAI BALAI A KINGDOM YAU, AN SHAWA YAR BAPPA ÆŠAN BAKIN MASIFA.

Gyarawa ya yi ya kwanta a kusa da ita kamar wata matarsa, har da juyowa ya É—an yi rugingine yana kallon fuskarta, jira yake yi ta dawo daidai su buga diramarsu, dan yasan ALLAH ne kawai zai raba wanna faÉ—a yau, ya É—ebo da zafi, to amma ya zai yi? Sai da ya ce mata kada ta sake yin magana taki bin umarninsa, shi kuma ba zai iya shanye maganarta a kurkursa da shi haka ba, dan haka ya cika aiki, da alama ya shirya duk diramar da zata buga yau.

------------------------🔥

Sosai ya bata tausayi ganin yadda yake ta kwarara amai tamkar zai amayar da dik wasu ƴaƴan hanjinsa. Tsorata ta yi na ganin halin da yake a ciki, bata taɓa ganin mutum yana amai irin haka ba, sai ta zaci zai amayar da kayan cikinsa ne dikka. Da gudu ta fito ta nufi room na momma, jikinta har kerma yake yi saboda tsoron kada ya mutu.

Zaune ta isko momma da Mahnoor, Mahnoor ta kwanto da kanta saman laps É—ib momma tana aikin matsa yatsun hannun momma É—in, ita kuma momma tana ta shafa kanta suna hira tamkar uwa da Æ´a.

Ko sallama Sweetie bata yi masu ba ta afko cikin ɗakin, hakan ya razana Mahnoor sosai, ita kuwa momma a dake take ta bita da kallo. A gabansu ta kariso tana faɗin momma ta zo Big Bro yana ta amai. Da sauri Mahnoor ta miƙe zaune, hakan ya baiwa momma damar miƙewa ita ma, ba tare da ta yi masu magana ba ta nufi waje da sauri.
Chapter 73 · 0% Book details