← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 130

Sashe 113

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru King ya yi yana kallon É—an nasa, su momma dik suna zaune a saman bed É—in suna kallon Big Bro dake zaune saman side sofa. Shi kansa king ya sani abin da Big Bro ya faÉ—a gaskiya ce, amma kun san zuciya bata da kashi ne!.
A daidai wannan lokacin Ramish ya shigo É—akin bakinsa a É—auke da sallama. Ganin momma, mummyn Chuchu, mama, King and Big Bro É—in ne yasa Ramish ya yunkura zai juya ya fita kenan Big Bro ya ce mashi ya zo nan.

A natse ya karisa ciki yana tunani me ya tarasu haka? Dan shi baya gidan tin da sassafe, so bai san me ake ciki ba, ya lura yanzu gidansu ya zama sai rikici ake yi kullum.

Cikin kaifaffar murya Big Bro ya ce. "Umarni nike baka Ramish, ka je ka É—auko matarka, domin faÉ—uwa ce a garemu ace wai dan ka auri Æ´ar makiya har su yi galaba a kanka wajen kwaceta dan su kuntatawa kingdom É—in nan, dan haka ka je har cikin gidansu ka É—aukota!!".

ÆŠan zaro idanu king ya yi, sai kuma ya fahimci Big Bro yana da gaskiya, ai yakamata ne su gwada masu fa sun fi karfinsu, kuma zasu iya yin komai da suka ga dama, zuwa har cikin gidansu da Ramish zai yi ya É—auki Leesharh ba karamar razanasu zai yi ba, zai sanya su shiga taitayinsu, lallai ba shakka wanna shawara ta yi, amma king ya yi mamakin yadda aka yi Big Bro ya fisa sanin ilimin mulki da dik wata tuggu sosai. Ni ko na ce ai dama baka haÉ—a ba King, Big Bro da tsawon rayuwarsa babu abin da yake yi face karance-karance da nazarin mutane, shi da mugunta ma karantarta ya yi ya koya, baya fita ko parlo, kai kuma King daga nan har birnin Sing zuwa kake yi, yaushe ma ka samu lokacin kanka bare wani kasance-karance da nazarin mutane, ai bama zaka haÉ—a kanka da shi ba, dik wani tsiya sanka-sanka Big Bro ya sani da kuke ganin san nan, wlh sai dai in bai yi niyyar yin abi ba!.

"Na yarda zan so Æ´aÆ´an Omranish, zan yi dik abin da kake so, amma nima ina da abin da nike so ka yi mun". King ya faÉ—a yana kallon É—an nasa.

Shi kuma Ramish wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da zama a saman É—ayan bed side sofa yana fuskantar su king, Amma ya gagara yin magana...... Shiru room É—in ya yi suna kallon King suna jiran jin me yake so. Gyaran murya ya É—an yi kafin ya ce.
"Ina son ka rinƙa girmama Abbas da Jahiz tamkar yadda zaka girmamani, they're my brothers, and ba zan so ka rinƙa yi masu magana haka anyhow ba, ɗazu ban ji daɗi ba, it hot me more, kawai na danne ne".

Shiru Big Bro bai amsa mashi ba for almost 2 mins sannan ya ce. "Dik wanda zai mun magana without respect to ba É—auka ba, ni sarki ne mai san mulkar duniya! Bana tolerating nonsense!!".

Kallon Momma King ya yi, ya ji sabon karatu wajen Big Bro, sarki mai son mulkar duniya kuma? Balain can, yau sun ji abin da ya sha gaban tinaninsu, ita kanta momma yanzu Big Bro ya fara kara ninka tsoronsa a ranta, kai lamarin ya sha gaban tinaninsu.

Momma ce ta daure da cewa. "Ba zasu rinƙa yi maka magana da tsawa ba, amma kai ma ka rinƙa ƙoƙarin tausar zuciyarka a kansu ka ji ko? Su ɗin iyayenka ne"...... A takaice ya ce. "Iyaye biyu nike da shi, ke and dad".

Alama king ya yi wa momma da hannu a kan ta yi shiru, dan sun lura a yanzu dai Big Bro ba zai taɓa fahimtarsu ba, shi girmamawa yake so, idan har za'a girmama shi to za'a zauna lafiya, akasin haka kuma zai iya hukunta kowa a duniyar nan banda mutum biyu, watau King and Momma, dan haka sai dai su rinƙa lallaɓasa har zuwa lokacin da ya daina zancen sarki mai mulkar duniyar nan, a lokacin zai rage izza da jiji da kansa, to a sannan za'a iya faɗa mashi suwaye Uncle Abbas kuma ya yarda.

Jin sun yi shiru ne yasa Ramish ya ce. "Big Bro, daddy, mummy and momma please ku tayani rokar mama da ta yi hakuri ta yarje mun in je in É—auko Aesh".

Kallon Mama dikka suka yi banda Big Bro da yake kallon Ramish É—in. "Sai ta ce ka je ka É—aukota? Matarka ce ko matarta? Ko ita ta aura maka ita?". Big Bro ne ya jefa mashi waÉ—an nan tambayoyi.

Cikin girmamawa Ramish ya ce. "Ko ɗaya, amma ta ce bata sonta ne, kuma ni ina son matata"......... Kai tsaye Big Bro ya ce. "To idan baka ɗaukota ba da ita take so ka rinƙa sex ne?".

Balain can ai King da kansa sai da ya tauna harshensa saboda nauyin maganar da Big Bro ya faÉ—a kuma ko a jikinsa, bai yi mashi ma kamar ya yi magana ba, to dama shi ina ruwansa? Ai maganarsa babu ruwana da a kan waye ake yi, shi fa baya King and Momma baya ganin kowa da wata girma!.

Momma Big Bro ya kara goge mata hadda yau, sai kuma ta ji zafin irin yanayin rayuwarsa, ta sake ALLAH ya isanta a kan wanda ya rabata da shi ya je ya kai shi wani waje, yanzu ta fara fahimtar babu addini a tattare da shi, domin kuwa in akwai addini ba shakka ko bai tashi da su ba abin zai yi sauki, amma sai abin suka haÉ—e mashi, ga rashin iyaye ga rahin addini, ai fin haka ma zai iya aikatawa.

Ramish da shi ma zancen tafi karfin kwakwalwarsa ne ya yi kasa da kai kawai, lokaci guda ya ji kunya ta rufesa, ya ji ba zai iya ɗagowa ya kalli su momma ba, Mama ma dai haddar dake kanta ya goge, addu'a take yi a kan ALLAH yasa kada Big Bro ya sake buɗar baki ya yi magana a room ɗin nan, dan maganarsa ɗaya tana razana ƙwaƙwalwa, tana sanyawa mutun ya fi tsawon shekaru yana tinanin maganganunsa.

King ne ya canza masu topic É—in hiran da cewa. "Ina matar taka take?". Ya yi tambayar yana kallon Big Bro........ Shiru ya É—an yi mashi for some minutes kafin ya ce. "Tana É—aki". Ya bashi amsa a sanyaye....... "Okey Rahilarh ki gabatar mun da su in anjuma da yamma, zan gansu, kuma na aminta su kasance matan Æ´aÆ´ana". Cewar King.

Ba karamin daɗi momma ta ji ba da jin kalaman King, cike da murna ta fara zuba mashi ruwan godiya. Miƙewa sumui sumui Mama ta yi ta nufi waje, dan bata son a sake sako zancenta a cikin Room ɗin, kada Big Bro ya sake caka mata magana, yanzu ma ya goge mata hadda. King da momma sun lura da fitarta, amma basu yi magana ba, dan suma ba zasu so Big Bro ya sake yin magana a kanta ba, saboda abin ba zai yi kyau ba ne.

"Daddy take good care of yourself". Big Bro ya faɗa tare da miƙewa ya nufi wajen. Daga King har momma an rasa mai dakatar da shi, kuma suna son tambayarsa sunansa, amma sun gagara.

Bedroom ɗinsa ya koma dan su yi breakfast. Slowly ya turo kofar ya shigo. Tana zaune a saman sofarta tana ta faman sauke ajiyar zuciya. Tana jin an turo kofa ta yi gaggawar kai kallonta wajen, ganin shi ne yasa ta miƙe tsaye da sauri, muryarta a ɗan dishashe ta ce. "King of heart ina Pretty ɗin? Ba'a sake yi mata komai ba ko?".

Idanunsa a kan dogon hancinta da ya yi jajir saboda kuka, purple lips ɗinta har ɓari yake yi, dik tana firgice. Gentle ya tako izuwa in da take a tsaye. "Ya isa haka Maysh, babu abin da zai faru kuma, zo ki yi breakfast".

Ya faÉ—a yana kai yatsansa É—aya saman lips É—inta dake ta faman kerma...... "Ni na koshi". Da kyar ta iya faÉ—a. Ya fahimci tsoron abincin take ji saboda abin da ya faru, sai ya ce mata. "Babu abin da zai faru, ko poison É—in da kansa kika ci kina tare dani ai".

Dik da ta yarda da maganarsa, amma zuciyarta na rawa a kan ta zo ta ci abincin nan gaskiya. Hannunta ya ja suka nufi wajen abinci. Dan dole ba dan ta so ba yau ta ci wanna abinci, zuciyarta na ta É—ari-É—ari har suka kammala. Sai da ta ga sun ci da kamar 30 mins babu abin da ya faru sannan ne hankalinta ya kwanta, ta samu natsuwa, ta kuma koma sama sofa ta kwanta, shi kuma Big Bro ya fita zuwa wajen aikin da ake ta faman yin.

------------------------------🔥

A yayin da dikka wannan abin yake faruwa Omaid ne tsaye a tsakiyar bedroom É—insu yana kai komo tamkar wanda ya yi wa yar sarkin aljanu cikin shege ake nemansa, dik da sanyin Ac dake cikin room É—in bai hana zufa keto mashi ta ko'ina a sassan jikinsa ba.

Sareena and Obaid suna zaune a saman bed, dik sun yi jugun-jugun, tamkar masu zaman makokin iyayensu.

Hannu Omaid dunkule yana dukan É—ayar tafin hannunsa da shi, cikin sauri da kakkausan murya ya juyo tare da kallon su Sareena ya ce. "How comes wani ya canza mana plan? Kenan akwai mai bibiyarmu ne? Ta ya za'ayi mu shirya abu sai kuma a canza plan É—in, waye ya canza poison É—in nan zuwa wanda zai iya kashe Yah Omerish? Poison da muka shirya plan wanda zai wahalar da shi ne, to waye yake neman rayuwarsa da zai yi amfani da plan É—inmu?".

Obaid ne ya ce. "Wanna abin ya É—aure mun kai, ta yaya wani ya bibiyi plan É—inmu ya kuma yi amfani da hakan ya shigar da tsarinsa na son kashe Yah Omerish cikin namu? Waye kenan? Kuma ta yaya ya canza gubar?".
Chapter 113 · 0% Book details