← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 130

Sashe 121

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan fa ya miƙe suka fara karawa su biyu shi kaɗai, Obaid ya jajirce ba zai bari a halaka mashi ɗan uwa ba, shi kuma guyson jibgarsu yake yi da gasken-gaske kuwa. Alama ta nuna ba karfinsu bane a jikinsu yaran nan, sannan wani abin mamakin kuma shi ne, sun ki yarda su illata lafiyar guyson dik ya kasance kamar basa cikin hayyacinsu, idan suka ce zasu dakesa wlh guyson zai iya mutuwa a hannunsu, dan basu bane, amma sai dai su shakesa ko da wasa basu yi yunkurin dukansa ba, dik wanda yake parlon nan ya lura da hakan, hakan yasa ba ƙaramin mamaki abin ya basu ba, meyasa suke shakkar taɓa jikin Omar dik da suna da zararrar iya mayarwa Omerish martani?.

Ganin abin is getting out of hand ne yasa Jaish ya miƙe dan ya rabasu. Hannu Big Bro ya ɗaga mashi alamar ya dakata, sai a lokacin ya kashe wutar creen na wayarsa ya ɗago da kallonsa a kan Jaish. Da hannu ya yi mashi pointining wajen zama a kan ya koma ya zauna. Ba musu ya koma ya zauna yana kallon yayan nasu. Gabaɗaya kallon jama'ar parlon ya koma suna satar kallon Big Bro, shi kuma hankalinsa yana a kan momma dake ta faman ƙoƙarin dannar zuciyarta tana kama sunan ALLAH a bakinta, dan gab zuciyarta take da bugawa, ta ga balain da bata taɓa gani ba, wai ƴaƴanta da suka samu tarbiya sama da kowa a gidan ne yau suke wannan abin? Ya za'ayi ba zata shiga damuwa ba? Dama ga matsalar da Sweetie ta faɗa mata.

Shi kuma King ya dakatar da Dr Raj daga rabon faÉ—ar ne ba dan komai ba sai idan ya shiga twins zasu yi mashi illah, dan a yanayin faÉ—ar Æ´aÆ´an momma ne ba zasu daka ba, dik wanda ya shiga tsakaninsu to fa komai ka iya faruwa ne.

Shi kuma Big Bro abin da ya sanya ya dakatar da Jaish shi ne dik abin da yake faruwa so ake a haÉ—a kan Æ´aÆ´an momma a gwara, su yi ta faÉ—a da junansu tamkar zakuna a dawa, har su illata kansu, kunga idan Jaish ya shiga an ci riba kenan, shiyasa ya dakatar da kowa daga rabon faÉ—ar.

Smart kuma tarasu yake yi, dan yana jin dik abin da yake faruwa, dannar zuciyarsa yake yi, saboda yana son tashi ya rabasu, amma baya son tashi a haka, zuciya zata iya É—ibarsa ya kashe É—aya daga cikinsu, shiyasa ya yi shiru yana son dannar kansa, ya kifa kai da gwiwa.

Jaish dai ya gagara hakura har sai da ya ce. "Omaid anya akwai hankali a cikin kanka kuwa? Ka san me kake yi kuwa?". Yana maganar ne cikin rauni, da alama tashin hankali ta kai makura a ransa, basu taɓa ganin irin wannan musifa ba. (Kun san dik faɗar da Big Bro and Smart suka yi kwanaki ba'a gabansu bane, a ɗakin Smart ne, na biyu kuma a Black World, so basu taɓa ganin irin haka ba.)

Cikin tsawa Omaid ya ce. "Sai dai kai ne baka da hankali ba ni ba!!.......". Ya mayarwa Jaish amsa a tsawace cikin fushi.

Ai yadda kuka san walkiya haka Smart ya miƙe, kafin ma Big Bro ya yunkura dan dakatar da shi har ya isa gabansu, a fusace ya damko wuyar Omaid, da karfi ya jijjiga shi ya yi jifa da shi gefe, zuciyarsa na tafarfasa ya nufesa, kafa yasa ya fara tattashi da shi irin dukan fitar hayyacin nan.

Da gudu Obaid ya saki guyson ya yi kan Smart yana faɗin ya kyale mashi ɗan uwansa kada su kashe shi. Hawayen da momma ke ƙoƙarin ɓoyewa ne suka fara zubo mata a kan fuska, sun fi karfinta ne.

Ai Obaid na zuwa Smart ya kwashe kafafunsa ya zube kasa shi ma, haɗesu ya yi ya hau ball da su babu tausayi babu tausayawa. Obaid na ihu shi kuma Omaid kokari ya yi ya miƙe, a maimakon ya badu hakuri sai ya ce. "Iya abin da zaku iya kenan duka! Baku isa ku gyara ɓarnar da muka yi ba ai, duka ce kuma ku yi iya yinku ku gaji ku barmu!".

Ai wani irin zaro ido da jama'ar parlon nan suka yi kwace kwayar idanunsu zai faÉ—i kasa, innalillahi wa innailarhi rajiun, wannan musifa dame ta yi kama?.

Miƙewa shi ma Obaid ya yi, da kyar ya iya cewa. "Azzalumai kawai, ALLAH sai ya yi mana sakayya tsakaninmu da ku!".

Ai dakatawa cak Smart ya yi da dukan nasu da yake yi, ji ya yi tamkar an kwaÉ—a mashi guduma a tsakar ka, sai ya rasa ma me zai yi.

Jifar Sweetie da wayarsa Big Bro ya yi tare da miƙewa ya nufo in da suke tsaye. A gefen Smart ya tsaya yana kallon twins, dik tsaurin idonsu da rashin kunyarsu sai ga shi sun yi kasa da kai, sun gagara kallon cikin idonsa, amma harshensu bai yi sanyi ba, domin kuwa a daidai wannan lokacin ma Omaid ya sake cewa. "Dik tsananinku da zaluncinku dai bai wuce ace ku kashemu ba ko? To kafin mu dayawa sun mutu! Bayan mu ma dayawa zasu mutu, amma ku ku zauna ku naɗe duniyar kada ku mutu!". With his full confidence yake magana.

Hannu Big Bro ya É—aura a saman shoulder É—in Smart tamkar zai rarrashesa, sai kuma ja janyesa baya da karfin gaske har sai da Smart ya yi baya baya ya faÉ—a saman sofa. Kafin su Omaid su É—ago kai dan ganin me yake faruwa sai ji suka yi ya damko gashin kansu ta bayan wuya haka.

Kafin su farga ya jawosu gabansa, yadda kuka san karfe da karfe haka Big Bro ya haÉ—e kan yaran nan da hannu É—ai É—ai ya dinga buga goshinsu da na juna.

Ya ilahi ya lillahi, hankalin kowa ne ya yi mummunar tashin a parlon, harta king sai da ya miƙe daga saman sofarsa, ya san Big Bro zai ɗauki mataki, amma bai yi zaton irin wanna duka ba, wannan ai kashesu kawai zai yi, dama ga jibga da suka ci wanda tin da suka zo duniya ko rabina basu taɓa ci ba.

Dafe saitin zuciyarta momma ta yi da karfin gaske, kafin a farga ta sulale saman sofar ta kwanta, take nunfashinta ya ɗauke ɗiff, ya ilahil alamina, baiwar ALLAH bata taɓa shiga musifa irin na yau ba, yadda Big Bro ya gwara kan yaran nan sai ta ji tamkar zuciyarta ya hau caccakawa mashi da karfi-karfi, matsayinta na uwa ba zata iya jura ba, ta zo har wuya da ba zata iya cigaba da jurewa ba.

Babu wanda ya lura da momma ta faɗi, saboda dik kallonsu a kan Big Bro, sun ga sabuwar horon azabar da basu taɓa gani ba!.

Da karfin gaske Big Bro ya cigaba da kwara kansu har sai da goshinsu dikkansu biyu ya fashe, jini ya wanke masu fuska gabaÉ—aya, amma dik da haka bai dakata ba, ihu suke yi tsakaninsu da ALLAH, amma bai kyalesu ba.

Ƙasa jurewa Smart da Jaish suka yi, da sauri kusan a tare suka nufesa dan dakatar da shi. Da yake guyson yana ta gaban Big Bro ɗin yana kallon fuskarsa, su kuma bayansa suke kallo, sai guyson ya ce. "Yah Omerish kada ku matso".

Ya faÉ—a yana É—an ja da baya shi ma, saboda ya ga idanun Big Bro sun canza kala wanda suka yi mugun É—aga mashi hankali. Da yake Smart ya san matsalar sai ya dakata daga wajen tare da rike hannun Jaish.

Ai Sareena fitsari ta saki a wado a wajen ganin abin da Big Bro ya yi wa su Omaid, Chuchu ta kankame Yah Jawad gam, saboda ta tsorata over. Aneesa ma dai yau ta yi mugun tsorata, ta kankame Mama gam, Mahreen ta kankame Mahnoor gam, Sweetie ta rike Ronnie, a kunne ta raÉ—a mashi da su je dakatar da Big Bro.

Ƙasa-kasa ya ce mata. "Ba Big Bro bane". Zazzaro mashi idanu ta yi kafin ta ce. "Bashi bane kuma?"....... Kai Ronnie ya jinjina kafin ya ce. "Yanzu ace maki Big Bro zai iya dukana kamar yadda yake dukansu zaki yarda?". Kai ta girgiza alamar a'a. Jinjina kai ya yi. "To kamar yadda in yana cikin hayyacinsa ba zai iya yi mun wannan duka ba haka su ma ba zai dakesu haka ba, yadda yake sona haka yake sonsu, ba shi bane, kuma dik yadda aka yi akwai dalilin da yasa yake yi masu wannan jibga".

Shiru Sweetie ta yi kanta ya shiga duhu ne sosai, bata gane komai a zancen Ronnie ba. Sai kawai ta yi shiru tare da kwantar da kanta a saman kirjinsa ta datse idanu dan bata son kallon abin da yake faruwa.

Sai da gaban goshinsu Omaid ya fara fitar da wani irin jini bakinkirin tamkar gawayi, sannan Big Bro ya sanya kafarsa ya daki kafarsu ta baya wajen gwiwowinsu, take suka zube gwiwowinsu a kasa, yana rike da gashin kan nasu bai saki ba, ya sunkuyar da kansu kasa wanna bakin jinin ya ringa kwaranya yana tsiyaya.

Tsabar tsoratar da kowa ya yi har numfashi a hankali-hankali jamar parlon nan suke yi.
Sai da wanna jini kaf ya gaba tsiyaya, sannan ne ya sakesu, yana sakesu suka sulale kasa basa numfashi. A tinanin jama'ar parlon sumar da su ya yi saboda wanna buga masu kai da ya rinƙa yi, sai dai ba haka bane, suma suka yi saboda sun samu lafiya, bakin jini na muguntar da aka saka masu ya gama barin jikinsu, yanzu sun koma ainahin yaran momma ɗinsu.

Da gudu guyson ya kariso kansu, a gabansu ya taugunna yana tattaɓa kumatunsu, sun yi mugun bashi tausayi dik da sun ɓata mashi rai, jini ba wasa ba. Da alama guyson ya dawo Omar ɗinsa, domin kuwa ace irin wannan abu ya faru bai yi wa su Omaid kuka ba ai daga nan za ku san cewa Omar ne wannan.

Slowly King ya koma saman sofarsa ya zauna yana cigaba da kallonsu, kowa komawa ya yi suka zazzauna cike da tsoro.

Tamkar wani zaki haka Big Bro ya juya ya dinfari jikin tsakiyar parlon. Su mama nan kirjinsu ya fara bugawa da karfi-karfi haka. Kai tsaye mama ya nufa, faÉ—uwar gaba tamkar zai kashe mama, amma bata motsa ba.
Chapter 121 · 0% Book details