Sashe 122
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana zuwa ya kai hannu, da karfi ya damko Aneesa dake laɓe a bayan mama ɗin. Ihu ta fara yi tana faɗin Mama ta taimaketa, ita tsoron Big Bro take yi. Sai dai kuma ina, babu wanda ya iya dakatar da shi. In da su Omaid suke ya kawo Aneesa, sannan ya miƙa hannu ya damki gashin kan Sareena, ita ma haɗata da Aneesa ya yi ya hau buga kansu yadda ya yi wa Omaid da Obaid.
Ai wani irin razana guyson ya yi ya miƙe tsaye yana kallon yayan nasa. A tsora ce mama ta kalli king da yake zaune hankalinsa a ɗan kwance ta ce. "Ka dakatar da ɗanka kada ya kashe mun yarinya, ban shiga harkarsa ba kada ya shiga tawa".
Juyo da kallonsu a kanta su mummyn Chuchu suka yi, har lokacin basu lura momma ta suma ba, saboda tashin hankalin da suke ciki. Hannu King ya ɗaga mata alamar ta yi mashi shiru, zuciyarta ne ya kara harzuƙa, abinku da uwa da ƴa, da sauri ta miƙe da nufin ta je ta kwaci Aneesa dake ta faman ihu tamkar ranta zai fita, a cewar mama ɗin sai da ya kasheta ita, amma sai ta karɓi ƴarta.
Zata wuce Smart ya daƙa mata tsawa a kan ta koma ta zauna kafin ya yi ball da ita, saboda tsoro da shakkarsa yasa ta koma ta zauna tana ruwan hawaye.
Aneesa da Sareena suma sai da wannan bakin jini ya zuba daga kansu sannan ya sakesu, suka sulale kasa basa numfashi suma. Tsuru-tsuru jami'ar parlo suka yi da ido suna jiran su ga saura su waye kuma next za'a capko.
Sai dai yanzu lamarin ya sha banban, dan kuwa unexpected suka ga Big Bro a gaban guyson dake tsaye yana kallon abin dake faruwa cike da mamaki. Wani irin razana guyson ya yi har ya ja baya, amma ganin Big Bro ne yasa ya sauke ajiyar zuciya dan shi yasan yayan nasa ba zai taɓa cutar da shi ba tin da bai aikata wani laifi ba.
Ware dogayen yatsunsa Big Bro ya yi tamkar za su gaisa da guyson haka, a tsakiyar cikin guyson ɗin ya caka mashi waɗan nan yatsun nasa da karfi, take guyson ya durƙushe kasa a wajen ya fara kwaranyo wani bakin amai, bakinkirin sosai, tamkar laida, ga wani gashi-gashi a cikin aman nasa.
Hannu Big Bro ya sake dunkulewa ya daki guyson a bayan wuya, take ya sake yin kasa da kai yana cigaba da kwarara aman nan.
A daidai wannan lokacin daga bayansu suka ji wani irin kakkausar murya tamkar muryar kato ance. "Kai karamar halitta! Ka tabka babban kuskure na dukan É—iyarmu da ka yi".
Ai a miliyan gabaɗaya parlo suka kai kallonsu kan mammie da ta miƙe tsaye tana zazzaro ido, idanunta sun zama dark purple gwanin ban tsoro, ga wasu hakwara biyu tamkar na damusa da suka bayyana a bakinta ta sama, ta zama suffar horuwa kawai a taƙaici.
Slowly Big Bro ya juyo da kallonsa a kanta, É—an karkata kansa ya yi yana kallonta. Take ya É—an mummuÉ—a wuyarsa yadda aljanu suke yi idan zasu yi rashin mutumci kenan, haka shi ma ya yi, yau faÉ—ar irin na second mother É—insa Elevender za'ayi kenan, matar nan ta koyawa Big Bro aljananci ta mutu ta barmu da aiki.
Haba dik waÉ—an da suke kusa da Mammie ne suka watse da gudu daga kusa da ita, sun tsorata sosai, su Smart ai a miliyan suka juyo da kallonsu a kanta. Uncle Abbas ma dai matsawa ya yi daga kusa da Mammie.
Family sun shiga gagarumin ruÉ—ani na wannan abin da ya faru, King kansa ya shiga ruÉ—ani, abin ya kulle masu kai sosai. Mammie kuma dukan Sareen da Big Bro yake yi ne yasa ta motsa tsafin nata, dan ta hukuntasa, a haka ba tsafi tana tsoron tinkararsa.
A hankali idanun guyson suka fara rufewa a lokacin da ya gama kwaranyo wanna aman, sulalewa kasa ya yi, shi ma ya sume a wajen. Da gudu Jaish ya yi kansa, Big Bro bai dakatar da shi ba sai ya bashi hanya ma. Da sauri shi ma Smart ya yi kan guyson É—in dan duba lafiyarsa.
Ita kuwa Mammie tamkar wata zakanya haka ta nufo Big Bro da nufin su kara, yana tsaye yana mamakin ne ma yadda aka yi ita mace take magic, dan shi fa dik balainsa yasan ba zai taɓa bawa mace magic ba, shiyasa kuka ji ranar ya zagi babansu Sweetie, dan yasan me illar hakan!.
Aka ce rashin sani ya fi dare duhu, Mammie na zuwa tasa hannu wai zata shaki wuyarsa. Ihu Sweetie ta zunduma tare da datse idanunta gam ta kara kankame Ronnie, ta ji tsoron za'a shake mata king of heart É—inta.
Mammie na kai hannunta jikin fatan wuyansa hannun nata ya kone tamkar wacce aka zubawa acid, lamarin da ya kara tada hankalin family, king ya yi gigicewar da bai taɓa yi ba, yadda kuka san an zubawa Mammie acid haka hannayenta suka zama, har sama wajen shoulders ɗinta, harta naman jikinta sai da ya dahu, ya yi jajir da shi tamkar an ɗaye fatar waje, ga wani irin hayaki mai kama da tiriri da yake tashi a jikin hannun nata.
Wani irin azababben ihu ta kurma wanda ya doÉ—e kunnuwan gabaÉ—aya jama'ar parlon, a nan take Mahnoor ta sume a wajen saboda razana, Chuchu ma dai ta fita a hayyacinta, sai wani irin azababben kerma da jikinta yake yi, ta kankame Jawad gam ta cusa kanta cikin kirjinsa, idanunta a datse gam bata ma ganin me yake faruwa.
Uncle Abbas da Uncle Jahiz dik kallonsu a kan King alamar karin bayani suke nema, basu san shi kansa King ɗin yanzu karin bayani yake nema ba, dan bai taɓa tinanin lamarin ɗan nasa ya yi tsamari haka ba. Bai san ɗansa magajin kujerun mulki har guda biyar bane, ciki har da sarautar aljanu, yo me ba zai gani ba kuma? Ai su da Big Bro a Kingdom ɗin nan sai ta ALLAH kuma, masu karamar ƙwaƙwalwa hauka zasu yi wlh.
Baya-baya Mammie ta fara ja tana ihun azaba. Takowa Big Bro ya fara yi yana nufar in da take, baya ta cigaba da yi har suka kurewa wall dake wajen, juye-juye ta fara yi tana neman hanyar sake gudawa, sai dai ina babu. Hannu Big Bro yasa ya damko gashin kanta dake cikin veil da ta yi rolling kanta, da karfi ya jijjigata kafin ya jefota tsakiyar parlon. Take su mama suka sake ja baya daga kusa da ita.
A gabanta ya zo ya tsugunna yana kallon face ɗinta, ta yi ƙasa da kai sai wani irin wahalallen kukan azaba take saki.
"Who are you?". Shi ne abin da Big Bro ya faÉ—a cikin natsuwa da sanyin murya wanda tin shigowarsa parlon bai yi magana ba.
Big Bro ba'a yi mashi musu a magana ko a faÉ—a mashi karya idan abubuwan nasa sun motsa, ko kaki ko kaso in ya tambayeka sai ka bashi amsa, saboda daidai yake da kai, dik wani hau dake kanka nashi ya dame naka ya shanye, shi kansa bai san adadin abubuwan dake kansa ba, dan haka dole Mammie ta buÉ—i baki ta hau jawabin wacece ita da dik abin da ta aikata, sai a wanna lokaci suka iya tina Fanan da ta buÉ—e baki ta faÉ—a masu cewa ta baiwa Zarina ita.
Ta fara faÉ—in dik irin tuggun da ta shiryawa Rizwan and Jawad dan kashesu, ta faÉ—i cewa ai mamarsu ma ba mutuwa ta yi ba, Zarina ta baiwa ita suka yi bakin tsafi, da ta baiwa Zarina maman su Jawad shi ne Zarina ta bata tsafi, da tsafin ta yi amfa wajen mallakar Uncle Abbas ta shigo gidan, hasali ita ta zo gidan ne bisa umarnin Zarina na cewa zata taimaka mata ta mallaki masarautar, dik wani tuggu da ta haÉ—a sai da ta warware masu tsaf.
Daga karshe ta ce ita ta kwantar da Akka jinya, ita ce sanadi saboda Akka ta matsa ta tsananta tsaro a kan Spender, ta hanasu su mallake shi, shi ne nan suka haÉ—ata da bakaken ruhanai suka kayar da ita jinya, shiyasa yanzu sai an É—aga sai an kwantar.
Wannan magana nata ya yi mugun ɗaga hankalin waɗan nan ahalali, take suka fara yi mata tofin alatsine. Jawad kam dai dafe kansa ya yi yana jin zuciyarsa tana yi mashi zogi, ashe bada mamarsu wannan azzaluma ta yi aka bata tsafi?. Ya ilahi ya lillahi. Rizwan kasa ya yi da kai yana wani irin huci mai ban tausayi da tsayawa a rai, dan in baku kanta ba shi ai ɗan ɗakin Mammie ɗin ne, kun manta tana nuna tana son shi sosai? Kuma shi ya riketa matsayin uwa da gaske, so hakan ya taɓa mashi zuciya, bai taɓa danasani kan wani abu ba sai a kan wannan mata, ya yi danasanin ɗaukarta matsayin uwa.
Bayan ta kammala bada jawabinta kaff, shiru Big Bro ya É—an yi for some second kafin ya É—an juya eyesball É—insa. Yawun bakinsa ya tofa mata a fuska, take fuskarta ta fara konewa tamkar ya zuba mata acid. Ihun azaba ta shiga yi tamkar makoshinta zai fashe.
Cikin azaba da fitar hayyaci tasa hannunta da ya ƙone over a kan fuskar tata da nufin ta ɗan kare ko zafin zai ragun mata, sai dai tana sanya hannunta wani irin fata ta fara kwayowa wanda ya gama dahuwa tamkar an ɗaura a wuta. Nan ma wani irin zababben ihu ta kara saki mai doɗe kunne wanda ya sanya numfashin Chuchu ɗaukewa ɗiff ta sumewa Jawad a jiki.
Yanke jiki uncle Abbas ya yi ya faɗi a wajen sumamme, da gudu su Dr Raj suka yi kansa. Miƙewa Rizwan ya yi da sauri ya fice daga parlon dan zuciyarsa gab yake da yin bindiga. Jawad dai ya gagara motsawa, tamkar an sassaƙasa a wajen.