← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 130

Sashe 124

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
Sumbata ya mannawa Smart a goshi, can kasan makoshinsa ya ce. "Ka yi babban laifi yau, kuma ba zamu yafe ba, amma ina fatan ka sama mana babys a wannan first karon kafin Maysh ta bamu nata"....... Kun san mutumin da son yara.

Da sauri Smart ya É—ago da kallonsa a kansa kafin ya ce. "Waye ya faÉ—a maka abin da na yi? Ni fa ta bakin momma kana bani tsoro guy É—in nan".......... Shafa fuskar Smart ya yi da tafin hannunsa, a natse ya ce. "I'm the successors to BLUE KINGDOM, then King of ICE KINGDOM, so ka daina mamakina". Yana magana yana shafa gashin kan Smart cike da tsantsar fresh kauna.

ÆŠan zazzare mashi idanu Smart ya yi. "Apart from Black World palace akwai Blue Kingdom and Ice Kingdom ne?".

Sai da ya ja dogon hancin Smart ɗin kafin ya jinjina mashi kai alamar e. "To amma how comes? And a ina su kuma suke? Ni fa ka sake kulle mun kai, ka rikitani". Ya faɗa tare da miƙewa zaune ya bar jikin Big Bro ɗin. Kai Big Bro ya ɗan ɗaga sama tamkar mai tinanin wani abin, ba komai yake tinani ba face yana kallon hanyar Blue Kingdom, dan ita dai a sama take ba'a duniyar mutane ba, kada ku manta sune masarautarsu second mom ɗinsa watau Eleveder. Hmmm dik yaran momma kusan suna da second mom, Smart ma yana da ita matar daddynsa na Paris, Omaid and Obaid suna da ita suma, kuma ita ce nan take sanya masu kiriniya. Guyson Auta dik suna da ita.

"Ba zaka gane ba ko na faÉ—a maka, so bar zancen". Big Bro ne ya bashi amsa da haka. Shiru Smart ya yi yana mamakin É—an uwan nasa. Baki a É—auke da sallama Sweetie ta shigo parlon tana sanye da hijabin Auta a jikinta, daga bedroom É—insu ta fito, ta gama shiri cikin sleeping dress É—inta ne ta ce bari ta duba momma dan tasan wani matsaya momma ta bata a yanzu, me zata yi.

Ganin su a zaune a parlon ne yasa ta kariso wajen, a saman sofa ta zauna tana faÉ—in. "Yah Omerish barka da dare"....... Kallo É—aya yai mata ya É—auke kai yana amsawa da yauwa. A maimakon ta É—agawa Big Bro ma gaisuwa sai ta ce. "Yah Omerish ina Pretty? Tin É—azun ban ganta ba, na yi knocking É—akinku babu kowa dan ba'a buÉ—e mun ba"....... Tin da ta fara magana kirjin Smart ya fara bugawa da karfi-karfi har ta kai karshe.

Ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya iya ce mata. "Tana barci ne, bata jin daɗi"............ Zazzaro mashi idanu tai. "Meyake damunta?". Tamkar zata yi kuka tai tambayar. "Zazzaɓi ne kawai, kada ki damu, ta ji sauki ma har ta samu barci".

Ya faɗa yana satar kallon Big Bro da ya kafeta da ido tamkar zai cinyeta da kallo. Jinkina kai tai. "ALLAH ya bata lafiya". Kanta a ƙasa ta faɗa, amma tana satar kallon king of heart ɗin nata. Da Amin Smart ya amsa.

Shiru parlon ya yi Smart yana jiran ya ji ta É—agawa Big Bro gaisuwa, amma sai ya ga akasin haka, gagara hakura yai har sai da ya ce. "Sister meyake faruwa ne tsakaninki da É—an uwana?"..... Da sauri ta ware idanunta a kansa alamar bata gane kan tambayar ba........ Ya gane nufinta dan haka sai ya ce. "Naga baki yi mashi magana ba tin da kika shigo".

Wani musulmin ajiyar zuciya ta sauke kafin ta saci kallonsa, a sanyayye ta ce. "Babu komai Yah Omerish"....... "Ban yarda ba, ai baki taɓa samunmu a waje ki gaidani baki kula shi ba, menene yake going?"........ Ɗan turo baki tai. "Kai Yah Omerish, ni fa babu komai, kawai dai na daina yi mashi irin wannan gaisuwa da nike yi wa kowa ne, nasa special ne, kuma ina jin kunyarka ne yasa ban yi mashi ba".

Ai a fili Big Bro ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, burin zuciyarsa kawai ya ji wani irin gaisuwa ta tanada mashi yanzu wanda ba irin na kowa ba. Shi kansa Smart ajiyar zuciyar ya sauke, da ya ji tsoron ace wani abin ne ya shiga tsakaninsu, to tin da ba komai ai shikenan.

"Yah Omerish Ina momma?".... "Momma tana zuwa ki jirata a nan". Ya bata amsa yana gyarawa ya kwanta, ya tada kai da laps na Big Bro. Kurawa juna ido suka yi ita da Big Bro, slowly ya motsa É—an bakinsa wajen cewa. "Wanna abin da kika sanya yai maki kyau sosai (Hijab)".

Murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Nagode"........ "I missed more maysh". Ya faɗa ta hanyar motsa lips ɗinsa kawai ba tare da wani sauti ya fita ba bare Smart ya jisa....... Ɗan miƙewa ta yi ta miƙo mashi wayansa dake hannunta wanda ya jefeta da shi ɗazun da zai fara dukan su Omaid.

Hannu ya miƙa ya karɓi wayar tare da ɗan shafa hannunta yana ɗan lumshe idanu. Komawa ta yi ta zauna tana kallonsa. Dik abin da suke yi Smart yana kallonsu, sai dai ya fi mayar da hankalinsa kan tinanin ya yar tsanarsa take a yanzu? Wani irin rauni ya ji mata? Ya damu sosai.

Vibrate wayarta ta É—an yi alamar shigowar sako, sai da ta saci kallonsa kafin ta kunna wutar screen light É—in, dan tasan shi kaÉ—ai zai turo mata sako. Tana buÉ—ewa sai ga cool smiling ya bayyana a kan face É—inta sosai. "Wanna kaya da kike sakawa suna da kyau, amma in zaki fita ne kawai suke maki kyau É—in, yanzu sun takura mun ki ciresu"...... Shi ne abin da ya rubuta mata a sakon.

Satar kallonsa ta sake yi kafin ta rubuta mashi amsa. "Dik yadda kake so in kasance fin haka zan yi a gidan aurenmu, a É—akinka na aurenmu na sunnah sai yadda kakeso za'ayi"................ Sosai ya ji daÉ—in kalamanta, sai ya rubuta mata reply da. "I wish mu yi aure da wuri".......... "Why?". Ta tura mashi.

"Because i love you, and bana son ratar da kike bani"......... Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke a fili kafin ta ce. "Ni kaina bani son yin nisa da kai, kawai juriya ce nike yi, I love you too King of my Heart".

Yana kokarin rubuta mata reply sai ji ya yi Smart ya kwace wayar yana faÉ—in. "Ya tabbata ku masoyan asali ne, watau gaka ga ta ma sai kun yi chat ko? To bari in ga me kuke cewa". Daidai lokacin ta turo mashi sakon. "Naga lips É—inka sun bushe, kana jin yunwa ko?".

Karance sakon Smart ya yi kafin ya ɗago ya kalli Big Bro, harara ya dalla mashi, da sauri Smart ya mai da kallonsa kan Sweetie, ƙasa da kai ta yi tana ƴan kame-kame. Kwace wayarsa Big Bro ya yi, a natse ya yi mata typing amsa da. "Yeah yunwa nike ji"........ Sake baki Smart ya yi yana kallonsu, dan sun goge mashi jadda ne.

"Eyya sorry bari yanzu zan kawo maka abinci ka ji?". Ta tura mashi tana ɗan shagwaɓe fuska. A natse ta yunkura zata miƙe kenan sakonsa ya sake shigo wayar, tsayawa tai dan ta duba.

"Babu wani abin da zai kawar da wannan yunwa da nike ji face ke, ke kaɗai ce abincin da zan iya...........in ƙoshi, babu buƙatar wani nau'in abinci".......... Ai sai da ta ji gabanta ya buga da karfi jin wanna kalaman nasa, da sauri ta ɗago da kallonta a kansa. Binta yake yi da wani irin mayen kallo, idanunsa suna ɗan lumshe tamkar mai jin barci, sun rage girma sun kuma ɗan sauya launi.

A daidai wannan lokaci momma ta shigo bakinta a ɗauke da sallama, da sauri Smart ya miƙe tsaye yana son tambayarta, amma baya san Sweetie ta ji. Kallon Sweetie ɗin momma ta yi kafin ta ce. "Omaish je ki kai maku abinci ɗaki ki zo zan yi magana dake". Sannan ta dawo da kallonta a kan Big Bro, kallo ɗaya tai mashi ta ɗan kawar da kanta izuwa kan Smart da ya tsareta da ido.

Miƙewa Sweetie ta yi ta nufi waje, abinci ta je ta ɗauka ta kai masu ɗaki, sai ta zauna a saman sofa, a ranta ta ce bari ta basu 30 ko 1h dan ta lura momma tana son yin magana da ƴaƴan nata ne. YARINYA MAI HANKALI.

A saman sofa dake fuskantarsu momma ta zauna. Slowly Smart ya koma ya zauna shi ma yana kallonta.

"Momma ya jikin Pretty É—in?". Smart ne ya tambaya cike da matsuwar son jin amsa....... Kai momma ta É—an girgiza kafin ta ce. "Ajiye wanna tambaya a gefe, dan in nace da sauki ma nai karya, amma musulmi ba zai gaji da cewa Alhamdulillah ba, dan godiya ga ALLAH wajibi ne a kan musulmi, yanzu ba wanna ba Unays magana nike son mu yi ka ji?".

Tin da ta fara magana gabaÉ—aya Smart ya rasa farincikinsa, jikinsa ya yi mugun sanyi, shiru ya É—an yi yana tinanin gaskiya sun Omaid sun cuceshi sosai wlh, addu'a ya fara yi mata ALLAH ya bata lafiya.

ÆŠago rinannun idanunsa Big Bro ya yi ya sauke kallonsa a kan momma alamar yana jinta kenan, bai dai yi magana ba.
Chapter 124 · 0% Book details