Sashe 2
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai Smart bai san yana kaunar King fiye da kansa ba sai yau, dan kuwa a miliyan ya miƙe tsaye tare da tattaro dikkan sauran karfinsa ya kaiwa Black Tiger naushi a bayan kunne wanda yasa dole ya saki King. Domin duka a bayan kunne komai taurinka sai ka jisa, yana kai mutum lahira nan take, ko kai da kanka ka sanya yatsa ka matsa bayan kunnanka sai ka ji azaban zafi bare a kai maka duka a wajen.
Ai wani irin ɗago kai da Black Tiger ya yi sai da yasa King Zuhair yin baya baya kamar zai faɗi, shi kansa Smart sai da ya razana, Mommah kam yau ta ga bala'in da bata taɓa zatan zata gani ba. Kamar walkiya haka Black Tiger ya sake dawowa gaban Smart ya kai hannu ya shaki wuyansa.
Tsabar tashin hankali Mommah bata san lokacin da ta isa gabansu ba, King na ƙoƙari dakatar da ita dan kada Black Tiger ya yi mata illah, amma ina, kafin King ya kai ga dakatar da ita har ta isa wajen. Cike da tsananin tashin hankali ta kai hannunta zata zare hannun Black Tiger dake wuyan Smart tana faɗa mashi ya bari kada ya kashe ɗan uwansa.
Ai a wani irin zafa ya juyo zai shaketa ita ma, sai dai kuma yana sauke idanunsa a kanta ya ji kamar wanda aka cakawa allura, kamar an watsa mashi ruwa mai sanyi a zuciyarsa, bai santa ba, bai taɓa ganinta ba sai yau, amma ya tsinci kansa da shakkar yi mata wani abin, zuba mata idanu ya yi yana kallonta har cikin ido ba tare da kyafawa ba, ita ma kallonsa take yi, sai dai tana cigaba da bubbuga hannunsa a kan dan ALLAH ya yi hakuri ya sake mata ɗanta kada ya kashesa .
Saboda sanyi irin ta uwa. Uwa ta fita daban, wlh bai san time da ya zare hannunsa daga wuyar Smart ba, sai gani suka yi Smart ya durkushe kasa yana faman tari. Da sauri King ya yi kansa yana yi mashi sannu.
Shi kuma Black Tiger cikin zafi ya nufi in da Pretty take a kwance ba tare da ya dai'na bin mommah da kallo ba, a cikin ransa yake jin kamar yana da alaƙa da ita, har can kasar zuciyarsa ya ji face ɗinta ya kwanta a ransa, ya ji dik duniya babu wani abin da yake da ƙayatarwa da daɗin kallo kamar face ɗinta, har ji ya yi kamar ya yi ta kallonta kada ya dakata.
Sai dai kuma dik da wannan, da suka ce mashi su ne iyayensa, kada ya je ko'ina, sai ya ce babu wannan magana, bai san su ba, shi ubansa ɗaya ya sani a duniya, kuma ya mutu, bayan shi bashi da wani Uba, dan haka kada su kuskura su kawo mashi wata maganar banza a nan, ransu ne zai ɓaci!.
Da suka ga ba zai taɓa yarda shi ɗansu ne a yanzu ba, sai suka ce su kyalesa zuwa wani ɗan lokaci, su bibiyu al'amarin a hankali domin su je mashi da hujojin da dole ya aminta ɗansu ne shi, saboda ba ta yadda za'ayi su kasance abu guda da Smart kuma ace shi ba ɗansu bane, da ma a iya kamar kawai ta tsaya to da sauki, amma ace fingerprint ɗin Smart ya buɗe nasa sannan ya ce shi ba ɗan su bane? Ko ciki ɗaya kuka fito da mutum fingerprint ɗinka ba zai taɓa buɗe nasa ba sai twins, twin's ɗin ma ba kowanne ba sai identical, sune harta DNA ɗinsu ma iri ɗaya ne, komai nasu ɗaya basu da banbanci, dan haka dole Black Tiger twin brother ɗin Smart Tiger ne, babu wata kwana-kwana.
Amma da yaki yarda sai Mommah ta ce su rabu da shi sai sun yi bincike sun tara hujojin da ba zai iya musawa ba.
Shi dai ko sake kallon in da suke bai yi ba yasa hannu ya saɓi Pretty a saman shoulder ɗinsa yana nufar hanyar fita da ita. Cikin zafa Smart ya tare gabansa tare da kai hannu ya rike Pretty. A tsorace Mommah ta ce. "Omerish lafiya? Ka kyalesa ya tafi nace maka". ALLAH sarki, bata son taga suna faɗa ne, dan tasan su ɗin abu guda ne!.
Ba tare da Smart ya kalli in da suke ba ya ce. "Mommah tafiya da ita fa zai yi"....... Cikin sanyin murya Mommah ta ce. "Ka kyale mashi ita ya je da ita, in har ɗanane, jinina ne, a cikina ya kwanta tabbas ba zai cutar da ita ba, dan haka ka kyalesa ya je da ita".......... Dik da tasan Smart yana bala'in son Pretty, amma ta ce ya sakewa Black Tiger ita domin gudun irin ɓarnar da Black Tiger zai iya yi masu idan aka hana shi burinsa! A yadda ta gansa bata ga alamar sauki a tattare da shi ba!.
Cike da mamaki Smart ya juyo da kallonsa a kan Mommah, tinani ya shiga yi a kan how comes zai barwa wani Æ´ar tsanarsa ya tafi da ita? Dik da yana jin tsananin kaunar Black Tiger a ransa, amma baya jin zai iya É—aga mashi kafa a kan matarsa.
Cike da damuwa ya dawo da kallonsa a kan King wanda yake ta famana binsu da kallo, shi burinsa ɗaya shi ne Black Tiger ya bar masarautar, idan ba haka ba hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba, saboda ɓarnar da ya yi masu ta wuci misali, shi ya yarda ɗansa ne, amma yana ganin kamar a yanzu Black Tiger ba shi kaɗai yake ba, dan haka barinsa Kingdom ɗin shi ne mafi alkhairi a garesu!.
"Omerish ka sake mashi ita ka ji?". Mommah ta sake faÉ—a a karo na biyu. Shi kansa Black Tiger baya son dukan Smart, domin tin da ya shigo cikin É—akin ya É—aura idanunsa a kan Smart yake mamakin kamannin dake a kan tsakaninsu, shiyasa kuka ga ya tsaya shiru yana karewa Smart kallo a lokacin da ya shigo É—akin, he was very shocked ne na ganin irin wannan kama, dole tasa yake jibgan Smart, amma ba wai dan zuciyarsa tana so ba, sai dan kawai ya shiga tsakaninsa da bukatarsa ce wato Pretty. Shi yanzu Black Tiger ma ba wai lallai saboda Spender zai É—auki Pretty, e akwai bukatar Spender a ciki, amma yanzu saboda ya kaita wajen Sweetie ya ga kyakkyawan murmushin dake bayyana a kan face É—in Sweetie É—in a dik lokacin da ta samu wani abin farinciki ne yasa ya ji ba zai iya barin Pretty ba, a takaice dai son Sweetie ta yi farinciki har ma ta yi mashi murmushi yasa zai É—auki Pretty!.
Ba don Smart ya so ba ya sake mashi Pretty, sai dan umarnin Mommah, ita kuma Mommah da biyu ta ce a bar Black Tiger ya tafi da Pretty!.
Yana sake mashi ita ya wuce ba tare da ya sake waiwayarsu ba, amma ta magic eyes ɗinsa yana ta kallan Mommah da baya jin zai iya gajiya da kallonta, haka ya nufi waje ya je ya tattare gabaɗaya warriors ɗinsa da ko kaɗan basu jiggata ba kuma basu gaji da yaki ba. Farko kenan a tarihinsa da ya taɓa zuwa yaki ba tare da ya shafe labarin masarauta a doron duniya ba ya koma empire ɗinsa, yau dai bai shafe su King Zuhair ba, ya tattari warriors ɗinsa suka wuce, kuma dik saboda Mommah yasa bai tsaya karisar da yakin ba, matar ta tsaya mashi a rai, sai yake jin kamar ma ya ɗauketa ya tafi da ita empire ɗinsa, ya je ya ajiyeta ya yi ta kallonta. Amma haka ya wuce.
Yana tafiya Smart ya yi gaggawar ficewa daga ɗakin saboda tsananin bakincikin da ya taso mashi. Kallon juna Mommah da kin suka yi, a lokaci guda suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. Dikkansu babu wanda ya ita cewa ɗan uwansa uppan, King ya wuce ya fita izuwa fada dan su tattauna kan batun ɓarnar da aka yi masu, ko in ce ɓarnar da ɗan cikinsu ya yi masu, ita kuma Mommah ta koma underground domin tattaro kan su Jaish.
Uhm Black Tiger yana kaunar marayu har ma yana renonsu, baya taɓa barin rayuwar maraya ta tagayyara, su Angela gabaɗaya marayu ne ya rena bawan ALLAH, kazalika kingdom of power suna ɗaukar marayu da daraja, saboda Mahnoor marainiya ce yasa suka bar aurenta da Jaish, A nan kun fahimci daga in da Black Tiger ya yi gadon renon da jin kan marayu?. Uhm ƴaƴan Mommah dikka they're gifted, Black Tiger yana da kaifin ƙwaƙwalwar da ku dubi yadda yake tafiyar da birninsa, ku dubi yacce ta gwammaci kasarsa ta mallaki komai a kan su fita waje suna saya, kuga yacce ya gyara birnin, common motoci a kampaninsa na Black Tiger auto motors ake kyarawa, kuga yacce yake da manya-manyan jiragen sama masu ɗauke da tambarin sunansa. Yana da sani a kan mulki sosai!.
In short sai da kingdom of power ta ɗauki almost 2 weeks suna gyare-gyare kafin su iya shawo kan ɓarnar da Black Tiger ya yi masu a kasa da awa biyu kawai. A lokacin da su Zarina suka samu labarin abin da ya faru da kingdom of power sun so zuwa su karisar da su kawai su huta, sai dai basu samu labari da wuri ba, sai hayan farfaɗowar kingdom ɗin ne suka samu labari, wanda hakan sam-sam bai yi masu daɗi ba. Sai dai basu wani damu ba, sun daure sun cigaba da gagarumin shirinsu na tinkararsu su yi masu kwaf ɗaya, sun haɗe sojojin yakinsu gabaɗaya a empire ɗin Zarina suna kara tsananta masu horo dan suna son yi wa Zuhair duka ɗaya ba tashi kenan!.