← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 130

Sashe 83

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sirrin dake ranki shi ne you love me over, and you don't want any distant between us right?".

Mamaki ne ya yi matukar kamata na yadda aka yi yasan sirrin dake zuciyarta, like wow abin ya yi balain ƙayatar da ita, ai bata san lokacin da murmushin da ya kara fito da kyanta ya kubce mata ba. Zuba mata ido ya yi yana kallon yadda take murmushi, yarasa meyasa baya iya controlling kansa a gabanta, a waje zai yi dik abin da yaga dama, amma a gabanta ko magana ta yi ba zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo bai amsa mata kamar yadda yake yi a waje ba, a waje ya kware da bada umarni, da zarar suna tare a ɗaki mai saukin kai yake zama.

Yadda take wannan murmushi ya kara susuta zuciyarsa a kanta, ya kafeta da ido babu ko kyaftawa......... Hannu tasa ta É—an rufe fuskanta kafin ta ce. "E haka ne, but kai ma ka faÉ—a mun abin dake naka zuciyar".

Tamkar mai raɗa ya ce. "Ai kema ba ke kika faɗa mun abin dake ranki ba, ni na gane da kaina, dan haka sai ki gane nawa". Ya kai karshen maganar tare da raɓawa gefenta zai wuce yana satar kallon tsala-tsalan cinyoyinta dake ta wani glowing mai ɗaukar hankali.

Ganin zai tafi yasa ta yi gaggawar riko hannunsa, tamkar zata yi kuka, ta marairace murya wajen cewa. "Ni ba zan iya gane komai kamar kai ba, kawai ka faÉ—a mun please"........ Jin yadda ta riko hannunsa ya sanya shi sauke nannauyar ajiyar zuciya, har cikin ransa ya ji rikosa da ta yi, yana jin tamkar ba zai iya sallake wannan ya cigaba da daurewa ba.

Slowly ya juyo tare da kurawa eyes É—inta idanu. "Babu abin dake a cikin raina wanda baki sani ba, sai dai in so kike ki ji wani sirrin da ni kaina ban san da shi ba".......... Ta fahimci me yake nufi, idan zata faÉ—a daidai yana nufin tamkar yadda yake son Ronnie haka yake sonta, matsayin sister kenan. Abin ko kaÉ—an bai yi mata daÉ—i ba, dan haka sai ta sake mashi hannu tare da juyawa da sauri ta nufi waje.

Bayanta ya bi da kallo yana jin tamkar ya jawota jikinsa, amma babu dama, dik wani motsawa da mazaunanta suke yi a kan idanunsa ne har ta kurewa ganinsa. Siririn ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tura kofar ya rufe sannan ya wuce ciki.

Shiryawa ta yi cikin wasu shaggun kaya, wandon jeans ne mai bakain kyau da riga top navy blue, wandan kuma fari. Ta gyara wannan kyakkyawan gashin kan nata, dan har da shi ya lalace ta sake wankewa, karo suka yi da Heleena ta yi mata wanka da coffee shi ne ta dawo ta sake yin wanka, to har gashin kanta coffee ɗin ya ɓata, saboda Heleena ta fita tsawo nesa ba kusa ba.

Tana gama shiri ta zuba turaruka zata nufi waje kenan ta ji motsin buÉ—e kofar toilet alamar ya fito. Ta wutsiyar ido ta saci kallonsa while shi kuma gabaÉ—aya kallonsa a kan waist É—inta da mazaunanta da suke tamkar zasu fasa wandon jikinta. Sai da gabansa ya faÉ—i ganin hakan.

Ta fahimci ita yake kallo, dan haka sai ta wuce zata nufi waje ba tare da ta gansa ba......... "Ina zaki je?". Ya faÉ—a a sanyayye sosai. Ba tare da ta juyo ba ta amsa da. "Wajen momma da su Mahnoor".

"Dawo ki zauna". Ya faÉ—a on a serious note. Tamkar zata fasa ihu ta juyo da kallonta a kansa, take ta yi rau-rau da idanu zata fara yi mashi kuka. ÆŠauke kansa ya yi daga kallonta ya wuce ya nufi closet É—insu.

Juyowa ta yi tana kunkuni, ga haushin ya nuna baya yi mata son soyayya sai dai son yaya da kanwa, ga haushin ya hanata fita, sai ta kwanta a saman sofa tare da jawo bargo ta rufe har kanta, wani irin zafi ta ji zuciyarta na yi mata, take ta fara ruwan zafafan hawaye, har da wani shessheka take yi.

-----------------------------🔥

Yana shiga bedroom ɗinsu ya isko Pretty sarkin son jiki kwance a saman bed, ta rungume pillows a kirjinta, ta yi ɗaiɗai a bed ɗin, ga uban bargo da ta lulluɓa da shi.

Cike da damuwa sosai a ransa ya dawo, dan hankalinsa a tashe kada blood power su yi wa King wani abin, shi kuwa Big Bro da yasan ba zasu yi saurin ɗaukar mataki ba ai kunga hankalinsa a kwance, bawan ALLAH Smart bai da sani a ɓangaren tsafi, kunga dole hankalinsa ya tashi.

Jin motsin shigowa É—akin yasa ta É—ago kai tare da waro idanunta waje, ashe dama ba barci take yi ba. Ai tana ganin shi ne ta yaye bargon da gudu ta diro kasa, kai tsaye ta nufesa. Tana zuwa ta faÉ—a jikinsa, at the same time suka sauke cool ajiyar zuciya.

Dik da yake a cikin damuwa sai da ya ji sanyi ta ratsa zuciyarsa na ganin irin kayan dake jikinta da kuma yadda ta yi hugging ɗintsa, rungumeta sosai ya yi yana sanya hannunsa ya riko santalelan cinyarta dake waje, dan short jeans ne zuwa cinyoyinta a jikinta, sai ɗan ƙaramin riga da bai gama rufe cibiya ba, ta saki gashi har baya, gari ya waye kowa ya fita ya gaggaisa da mutane amma ban da Pretty, tana ɗaki abinta, ko Sweetie bata nema ba.

"Yah Omerish ina ka je tin da sassafe?". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Ɗaukarta cak ya yi suka koma saman bed, ya kwanta da ita a jiƙinsa kafin ya sanya hannu ya tattare dark black curly hair ɗinta gefe, ya samu damar ganin face ɗinta da kyau, ta shagwaɓe fuska tana turo mashi ɗan baki.

Sumbatar bakin nata ya yi kafin ya ce. "Rigimamma, yau ba zaki yi breakfast bane? Dan nasan baki yi ba"......... "Kai nike jira ai ka zo ka bani a baki". Ta faÉ—a ita ma tana sumbatarsa a kyawawan lips É—insa.

"Da gaske yau ni ake jira?". Cikin zolaya ya yi maganar......... Kai ta jinjina mashi alamar e a shagwaɓe........ "Wai ni waye ya koya maki soyayya ne yanzu?".

Ɗaure fuska ta yi tare da yunkurawa zata bar jikinsa tana faɗin. "Kome na yi maka sai ka ce koya mun aka yi, ni ba zan iya abu da kaina ba, ni mahaukaciya ce kenan ko jahila? Watau ni ba zan iya abu ba sai mutane ne zasu iya ko?". Ta faɗa tana wani irin huci, kun san akwai zafi a rinƙa cewa mutum bai iya abu ba, komai ya yi sai ace waye ya gaya mashi, shi ba zai koya ba zai tabbata ana faɗa mashi kenan? Dole ta ji haushi.

Rikota ya yi da sauri yana faÉ—in. "Oh rigimammiyata kawai, sorry to, nasan ke kika koyi kayanki babu wanda ya faÉ—a maki, zolayarki nike yi".

Da yake a kansa tana da saukin kai sai ta saki kyakkyawan murmushi tare da cewa. "To muje ka bani breakfast, yau kai zaka mun wanka". Ta yi maganar tana komawa jikinsa ta kwanta, sannan ta fito da dogon tongue É—inta ta fara lasan lips É—insa tana kallon cikin idanunsa.

Bakinsa ya É—an buÉ—e ya capki lips É—in nata, a natse ya fara tsotsa yana kai hannunsa saman mazaunanta. "I really love you my wife". Ya faÉ—a tare da capko lips É—inta na kasa, ya fara bata hot kiss, take dik wata damuwa dake cikin ransa ta ragu, ya rungumi yar matarsa ya hau rage zafi.

--------------------------🔥

CROWN OF JUSTICE.

Yana fita kai tsaye side na su Ansar ya nufa, yana zuwa ya tura kofa ya shiga tare da yi masu sallama. Suna zazzaune saman sofa suna hira. Ai suna ganinsa suka mimmiƙe alamar girmamawa, ɗan ɗaure fuska ya yi, cikin wannan sanyi nasa ya ce. "Me hakan kuma?".

Ansar ne ya ce. "Girma muke baiwa yarima mai jiran gado"....... Harara ya dalla masu kafin ya ce. "Bana son hakan fa, ni Hoorain da kuka sani ne abokinku, ba wani Prince".

Anwar ne ya tari numfashinsa da cewa. "To dik da haka ai kai gaba kake damu a cikin warriors É—in ma".

Karisawa ya yi ya zauna yana cigaba da harararsu kafin ya ce. "Ya kuka tashi tuzurai?"....... Zama suka koma suka yi suna amsawa da. "Awww gori ake yi mana ma kenan".

Kai ya jinjina masu. "E gori nike maku, dik wanda ya ji zafi cikin satin nan ya fito da mata ya yi aure".......... Anwar ne ya ce. "Dik ba wannan ba, yanaga kamar Lion namu yana cikin ɓacin rai ne?".

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
------------------------------------------🔥♥️

SABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥

Anwar ne ya ce. "Dik ba wannan ba, yanaga kamar Lion namu yana cikin ɓacin rai ne?"........... Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Babu komai". Dafa shoulder ɗinsa Ansar ya yi. "Baka taɓa ɓoye mana komai naka ba, meyasa yanzu zaka fara ɓoye mana? Ka manta tare muke kuka kuma mu rarrashi juna?".

Kai ya girgiza kafin ya ce. "Tare muke komai, amma ku yarda dani ba wani abin ke damuna ba, kawai na ji babu daÉ—i ne da nazama sanadiyar zuban hawayen Zunaira yau".

Murmushi Ansar ya yi tare da cewa. "Awwww batu ake na ma'aurata, to shikenan a wannan gaɓa bamu nemi jin me yake damunka ba, je ka yi rarrashi, idan anki kulaka kuma sai ka dawo mu kwana a nan, mu ba zamu hanaka wajen kwana ba kuma ba zamu kiraka tuzuru ba". Cikin zolaya ya yi maganar.
Chapter 83 · 0% Book details