← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 130

Sashe 27

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shaga da kalle-kalle yana mamakin irin ɗinbin dukiya da ALLAH ya yi masu, dik wayewansa sai da ya jinjinawa empeir ɗin Black Tiger, dan bai taɓa ganin gini mai tsaruwar wannan ba.

"What brought you here?". Daga saman staircase ya ji murya mai kama da tasa ta yi mashi wannan tambayar, ko bai É—ago ba yasan É—an uwan nasa ne saboda muryar.

Fuskar Black Tiger yadda kuka san an aiko mashi da saƙon mutuwa, a ɗaure tamau, babu alamar wasa, lokacin da Smart ya ɗago ya kallesa sai da ya ɗan jin shock na ganin fuskar ɗan uwan nasa, amma sai ya dake da cewa. "Ɗaukarka na zo yi mu koma gida". Ya yi maganar yana kallan cikin idanunsa cike da tsantsar kaunarsa.

Datse idanunsa gam Black Tiger ya yi, dan ya tsani jin kalmar da Smart ya faÉ—a, baya son yana dangantasu, dan shi ba zai yarda su Æ´an uwa bane.

Da hannu ya nuna mashi hanyar fita game da cewa. "Get out before!". With harsh voice ya yi maganar.

Gyara tsayuwarsa da kyau Smart ya yi. "I can't go anywhere without you my blood". Sake datse idanunsa ya yi ya sake warosu a kan Smart ɗin, take black heart ɗin ta motsa mashi, gadan-gadan ya sauko ƙasa. Yana zuwa bai yi wata wata ba ya shake Smart, cikin fusata ya ce kada ya sake dangantasu, dan shi ba jininsu bane.

Shi kuma Smart da shi ma ransa ya fara ɓaci ne ya ce. "You're my blood, ko kaki ko ka so, idan ka musanta hakan ka cire kamanninka dake kan fuskata ko ka zo mu je ayi gwajin jini".

Buga Smart da jikin bango da karfi ya yi tare da kara shake mashi wuya, sannan ya ce. "Bani da wata haÉ—i da ku, wannan shi ne last maganata!".

Shi dai Smart tin da ya san Black Tiger yayansa ne baya jin zai sake yin gigin É—aura hannunsa a jikinsa bare har su yi faÉ—a, domin kaunar Big Bro ta ratsa jini da jijiyarsa gabaÉ—aya, dan haka bai yi niyar ramawa ba, kawai ya tsare shi da ido.

Dai'dai lokacin Ronnie ya shigo parlon, ai ruÉ—ewa Ronnie ya yi ganin yacce fuskoki biyu suka zama É—aya, yayansa da mai kama da shi, murza idanunsa ya shiga yi yana son tabbatarwa da shin abin da yake gani gaske ne ko dai almara ne?.

Ganin gaske ne kuma ga shi suna faÉ—a ba halin ya tambayi yayansa yasa ya watsa da gudu ya yi sama. Jim kaÉ—an sai ga Sweetie ta fito da saurinta, shi kuma Ronnie ya wuce neman Pretty, dan ita ma ta zo ta ga abin al'ajabin da ya gani.

A saman staircase in da Black Tiger ya tsaya É—azun Sweetien ta tsaya, baya iya ganin face É—in Smart saboda ya bata baya, tana dai iya ganin Black Tiger ya shake mutum.

ÆŠaga hannunta sama ta yi ta kyasta Æ´an yatsunta da basu wuce a kama a kakkaryen nan ba. Hakan yasa gabaÉ—aya suka kai kallonsu a kanta, ta wani tsaya kamar wata babbar mace, hannunta É—aya ta riko waist É—inta da shi tana dallawa Black Tiger wani irin kallo mai kama da harara, yacce kuka san faÉ—a suke yi ko wata mai jin haushinsa, ko da yake tana jin haushin abin da ya aikata, shi kwata-kwata bashi da hakuri kuma baya tsayawa ya fahimci abu, ni kuwa na ce gaskiya baya tsayawa ya saurari abu, dan ai koba komai zai tsaya su yi magana ta fahimta da Smart, amma kawai ya shakesa yana neman kashesa ba tare da ya yi mashi laifin komai ba.

Wato hajiya Sweetie Aunty Babba ta zo raba gardama, kai wlh Sweetie kamar wata renon tsofaffi, sai iyayi da son girma!.

Slowly Black Tiger ya zare hannunsa daga wuyar Smart yana kallonta, lokaci guda kuma ya yi kamar mai acting ɗin rashin gaskiya, kamar kuma yana shakkarta, sai ya ɗan yi ƙasa kaɗan da kai yana satar kallonta. Shi ma Smart ita yake kallo da mamaki, dan a tinaninsa Pretty ce, bai lura da kalar gashin kanta ba, da yake ma ta sanya siririn silky headband a kan nata, amma dik da haka gashin nata a waje daga ta tsakiya, shi dai kawai yana kewar Pretty sosai ne yasa ya yi mata kallon ƴar tsana!.

Ta yi fitinannen kyau a cikin kayan da ta sauya, irin Malesian gown É—in nan ne wanda ya bi jikinta ya lafe, ya fito da tsantsar surar da ALLAH ya yi, wannan dalilin ya sanya Black Tiger zame hannunsa daga wuyar Smart babu shiri, dan kyan da ta yi yanzu ya ninka na É—azun nesa ba kusa ba

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
Ai juyowar Smart ke da wuya ta yi balai'n ruɗewa, take ta fara wuwwuga eyesball ɗinta, ta kalli Black Tiger ta juya ta kalli Smart Tiger, kanta ya yi mugun shiga duhu da ruɗani, ta zaro eyesball tamkar zasu faɗo ƙasa, karfin hali irin nata yasa bata gudu ba ta daure, saboda Black Tiger yana a wajen, tasan koma menene ba zai bari a cutar da ita ba, amma dik da haka ta yi balai'n girgiza na ganin su biyu masu kama ɗaya.

Ba dan Black Tiger ya fita daban ba, dan ko a cikin irinsa miliyan Sweetie zata iya zaƙulo shi, ba dan haka ba da ta gagara gane wane shi na ainahi, amma yanzu ta gane kasancewar ga shatin ɗan bakinta a kumatunsa na janbakinta, sannan ga lips ɗinsa sun kara bala'in ja saboda haɗe bakinsu da ya yi ɗazun, janbakinta ya kara tura kalar lips ɗin nasa, and da ta zuba masu ido sosai sai ta ga Black Tiger ya fi haske fata sosai, fatar jikinsa ma ta bambamta da na Smart sosai, tsabar bin kokkofi irin na Sweetie sai ta gano idanunsu yana da ɗan bambanci kaɗan, na Black Tiger ma ya fi girma da kaɗan.

Dik da haka yarinyar nan bai ishata ba, cigaba ta yi da kare masu kallo tana tantance ƴan bambance-bambancen da ba kowa mutum ne zai iya gani ya banbantasu ba, sai mai kaifin ƙwaƙwalwa.

Almost 5 mins for silent, tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta fara tako saman staircase É—in a hankali-hankali, kai tsaye ta tinkarosu idanunta a kan Black Tiger babu ko kyaftawa. While shi ma ita yake kallo from head to toe.

Tin daga kan yanayin tafiyarta Smart ya sha jinin jikinsa cewa ba Pretty bane, saboda Pretty bata yi wayon tafiya cikin yanga da yauki yadda Sweetie take yi ba, Sweetie ai kunga ta fi Pretty wayewa da sanin abubuwa sosai, ita kuma Pretty ta fita iya shagwaɓa da shegen son jiki. Ko da yake bama za'a haɗa ba ai, Sweetie har school ta shiga ga Ronnie na yi mata lesson a gida, dole ta fi Pretty wayewa sosai!.

Sai da ta kusa karisa saukowa daga staircase ɗin Smart ya sake tabbata wa kansa ba ƴar tsana bace, dan ko yanayin surar jikinsu akwai banbanci, renon Black world da kingdom of power ba ɗaya bane ai, cimarsu ma daban-daban, dan haka harta soft skin na Sweetie ya ninka na Pretty kyau nesa ba kusa ba, da ta matso ma sai ya kara gane cewa Sweetie ta ɗan fi Pretty tsawo, ita kuma Pretty ta fita garin jiki, wato ta fita ɓul-ɓul.

Da yake staircase ɗin yana da tsawo, escalator ɗinsu ne fa, yau ba'a kunna shi bane kasancewar yanzu gari ya waye, kunga kuwa yana da tsawo sosai, dan a kallah step dake wajen takawa ka hau ya kai step 35 zuwa 40 haka, shiyasa bata sauko ƙasan da wuri ba, ga wani tafiyar yanga da take yi, ashe daga bayanta ba doguwar rigar tana ja mata har ƙasa.

Ai bata karasa ruÉ—ewa ba sai da ta sauko ta tabbatarwa da kanta fuskoki biyu masu kama É—aya take gani, har lokacin bata yarda mutum biyu bane, a É—an nesa da su ta tsaya tana cigaba da rarraba eyeballs É—inta a kansu, lokaci guda ta shiga kyafta idanunta tana sake buÉ—ewa, dik bai isheta ta gasgata abin da take kallo ba, hannu tasa ta fara murza idanunta tana girgirza har da cewa. "Burrrrrrrrrrr ba gaskiya bane, kawai shashatau ne, kai ina a'a wasa da hankalina Big Bro yake son yi".

Lokaci guda kuma ta ce. "Cool down Sweetie cool down, wasa da brain É—in Sweetie kawai Big Bro zai yi ya raina mata hankali, dan haka ba zan yarda da shi ba, mutum É—aya ne, mutum na biyun ni kaÉ—ai nike ganinsa na tabbata, dan shashatau ne, cool down Sweetie".

Wata iriyar dariya ta saki kamar zararriya kafin ta fara takawa izuwa in da suke, ta yarda manna mata hauka Black Tiger ya yi, har da cewa da magic ɗinsa ya yi amfani wajen kirkirar mai kama da shi dan ya wasa ƙwaƙwalwarta, dan haka ta ganosa har da cewa zata yi maganinsa kuwa.

A gabansa ta dakata tana kallon cikin idonsa, shi dai Smart kusan suman tsaye ya yi saboda yacce ya fahimci ba Æ´ar tsanarsa bace, idan kuwa haka ne to wacece ita? ALLAH MAI IKO! TANA MAMAKINSA SHI MA YANA MAMAKINTA.
Chapter 27 · 0% Book details