← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 130

Sashe 112

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yunkurawa Uncle Abbas ya yi zai yi magana kenan King ya É—aga masu hannu wanda hakan yasa uncle Abbas ya yi shiru. Riko hannun Big Bro King ya yi suka nufi saman sofa, hakan ya kara fusata uncle Abbas, saboda a tarbiyya irin na masarautarsu da al'adarsu dole Big Bro ya fuskanci hukunci na sa in sa da ya yi da uncle Abbas matsayinsa na kanin mahaifinsa kuma babba a kansa.

Amma king ya nuna ya fi son É—ansa sama da zumunci, wannan abin ya yi mugun konawa dayawa daga cikin parlon rai, ciki har da uncle Jahiz, bai ji daÉ—in yadda king bai dakatar da Big Bro ya gwada mashi cewa su uncle Abbas suna da mahimmanci a wajensa dan haka ya girmasu ba.

Kwace rikon da king ya yi mashi Big Bro ya yi yana huci ya ce. "Dad ku faÉ—a mun wanda yasa a kama Omaish".

Cikin tausasawa da sigar rarrashi king ya ce. "Calm down, nine na saka a fitar da su". A fusace ya juyo da kallonsa a kan King É—in. "For what reason?".

Uncle Abbas ne ya juya cikin fushi ya fita daga parlon, da sauri uncle Jahiz ya rufa mashi baya dan ya taushesa, saboda babu karya king ya baƙanta mashi rai, misali shi zai goyi bayan su Rizwan su faɗawa king magana ne da king zai rinƙa bin bayan yaransa? To ai ƴaƴa basu fi ƴaƴa ba.

Jawad dafe kansa ya yi yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, dan abin da bai taɓa faruwa a kingdom ɗin bane yake shirin faruwa, iyayensu suna faɗa, kai abin dai sai shiru. Ganin haka yasa Jaish ya yi gaggawar riko hannun Jawad ɗin, ya jasa dan su bar parlon, saboda sun ga abin is getting out of hand.

Umarni king ya yi wa warriors dake wajen a kan su fita, sannan ya umarci su Sareena dik su fita. Cike da takaicin su Sareena suka miƙe. Sweetie and Pretty sun kara samun mugun bakin jini a cikin family, babu wanda bai tsanesu ba sai mazan gidan, a mazan ma Obaid and Omaid sun tsane su matuƙa.

Kowa waje ya nufa saura Ronnie, Sweetie and Pretty, sai King and Big Bro, har lokacin su Pretty suna kuka basu dakata ba. Kallonsu King ya yi kafin ya ce su fita mashi a parlo. Da sauri Big Bro ya ce. "Babu in da zasu je dad, ka faÉ—a mun dalilin da yasa ka ce a fita da Omaish?".

Ƙoƙarin tausarsa king ya yi, amma ina ya kafe har sai an faɗa mashi dalili, kai tsaye King ya ce mashi. "Saboda na tsani jinin Omranish".......... Kallon tsab Big Bro ya yi mashi kafin ya ce. "Su suka yi maka laifi ko ubansu?". A tsaitsaye yake maganar yana kallon king har cikin ido.

"Amma kuma ai da sa hannunsu aka yi poisoning Omerish ko?". King ya faɗa cikin muryar dake nuna alamar ransa ta fara ɓaci. "Omnish ce take da sa hannu ba Omaish ba, dan haka Omnish zaka hukunta". Ya faɗa yana juyo da kallonsa kan su Sweetie da suke kankame da Ronnie.

Da hannu ya yi masu alama a kan su zo. Da gudu Sweetie ta tafi ta faÉ—a jikinsa, shi ma Ronnie ya matsa ya faÉ—a jikinsa ta gefe, ita kuma Pretty tsoronsa da shakka ga tuhuman da yake yi mata ne yasa ta ja baya tana kallonsu tana kuka, bata nufosa ba.

"Idan kana da matsala da mahaifinsu wanna bai shafesu ba, ina sonsu tamkar raina, in har zaka cigaba da korarsu to ni zan bar maka kingdom É—inka, zan É—aukesu ne mu tafi!". Ya faÉ—a cikin É—an É—aga muya yana shafa bayan Sweetie da hannunsa É—aya alamar rarrashi.

Durkushewa ƙasa saman gwiwowinta Pretty ta yi tana wani irin kuka mai taɓa zuciya. Unexpected daga bayanta ta ji an taɓa shoulder ɗinta. A gaggauce ta ɗago da kanta tare da juyowa. Wani irin zabura ta yi ta miƙe tsaye, muryarta har yana rawa waje ƙoƙarin kama sunasa amma ta kasa. Yana dafe da gefen cikinsa alamar ciwo yake yi mashi kenan, muryarsa can kasa-kasa a ɗan dashe ya ce.

"Koda kowa zai yi yunkurin kasheni a cikin familyn dake gidan nan to banda Omnish Daddy, ba zata taɓa iya kasheni ba, nasanta sama da kowa, ko sauro ba zata iya kashewa ba, muguwar matsoraciya ce wadda ko waje bata iya fita a lokacin da muke Paris sai Zunaira ta rakata, ba zan taɓa yarda a ce ita ce ta saka mun guba a abinci ba, ta taka sahun ɓarawo ne". Da kyar ya iya kai karshen maganar tare da jawota jikinsa, ya rungumeta ta gefen lion chest ɗinsa yana ɗan bubbuga bayanta da hannu ɗaya alamar rarrashi.

"Kada ka manta dad tun ina karami ake farautar rayuwata a gidan nan, to dan yanzu an yi poisoning É—ina ai ba wani abin mamaki bane ko abin da za'a tuhumi matata! Ka manta cewa tin kan asan za'a haifeta ake neman rayuwata ne? Meyasa zaka yi amfani da fushinka dake kan mahaifinsu ka É—aurashi a kansu? Please dad ka nunawa su Omnish so tamkar Æ´aÆ´a, saboda basu da laifi, hasalima zaluntarsu mahaifin nasu ya yi, kada ka manta fa a daji aka haifesu, suka girma a can, basu san komai ba face dabbobi, a hakan basu cancanci a tausaya masu ba?". Ya kai karshen maganar yana wani irin haki numfashinsa na yin sama-sama, ga idanunsa jajir tamkar wuta.

Sake su Sweetie Big Bro ya yi ya matsa ya rike Smart É—in da kyau. "Amma Omerish bana ce kada ka fito ba? So kake ciwon ya tsananta ko?".

"Dik abin da yake faruwa ina ji ne ɗan uwana, ba zan iya jurar avoiding ɗin Omnish da daddy yake yi ba, bullying da ake yi masu tai yawa, shiyasa na fito dan in faɗawa daddy gaskiya"........ "Ya isa haka maganar, mu je ɗaki ka kwanta kuma kada ka sake tashi yanzu, kada ka jiƙa mana aiki". Big Bro ya faɗa tare da fara taimaka mashi suka nufi hanyar komawa room ɗinsu.

"Daddy zan dawo mu yi magana". Big Bro ya faÉ—a. Da sauri su Ronnie suka rufa masu baya. Smart ya rike hannun Pretty gam har suka karisa cikin É—akinsu. A nan Big Bro ya kwantar da shi suka fito shi da su Ronnie suka barsu tare da Pretty suka koma parlon King dan zancen bata kare ba, yanzu ne ma zata fara. Waye ya zuba poison a abincin? Ya king zai kare da kannensa da suka yi fushi saboda ya nuna fin son Æ´aÆ´ansa a kansu? Uhmmm muje zuwa.

Har lokacin tana kuka sosai, hannunta Smart ya jawo ta zauna a gefen bed ɗin, da kyar ya iya cewa. "Ya isa haka kukan to"........... Ai kamar jira take yi ya yi magana, da sauri ta faɗa jikinsa tana ƙoƙarin shanye kukan nata.

"Meyasa kika ce maganin mutuwa kika saka mun a abinci? Kenan kin san da an saka mun wani abin ne?". Muryarsa ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta........

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
"Meyasa kika ce maganin mutuwa kika saka mun a abinci? Kenan kin san da an saka mun wani abin ne?". Muryarsa ya daki dodan kunnenta. Da sauri ta É—ago da kanta daga kirjinsa, ga idanunta sun kumbura luhu-luhu, kai ta shiga girgizawa. "A'a ban sani ba, kawai dai ban san ya aka yi na faÉ—a ba, kuma kaga mun yi faÉ—a, da ka ce me na saka maka a abinci ne sai abin ya bani haushi tin da naga kasan bani nike girka abinci ba, kuma kasan ni me nike da shi da zan saka maka a abinci? Da farko ma na É—auka wasa kake yi shiyasa ban kira su momma a lokacin ba, sai da naga ka daina motsi ne na gane da gaske ne". Zafafan hawaye suna biyowa kuncinta ta kai karshen maganar.

Tin da ta fara ya zuba mata idanu yana kallonta har ta kai karshe, nisawa ya yi kafin ya ce. "To kinga illar dake cikin magana cikin fushi ko?". Kai ta jinjina mashi alamar e ta gani.

"To daga yau ko wani irin fushi kike yi da mutum ki rinƙa tauna magana kafin ki furta shi garesa, saboda gudun faɗawa irin wannan matsala kin ji ko?". Ya kai karshen maganar tare da kai hannu saman fuskarta. A hankali ya fara goge mata hawayen nata.

Kai ta jinjina. "Ba zan sake ba In Sha ALLAH"......... "Kin yi breakfast ne?". Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a.

"Okey bari in saka a kawo maki to". Nan ma kai ta girgiza da sauri tana faÉ—in. "Na koshi".. ........... Ya fahimci ta tsorata da abincin ne, tana tsoron cin gubar ita ma, dan haka sai ya ce. "Kada ki damu ba irin wanda na ci za'a baki ba, yanzu tsaron abincinmu zai tsananta fiye da na da, kafin mu ci abinci ma sai an dubata tsab dik da cewa a da É—in ma ana dubawa, yanzu za'a tsananta".

Mayar da kanta saman lion chest É—insa ta yi, ta kwanta shiru tana tinani bata iya cewa komai ba.

A yayin da a can gefe kuma Big Bro yake ta fama da king a kan wannan gaba tasa da Omranish, cikin sanyin murya ya ce. "Dad already kun rigada kun zama É—aya da Omranish É—in nan, ban goyi bayan ka yafe ka kyalesu a kan cutar da suka yi maka ba, but ba zan goyi bayan ka hukunta waÉ—an da basu da hannu a cikin faÉ—ar ba! Me laifinsu Hoorain? Kawai dan sun so Æ´aÆ´anka? To ai kaima Æ´aÆ´anka sun so nasu ko?".
Chapter 112 · 0% Book details