Sashe 64
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Jaish ya yi mamakin karfin halin Mahreen, hakan yasa ya ji a ransa dole ma a aura mata guyson dan ta gane shi ba yaro bane, in ba haka ba ba zata daina raina mashi wayau ba, sai ranar da ya koya mata hankali, sosai ya yi mata faɗa ya ce kada ta sake raina nagaba da ita, ta rinƙa ce mashi yaya, ba ya fita shekaru ba!.
Shi ne fa take ce mashi yaya, amma fa tana fushi da shi, dan yau kwanaki uku da faruwan hakan bayan gaisuwa bata kula shi, ko ya yi mata magana bata amsawa, wai shi ne ya je ya sa Jaish ya yi mata faɗa, dan haka babu ita babu shi, sosai bawan ALLAH ya shiga damuwa, ya yi ya yi da ita a kan ta faɗa mashi me ya yi mata take fushi da shi ya bata hakuri. Amma taki kula shi, daga karshe ma taki bashi lokacinta, sai dai idan sun haɗu a hanya ta sauya hanya da sauri, taki bari su zauna ko na minti ɗaya bare ya ji damuwarta ya san ta in da zai ɓullo dan gyara alaƙarsu. Wlh yana tsananin son yarinyar nan da zai iya jure komai a kanta amma ban da fushinta.
Yau ma tin da ya tashi da zafe da ɗan zazzaɓi ya tashi, kuma dik damuwar bata kula shi ne sila, hankalinsa ya tashi har ya shiga zazzaɓin firgici. Sanye yake da sleeping dress zubin pj's ya fito daga room ɗinsa, har ɗan rawan sanyi yake yi.
Bedroom na momma ya wuce kai tsaye, sai dai ya yi mamakin ganin yadda ake ta abubuwa a gidan nasu, ana ta shirye-shirye da girke-girke. Zaune a saman sofa ya isko momma tana rike da waya, a kusa da ita ya zauna tare da kwantowa jikinta yana É—an turo baki.
"Shalelena yau kuma waye ya taɓoka?". Momma ta faɗa tana shafa wannan kyakkyawan arabs hair ɗin nasa mai matuƙar ɗaukan hankali. "Momma biki ake yi a gidan nan ne naga ana ta hidima?". Ya faɗa yana kallon fuskarta cike da tsananin kauna. "Yayanku ya kirani da safe ya ce muna da manyan baki a shirya masu tarba ta musamman, shiyasa ake shirya masu".
Ɗan zaro ido ya yi. "Momma ko dai shi ne zai dawo?". Kai momma ta girgiza kafin ta ce. "A'a idan shi ne zai faɗa mun, ya dai ce bakinsa ne zasu zo". Ɗan kwaɓe fuska ya yi alamar bai ji daɗi ba da aka ce ba Smart ne zai dawo ba, yana kewan yaya nasa.
"To momma shi yaushe zai dawo?". Hannu tasa ta É—an shafi lallausan kumatunsa kafin ta amsa da. "Yanzu dai ban sani ba, amma ya ce soon zai dawo".
Sam momma bata san sune suke hanya ba, a tinaninta baƙin Smart ne zasu zo daga Paris, yaki faɗa mata ya yi nasara ne, yana son yi mata bazata.
Miƙewa guyson ya yi yana faɗin. "Dama na zo dubaki ne momma na, tin da kin wayi gari lafiya bari in yi wanka in zo mu yi hira". Ya kai karshen maganar tare da manna mata sumbata a kumatu. Cool smile ta sakar mashi kafin ta ce. "ALLAH ya yi maka albarka shalelena".
Da amin ya amsa kafin ya wuce ya nufi waje, cike da kallon kauna Momma ta bishi tana jin tamkar dik cikin ƴaƴan nata ta fi sonsa, yana da tsananin shiga rai tamkar Big Bro, shi fa guyson da alama jininsa ma irin na Big Bro ne, idan ana maganar Big Bro kuma kun san ba'a banbanta shi da Smart, so ba sai na kama sunan Smart ba, kada ku rinƙa matawa they're identical!!
Yana fita ya nufi bedroom na Mahreen cike da muradin ya fara kyakkyawar safiyarsa da kyakkyawar face É—inta bayan na mommarsa. Bakinsa a É—auke da sallama ya tura kofa kai tsaye ya shigo ciki.
A miliyan ta juyo da kallonta a kansa, tana tsaye a tsakiyar É—akin daga ita sai towel a kirji wanda bata ma É—auresa ba, tana rike da shi ne, daga wanka ta fito, ta tsaya tana tinanin kalar kayan da zata sanya ne ya afko mata ciki.
Ai juyowar da ta yi bata san time É—in da ta saki towel É—in ya yi kasa ba, dan ta tsorata jin mutum a É—akin. Subhanallah ai suman tsaye guyson ya yi idanunsa a kanta, ya ga abin da ya juyar mashi da kai. A miliyan ta duka ta É—auki towel É—inta ta É—aura daga kirjinta tana dalla mashi wata uwar harara kafin ta ce. "Me ka kalla?".
Tambayar ma dariya ta so bashi, wai me ka kallah, to shi kam me zai ce mata ya kallah?. "Fita mun a É—aki kuma kada ka kara shigowa in ba haka ba in faÉ—awa Yah Jaish kana shiga harkata, É—an iska kawai, dama na jima da sanin É—an iska ne kai".
Shiru ya yi bai amsa mata ba, yana dai ta binta da wani irin mayen kallo from head to toe. "Ba zaka fita daga É—akin nan ba?". A fusace ta faÉ—a.
Slowly ya ɗan motsa lips ɗinsa wajen cewa. "Babu abin da na kalla face kayana, kuma ni ba zan fita daga ɗakin nan ba har sai kin faɗa mun me na yi maki kike shareni, ko na yi maki magana bakya amsawa". Muryarsa shar ya yi maganar, da alama abin da ya gani yasa ya wartsake daga kasala da yar zazzaɓin da yake ji.
"Kayanka kuma a jikina?". Cikin tsiwa da masifa ta yi maganar tana dalla mashi harara. Shi kuwa cikin sanyin murya ya ce. "Ki rage hararana kada idanunki su faÉ—i kasa, kayana na gani mana, baki san ke kanki tawa bace ko?".
Cikin zafi ta ce. "Saboda kai ka halicceni ai dole na zama taka, wlh ka fita mun a É—aki in ba haka ba kome na yi maka kai ka nema, kaga bana shiga harkarka kai ma ka fita nawa!".
Siririn smile ya saki kafin ya ce. "Ba zan fita ba har sai kin faÉ—a mun dalilinki na guduna, me na yi maki? Kina cutar da zuciyata sosai wlh".
Wani irin kallo mai jefa mutum cikin shakku ta wurgesa da shi kafin ta ce. "Ra'ayina ne in yi maka magana ko kada na yi, dan haka dik wata alaƙa da kai na datseta, bani babu kai, dan haka zaka iya tafiya". On a serious note ta yi maganar, ita nan har ga ALLAH fushi take yi da shi, wai sun raba jaha!.
Nisawa ya É—an yi. "Ni kuma ba zan iya hakura in barki ki fita daga harkata ba, Please Mahreen, ki yafe mun idan ma wani laifi na yi maki, kin ga dai na baki hakuri ko?".
Kallon up and down ta yi mashi kafin ta ce. "Bana alaƙa da ƴan iska, ko kaɗan baka ji komai ko ka bani hakuri ba na ganina tsirara da ka yi, hakan ya kara tabbar da sunanka a gareni na ɗan iska, dan haka kawai ka fita mun a ɗaki". Ta yi maganar cikin faɗa tana yi mashi pointing door da hannunta.
"Mahreen ya za'ayi in ji babu daÉ—i dan na kalleki a haka? Kayana na gani, to menene kuma zan ce ban ji daÉ—in hakan ba, very soon fa zaki zama........" Bai idasa maganar ba ta katse shi cikin faÉ—a da zafa. "Wai uban me naka a jikina da tin É—azun kake ta cewa kayanka a jikina ka gani?".
Hannunsa har yana É—an rawa ya É—agosu ya nunata da yatsa kafin ya ce. "Ke kanki gabaÉ—aya, Please Mahreen ki saurareni kin ji? Zan yi dik abin da kike so"...... Ai wani irin É—aure fuska tamau ta yi kafin ta ce. "Ni É—in ce taka? To sannu ubana, wlh ka fita a É—akin nan tin kafin in É—auko wani abin in buga maka".
Yana tsaye ko gezau bai yi ba, idanunsa a kan É—an bakin masifar nan tata dake mugun bashi sha'awa yana É—aukar hankalinsa. Ganin bai motsa ba yana karewa albarkatun jikinta kallo ne yasa ta kara fusata tare da rarumo kwalbar turare a fusace ta yi kansa da shi da nufin ta buga mashi. Sai dai tana zuwa ya riko hannun nata da hannunsa É—aya, tare da juyar da ita ya mannata da jikinsa, ya zamana bayanta ya mannu da kirjinsa.
Slowly ya kwanto da kansa a saman shoulder É—inta, sai kokarin kwace hannunta da ya rike take yi amma ta gagara.
"Mahreen don't you know that i love you ne da kike mun dik wannan abin? Meyasa kike wahalar da zuciyar da bata san komai ba face sonki ne wai?".
Kam balai, ai wani irin É—aure fuska da ta yi, da karfin tsiya ta juyo garesa tare da daddagewa ta ture shi baya, cikin faÉ—a ta ce. "Ni Mahreen kake so?".
Kai ya gyaɗa mata almar yeah ita fa. Ai wani irin shegen dariyar da ga sheke da shi sai da ya saki baki yana kallonta, sai da ta yi mai isarta sannan ta tafa hannayenta biyu cikin juna kafin ta ce. "Ni Mahreen kake so? Haba dai yaro! Ai babban goro sai magogin karfe in faɗa maka, na fi karfin yaro kamar kai, to kai me zaka mun ma idan na aureka? Yaro da kai". Ta faɗa cikin rashin sanin ma'anar kalaman nata, shi kansa babban gore sai magogin karfe Chuchu ke faɗa mata hakan, ta ce ita babbar goro ce sai magogin karfe, bata san Chuchu na nufin ita sai ƴan gidan sarauta ko kuma masu muƙami a gwamnatance ba, ba'a ce mata girman shekaru ba, da yake kan nata ba natsuwa sai a hankali kun ji haukar da take zubawa, har da wani wai me zai yi mata idan ya aurenta yaro da shi, sai kace tasan me ake yi ma a gidan auren, kawai dai surutunta take zubawa cike da hauka da faɗa.
Tin da ta fara magana bai katseta ba har ta dasa aya, sannan ne ya ce. "Mahreen kina nufin ni baki sona? Please kada ki ce hakan, zan yi dik abin da kike so kin ji?".