← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 130

Sashe 44

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mannesu ya yi sosai, slowly ya rantwafo da kansa a kanta, kamar zai yi mata raɗa a kunne, sai kuma ya dawo da bakinsa dab lallausan kumatunta. Banza da shi ta yi, saboda ranta ya kai kololuwar ɓaci, tin da take babu wanda ya taɓa yi mata maganar mom ɗinsu sai shi yau, sannan ya ce kada a sake yi mashi maganar! Uwa fa ake magana! Ko dan shi bai san daɗin uwa bane yasa yake ɗaukarsu a matsayin abu guda babu wata banbanci. TO OUR BIG BRO, UWA DABAN TAKE DA KOMAI, DOLE RAN SWEETIE YA ƁACI, IDAN KAI BAKA DA SHAUKIN UWA TO SU SUNA DA SHI!.

Kura mata idanu sosai ya yi, yau ya ga tsantsar bacin ran da bai taɓa ganin ko kwatansa a kan fuskarta ba, gabaɗaya sai ya ji babu daɗi.

Da karfi ta yi kokarin fisge rikon da ya yi mata, sai dai kuma ina, ta gagara. Shiru shi kuma ya yi bai yi magana ba, kamar yana son cewa wani abin kuma. Almost 5 mins suna a haka, sai dalla mashi harara take da faman yi, tamkar ta rufesa da duka haka take ji, ga idanunta sun yi jajir da su.

Tin tana kuka da ɗan sauti har kukan nata ya daina fita gabaɗaya, daga karshe ma ta yi shiru tsit, shi dai ko ci kanki bai iya ce mata ba, babu ma abin da yake tunawa irin zazzafar tsana da mom twis ta yi mashi, har ikirarin ɗaukar fansa ta yi a kansa, dan tana da bakin zuciya na gasken-gaske kaman Mammar Kamran haka take, a lokacin da yake gana mata azaba ya buƙaci da ta buɗi baki ta faɗa mashi a ina spender yake, ya azabtar da ita fiye da tinaninku, sai dai kuma a dik lokacin da ta buɗi baki cewa take yi. "Dik ran da na samu dama nice zan zama ajalinka, ba zan taɓa barin azzalumi irinka a doran duniya ba, nice mai kawo karshenka! Ka rubuta ka ajiye, na yi rantsuwa da ALLAH ɗaya in har na samu damar kuɓuta daga hannunka sai na ga bayanka!!". TASHIN HANKALI!

Gabaɗaya yanzu kalamanta ne kawai suke ta yi mashi yawo a kansa, bai san time da Sweetie ta kwace kanta daga rikon da ya yi mata ba, sai ganinta ya yi tana barin wajen, kansa ta ɗan dauki zafi yana buƙatar hutu idan ba haka ba kuma a samu matsala gagarumi. Dan haka sai ya fito ya wuce sama shi ma, da alama jikinsa dik ya yi mugun sanyi sosai.

CROWN OF POWER.🔥

Tin da King ya yi furucin zai sanar da Smart gaskiyar abin da yake faruwa ya shiga tashin hankali da damuwa, gabaɗaya ya zabge ya rame kamar bashi ba, ga ciwon zuciya da yake fama da shi, da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci yana cikin mawuyacin hali, Mommah ta shiga damuwa na wuce misali, ka zalika mummyn Chuchu ma dai tana cikin damuwa matuƙa, sai dai kuma ita Mama ko a jikinta, bata wani damu ba, kokari ma take yi na neman hanyar da Ramish zai maye gurbin babansa, so gabaɗaya hankalinta ba'a kansu yake ba.

A yayin da shi kuma Ramish yana can yana ƙoƙarin shirin zuwa ɗauko Leesharh, sai dai ya ɗan dakata da kudurin nasa sakamakon ganin halin da king yake a ciki, tafiyarsa zai iya kara tada hankalin King har yasa ciwon ta karu su da suke neman ya samu lafiya, dan kun san yadda halin king yake a kan makiyasa, yana jin Ramish ya je Evil Crown zuciyarsa ce zata karisa bugawa kowa ya huta, dan haka Ramish sai ya ɗan dakatar da kudurin nasa, amma ba wai ya fasa bane.

A ɓangaran Momman kuwa matar nan tana cikin tsananin damuwa na wuce misali, gabaɗaya walwala ya kauracewa kan fuskarta, har rama ta yi sosai, mom ɗin Smart ta sake zuwa bayan komawa da ta yi kafin ayi yaki, yanzu ta zo tana a tare da Mommah tana kwantar mata da hankali, amma ina Mommah hankali ya ki kwanciya, burinta kawai Smart ya dawo, dan har ga ALLAH ko barci bata iya yi tin da ya tafi, kwana kan dadduma take yi tana kwararo masu ruwan addu'ar ALLAH ya ɗorasa kan ɗan uwansa ya yarda dasu ya dawo gida. NI KAM NA CE KAMAR ABU NE WANDA BA ZAI YIWU BA BLACK TIGR YA DAWO GIDA, AMMA DAI ZAMU GANI, BA ZAI IYA RAYUWA A CROWN OF POWER BA, SABODA GANI YAKE YI TAMKAR KURKUKU NE KO KEJIN KAJI, DAN DIK GIRMA DA DAULAR CROWN OF POWER KO RABIN DAULARSA BASU KAI BA, KADA KU MANTA DA ƊANYAR GOLD AKA YI GININ ROYAL PALACE ƊINSA FA, UHM ZAI RAINA TATTALIN ARZIKINSU NE, BASU MA DA QUALITIES ƊIN DA ZASU IYA JANSA YA ZAUNA A CIKINSU, AMMA KILA YA IYA YARDA SU SUKA HAIFESHI IDAN SUKA BASHI HUJJOJI, BARI DAI MU GA ME ZAI FARU, AMMA KU ME KUKE TINANI?.

---------------------🔥

Yau ta kama Monday, CROWN OF POWER tana nan yadda take, tana cigaba da guda kamar yadda take a kullum karkashin umarnin da kaddamarwar King Zuhair, bisa tallafawar Uncle Abbas kasancewar King bashi da lafiya, so yana tallafa mashi. While Aunty MieMie ita ma tana iyaka nata bakin kokarin, shi ma uncle Jahiz haka, Akka ma dik da bata da lafiya tana bada nata gudunmawar sosai, a haka dai suke lallaba rayuwar.

GabaÉ—aya Æ´an'matan King suna a zazzaune a katafaren main parlor, ciki har da Sareena da bata san Smart ya dankara mata red card na saki uku ba, dan Momma ta mance bata isar da sakon ba. So har yanzu tana É—aukar kanta matsayin matar Smart ne, nan gagarumin shiri suke ta faman shiryawa na yadda zasu shawo kan Smart ita da su Omaid.

Ta yi wa su Omaid alkawarin matuƙar suka tallafa mata ta samu kan Smart, to za su huta ne, har da ce masu zata sanarwa da Smart kada wanda ya saka masu ido, sanan su ci karansu babu babbaka babu mai horasu, wannan alkawari yasa suka zage dantse wajen ganin sun sama mata hanyar da zata mallaki zuciyar Smart, su dai damuwarsu su yi ta shaiɗancinsu kada a hukuntasu ko a takurawa rayuwarsu.

Su Mahreen dik suna parlon, kowa dai yana wajen, sai wani harare-hararen juna suke yi tamkar ba Æ´an gida guda ba, bare ma Sareena da ta matsawa Mahnoor da harara tamkar ta tsare mata wani abin, abin mamaki kuma shi ne har yau dai babu wanda ya nemi Fanan.

Zee ta zuba uban tagumi tana ta tinanin Khadija, dik da Aunty MieMie ta faÉ—a mata Khadijah na lafiya, amma hankalinta yaki kwanciya ko kaÉ—an.

Unexpected suka ga anturo kofar parlon daga ta waje. GabaÉ—ayansu suka wurga eyesball É—insu a kan kofar dan ganin mai shigowa, Mahreen da shegen gulma har da wani zazzaro ido waje tana wani wuwwurgasu, ta wani kwanta saman sofa tana wani shan kamshi ita a dole ta yi kwalliya.

Almost 1 min da turo kofar wata kafa ta tako ciki, ai tin daga kasa suka fara ganinta har zuwa sama. Sanye take da wannan shiga tasu ta masu jajayen kunnuwa, hannunta rike da echolac tana ja, ta saki gashi tamkar wadda ta yanko daga kudancin duniya, ga wata uwar glass kamar babban yaron Smart mai suna Robert ne ya bata aro. HELEENA.

Wani irin matsiyacin kallo suka fara binta da shi tamkar za su cinyeta da ido, bare ma Sareena da tin da ta É—aura idanunta kanta ta ji ta tsaneta sosai, a gefen ita ma Heleena tana É—aura ido kan Sareena ta ji yarinyar bata yi mata ba sam.

Tamkar yadda suke binta da wani irin matsiyacin kallo haka ita ma take binsu da shi daga cikin glass, basa ganin idanunta ne yasa basu gane ba.

Ko sallama bata yi masu ba hakan yasa gabaɗaya ransu ya ɓaci sosai, sai suka ɗauke kansu daga kallonta. Ganin haka yasa ta tako cikin nuna ita mai ji da kanta ce, ta nufo in da suke, a tsakiyar parlon ta dakata tana binsu one by one da kallo, da hannu ta yi pointing na Sareena kafin ta ce. "Da alama kece babba a cikinsu, baku iya girmama manya bane?!".

Yadda kuka san bango Heleena ta yi wa magana ba su ba. Suka baiwa banza ajiyarta, kun san mutanen akwai ji da kai ga izzar balai, basa wulakanta mutum haka kawai, amma basa ɗaukar raini, idan ka mutumtasu ka kama kanka zasu baka mutumci, idan kuma ka nuna ji da kai zasu nuna maka gidanta ka zo. BATU NA GASKIYA BA WASA BA, WLH DIK MAI WULAƘANTA ƊAN ADAM KU BINCIKA AINAHINSA MATSIYACI NE, DIK WANDA YA TASO CIKIN DUKIYA CIKIN DAULA WLH BAYA KULAKANTA MUTANE SAM-SAM, KU LURA KUMA ZAKU CE NA FAƊA MAKU, AINAHIN MASU ABIN BASA WALAƘANCI!!.

Ganin sun bawa banza ajiyarta ne yasa ranta ya ɓaci sosai, cikin fushi ta ce. "Ba daku nike magana ba wai?". Nan ma dai banza yaran nan suka baiwa ajiyar Heleena. Ji ta yi tamkar ta rufesu da duka, amma bata da karfin yin hakan, dan haka sai ta yanke shawarar ta kira ɗaya daga cikin bodyguards da ta zo da su ya zane mata su, ta ɗauka fa nan Paris ne, bata san gidan sarauta take ba, kuma shi gidan sarauta basa ɗaukar wargi da wani shashanci!.

A ƙaida ta gidan sarauta wani daga waje bai isa ya keta izuwa in da family part yake ba idan ba King bane ya bashi izini, warriors dake tsaron gate na shigowa ma ai basa karɓar maganar kowa face na King, dan haka babu wanda ya isa ya wuce gate ɗin ba tare da King ya umarcesu da su bashi hanya ba, sai kuma Mommah, ita ce Princess da ake ji da ita, tana da damar aran bakin King a wasu wuraren, sarautar Crown of power na faɗa maku tsagwaran sarauta ce mai tsari da kuma bin dokoki, basa ɗaukar wargi ko wasa!.
Chapter 44 · 0% Book details