Sashe 79
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Da mahaifina, da kakansu Hoorain, da ɗan uwan mahaifina sarkin yammaci (Kakansu Bobo) da mahaifinsu Abdul Raof (Kakansu Leesharh) su ne suka hasasa blood power a cikin zuri'armu, a lokacin da suke manyan abokai kuma suke a kan mulki, yadda kuka ga masarautar su bobo wato Blood Crown take tafiya a kan tsafi har yau har gobe to haka dikka sauran kingdoms nan suke, ciki harda wannan masarauta, suna amfani da tsafi dan karfafa mulkinsu, shiyasa masarautu biyar ɗin suka yi karfin da ba'a iya yakansu a lokacin, sun kafa kasautunsu da karfin ikon jini, ni ban san yadda suke tsafi ba, kawai dai abin da nasani shi ne a lokacin da na hau mulki blood power ta buƙaci da na bada wanda na fi kauna domin a karawa rawanina karfi, shi ne ni kuma na ce ba zan yarda da tsafi ba, domin ni na samu wadataccen ilimin addini, nasan ba hanya mai ɓullewa suka bi, shi ne na tirge na bijirewa Blood Power, na ce masu ni mulki irin wanda ALLAH da manzonsa suka ce zan yi. (Kun tina labarin da na baku na Bobo time da zai hau mulki? Ba ance sai na bada wanda yake kauna ba? Kun tina ko? To haka tsarin Blood Power yake, su iyayen Bobo har yanzu sun ki saranda su cire kansu wannan, amma mu je zuwa bari King ya gama bamu labari)".
"Sun yi juyin duniyar nan naki yarda da mulkin tsafi, to a lokacin bani da karfin da zan iya yakansu, sai na buƙaci sauran masarautun da mu haɗu mu yakesu dan mu kafa daula ta gaskiya ta musulinci, sai dai kash a wannan zama da muka yi dan haɗin gwiwa, Omranish (Mahaifin su Sweetie) shi ne ya fara miƙewa ya ce ba zai yarda ya bar tsafin mahaifinsa ba, dan haka zai cigaba da yi wa Blood Power biyayya suna bashi karfin mulki ya juya wanda yake so. Daga ya faɗi haka shi ma Herry (mahaifinsu Bobo) ya ce ba zai bar Blood Power ba dan suna bashi karfi dan haka zai iya juya duniya idan yana tare da su, da jin haka shi ma Abdul Raof ya ce ba zai bar Blood Power, suna son shi, na yi ƙoƙarin sanar da su illar da hakan zai haifar masu, amma suka yi burus da maganata, hakan yasa na ce to ni zan yaki Blood Power da karfin da ALLAH ya bani".
"Tsawon sati na shafe ina tinanin mafita, daga karfe naga bani da karfin iya yakarsu, a wannan lokacin suka kashe mahaifina wai saboda naki yarda na basu jini, dik da haka ban sare ba kuma ban rusunar da kai a garesu ba, na sake tsananta tinani dan samun mafita, a wannan gaɓa Rahilarh ta zo tana da cikin Su Omerish, hankalina ya tashi dan nasan confirm zasu ce zasu ɗauki ɗana tin da naki yarda in zaɓi wanda nike so, sun san dole ina son ɗana ai, to ban sani ba ashe Umaiyya ma ta riga Rahilar samun cikin MieMie, na shiga damuwar da ko barci bana yi, to matsalata ma shi ne idan na basu ɗan nawa ba iya haka zasu tsaya ba, sun rinƙa karɓar ƴaƴana kenan a dik lokacin da suka tashi, shiyasa naki yarda tin farko".
Dakatawa ya yi yana goge hawayen dake zubo mashi yana mayar da numfashi. A hankali ya ajiye cup na cappuccino dake hannunsa ya kalli Smart ya ce. "Omerish bani ruwan sha". Ya faÉ—a yana haki a hankali-hankali.
Da sauri Smart ya miƙe ya ɗauko mashi ruwa, ya koma ya zauna tare da ɓalle mashi bakinta. Karɓa King ya yi ya kafa a bakinsa, sai da ya shanye kusan rabi sannan ya cire ya miƙawa Smart yana cigaba da sauke numfashi a hankali hankali.
Dukkansu sai binsa suke da kallo, momma ma idanunta ya cika da kwallah tin ma bata ji karshen zancen ba. Ɗan hutawa for 5 mins King ya yi kafin ya cigaba da cewa. "Da naga ba zan iya dasu ni kaɗai ba sai na nemi mu yi zama da shuwagabannin Blood Power ɗin, a nan ne suka kafamun sharuɗan cewa in dai ina son tsame su Abdul Malik da zuriarsu daga Blood power dole fa sai na bada jini kamar yadda da suka buƙata tin farko, idan na yi hakan zasu yarda su zare sunan waɗan nan four kingdoms ɗin a list, daga nan suka tsara mun yadda zan bada jinin da suke so daga gareni. A lokacin na dawo gida sati babu cin abinci babu barci, ina ta tinanin yadda zan yi, daga karshe dai bani da mafitan da ya wuce in sake komawa in yarda da sharuɗansu, a nan ne na ce masu na aminta, amma ba zan iya basu ƴaƴana na farko ba, su mun afuwa in samu na biyu sai in basu, sun yarda da buƙatata, amma suka kafamun sharaɗin cewa dik ranar da na buɗi baki na sake yin maganarsu ko na faɗi wannan yarjejeniya da muka yi ga wasu to Blood Power zai dawo cikin zuri'ar Abdul Malik, dan Abdul Malik shi ne sarki a Blood power, ba da son ransu ma suka kashe shi ba, ba yadda suka iya ne, ruhanin tsafi na buƙatarsa shiyasa suka yi hakan, dan ya karya masu doka ya gagara sanya ɗansa ni kenan in bada jini, dan haka idan na kawo ƴaƴana biyu da suka buƙata zasu shanye jininsu, sai su keramin makullin da zan rufe black door da mahaifina ya gina da kansa domin zuwa blood power, suka kara gargaɗana a kan kada na kuskura na faɗi wannan magana ga kowa, da zarar na faɗa to shikenan alkawari ya karye har sai na sake basu wasu ƴaƴan nawa, wanda a lokacin tin ban san zan haifi Omar da Aneesa ba suka nuna mun su cikin ruwan tsafi, suka ce a cikin ƴaƴan da zan haifa akwai waɗan nan biyun, kuma sun kwaɗatu da jininsu, in har na buɗi baki na yi magana zasu ɗaukesu daga gareni ne, shiyasa da Omerish ya nemi jin gaskiya hankalina ya tashi, dan bana son sake rasa ƴaƴana, na yi kuka tamkar zan yi hauka a ranar da na ɗauki jariraina guda biyu da kaina na kai masu, ina ji ina gani, ina tsaye a gabana suka ɗauki jaririn nan suka caka mashi wuka a tsakiyar maɗigar kansa, suka ɗaga kafafunsa sama jininsa ya zazzaga a kan wani gunki da ban san na mecece bane, amma dai halittar macece, haka jinin ya rinƙa zuba a kanta yaron nan yana ta hargagin fitar rai har ya yi sanyi, sai da jininsa ya dakata da zuba cak, sannan suka jefomun gawarsa suka ce in rike bari a kashe ɗaya sai a zo a haɗa mun makullin rufe black door da kashin bayansu, kuma a dokarsu ne dole sai ina tsaye a gabana za'a kashe yaran".
"Ba yadda na iya, dan na ceci zuri'ata na aminta da hakan, ina kuka tamkar karamin yaro haka suka kashe ɗayan jaririn a gabana suka sake jefa mun gawarsa, a can gida kuma na bari ana ta kukan yara biyu sun mutu, suka je suka binne gawar da Blood Power ta basu a matsayin yaransu, dan da na ɗauke yaran sun ajiye masu wata gawa ta karya ta yadda ba za'a gane ɗaukar yaran aka yi ba, dik wannan balain ina tsaye, haka ina ji ina gani wani kato mai kama da dodo ya zo ya karɓi gawan yarana da ko suna ban saka masu bama, a gabana yasa hannu ya ɓallo kasusuwan bayansu sannan ya yi jifa da gawarsu cikin wani rami mai zurfi dake wajen, ya wuce da kasusuwan izuwa wani ɗaki dan kera makullin Spender".
Ya dakata yana wani irin kuka mai taɓa zuciya wanda ita ma momma kukan da take yi kenan, Big Bro ya rungumeta yana ɗan jijjigata, Smart da Ramish idanu sun yi jajir tamkar wuta, sun ji tashin hankali yau.
King kuwa shi kaɗai yasan balain da ya gani a wancan rana, ya ga tsagwaran rashin imani, har yau idan ya tuna kuka yake yi tamkar ransa zai fita, a idanunsa yana ganin yadda jaririran nan ke magajin azaba suna wani irin jijjiga jininsu na zuba jajir da shi, kai wannan tashin hankali ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwarsa, ba zai taɓa yafewa sarkin Blood Power ba, kuma har yanzu sarkin yana a raye shi ke rike da karagar wajen bayan mutuwar King Abdul Malik.