← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 130

Sashe 54

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwance bisa gado ta yi ɗaiɗai tana danna waya, wutar ɗakin a kashe, chat take yi da su Omaid suna kara shirya mugunta. A hankali ta fara takawa har ta isa gaban bed ɗin ba tare da Sareena ta jiyota ba. Cikin sanɗa ta duƙo a ta kan gadon gefen side drawer tare da leƙo da kanta tana kallon screen na wayar da Sareena ke rike da shi, irin dai kana latsa waya aljana ta kawo maka jiyara haka.

Ai jin kamar mutum na kallon screen É—in yasa Sareena ta juyo a wani irin slow. Ai tana juyowa babu abin da ta gani sai fararen ido gulu-gulu. Wani irin ihu ta zunduma tare da zabura a miliyan ta yi jifa da wayar gefe.

Miƙewa tsaye Mahreen ta yi tare da cewa. "Idan kika motsa sai kin mutu". Na rantse yadda ta yi magana ba zaka taɓa zatan ita bace, saboda muryar gardawa ta yi.

Ai wani irin wiki-wiki da ido Sareena ta yi, a zuciyarta tana ambato sunan ALLAH, makoshinta sai sama yake yi yana kasa alamar tana haÉ—iyar yawu da kyar.

Laluɓar remote na lamp Mahreen ta yi ta kunnasa, take haske ya ɗan gauraye kusa da su, hakan ya baiwa Sareena daman ita ganin aljanar cikin fararen kaya. Ai wani irin tsorara ta sake yi, jikinta ya hau kerma, ta gagara ɗago ido ta kalli fuskar aljanar saboda tsoron abin da zata gani. Tsabar razana har fitsari ta saki a wandonta a wajen, idanu dik sun raina fata.

Dariya ne cike tab a cikin Mahreen, amma ta dake tare da cewa. "Ku bil adama bakwa jin magana sam-sam, musamman ma ku fararen fata da kuke nuna kun tsani bakaken fata, yanzu dik farinki kin kaini haske ne?". NI KUWA NA CE KE DA KIKE DA FARIN HODA YA ZA'AYI TA KAIKI HASKE FISABILILLAH?😸

NA RATSE MAHREEN ƳAR DUNIYA CE NA WUCE MISALI, KAI JAMA'A, YARINYA TA SANYA SAREENA FITSA A WANDO.

Jiki na ɓari, murya na rawa Sareena ta ce. "A'a ban kaika haske ba". Tana magana hawaye suna tsere a kan fuskarta.

Jinjina kai aljana Mahreen ta yi. "To mu jinnu da muka fiku haske kunga muna tsanar ku ne? Ku ku baku........

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
-------------------------------------------🔥♥️

ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥

Jinjina kai aljana Mahreen ta yi. "To mu jinnu da muka fiku haske kunga muna tsanar ku ne? Ko ku baku san mun fiku haske bane?".

Tsabar kerman da jikin Sareena yake yi yasa ta gagara yin magana, ga dai fitsari nan ta malala ta jika mattress da jikanta sharkaf.

"Bari ki ji in faÉ—a maki wani abin da baki sani ba, bakaken fata sun fiku daraja, ko baki san uban kowa baki bane? Baki san farkon halitta Annabi Adam (AS) baki bane ko? Ke kanki baka ce, yanayin weather ya canza fatarki izuwa fara, ko baki san haka bane?". Ta faÉ—a tana zaro mata idanu.

Gagara magana Sareena dai ta yi, baki ya rufe ruf. Sake gyara tsayuwarta Mahreen ta yi, wai irin ta gwada ita hegiyar nan, ta ƙara kausasa murya kafin ta ce. "Daga rana irin ta yau! Girmamawa na musamman zaki rinƙa yi wa bakar fata, dan ta fiki daraja, kina jina? Kuma ƴan Nigeria da kike gani babu irinsu a duniya, su kaɗai ne, kyautar ALLAH ne su, ki san da cewa sun fiku komai, yanzu maza ki faɗa tare da ni cewa bakar fata sune gaba da kowa kuma sune farkon halitta". Ta kai karshen maganar tana zaro wayar chaza da ta sanya a aljihunta kafin ta fito.

"Ba zaki faÉ—a cewa bakar fata ita ce gaba da kowa ba!". Ta faÉ—a a tsawa ce. Ai da sauri Sareena murya na kakkarwa ta fara in da in da tana kokarin tattaro kalmar da zata haÉ—a wajen cewa bakar fata ita ce gaba da kowa, sai wani irin uban gumi da take haÉ—awa tamkar wacce aka tsamo daga cikin ruwa, ta yi sharkaf, idanu duk sun raina fata, ta zama abin tausayi.

Hegiya Mahreen ban da dariya da take kokarin dannewa babu wani abin da take yi, ba komai yake bata dariya ba kuma face tana tina irin zane Sareena da zata yi yanzu.

"Ba..... Ba ..... Baka...... Ken .... Fa fa fata...... Sune a sama..... Da kowa". Da kyar waÉ—an nan words suka iya samun damar kubcewa daga bakinta suka fito, saboda tsananin tsoro.

Mahreem kuwa gyara tsayuwa ta yi tare da yin wani irin girgiza ta ɗaga kai sama, wai ita nan sarkin shaiɗau. "Sunana Falcama ƴar sarkin aljanu, babana na ji dani, ki sani dik in da zaku shiga a duniyar nan ina iya ganinku, idan na kara ganin kin wulaƙanta wata bakar fata ko da harararta kika yi sai jikinki ya gaya maki! Ƴan Nigeria sun wuce da saninku, ba sa'an yinku bane! Yanzu ma ki kwanta ki mike flat, ki datse idanunki, ko me zai faru kika kuskura kika buɗe ko kika yi ihu mutuwa ta wajaba a kanki!"..

Tuni cikin Sareena ya kara É—urar ruwa, ta yi danasanin nuna kiyayya ga su Zee, yau ta ga bone. Mahreen dai ko a gefen kafarta, so take ta zaneta ko bulala biyar wai dan ma kada Sareena ta É—auka wasa take yi mata.

"Dan ALLAH kada ki kasheni, wlh zan rinƙa son bakaken fita har gaishesu zan rinƙa yi". Sareena ta faɗa cikin in da in da.

"Ai sonsu dama ya wajaba a kanki tin daga yau, yanzu ni ba kasheki zan yi ba, amma da zarar kin sake aikata wani kyara ga yan Nigeria nan ne zaki mutu!!". Babu wasa a tattare da Muryar gardawar da ta yi, da gaske take yi!.

Kara yin tsuru-tsuru da ido Sareena ta yi, tsawa Mahreen ta sake daka mata a akan ta yi gaggawar kwanciya kafin ranta ya ɓaci. Ai ba shiri Sareena ta kwanta flat tare da datse idanunta tana wani irin kuka mai ban tausayi. Mahreen ba tausayi babu imani yarinyar nan ta ware wannan igiyar chaza ɗin ta daddage ta tsulawa Sareena a gadan bayanta.

Wani irin azaba da Sareena ta ji ne yasa ta sanya hannu ta toshe bakinta, saboda wani irin kuka da ya so kubce mata. Ko kaÉ—an Mahreen bata damu ba, ta sake daddagewa ta tsula mata, zafafan hawaye Sareena ta shiga yi, har wani jijjiga jikinta yake yi saboda azaba. Amma Mahreen bata kyaleta ba sai da ta shinfiÉ—a mata bulalu goma daidai, dik jikin Sareena ya yi ruÉ—u-ruÉ—u ya yi jajir abinku da farar fata.

A walaƙance Mahreen ta ce. "Da bakaken fata ne yanzu jikinsu lahiya lou yake saboda sun fiku qualities, tashi ki fara frog jump yanzun nan". Ta faɗa tana zazzaro mata idanu.

Ba shiri Sareena ta miƙe tamkar zata mutu yarinyar nan, sai hakuri take baiwa aljana Mahreen amma yarinyar nan taki sauraronta, ta ce ta yi frog jump kafa dubu yanzu a nan. Sosai Sareena ta rinƙa gamata da girman ALLAH a kan ta yafe mata, amma Mahreen ta ce idan bata yi kafa dubun nan ba zata mutu.

Jin haka yasa Sareena ta daddage ta tattaro dikkan sauran karfin da suka rage mata ta fara frog jump ɗin nan babu kama hannun yaro, sai da Mahreen ta barta ta juyo daga wajen kofa ta nufi wajen toilet sai ta lallaɓa ta fice waje da gudu abinta ta bar Sareena sai frog Jump take yi tana cauting, ita a dole zata yi kafa dubu, idan bata yi dubu ba zata mutu.

Tana fitowa daga É—akin ta baro part É—in abinta, bata zame ko'ina ba sai family part, ta so zuwa É—akinsi Chuchu dik da take auntynta mai goya mata bayan, amma da ita aka zagi Æ´an Nigeria, so ta so haÉ—awa da ita ta É—auki fansa, sai dai kuma ta tuna Jawad yana nan, ba kowani namiji bane mai tsoron aljanu, kada asirinta ya tonu, dan haka sai ta ce bari ta je wajen Aneesa kawai, ta yafewa Chuchu tin da dama bata zagi Æ´an Nigeria sosai ba, kuma ko ba komai bata nuna tana kyamansu ba, kunga ita take yi wa Mahreen É—in ma kwalliya wani lokaci, ita ta koya mata wasu abubuwan ta wayar mata da kai.

Mahreen and Mahnoor fararen fata ne, but kowa yasan hasken Nigerians da waje akwai banbanci, dik hasken É—an Nigeria idan ya shiga cikin masu jajayen kunnuwa baki yake zama, shiyasa suke yi masu kallon bakake.

Zata wuce part na Mama wajen Aneesa sai ta hango door nasu Omaid a buɗe yake, nan ta tuna cewa sun taɓa yi mata rashin mutumci, dan haka yau ranar ɗaukar fansa ce, dik wanda ya yi mata ba daidai ba yau zata ɗauki fansa, hakan yasa ta ce bari ta fara shiga wajensu.

Kai tsaye babu ko tsoro ta nufi room É—in. A hankali ta shige ciki. Ga mamakinta sai ta ga mutum É—aya ne a kwance a saman bed É—in yana barci, bata iya banbanta su, hasalima ko sunayensu bata sani ba, dan haka bata san wanene daga cikunsu bane, shin wanda ya ce sai ya kakkaryara ranar ne ko ba shi bane, wato Obaid kenan, kun san shi ne mai saurin É—aukan zafi kuma shi ne ya ce sai ya kakkaryata Omaid ya ce ya yafe mata.

Aikuwa bata sani ba Obaid É—in ne yake kwance yake barcin, Omaid yana can garden yana hirar soyayya da wana school mate É—in nasu.

Kashe wutar É—akin nasu ta yi sai ta kunna masu lamp dan tsabar kokari irin nata. A dede kayin bed É—in nasu ta zo ta tsaya ta yadda Lamp É—in nasu zai haskata da kyau su ga aljana.
Chapter 54 · 0% Book details