Sashe 94
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanunta sun cicciko da kwallah na jin Pretty ta kirasa da sunan husband ta juya da gudu ta nufi waje, wani irin kukan takaici ne ya kubce mata. Shi kuma Smart ya rungumi Æ´ar tsanarsa yana zuba mata ruwan albarka tare da rarrashi, rigima ta hau zuba mashi kan ita bata yarda yana kula wasu ba, rarrashinta ya fara yi cikin so da kauna game da alkawarin ba zai sake kula wata ba.
-------------------------------🔥
Suna shiga room ɗinsu ta kai hannu ta saƙalo wuyansa, raɗa ta fara yi mashi a kunne, da sauri ya juyo da kallonsa a kanta, kaɗan ya motsa lips ɗinsa wajen cewa. "To faɗa in ji". Make mashi kafaɗa ta yi game da cewa. "Saukeni to tin da mun zo ɗakinmu". Ba musu ya sauketa ƙasa, saman bed ɗinsa ya nufa, zama ya yi yana binta da kallo from head to toe.
Ganin hakan yasa ta koma saman sofa ta zauna shiru tana satar kallonsa, ɗan bakin da ya rinƙa zuba mashi shagwaɓa ɗazun kawai yake bi da kallo. Dik sai ta ji ta takura da kallon nan da yake yi mata, dan haka sai ta ce. "Big Bro in je wajensu Mahnoor?". Ta faɗa tana ɗago da kallonta a kansa..
Banza da ita ya yi tamkar bai ji ba, sau uku tana faɗa tana karawa, amma dik tamkar bai ji ba, da ta ga ba zai amsa ba sai ta miƙe ta dawo kusa da shi, a gefen bed ɗin ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Please Big Bro ka yi magana mana, In je wajensu Aunty Mahnoor?".
Wani irin kallo ya bita da shi wanda sai da yasata haɗiyar yawu mai wuyan wucewa, in a cool way sosai ya ce. "Kada ki sake kirana da Big Bro". On a serious note ya faɗa. Mamaki ne yakamata na jin abin da ya faɗa, ɗan zaro mashi idanu ta yi kafin ta ce. "To da wani suna zan rinƙa kiranka?".
Banza da ita ya yi tare da gyarawa ya kwanta. Ganin hakan ya yi matukar tayar mata da hankali, sai ta matsa kusa da shi dab, tamkar mai raɗa cikin natsuwa ta ce. "Please ka faɗa mun ka ji?". Idanunsa a kan ɗan bakinta ya yi shiru bai yi magana ba, for almost good 5 mins, da ta ga bashi da niyar sake yin magana sai ta miƙe zata bar wajen idanunta na ciccikowa da kwallah.
Tana miƙewa ya riko hannunta, da sauri ta juyo, ya bari sai da ta juyo sannan ya jawota jikinsa gabaɗaya ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa. Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke, hannunsa ya ɗaura a saman bayanta, face ɗinsu na fuskantar juya, ai take suka kashe juna da wani irin sanyanyayyen musulmin kallo mai narka zuciya.
"Wani suna kika kirani da shi a parlo?". Ya faɗa ta hanyar motsa laɓɓansa kawai ba tare da wata sauti ba. Dama tin ɗazun ta gane me yake nufi, kawai so take ya furta da bakinsa ya ji daɗin sunan ne, shiyasa ta nuna tamkar bata gane nufinsa ba.
Harararsa ta É—an yi cikin wasa, muryarta a sanyayye ta ce. "Ni ba zan cigaba da faÉ—a maka wannan suna ba har sai ka faÉ—a mun gaskiyar yadda ka É—aukeni". Da iya gaskiyarta ta yi maganar. Ta faÉ—i haka cike da tsammanin abin da zata ji daga bakinsa mai daÉ—i ne, sai dai kuwa da buÉ—ar bakinsa sai ya ce. "Matsayin sister É—ita kike mana".
Ajiyar zuciya ta sauke tare da yunkurawa ta bar jikinsa, bai dakatar da ita ba, ta koma saman sofa ta zauna, daga karshe ta kwanta tare da jawo bargo, tin daga wannan lokaci kalmar A bata sake haɗasu ba, ta daina kulashi, wunin ranar bata fita ko parlo ba, kuma bata ci abinci ba, ko da Momma ta tashi ta sanya aka kirata, ta zo ta ɗauka mashi abinci, ba musu ta je ta ɗauka ta kawo mashi room ɗin, ta wuce ta kwanta, ba yadda bai yi da ita ba a kan ta zo su ci abinci, amma tai mashi rantsuwa da ALLAH ba zata ci ba, dik da haka ya yi ƙoƙarin tursasata amma sai ta tirje, dole ya hakura ya kyaleta, yana ji yana gani ta wuni kwance saman sofa, sallah ɗai ke tada ita.
Bawan ALLAH dik ya shiga damuwa, hankalinsa ya tashi, amma sai ya daure ya kawar da kansa har yamma, ya ga da gaske take zata iya cutuwa da yunwa fa, around 5 na yamma haka ya ji bafa zai iya jurewa ba, ko breakfast bata yi ba, bata ci lunch ba, ga yamma ta yi, fitowa ya yi ya nufi room na momma domin ya É—auko mata abinci da kansa. Ai yana fita ta tashi ta rufe kofar É—akin da key, da sauri ta afka toilet.
A gurguje ta yi wanka, ta dawo ta tsala shirinta cikin wandon jeana baki da top fari, ta yi mugun kyau, ta gyara gashin kanta tare da zuba turarruka a jikinta. Sai da ta gama komai kafin ta koma ta buɗe door ɗin, sannan ta koma saman sofa ta kwanta hada jawo bargo ta lulluɓa tamkar bata motsa ba. Ta kuwa yi saa hatta kammala komai bai shigo ba, ya tsaya magana da momma, sannan ya sanya ne a girka mata sabon abinci, sai ya zauna zaman jira, sai rarrashin momma yake yi yana faɗa mata babu abin da zai faru, King zai wastsake, dan ma sun kara mashi da alluran barci ne sabida suna san ya samu cikakken natsuwa sosai, dan kwakwalwarsa ta taɓu sosai, hankalinsa ya tashi na tina baya, ace a gaban idanunka a yi wa ƴaƴanka biyu irin wannan kisa, ƴaƴan da ko suna baka raɗa masu ba, ya zakaji, ku kwatanta da kanku, idan kune a wannan lokaci ya zaku ji? Kunga dole king yana buƙatar hutu sosai ai, in ba haka ba sai a samu gagarumin matsala.
Sai around 5:50PM suka kammala shirya mashi abincin, abin da bai taɓa yi ba a rayuwarsa wai ɗauko kayan abinci, sai ga shi da kansa ya ɗauko ya nufi room ɗinsu, kamar momma zata ce mashi ina Sweetie ta zo ta ɗauka mana, sai kuma ta yi shiru dan kada ta tambayo wani abin, a cewarta tin da yake neman abinci a yanzu ba lokacin cin abinci ba to da walakin goro a miya, kila wani abin ya yi wa Sweetie, tina hakan yasa ta ce. ALLAH ya bata jika daga ɓangarensu da wuri, dan zataso su su fara samun baby kafin kowa a gidan, dama King Zuhair bashi da jika ko ɗaya, to zata yi fatan Big Bro ya fara basu jika, daga karshe ta yi addu'ar ALLAH yasa yaron yazamana mai irin gashin Sweetie, dan ita kanta momma gashin ya tafi da ita!.
Lokacin da ya turo kofar ya shigo sai da ya ji gabansa ta É—an amsa, a hankali ya dakata ya É—an shaki kamshin dake tashi a É—aki har da lumahe idanu kafin ya wuce ya nufi in da suke ajiye abinci. Bayan ya ajiye ya nufo sofar da take kwance.
Yana zuwa ya tsugguna a gaban sofar, a natse yasa hannu ya yaye bargon nata. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kara shakar kamshinta yana É—an lumshe ido. Sanyayyar voice É—inta mai daÉ—in saurare ne ya daki dodan kunnensa, amma cikin masifa ta yi maganar.
"Me zaka wani buɗe mun bargona? Ba nace babu ruwanka dani ba?". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa zaune.
Hannunsa yasa ya riko nata, can kasan makoshi ya ce. "Zo kici abinci".................. Kwace hannunta ta yi. "Ai tin É—azun nace maka ba zanci ba ko? Please ni ka rabu dani".......... "Wai meyasa kika zama rigimammiya ne yanzu? Meyasa kike fushi haka?". Da alamar damuwa a kan fuskarsa ya yi maganar....... Da hannu ta yi pointing É—insa kafin ta ce. "Kai ne sila ai, kome na zama kai ka ja".
Pointing kansa ya yi shi ma kafin ya ce. "Ni kuma?". Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "To me na yi?"......... Harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Nima ban sani ba". A kufule ta faɗa, ya fahimci ranta a ɓace yake, dan haka sai ya sake riko hannunta, yana shirin yin magana kenan ya ji muryarta ta katse shi da cewa.
"Ni dai nasan a baya baka taɓa faɗar abin da ba gaskiya ba, baka iya faɗar kishiyar gaskiya ba, but yanzu dik ka canza".............. "Me na faɗa wanda ba gaskiya ba?". Yana ɗan matsa yatsunta ya yi maganar......... "Abin dake cikin zuciyarka, wlh kishiyar gaskiya ka faɗa". WATAU SWEETIE AKWAI HANKALI, BA ZATA CE YA YI KARYA BA, SABIDA HAR YANZU TANA BASHI GIRMA DIK FAƊAR DA ZASU YI!.
"E gaskiya kika faÉ—a, ban faÉ—i sirrin dake raina ba, but ai na ce ki gano da kanki kamar yadda na gano naki, koma me ya faru ke kika matsa mun kika sakani faÉ—ar ba daidai É—in ba". Ya kai karshen maganar yana riko jelar gashinta da hannunsa É—ayar.
"To ai ni na faÉ—a maka ba zan iya gane komai ba, kawai ka faÉ—a mun"....... "Omaish meyasa kike son jin sirrin dake zuciyata wai?"......... "Sabida ka ji nawa nima, shiyasa nike son jin naka".
Ɗan kwanto da kansa a saman laps ɗinta ya yi, yana cigaba da ɗan murza jelar gashinta ya ce. "Kina son kureni Omaish"......... Shiru ta yi tana sauraronsa ba tare da ta ce komai ba, kallonta a kan dark black hair ɗinsa dake ta faman sheƙi.
"To zan faÉ—i sirrin dake raina, but in na faÉ—a tukuicin me zaki bani?". Ya yi maganar yana É—ago kansa ya kalleta. Lallausan kumatunsa ta shafa kafin ta ce. "Mekakeso?"........ Shiru ya É—an yi kan ya amsa da. "Zan faÉ—a maki, amma ba yanzu ba, kawai dai ki yi alkawarin zaki bani dik abin da na tambaya".
Mancewa ta yi da zai iya tambayar komai sabida ba addini ne da shi ba, ga kuma zumuÉ—in son jin menene sirrin dake ransa ta amsa mashi da. "Na yi alkawarin bayarwa". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya matsa dab da kunnenta, cikin raÉ—a ya ce. "Me kike tsammanin ji daga gareni?".