← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 130

Sashe 49

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wani irin zafa ya damko wuyar rigar Smart da karfi, a fusace with harsh voice ya ce. "Dama kasan daddyna yana a raye? Dama kasan da cewa yana nan shi ne ka ɓoye mun? Me haɗinku da mahaifina? Ka kira shi yanzu ko kuma in kasheka!!". BABBAR MAGANA!!

Zazzaro mashi ido Smart ya yi. "Waye daddyn naka daga cikinsu?".

Wani irin zazzafar mari ya sakarwa Smart a kumatu har sai da Smart ya ga wasu taurari sun gilma ta cikin idanunsa. "Kafi kowa sanin waye ne, meyasa zaku ɓoye mahaifina ku musanya mun shi da wancan da kuke ikirarin shi ne babana? Dama nasan cutar dani kuke son yi shiyasa kuka yi kutse a cikin rayuwata, dan haka ko ka kira mahaifina yanzu ko in kasheka!!". Yana magana yana wani irin huci mai firgitarwa, tamkar zai kama da wuta.

Smart ya gama hasala ya zo har wuya, saboda bai san me Big Bro yake so da shi ba kuma, dik wani abin da yakamata ya yi mashi ya yi mashi, to bai san me kuma yake so ba yanzu, ga shi abin takaicin ma bai san waye Big Bro É—in ya gani ba da yake ikirarin shi ne mahaifin nasa ba, sannan ga shi ya ragargaza wayar bare ya sake kiransu ya ji da waye Big Bro ya yi magana last ko fuskar waye ya gani last.

Wani irin shaƙa da Big Bro ya yi masa ne yasa ya ji tamkar ana zare ransa, hakan ba karamun fusata shi ta yi ba, da karfi yasa hannu bibbiyu ya hanƙaɗe Big Bro, sai dai ko motsawa Black Tiger bai yi ba, ba ƙaramin fusata zuƙatansu dikkansu biyu ya yi ba, sun yi mugun harzuƙa, cikin fushi shi ma Smart ya damki wuyan Big Bro, cikin tsananin zafa ya ce. "Who the hell you are da zaka rinƙa mun abin da ka ga dama ina shanyewa?! Kamar yadda kake ji da kanka kowa ma haka yake ji, do you think that ina tsoronka ne yasa nike binka a yadda kake so? Ko ɗaya, just kaunarka nike yi ba tsoro ba, shiyasa nike lallaɓaka, but ba zan cigaba da jurar abin da kake mun ba, you say that zaka kasheni ba, okey do it now!! Kill now if not ni zan yi abin da kake ikirarin in kasheka kowa ya huta, ka hana mun iyayena kwanciyar hankali, ka jefa mun su cikin zulumi da damuwa, dik kai kaɗai, who are you?!!". Cikin tsananin fushi Smart ya yi maganar! Da alama yau ran maza ta kai kololuwar ɓaci!.

Shiru Big Bro bai yi magana ba, sai wani irin huci da yake yi, sai da Smart ya kai aya, sannan ne ya dakarkare ya É—aga Smart sama ya yi jefa da shi sama bed ya mirgina ya faÉ—i kasa.

"Where's my father? Dik surutun da kake yi ba shi ne damuwata ba, ka kira waɗan nan iyayen naka su dawo mun da daddyna if not sai na tashi gabaɗaya masarautarku, kuma idan ko kwarzane ya taɓa jikin daddyna sai na karar da dikkan zuri'arka, ba zan bar ko guda daga zuri'arku ya cigaba da shakar numfashi ba!!".

Ya yi maganar tare da nufo Smart gadan-gadan. A wannan karon da yake Smart ma ya kai kololuwa wajen ɓacin rai, sai ya miƙe cikin fushi ya nufo Big Bro. Faɗa suka fara gwabzawa tamkar wasu mayunwatan zakuna, babu imani babu tausayi suke jibgar junansu tamkar ba jini guda ba ne su. Big Bro yana tambayar ina mahaifinsa, Smart ya fitar mashi da mahaifinsa, shi kuma Smart yana faɗin waye mahaifin nasa a cikin uncle's ɗin nasa?.

Dik kansu dai babu wanda ya saurarawa É—an uwa, dik suka jiwa kansu muggan raunika, sannan dik suka yi watsa-watsa da É—akin, dik wasu glass sai da suka ruguje shi, gabaÉ—aya sun yage kayan jikinsu, sai wani huci suke yi suna wani irin buga kirazansu yadda kuka san ba mutane ba.

Harta bed na Big Bro basu bari ba, suka watsa komai, yadda kuka san yakin badar aka yi a cikin wannan ɗakin, harta curtains sai da suka ɓaɓɓale suka zubar, yau Smart ya yi alkawarin idan Big Bro bai bada kai ba shi ma ba zai bayar ba, sai dai su kashe kansu, saboda ya zo har wuya, ga shi babu mai rabasu, Pretty tana barci, su Ronnie basa nan, abin dai ya munana matuƙa, dan Smart ya samu rauni a wuya na glasa da Big Bro ya caka mashi a gefen wuya, ta fasa wajen sai jini ke malala, shi kuma Big Bro a gefen ciki Smart ɗin ya caka mashi glass ɗin, shi ma jininsa nata malala, abin dai ba kyan gani sam-sam.

Wlh yadda kukan duwatsu ne jikinsu ba tsoka da jini ba, haka suke jibgar juna. WA KUKE TINANIN ZAI IYA RABA WANNAN FAÆŠAR? UHM NI DAI NA JUYA GABAS DA YAMMA KUDU DA AREWA BANGAN SA BA! AMMA BARI IN JE CROWN OF JUSTICE IN DAWO KILA MU YI DACEN SAMUN MAI RABA WANNAN BALAIN FAÆŠAR!!.

CROWN OF JUSTICE.🔥🔥

A firgice ta farka daga barcin nata game da zunduma wani irin ihu mai sauti wanda ya sanya shi gaggawar juyowa, dama yana tsaye ne a gaban mirror yana gyara kyakkyawan hairnsa irin na Sweetie, ya fito daga wanka É—aure da towel white a waist É—insa.

Cikin zafa ya nufeta, hayewa saman bed É—in ya yi tare da rikota yana faÉ—in. "Hoonaira lafiya kuwa?".

Bata yi magana ba sai kuka da take yi tana wani jan dogon numfashi da karfi-karfi. Ya fahimci mummunar mafarki ta yi, hakan yasa ya rungumeta sosai a jikinsa, a natse ya fara karanto addu'oin tsari daga shaiÉ—anu yana tofa mata.

Tin tana ihu har yazamana ta koma kuka a hankali-hankali, daga karshe ma sai ta yi tsit alamar ta samu natsuwa. Ajiyar zuciya ya sauke, can kasan makoahinsa ya ce. "Hoonaira are you okey now?".

Tana daga kwance a kirjinsa ta gyaÉ—a kai alamar e, sai kuma ta ce. "Meyasa ka tafi ka barni?". Cikin muryar kuka ta yi maganar. "Am so sorry, amma ban je ko'ina na barki ba, ina a tare dake".

Cikin kuka ta ce. "Ka tafi mana ka barni, ba ga shi wannan Udey É—in ya zo zai kasheni ba". Wani irin zaro idanu waje ya yi, da sauri ya maimata sunan. "Udey! Kuma ya zo zai kasheki? For what reason?".

Mafarki ta yi a kan laɓen da ta yi ranar tana jin hiran Udey da Zarina in da suke cewa basu bane iyayen Hoorain, kun tuna wannan rana? To shi ne ta yi mafarkin wai asirinta ya tonu Udey ya ganota shi ne ya biyota zai kasheta.

JAMA'A KU CE ALLAHU AKBAR, WATO IDAN KA YARDA DA ALLAH KA HUTA, YANZU GA SHI CIKIN RUWAN SANYI ALLAH YA SANYA TA KAMA SUNAN UDEY A BAKINTA, WANDA HAKAN ZAI SA SHI KANSA HOORAIN YA FARA ZARGIN UDEY KO DA BAI BAYYANA A ZAHIRI BA, KUNGA DAGA NAN ZAI FARA SAKA MASU IDO.

Zabura ta yi ta buÉ—e idanunta da suke jajir saboda barci da tsoro. "Mafarki na yi wai ka tafi ka barni shi ne na bika da gudu, ina sauka staircase na haÉ—u da Udey sai ya kamani wai zai kasheni tin da na ji sirrinsu, kuma ni ban ji komai ba".

Tin da ta fara magana zuciyarsa ya shiga zargi da tinani, yasan Zunaira bata karya, bugu da kari tana da hankali sosai, me zaisa ta yi mafarkin Udey, dik da yasan mafarki ba gaskiya bace, kuma tana zuwa a kowacce siga, and kawo sittin cikin ɗari ba gaskiya bace, amma akwai mutanen da ALLAH ya zaɓa bayan manzanni waɗan da yake gwada masu ayoyi a cikin mafarki. Tabbas akwai wata a ƙasa. Amma sai ya basar da cewa. "Sharrin mafarki ne kawai, jeki yi wanka ki zo ki shirya mu je mu yi breakfast".

Ya yi niyar yi mata dabara ta faɗa mashi wani sirri nasu ta ji, amma sai ya ce bari ya kyaleta zuwa dare idan suna cikin yanayin farinciki zai mata dabara, dan a ransa yasan wlh ba haka kawai ta yi mafarki Udey ba, dole ta shiga gonarsu ne, akwai abin da ta sani, lokacin guda ALLAH ya jefo mashi tinanin matsa mashi da take yi a kan ya buɗe tsohuwar fada, shiru ya ɗan yi, yanzu ya fahimci Zunaira ta san wani abin, kawai ɓoye mashi take yi, amma soon zai gwada mata fifikon shekaru!.

"Ni dai my hero ba zan iya zuwa toilet ni kaÉ—ai ba, ina jin tsoro, sai dai muje a tare". Cike da tsantsar sonta a ransa yasa hannu ya fara shafa kanta. "Kin yarda in rakaki É—in?".

Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e, dik a tsorace take, tana wani irin haÉ—a uban gumi tamkar wadda ta yi tsere da dawakai a cikin tsakiyar rana mai zafi.

"Amma fa idan na rakaki fitowa zan yi ko?". Cikin zolaya ya yi maganar. Da sauri ta girgiza mashi kai. "A'a zaka tsaya sai na gama wanka".

Ɗan leƙo fuskarta ya yi. "Da gaske ba za'a ji kunyata ba?". Kai ta gyaɗa mashi kafin ta ce. "Da wando a jikina zan yi wankan ai". A shgwaɓe ta yi maganar. "An taɓa yin wanka da wando ne?". Kai ta jinjina mashi kafin ta ce e.

"To shikenan tashi muje". Make mashi kafaÉ—a ta yi. "Ni dai ka É—aukeni da kanka ka kaini". Cikin zolaya ya ce. "Bani da karfi fa".
Duka ta kai mashi a damatsan hannunsa. "Wannan fa menene?".

Ɗan rankwafowa kanta ya yi, a kunne ya yi mata raɗan da ya sanyata zabura ta miƙe zaune tana fuskantarsa. Da sauri ya yi kasa da kansa yana faɗin. "Iya wannan karfin nike da shi ban da na ɗaukarki".

"My hero an lalata mun kai, yanzu ka dawo baka da kunya sosai". Ta faÉ—a tana turo baki. Bai yi magana ba kawai ya yunkura ya sauko kasa, sannan yasa hannu ya É—auketa cak suka nufi toilet.
Chapter 49 · 0% Book details