← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 130

Sashe 86

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan rungumo Abbon Hoorain ya yi tare da ɓoye kansa jikin Abbon wai ya ji kunya. Muryar Kamran ce ta katsesu da cewa. "Ba fa irin forest da kuka sani bane, wajen yana da nisa da wancan masarauta da suka kwace Pretty, sannan kuma ragwaye basa iya zuwa wajen, mutuwa zaku yi da namun dawa, ko da yake kai naga kana da jarunta tin da ka iya faɗa dani". Ya yi maganar yana pointing Hoorain da hannunsa. BALAIN LALLAI KAMRAN YA RAINA SU ABBO, WAI JARUMAI NE SUKE ZUWA FOREST, SHI FA YANA GANIN BABU WANDA YA KAISA JARUMTA, SAI DAI KAI RENON LIONESS MAMMARSA.

Babbar magana, zaro idanu Hoorain ya yi, dan kuwa yasan in kuwa haka ne wajen yana da mugun nisa, shi yanzu Kamran bai san a takamamman in da yake bane, amma wlh forest É—in da nisa, in dai ta kingdom of power ne kuma to ai forest guda É—aya ce a wajen wadda take a tsakanin masarautu biyun ta zame masu kamar border, kuma ita ce forest da ya tsinto Zunaira a ciki, idan zai iya tina komai daidai matar da ya taimaka har yake ganinta tamkar ya san fuskarta sabida kama ta jini da ta so yi da shi, to tabbas ita ce kenan? Ye jefi kansa da tambaya.

A fili ya ce wlh ita ce, har sai da su Abbo suka É—ago suna kallonsa. Kamran ne ya ce. "Ita ce wa?". Hararar Hoorain ya wurga mashi. "Kai baka gajiya da faÉ—a da zafin zuciya ne?". Hoorain ya tambayi Kamran.

ÆŠaure fuska Kamran ya yi kafin ya ce. "A haka aka reneni na zama mafaÉ—aci". Ya faÉ—a a faÉ—ace yana zarewa Hoorain idanu tamkar zai dakesa!.

"To yakamata yanzu kasan ni yayanka ne, ka rinƙa tausasa harshe a kaina, ba zan juri komai daga gareka ba, ɗaga maka kafa kawai nike yi"........... Ɗan taɓe baki Kamran ya yi. "Me kuma yaya?". Ya tambaya on a serious note, dan har ga ALLAH shi bai sani ba. Ɗaure fuska tamau Hoorain ya yi alamar ransa ya ɓaci, dan yana ganin tamkar manna mashi hauka Kamran yake yi, bai san iya gaskiyarsa yake faɗe ba, zai yi magana Abbo ya rigasa da cewa.

"Hoorain dole ka ajiye zafin zuciyarka gefe idan kana son ku shirya da É—an uwanka, ka bisa a hankali saboda wlh iya gaskiya yake faÉ—a maka bai san komai ba"........ Shiru Hoorain ya yi yana É—an jinjina kansa alamar haka ne.

Shi kuma Kamran ya bisu da ido dan ba wani jin larabcin nan yake yi ba, suna ɓadda harshe suna magana su barshi a duhu, su kuma sun saba ne da magana da larabci shiyasa, take tinanin Rockey ɗinsa ta faɗo a ransa, ALLAH sarki ya yi wa Rockey wayau ya gudu ya barsa a forest, dan yana son ya je ya taimakawa Mammarsa kada a barta da kewa ita kaɗai.

Haka suka cigaba da tattaunawa Hoorain na kokarin kai zuciyarsa nesa dan su sasanta da Kamran, Abbo na ta kara tausan zukatan zakunan dikka biyu dan a samu sasanci da fahimtar.

--------------------------------🔥

CROWN OF POWER.🔥

Kuka sosai Sweetie take zubawa, dan takaicin hanata zuwa wajen su Mahnoor ɗin da ya yi, a dik mutanen da Sweetie take haɗuwa da su babu wacce ta so ta kaunata kamar Mahnoor, a tashin farko ta so Mahnoor matuƙa, saboda kyawawan halaye da saukin kanta, sannan tana jin daɗin yin hira da ita, amma kawai ya zo ya wani hanata fita, dole ta ji haushi.

Slowly ya tsuggunna a gaban sofar da take, yana sanye da wandan Jeans irin rippet É—in nan launin light ash, sai round neck polo shirt ita kuma fara tas, ya yi balain kyau sosai, ya fito a ainahin balarabensa, sai tashin fitinannen Kamshi yake yi.

A hankali ya kai hannunsa ya yaye bargon da ta lulluɓa har kanta. Sai da ya ji kirjinsa ta buga ganin yadda take ruwan hawaye, dama ya zargi hakan shiyasa ya ce bari ya dubata. Ita kuwa wani irin mugun harara ta dalla mashi kafin a kufule ta ce. "Me ruwanka dani to?". Yadda ta yi maganar ba karamin narka zuciyar Big Bro ta yi ba, ya kurawa ɗan bakinta idanu, wasa-wasa ta fara koyan mahaifa yarinyar nan, har da su murguɗa baki.

"Ni ka daina kallona kuma ka rufa mun bargona". Cikin faɗa da kuluwa da haushi ta yi maganar. Kun san halin mutumin, shiru ya yi bai yi magana ba har na tsawon mintuna 3, ranta ne ya kara ɓaci ta yunkura zata tashi kenan ya yi gaggawar rikota, in a cool way sosai ya ce. "Meyasa kike kuka?".

Ai tsabar bakinciki da takaici bata san lokacin da ta ce mashi. "Ban sani ba, wai ina ruwanka da rayuwata ne?"....... "Akwai ruwana da rayuwarki sabida rayuwarki tawa ce". Ya faɗa a sanyayye sosai, wanda hakan ba karamun kara tunzura zuciyarta ya yi ba, sai ya rinƙa nuna kamar baya fahimtar abubuwa dan rainin wayau, yana nufin bai san meyasa take kuka bane da zai wani tambaya!.

Zazzaro mashi idaunta da suka yi jajir ta yi, tamkar zata cinyesa da masifa ta ce. "Rayuwata ba zai taɓa zama naka ba, ni yanzu ma na fasa bana buƙatarka matsayin yaya, Ronnie kawai ya isheni, a gida ina da Kamran, bayan shi kila ina da wasu, bana bukatarka kuma!". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin kwace rikon da ya yi mata, sai dai ta gagara, domin kuwa karfi ba ɗaya ba.

Tin da ta yi wannan magana ya fahimci ranta ya kai kolokuwa wajen ɓaci, bata da raina manya, tana kuma tauna magana kafin ta faɗa, ya yi mata uzurin cewa bata cikin hayyacinta ne. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik yadda kika ɗauki abin bai kai haka ba, amma ban san me zan ce maki ba, please stop talking about Kamran or some mens here in a front of me, dan bana son kara maki ɓacin rai kan wanda kike ciki, am trying to control my self, be patient please".

Tin da ya fara magana ta natsu take sauraronsa, watau sorry ne ba zai taɓa ce mata ba bayan shi da kansa yasan ya yi mata ba daidai ba. A ranta ta kuduri niyyar sai ta santa wannan ɗan bakin nasa ya furta sorry a gareta, dan haka sai ta shammacesa sai da ta bari ya saki jiki ta kwace rikon da ya yi mata, da gudun gaske ta miƙe zata nufi waje.

Aikuwa yana miƙewa taku ɗaya ya yi ya capko waist ɗinta, bata ankara na sai jinta ta yi a saman lion chest ɗinsa, wage baki ta yi zata zunduma mashi ihu ya yi zafin sanya hannunsa ya toshe mata baki da hannunsa ɗaya. Mutsu-mutsu ta fara yi tana son kwace kanta, sai dai ina ta kasa, shi kuwa shiru ya zuba mata ido har sai da ta gaji da kanta ta natsu tsit a jikinsa.

Sai da ya ga ta natsu tana ruwan hawaye ne ya zame hannunsa daga bakinta, a sanyayye sosai ya ce. "Please Omaish, stop doing all this, kada ki bani wahala kisa in gagara controlling kaina a kanki". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga bakinta gabaÉ—aya.

Cikin kuka ta ce. "Ni ba zan zauna da kai a ɗakin nan ba, ALLAH komawa ɗakinsu Mahreen zan yi, tin da ni na sadaukar da farincikina don in faranta maka, na yarda zan zauna da kai a cikin ɗaki matsayin ma'auratan boge, amma shi ne kake ɓata mun rai, ka sanyani kuka ka kunsa mun bakinciki bayan ni farinciki kullum nike sakaka".

Tin da ta fara magana ya yi shiru yana kallonta har ta kai karshe, sannan ne in a cool way sosai ya ce. "Menene na yi wanda bai yi maki ba zan gyara? But kada ki ce zaki rusa abin da muka shirya, kinga ina kokari cika dik promise dana ɗauka maki, kin ce kada na taɓaki and na yi hakan, komai kika ce am trying my best to force myself in yi hakan because of your happiness, ban san me kike so ba kuma".

Yanzu ta gama fahimtar bafa zai ce mutum ya yi hakuri ba, sai dai ya ce zai daina yin abu, lallai ma shiɗin nan. Tana shessheƙa ta ce. "Ai na ce ka faɗa mun sirrin dake zuciyarka kaki faɗa mun, dan haka ina fushi da kai".

ÆŠan kura mata idanu ya yi, slowly ya matso da face É—insa dab da nata tamkar zai yi mata wani abin, can kasan makoshi ya ce. "Me kike son sani to?". Tana turo baki ta ce. "Ai kasan abin da nike son ji"......... Slowly ya sake kai É—an bakinsa har kamar zai sumbace nata, suna iya jiyo numfashin juna suna kuma shaka. "Omaish kin san sirrin dake raina fa, but why kike wahalar da kanki?".

Ganin lips ɗinsa zasu iya taɓa nata ne yasa ta yi gaggawar janye kanta baya kaɗan. "To na ji shikenan saukeni". "Kin huce? Baki fushi dani kuma?". A natse ya tambaya. A fili ta gyaɗa mashi kai, amma a cikin zuciyarta ita kaɗai tasan abin da ta shirya mashi, dan ta ce ba zata kyalesa ba. Sauketa kasa ya yi tare da ɗan janyota jikinsa, sai da ya goge mata hawaye tsab sannan ya saketa. Hannunta ya riko zuwa saman sofarta, ya saketa a wajen ya nufi saman bed ɗinsa, zai zauna kenan suka ji hayaniya mai karfi daga main parlo yana tashi, kallon juna suka yi kafin ta ce. "Hayaniyar me haka kuma?".

Alama ya yi mata da hannu a kan bai sani ba ba tare da ya yi magana ba. "Mu je mu gani". Ta faÉ—a tana É—an zare idanu. Kai ya girgiza mata alamar ba zai je ba, ya haye gado zai kwanta kenan ta ce mashi. "Big Bro voice É—in Ronnie nike ji, tamkar da shi ake hayaniyar fa".

Ai fasa kwanciya ya yi, bai ma san time da ya miƙe ya nufo waje ba. Da sauri ta rufa mashi baya, kai tsaye suka nufi in da suke jiyo hayaniyar.
Chapter 86 · 0% Book details