← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 130

Sashe 102

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan zaro idanu Sweetie ta yi kafin ta ce. "Bakinciki kuma?". KADA KU MANTA SWEETIE TANA JIN LARABCI DAN MOM ÆŠINSU NA YI MASU KAFIN TA RABU DA SU.

Jinjina kai Aneesa ta yi kafin ta ce. "E mana bakinciki". "Wani irin bakinciki to?". Sweetie ta tambaya. Gyara zama Aneesa ta yi kafin ta hau kora mata bayanin cewa Sharifa na son Big Bro, kuma suna can suna shirin yadda zasu samu soyayyarsa, daga karshe ta ce. "Amma kada ki damu ni zai taimaka maki wajen tayaki mu rushe dik shirin da suke shiryawa".

Siririn murmushi Sweetie ta yi kafin ta ce. "Macen da bata cika mace bace take tsoron wata aba wai kishiya, ai ko mata É—ari ne zasu ce suna sonsa ba zan damu ba, dan nasan waye shi kuma na yarda da kaina, ba dik kai zasu iya kishi dani ba ai, dan in ina waje ma kallon namiji zai yi wa mata, dik mai sonsa ta zo zan yi mata hanyar zuwa wajensa, amma ta shirya likkafani, dan ciwon zuciya ce zai kasheta, ni ai bazasu iya dani ba, saboda soyayyar da na tanadawa mijina wlh ba ma zai iya kula kowace mace ba ko ance ya kula". With her full confidence take maganar, irin ita zata narka zuciyar Big Bro da kauna ba zata baiwa wata space na shiga ba. SAI DAKE SWEETIE MAI BAKACITY!.

Tin da ta fara magana suka tsareta da ido har ta kai karshe, ajiyar zuciya dik suka sauke, Pretty ce ta ce. "Ke wlh ban san yaushe kika zama haka ba, daga yin aure kin zama yar iska, yanzu ko kunyata baki ji kike faÉ—in kashe zuciyar bawan ALLAH da soyayya ko?".

Harara Sweetie ta dalla mata kafin ta ce. "Ni shiyasa bana son yin magana idan kina waje, bari ma in tafi, mom ta baki amanata amma yanzu kin daina kula dani sai faɗa". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin sauka daga gadon. Da sauri du Aneesa and Chuchu har suna haɗe bakin cewa. "A'a zo ki bamu sirrin, irin wannan karfin hali da yarda da kai haka? Zoki bamu gaskiya".

Kasa ta sauko kafin ta ce. "Idan wannan mai manya-manyan idon ta tafi zan zo mu sha hira da safe". Tana kai karshen maganar ta watsa da gudu dan tasan Pretty ba barinta zata yi ba. Aikuwa yunkurawa Pretty ta yi zata kamata É—in ta ga ta gudu, kwafa ta yi da cewa. "Zaki zo hannu ne".

Aneesa ce ta ce. "Za'a bamu sirri kin koran mana ita". Siririn tsaki Pretty ta ja kafin ta amsa da. "Ai sai ku bita"...... Da yake su suke son abu sai suka lallaɓa suka ja baki suka datse, daga nan suka miƙe suka fita, Chuchu ta nufi ɗakin mijinta, ita kuma Aneesa ɓangaren mama, to suna zuwa ne King ya yi kiran wannan gaggawa, suka tafi room ɗinsa, baya na ɗan dawo dan in faɗa maku zuwan Sweetie wajensu, yanzu mu cigaba!.

Abinci ta je ta É—auka masu ta nufi room É—insu da shi, tana zuwa ta ajiye abincin ta haye bed É—insa ta kwanta, dan ta gaji da kwanciya a saman sofa. Kunna tv ta yi tana kallon film É—in larabawa har barci ya fara É—aukarta. Sai around 10:30 ya dawo É—akin. A lokacin ta kashe light na É—akin ta kunne dim, haske kaÉ—an kaÉ—an ne.

Shakar kamshin perfume ɗinta ya yi kafin ya kariso ciki, bai yi tinanin tana saman bed ɗinsa ba, sai da ya matso dab ya ganta. Da sauri ta sauko ƙasa tana ce mashi. "Ina ka je ka tsaya tun ɗazun yunwa nike ji?"........ Shiru ya yi har sai da ya zauna a gefen bed ɗin kafin ya amsa da. "Wajen daddy".

Wucewa ta yi ta nufi wajen abincin tana faÉ—in. "Zo to mu yi dinner, cos I'm feeling hungry"........ Kai ya É—an girgiza. "Ki yi kawai, I'm okey".

Ai saka mashi shagwaɓa ta yi a kan lallai sai ya zo sun ci, bashi da zaɓi dole ya mike ya zo, zuba mashi kaɗan ta yi dan tasan da daddare baya cin abinci sosai, ta tura mashi a gabansa kafin ta zuba nata. Kafin ya ɗauki spoon sai da ya miƙo mata kwalin wayarta. Cike da zumuɗi ta karɓa, haba wani irin murna ne ya bayyana a kan fuskarta, fasa ɗaukar spoon ɗin ta yi, jikinta na rawa ta hau buɗe wayar, like wow wayar ta haɗu over to over.

ÆŠagowa ta yi ta kallesa sai taga ya É—auki spoon yana cin abinci kuma yana kallonta. "Thank you so much King of my heart". Ta kai karshe tana sumbatar wayar. ÆŠan lumshe idanunsa ya yi, dan ji ya yi tamkar shi ta sumbata. Da hannu ya yi mata nuni da ta ci abinci dare na kara yi, kada ta zo taci ta kwanta ya yi affecting É—inta.

Rungume wayar a kirjinta ta yi ta É—auki spoon, ta É—ebo abinci zata kai baki kenan sai ta ga ya kai hannu ya zare wayar daga kirjinta ya ajiye a gefe. Kasa-kasa ya ce. "A kan me za'a ajiye shi a muhallina?".

Ta gane nufinsa, watau ta rungume waya a kirjinta bayan muhallinsa ne wajen, ai ajiye spoon É—in nata ta yi, tasa hannu bibbiyu ta rufe fuska tana murmushi. "Kai king of my heart, ka sakani na ji kunya fa"......... Hannu ya kai ya buÉ—e hannayen nata tare da É—ebo abinci a spoon É—insa ya sanya mata a baki, can kasan makoshinsa ya ce. "Ki ci abinci sosai ki kara girma dan iya jure mun".

A yanzu ma ta fahimci me yake nufi, hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Uhmmm ALLAH ya kaimu lokacin aurenmu, zan tina maka wani abin"............ Jinjina kai kawai ya yi tare da cewa. "ÆŠauki wayar ki saka a chaji". Da sauri ta É—auka ta je ta jona sannan ya dawo ta zauna.

Sake ɗebo abincinsa ya yi ya kai mata baki yana satar kallon tula-tulanta da suke yi mashi kwalele, da ya zo kwace wayar ne ya ja mata wuyar riga tai ƙasa suka bayyana, ji yake tamkar ya kai hannu ya taɓasu saboda tsabar kyansu da ɗaukar ido, shi kaɗai yasan me yake ji a halin yanzu.

Muryarta ce ta katse shi da cewa. "Ba zan yarda da wayanka ba, kana ta tura mun abincinka zaka sanya in kasa cin nawa, kai kuma kaki ci ko?"...... Shiru ya yi saboda ta ganosa, so ya yi dama yai mata wayau ta cinye abincin nasa dikka, dan baya son ci, shagwaɓar da ta zuba mashi ta narka zuciyarsa ne yasa ya zo ci.

Kin sake karɓar abincinsa ta yi, ta ce kowa ya ci nasa. Dole ba dan ya so ba ya rufe idanu ya cinye, ita ma ta cinye nata, miƙewa ya yi ya ɗauketa cak sai toilet kamar ɗazun. A yanzu brush ɗaya ya ɗauka ya zuba kayan goge baki. A bakinsa ya fara sanyawa ya goge kafin ya ɗago haɓarta suna kallon juna ta cikin mirror ya sanya mata brush ɗin, a hankali ya goge mata baki tsab kafin ya ɗauraye masu da ruwa. Kamar yadda ya ɗaukota ya kawota haka ya ɗauketa ya fita da ita. A tsakar ɗakin ya sauketa ya wuce saman bed ɗinsa.

Sai da ya kwanta ya jawo bargo sannan ya ce. "Idan zaki kwanta ki É—auki wayarki mu yi chat". Ya faÉ—a tare da kara jan bargon sama. Kai ta jinjina mashi kafin ta wuce ta tattare kayan abincin dikka ta yi waje da su. Ta gyare wajen tsab sannan ta nufi saman sofa, har zata kwanta ta tuna da wayarta, da sauri ta É—aukota ta dawo ta kwanta.

Kunna wayar ta yi haÉ—e da jawo bargo, ga mamakinta sai ta ga wayar da sim card harma da su Whatsapp, bata yi magana ba sai ta ja bargo har kanta ta rufe, da yake in baku manta ba tana danne danne a wayar Ronnie so yasan abubuwa da dama, kai tsaye ta shige Whatsapp. Sai da ta shiga ta kunna data, aikuwa tana kunnawa sai ga sakonsa ya shigo, dik da bata da tabbacin shi ne ta yi farinciki, tasan da wuya idan wani yana da wannan number.

Duba chajin wayar ta yi sai taga bata yi chaji sosai ba, dawo da kallonta kan sakonsa ta yi, dik da bata iya karatun turanci sosai ba ta karanta Queen of my heart da ya rubuta, murmushi ne ya kubce mata. Sai yau ta fahimci matsa mata da Ronnie yake yi a kan karatu, ga shi ya amfaneta, a cikin ranta ta ce ALLAH ya yi wa Ronnie albarka, ya dake sosai wajen ganin ta iya reading, ga shi kuma ta iya, dama shi karatun Arabic ta iya sosai.

"King of my heart". Shi ta rubuta ta tura mashi. "Na yi zaton zaki bani hot kiss na barci amma baki bani ba". Abin da ya sake rubuta mata kenan. "Idan muka yi aure sai ka gaji da shi". Amsar da ta mayar mashi kenan.

"Ina son mu koma birninmu domin mu yi wannan auren dai in huta". Murmushi sosai ta yi kafin ta ce. "Nima ina son hakan". Ta faɗa mashi ne dan ya yi farinciki kuma ya samu barci mai daɗi, amma ta kuduri niyyar faɗawa momma gaskiyar komai idan ta kara gina soyayyarsu kafin ya tada batun komawa, shiyasa yanzu kuka ga tana biye mashi, tana tsoron ya ce ba zai musulunta ba ko zai rabu da ita, dalilin da yasa take shiga jikinsa dan gina soyayyarsu da katangar karfe wanda ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba ko da ance dole ya musulunta.

"Smiling yana maki kyau over, zan samu ganinsa kafin in yi barci?". Abin da ya sake turo mata kenan. "Me zai hana kai da mallakinka, ni fa taka ce". Ta tura mashi....... "In dai da gaske kike yi ke tawa ce to zo mu kwanta a nan". Shi ne amsar da ya bata....... Jim ta ɗan yi tana tinanin amsar dayakamata basa, dan wlh ba zata je ba, tab ba wannan magana, kuma bata son ransa ya ɓaci, magana mai taushi take son faɗa mashi dan ya samu barci mai mugun daɗi, to meyakamata ta ce mashi kenan? Ta jefi kanta da tambaya.
Chapter 102 · 0% Book details