← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 130

Sashe 74

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu Sweetie ta rufa mata baya. Har lokacin yana cikin toilet É—in yana tikar amai sosai, ciki momma ta shiga, ita kuma Sweetie ta tsaya a tsakiyar É—akin tana kai komo tamkar wadda aka ce mata mom É—inta ce a icu.

Almost 5 mins da shigar momma cikin toilet ɗin sai gasu sun fito a tare tana rike da hannunsa, har fuskarsa ta yi jajir saboda wahala, da wuya idan ya taɓa yin amai irin haka a rayuwarsa. So mugun wasa, Sweetie bata san lokacin da ta isa gabansu tana faɗin. "Meyasaka yi amai? Meyafaru?".

Momma mace mai fahimta, sai ta riko hannunta tana faÉ—in. "Babu komai, kada ki damu babu abin da ya same shi, abincin namu ne bai yi mashi ba, bari in yi wa mom Omerish magana tana nan zata girka maku irin abincinku, dan dik tafiyar abincin naku kusan iri É—aya ne, zan sa a kwashi waÉ—an nan yanzu".

Sai a lokacin Sweetie ta ji kunya ya kamata, da sauri ta É—an ja baya ta basu hanya tana wani yin kasa da kai. Nan ma momma ta fahimta sai ta ce. "Kadaki damu, na kara tabbatarwa da É—ana ya samu wacce ta dace shi, kuma wacce zata kula da shi sosai, ba shakka kina sonsa sosai".

Ƙasa ta yi da kai sosai, momma kuma ta saketa ta wuce gaba, a bakin bed ɗin ta zaunar da shi kafin ta ce mashi tana zuwa. Kai ya jinjina mata kallonsa a kan Sweetie, ya yi mamakin ganin yadda ta birkice sosai ta tashi hankalinta dan ya shiga wannan hali, ya kuma ji mugun daɗi over.

Momma na fita ta É—ago kai da kallonta ta sauke a kansa, sai ta ga ai ita yake kallo. A hankali ta motsa bakinta wajen cewa. "Sannu ya jiki?".

Shiru bai amsa ba kuma bai daina kallonta ba. Ganin hakan yasa ta wuce izuwa saman sofa zata zauna kenan muryarsa ya daki dodan kunnenta. "Momma fa tana dawowa". Ya faÉ—a tamkar ba shi ya yi maganar ba.

ÆŠan turo mashi baki ta yi. "To me zan yi kenan?". Tana kallonsa ta yi maganar. Da hannu ta nuna mata gefensa a kan ta dawo wajen ta zauna. Bata musa ba ta nufesa, zama ta yi tare da É—an juyo da kallonta a kansa. Haba take idanunsu ya sarkafe cikin na juna, har momma ta yi sallama ta shigo basu jita ba, sun lula wata duniyar da su kansu basu tantance a takamaiman wace duniya suke na, Mercury ne ko Jupiter, sun dai lula duniyar sama.

Ba karamin daÉ—i momma ta ji ba na ganin yadda suke balain son juna a tinaninta, sai ta ce ba zata katse masu jin daÉ—i ba, dan haka bata yi masu magana ba tasa kuyangun da suka biyota suka kwashe kayan abincin suka yi waje da su, ita ma ta rufa masu baya.

Ajiyar zuciya dikkansu suka sauke a lokacin da suka fuskanci mutum ya fita daga ɗakin, da sauri suka kai kallonsu kan hanyar fita, nan suka ga an kwashe kayan abincin, a hanzarce suka dawo da kallonsu a kan juna, mamakin kansu suka shiga yi ta yadda har aka shiga ɗakin aka fita basu sani ba, lokaci guda Sweetie ta saki murmishi tare da miƙewa tsaye ta nufi saman sofa. Shi ma kiƙewa ya yi ya nufi hanyar fita, bata ce mashi ko uppan ba shi ma haka ya fice daga ɗakin.

Bai zame ko'ina ba face room ɗin Smart dake kusa da shi, to shi da ba addini ba ina ruwansa da sallama, kawai ya tura masu kofa ya shiga. Manne da juna ya samesu, Pretty sai zuba mashi shagwaɓa take yi, sun ci sun ƙoshi abinsu, Smart na kwance saman bed daga shi sai doguwar wandon pj's, ya cire rigar, ita kuma Pretty ta kwanta a saman lion chest ɗinsa tana kuka wai sai ya yi mata kwalliya, bafa a fuskarta zai yi kwalliyar ba. A'a a fuskarsa zai yi ta ga ya zai zama, wai yana da kyau a haka ma, amma idan ya yi kwalliya sai ya fi kyau, rigimar da take ta yi mashi kenan yaki kulata, shi ne take ta faman jan mashi dogon hanci.

A karo na farko yau sai da gaban Big Bro ya faɗi da ya gansu haka, a ransa ya shaida shi ma yana buƙatar irin wannan rayuwa, sannan yana son mace mai balain shagwaɓa da son jiki irin Pretty, ita Pretty idan Smart yana waje bata taɓa zama bata manne mashi a jiki ba, kun tuna ita da Kamran a Forest saboda shegen son jiki ba haka take lafe mashi a jiki ba? To haka take ita, Big Bro yana son hakan sosai, shiyasa Pretty take burgesa, ba dan haka ba ma ranar da ta daki Sweetie da wlh ba zai barta ba, sai ya hukuntata, amma saboda yana fatan ta koyawa Sweetie waɗan nan ɗabi'un nata yasa ya ɗaga mata kafa ya yafe.

Hannu Smart ya É—aura a saman bayan Pretty kafin ya ce. "Big Bro akwai wani abin ne?"......... Harara ya dalla mashi kafin ya ce. "Zo ka rakani waje"....... Cike da mamaki Smart ya ce. "Waje kuma?".

Shiru bai amsa ba, bashi ma da niyar sake yin magana, dawo da kallonsa a kanta Pretty ya yi kafin ya ce. "To tashi mun a jiki bari in rakasa waje".

Baki ta É—an turo. "Idan ka dawo zaka yi kwalliyar?". Kai kawai ya gyaÉ—a mata, É—an bakinta ta kai ta manna mashi sumbata a kumatu kafin ta mirgita ta sauka daga kirjin nasa ta koma saman gadan. Dik abin da suke yi Big Bro yana kallonsu, shi ma dai yana ta kara kwaÉ—ayin irin wannan rayuwa tasu.

Bargo Smart ya ja ya rufa mata har zuwa wuya, sannan ya sumbaci forehead ɗinta kafin ya sauko kasa. Rigarsa ya ɗauka ya sanya, dik Big Bro yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa. Smart na zuwa gabansa ya ɗan kai mashi dukan wasa a kirji kafin ya ce. "Sistermu ta yi barci ne?".

Kai Big Bro ya É—an girgiza alamar a'a kafin ya juya suka nufi waje. "Mezaka je yi a waje?". Smart ya tambaya. Shiru bai amsa ba har suka hau elevator suka sauka kasa. Ainahin harabar kingdom É—in suka fito ba harabar family part ba. Tafiya suka fara yi suna É—an hira jefi-jefi Smart yana ta yi mashi bayanin dik wasu abubuwan da suka dace, dik in suka wuce waje sai ya yi mashi bayanin wajen. Shi dai shiru bai cewa komai ba.

Ai jin Big Bro ya fito yasa dikka su Sareena suka fito kallonsa, sai dai kuma fa har yanzu dik wanda ya kallesa sau É—aya baya iya maimaita na biyu a lokacin, Sharifat da ta kallesa ta ce to wlh ita yanzu shi take so ba Ramish ba, ta hakura ta barwa Leesharh Ramish.

Ita ƙuwa Sareena ta ce zata yi faɗa domin samun soyayyan ɗaya daga cikinsu, a ranta ta san Big Bro ko gawarsa ta fi karfinta, shiyasa bata ɗaurawa kanta azaba ba, bata fara abin da ta san ba zata iya ba, commond kallon sa sau biyu a lokacin guda basa iya yi to ina ita ina iya neman soyayyarsa? Ai ta ce da shi da Smart dik abu ɗaya ne, dan haka gara ta tsaya wajen Smart ɗin sai ya fi mata sauki. AI BAKIN RIJIYA BA WAJEN WASAN MAKAHO BANE SAREENA, WAYA CE MAKI BORNO GABAS TAKE? BIG BRO AI SAI DAI IYAYEN YARA, WANE KAN YARO.

Ita dai Sharifat ta É—ebo da zafi, ta ce yanzu Big Bro take so. Dik cikin Æ´aÆ´an King har da waÉ—an da suke uba É—aya da Big Bro babu wanda bai ji sonsa a ransa ba, dan shi É—in na daban ne, sai dai kuma babu wanda ya sawa kansa zai samu, sun dai bar son a ransu.

-------------------🔥

Sun sha kewaye sosai har aka fara kiraye-kirayen sallar mangariba, a nan ne suka nufo family part. Suna tafiya ne Big Bro ya hango side na uncle Abbas, murya a sanyayye sosai ya ce. "Wannan part na waye?". "For our uncle". Smart ya bashi amsa yana kallon Smart É—in.

Shiru Big Bro ya É—an yi idanunsa suna ganin masa abubuwan tsafi dayawa a cikin wannan part É—in, a ransa ya ce kenan suma a nan suna yin amfani da magic ne ko yaya?. Smart ne ya katse mashi zancen zucin nasa da cewa. "Meyasa ka yi magana a kan su Omaid É—azun?".

Shiru ya yi har sai da suka hau elevator sannan ya ce. "Akwai dalili, but not now zaka sani, yanzu dai ina Omar?"........... Shiru Smart ya É—an yi kafin ya ce. "I think yana room É—insa, da wani abin ne?"....... Kai ya É—an jinjina alamar e. Dawo da kallonsa a kansa Smart ya yi kafin ya ce. "Zan iya sani yanzu ko shi ma sai gaba?".

"E to kusan hakan, sai na san waye ya haÉ—a shi da wannan ciwo tukun nan, yanzu dai mu je ka bani wayarka na nan bari in yi magana".

Smart ya so tambayar wani ciwo kenan?. Sai kuma ya yi shiru, dan yasan ko ya tambaya ba samun amsa zai yi ba. Shiru suka yi har suka isa bedroom na Smart, ya É—auko waya ya baiwa Big Bro, a wajen Big Bro ya tsaya ya shigar da numbar da yake son kira.

Ana ɗagawa ya hau yin magana a natse cikin bada umarni. Shiru Smart ya tsaya yana mamakin jin kalaman ɗan uwan nasa. Umarni ya bada da a kwaso kayan aiki a cikin jiragensa, a zo a ginawa mahaifinsa palace ɗin da babu wani sarki a wannan zamani da ya taɓa mallakan makamancinsa, fitan da ya yi yanzu suka yi kewaye fili ya duba, dan haka ya samu ishasshen filin da yake ganin zasu isa a gida har da katafaren airport a cikin palace ɗin wanda jirage zasu iya sauka ko tashi, kun ga idan wani zai yi tafiya a family no need na zuwa airport.
Chapter 74 · 0% Book details