← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 130

Sashe 81

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Ramish ya ɗan yi yana tinanin ko dai babban yayan nasu likita ne? Amma kuma abubuwan da yake yi suna da al'ajabi da sanya mutum a ruɗani, ga shi da magana ɗaya, sannan yana jimawa kafin ya yi magana ɗayan, idan yana magana sai ka rantse da ALLAH saukar mashi da wahayinta ake yi, ba shakka akwai mugun ilimi a tattare da shi wanda kwakwalwar ɗan adam ba zata iya ɗauka a lokaci guda ba. TABBAS BAKA YI KARYA BA RAMISH, AKWAI ILIMI KAM, BIG BRO BA MUTANENEMA SUKA KARANTAR DA SHI BA, AMMA IDAN KUKA JI TARIHIN YADDA AKA YI YA BAR KINGDOM OF POWER ZAKU GANE ME NIKE FAƊE, DIK CIKIN KINGDOM ƊIN NAN A DAI BOKO BABU WANDA YA KAISA ILIMI, DOCTOR NE A ƁANGAREN KARATU BA AIKIN LIKITA BA, AMMA BA'A MAKARANTAR MUTANE YA YI KARATU BA, ABU ƊAYA NE BA'A TAƁA KOYA MASHI BA A RAYUWARSA SHI NE ILIMIN ADDINI, DAN ALJANNUN DA SUKA KARANTAR DA SHI DIKKA KIRISTOCI NE, HAKAN YASA YA TASHI DA SANI SOSAI A KAN ADDININ KIRISTIYANITI, YA SAN BIBLES ƊINSU DIKKA SOSAI, AMMA BASU BARI YASAN AINAHIN INJILA TA ANNABI ISA BA, DAN SUN SAN YANA DA BAIWA DA KAIFIN ƘWAƘWALWA TSAB ZAI GANE GASKIYA, DAN HAKA KO SU SMART BA ZASU GWADA MASHI ILIMIN BOKO BA, SAI DAI NA ADDINI, KUMA BIG BRO BA ZAI TAƁA YARDA YA MUSULUNTA BA SAI SUN RABASHI DA ABU ƊAYA ZUWA BIYU WANDA SU BA ZASU TAƁA ƊAUKAR ABIN DA MUHIMMANCI BA, SHIRI AKA SHIRYA MASHI A KAN HAKAN, SUN JUYA ZUCIYARSA TA YADDA ZASU YI AMFANI DA SHI DAN YAKAR ADDININ MUSULUNCI, DIK SABODA BAIWAR DA YAKE DASHI YASA SUKA ZAƁESA, ZAƁAƁƁE NE SHI. DAN HAKA IDAN ANA SON YA MUSULUNTA DOLE ZA'A RABASHI DA WASU ABUBUWA BIYU DA SUKA SANYA MASHI A JIKI BA TARE DA SANIN KOWA BA, DIK BA ZAKU GANE YANZU BA, SAI KING YA FARKA YA NEMI JIN A INA BIG BRO YA YI RAYUWA, IDAN AKA ZO MAI DA MAGANA MASU KAIFIN BASIRAR ZA SU IYA GANO MENENE AKA YI MASHI GUDA BIYU A JIKINSA DA ZAI HANA SHI MUSULUNTA HAR SAI AN RABASHI DA SU, DAN HAKA DIK ABIN DA BIG BRO ZAI YI A KAN ADDINI KADA KU GA LAIFINSA, BAI MA SAN YANAYI BA!.

----------------------🔥

Da sauri Ramish ya nufi saman bed É—in, a natse ya fara tofawa king addu'oi yana fatan ya farka cikin koshin lafiyarsa.

Bedroom na Momma Big Bro ya nufa, sai dai yana sanya kai zai shiga Smart na fitowa, karo suka É—an yi Smart ya ja baya yana kallon fuskarsa, hankali a tashe ya ce. "Ya jikin daddy?". ÆŠan lumshe idanu Big Bro ya yi alamar komai normal kafin ya ce. "What of mommah?".

"Alhamdllh ta samu barci da kyar, tana buƙatar hutu sosai"........... Ɗan jinjina kai Big Bro ya yi, a tare suka juya suka nufi waje, a parlon momma suka zauna suna tattaunawa kan abin da yakamata su yi, da kuma me mafita. Sai yanzu Big Bro ya san cewa to ai blood power da yake neman mallakewa ma tasa ce tun da gadon King Zuhair, da King ya gaji kayansa kunga yanzu Big Bro ne zai gajeta, dan kowa sai ya bar magaji saboda wajen ta cigaba da kasancewa da rai kada ta mutu, shiru Big Bro ya yi yana tinani.

Ni kuma na ce ya akayi matsafa dake blood power ba su suka reni Big Bro ba? Wanda ya renesa bashi da alaƙa da blood power, kuma a wajensa Big Bro ya fara ganin magic har ya ce zai koya kuma ya koya! Lokacin da King ya ki accepting blood power momma tana da cikin su Big Bro, tabbas a lokacin su sunga cikin, dama sun yi niyyar ko King bai aminta ba zasu ɗauke wannan cikin, yana daga cikin abin da yasa basu takurawa King ba, dan wajibi ne a kansa ya bada jini tamkar yadda da mahaifin su bobo yake yi in ba haka ba su sha jinin king ɗin, to basa dai son shan jinin King kai tsaye, saboda sun sha jinin ƴaƴan Abdul Malik ba sau ɗaya ba. (Kun ga which means King yana da borders kenan.)

Bugu da kari sun kwallafa ransu a kan cikin momma lokacin, shiyasa ma cikin ya gagari kowa, dan an yi yunkurin zubar mata da shi ya fi sau goma, bana faɗa maku sai dai ta yi bleeding amma cikin yana nan ba, to sun so Smart and Big Bro kamar zasu yi hauka, saboda miƙa wuya da King ya yi ya nemi sulhu ne yasa suka hakura da su (kunga a nan ma ya tabbata akwai wasu azzaluman a cikin gida kenan dake son cikin momma ya zube, kai akwai fa case, akwai wasu sauran rina a gaba sosai, yanzu bamu yi komai ba, sai wasu daga cikin labarin nan sun bamu waje za'a fara ainahin wasa! Dama gidan sarauta gidan rikici da munafurci, ga cin amana, kai komai ma ya tara!.)

Mai tsorata momma daban, kazalika wanda ya salwantar da rayuwar Big Bro ya bibiyi Smart dan kashesa shi ma daban ne, and wanda ya reni Big Bro shi ma daban ne, dik basu da alaƙa da Blood Power, shi blood power wani abin ne na daban, wanda kuma har yau har gobe a cikin ƴaƴan king suna balain son Big Bro and Smart, sannan suna son guyson and Aneesa, waɗan nan mutum huɗun sun gagara hakura da su, dannewa kawai suke yi dan kada su karya alkawarinsu da King Zuhair, sai dai kuma yau ga shi King da kansa ya karya alkawarin, kun sa kuwa akwai case, dan ba zasu hakura ba!!.

-----------------------------🔥

A yayin da Big Bro da Smart ke zaune suna tattaunawar neman mafita, su kuma su Sareena suna can suna shirya plan yadda zasu tafiyar da aikinsu, yanzu tin da Sareena ta gano cewa ai ba aljanar gaske bace, yi masu aka yi dan basu tsoro, shikenan ta koma shaiÉ—ancinta da ta saba, suna zaman meeting a side na Uncle Abba. Da ita, Omaid, Obaid and Sharifa. Suna zaune suna meeting É—in yadda zasu tsara komai.

Cikin nuna takaici Sareena ta ce. "Ni yanzu so nike mu fara wargaza soyayyar Yah Raj da wannan Zee É—in, dan idan ina ganinsu a tare tamkar in kashe kaina nike ji, na tsani ganinsu a tare, idan muka wargaza soyayyar tasu sai mu wargaza ba Yah Smart É—in".

Jinjina kai dikkansu suka yi, Omaid ya ce. "Jiya ma na gansu a parlon Aunty MieMie tana kuka yana rarrashinta, tamkar in naÉ—a masu duka na ji!!!".

Obaid ne ya capki zancen da cewa. "Haka ranar na gansu a garden ya rike mata hannu har da wani sunkuyowa kanta yana mata kalamai". Ya kai karshen maganar yana jan doguwar tsaki irin ransa bai so ba...... Sareena ce ta ce. "Dik ku bar faÉ—a mun kayan takaicin nan, yarinya kullum sanye da hijabi tamkar mai takaba, wlh na tsaneta, bata da sura mai kyau ne yasa kullum take sanya hijabi shegiya zata cuci yayanmu, sai an aura mashi ita ya yaye hijabin yaga bakomai..........". Da sauri Omaid ya katseta da cewa. "Ya ga gardi aka aura mashi matsayin mace ba".

Kai suka jinjina a tare, Sareena ta ce. "Ta ya za'ayi mu rabasu ne wai?". Omaid ne ya ce. "Wannan ai mai sauki ne, kun sa kishi a jininmu yake, dik wanda ya sanmu ya shaida wannan, to da shi zamu yi amfani wajen sanya Yah Raj ya tsaneta, shirya mata soyayyar karya zamu yi, a hankali mu ja ra'ayinta, idan ta kama mu É—auki hayan wani, mu biyasa makudan kuÉ—aÉ—e, mu bugar da ita mu kai mashi É—aki sai ya yi mana video da ita ba kaya, zan sayi sabon sim card in yi amfani dashi wajen turawa Yah Raj videon, kinga daga nan ko yar gold ce wlh ya rabu da ita kenan har abada.......". BALAIN CAN, LALLAI OMAID DA OBAID SUN WUCI TINANI NA, KAI KUN JI WATA SHARRIN DA SUKA SHIRYA? WAÆŠAN NAN YARA FA HAR YANZU KO 20 YEARS BADU CIKA BA, GASKIYA DOLE BIG BRO YA YI SHIRI A KANKU, DAN GABA SHARRINKU MUTUM BA ZAI IYA ÆŠAUKA BA!!.

"Irin wannan yakamata mu yi wa wancan shegiyar Pretty yar talakawa wacce ba'a san asalinta ba mu rabata da Yah Omerish". Cewar Sareena dake ta faman cika tana batsewa. Sharifa ce ta katsesu da cewa. "Wai dama ba'a san asalinta ba?". Kai Sareena ta jinjina. "Daga daji suka fito, a can Zunaira ta tsintota".

Taɓe baki Sharifa ta yi kafin ta ce. "Tab lallai wannan bata cancanci familynmu ba gaskiya, dole kam a fidda ita". Ran Sareena ya yi sanyi da jin wannan magana, dan haka sai ta ce. "Shiyasa na ce zamu yi mata irin na Zee". Ta yi maganar tana kallon Omaid.

Girgiza mata kai Omaid ta yi kafin ya ce. "Har yanzu Aunty Sareena baki san waye Yah Omerish ba shiyasa kike nufansa da kananan plan irin wannan, ai na rantse maki da ALLAH kina kuskura kika yi wa wannan Pretty É—in irin wannan plan É—in, idan bai kashe rabi da kwatan waÉ—an dake kingdom É—in nan a kokarinsa na gani waye muka saka ya yi mata hakan ba, ke wlh dik wani iya duniyancinki ki kalli Yah Omerish ki barsa a nan, idan kuma so kike yi mu mutu a lokaci guda kuma to, dan wlh idan ya gane ko bai kashemu ba ba zamu sake moruwa ba, kuma kin dai san ganewa kwana É—aya tai mashi yawa ya gano, tsab zai san plan ne tin da ita Pretty daga daji ta fito, so bata san kowa a duniyar mutane ba sai Auta, kinga kuwa yana gani zai san plan ne, Aunty Sareena kanki baya ja sosai shi ne matsalata dake!". Ya kai karshen maganar yana kaÉ—a kai irin bata san waye Smart É—in nan ba.
Chapter 81 · 0% Book details