← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 130

Sashe 68

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa tsaye Big Bro ya yi da ganinsu, take su Ronnie ma suka mimmike tsaye suna kallanta. A tsakiyar parlon Smart ya kawota tare da tsaidata saitin face ɗin Big Bro dake binsa da kallon kauna, sannan ne ya ce. "Momma are you ready?".

Kai kawai ta iya jinjina mashi, saboda jikinta ya rigada ya bata ga abin da zai nuna mata, ta ji cewa first love É—inta ne ya aminta ya biyosa. Slowly ya zame hannunsa daga kan fuskarta, ai a hanzarce ta buÉ—e ido kai tsaye kallonta sai kan Big Bro wanda shi ma ya dawo da kallonsa a kanta.

Ai bata san lokacin da ta matsa dab da shi tana ɗan blinking eyes ɗinta alamar tana son tabbatarwa da gaske ne ko mafarki?. Shi ma matsawa dab da ita ya yi ya bata hot hug sosai, lokaci guda ya ji wani irin tsananin kaunarta ya shigesa, bai taɓa sanin daɗin uwa ba, amma yau da ya rungume mahaifiyarsa ta ainahi sai yake jin tamkar a hannunta ya girma.

Guyson da ya gama ruÉ—ewa ne muryarsa na rawa ya ce. "Momma ya naga Yah Omerish ya zama mutum biyu?".

Omaid and Obaid dik sun tsaya sai zazzare idanu suke yi suna raba kallonsu a kan Smart and Big Bro, sun ruÉ—e, sai suke ganin kamar kansu ne yake juyawa kawai ai mutum É—aya ne. Jaish ma dai da ya gagara gane komai ne ya ce. "Yah Omerish wanene wannan?".

Dawo da kallonsa a kansu Smart ya yi. "Our Big Bro". Ai har suna haÉ—e baki dikkansu wajen cewa Big Bro É—insu kuma?. Jinjina masu kai ya yi alamar kwarai kuwa. ÆŠago kai daga jikin Big Bro momma ta yi tare da yi wa su Smart alamar da hannu a kan su zo. Da sauri suka karisa wajenta, nan fa ta haÉ—esu waje guda ta rungume sosai a jikinta, suma dikka rungumeta suka yi cike da kauna.

Almost 5 mins suna a haka kafin momma ta sakesu ta É—ago da kallonta a kan Big Bro, idanunta sun cina tab da kwallah, suna haÉ—a ido kwallar nata ya zubo kan kunatunta. Hannu Big Bro yasa ya hau goge mata hawayen nata kafin ya ce ta daina kuka please.

Daidai lokacin King ya shigo cikin rashin kwarin jiki, kana ganinsa kasan bashi da lafiya. Da mamaki yake ta faman binsu da kallo, wani irin farinciki mara misaltuwa ne ta bayyana a kan fuskar king, dik da ba'a faÉ—a mashi ba yasan cewa Smart ya yi nasarar dawo mashi da first love É—insa ne.

Da kallo É—aya Big Bro ya yi wa king ya ji wani irin azabbaben sonsa ya kama shi, hakan yasa ya matsa kusa da king ya rungumosa a jikinsa yana jin tamkar wani part na rayuwarsa ne king, tamkar kuma sun daÉ—e suna rayuwa ba yanzu ba.

Smart ya ɗan yi mamakin ganin yadda Big Bro ya karɓi King, saboda yasan Big Bro da kaifin basirar iya gane mai laifi, a saninsa kuma King bai yi masu adalci ba, amma meyasa Big Bro tashi ɗaya ya yi na'am da shi?. Ya jefi kansa da tambayar da bashi da amsarta, hakan yasa ya matsa shi ma kusa da su, dan King sai yi mashi alama da hannu yake yi a kan ya zo ya haɗesu ya rungume please.

Da sauri ya je ya faÉ—a jikin king yana sauke ajiyar zuciya, su Jaish dik suka tafi jikin King suka rurrugumesa suna murna. Nan ma almost 5 mins suna rungume da juna kafin Big Bro ya zare jikinsa, sai É—aya bayan É—aya suka zare jikinsu. Smart ne ya taimakawa king izuwa saman sofa ya zauna, sannan ya umarci kowa da ya zauna.

Da sauri suka zazzauna, momma ta zauna a kusa da King, Smart and Big Bro suka zauna a sofa guda, Obaid and Omaid sofa guda, guyson zai tafi wata sofar Smart ya matsa mashi tsakaninsu shi da Big Bro ya ce ya zo ya zauna a nan. Sai a lokacin Big Bro ya É—ago ya kalli guyson, ai da kallon farko ya ji wani kaunar yaron nan a ransa. NI KUWA NA CE JININKU DA HALINSU IRI ÆŠAYA AI DOLE KA SO SHI.

Hannu ya kai ya shafi kan guyson, can kasan maƙoshinsa ya ce. "Menene sunanka?". Har yanzu kallon mamaki guyson yake binsa da shi ya amsa da. "Sunana Omar". Omar Big Bro ya maimaita sunan, daga haka bai sake yin magana ba, ya ɗago kai da kallonsa unexpected sai kan fuskar Sweetie dake sharar kwallah.

Kuma ita ma shi take kallo, a wannan karon dai sai ya gagara zare kallonsa daga cikin nata, yanayin yadda yake kallonta tamkar wanda ya ga bakuwa daga wata duniya, ita kuma kallo mai kama da harara take binsa da shi alamar haushinsa take ji.

Sun jima suna kallon juna har King ya c bari a kira family dik su zo, shi Big Bro bai ji ba yana ta faman kallonta, dik hankalinsa ya tashi na ganin yadda damuwa sosai ke kwance a cikin idanunta, sai ya kara jin tausayinta ya kama shi.

One by one family suka fara shigowa cikin parlon, kowa ya shigo sai ya gwada ruɗewarsa a fili na ganin Smart ya zama biyu, sai sun natsu daga baya sai suka banbancin hasken fatar Smart da Big Bro. Sai dai lokacin da uncle Abbas ya shigo cikin parlon sai da Big Bro ya ji kirjinsa ta buga da karfi da ya gansa, sai yake jin tamkar ya taɓa yin rayuwa da shi a wata duniyar, kun san da yake ya mance da komai na duniyar shaiɗanu, so ya mance da dad ɗin nasa ma.

Shi kuma uncle Abbas sam bai nuna kamar ya san Big Bro bama, sai dai shi ma ya ruÉ—e sosai da ya gansu su biyu, sai tambayar King yake yi wai dama su biyu ne? A ina É—ayan ya girma to? Ko dai shi ma a Paris ne, dik ya damu sosai ya shiga ruÉ—ani.

Amma King bai ce da su komai ba har sai da family dikka suka gama haÉ—uwa exept irinsu Heleena, Zee da Mahreen waÉ—an da dai suka kasance ba Æ´aÆ´an King ba, dan har Uncle Taheer babu shi a wajen. Sai dai suka gama haÉ—uwa dukkansu sannan ne King ya sanar da su waye Big Bro.

Nan fa kallo ta koma kallon kallo a parlon, masu mamki suna yi masu murna suna yi, Maman Yah Ramish ta yi tsalle ta dire ta ce wlh ba zata yarda da cewa dik wanda aka kwaso sai ace mata É—an King bane, ba zai yiwu ba, anyi na Smart sun yi shiru, yanzu kuma a sake kawo masu wani! Ba zasu yarda ba, tana masifar tana kallon Momma, ko kaÉ—an bata yarda ta kalli Big Bro ba, dan wlh dik cikin parlon bayan momma da King babu wanda ya kalli Big Bro sau biyu, da kallo É—aya ba kari suke zare idanunsu.

Ai dik rashin kunyar Sareena sa É—aya ta kallesa bata sake ba, tana balain son kallonsa amma tsoro ya hanata, kun san idanun Big Bro ba daga nan ba a kaifi da razana mutum, wlh dik balain tsoro ya basu.

Shi kuwa tin da ya zauna a wajen kallonsa a kan Sweetie da ta yi kasa da kai bayan ta ga bashi da niyar daina kallonta, kun san idan ya kafeta da ido zai iya É—aukar mintoci masu yawa bai kyafta kallonsa ba. Jin sun fara surutu ne yasa kasa ta É—an fara juya mashi, ita kanta Sweetie juya mata kanta ya fara yi, basu saba da hayaniya ba, sai suka ji ina na zasu iya zama a wajen ba.

Momma ce ta ce. "To me kike nufi kenan da zaki ce ba Æ´aÆ´ansa bane?". Cikin tsananin takaici momma ta yi tambayar, da mama ta kure hakurinta, ta yi mata a kan Smart ta shanye, yanzu kuma so take ta sheganta Big Bro ne ko me?.

"Kin fi kowa sanin me kika kullah, amma dai ke kanki kin san waÉ—an nan ba Æ´an gidan nan bane, ke baki ga yanayin idanunsu bane? Wlh ba jinin gidan nan bane, kekika san in da kika kwasosu........". Tana magana tana hararar mommah.

Sai dai bata kai karshen maganar ba ta wani ci uban birki sakamakon miƙewa da Big Bro ya yi da nufin ya bar parlon, bai san a kan me suke tattaunawa ba, dan baya jin larabci, sun dai cika mashi kunne kawai zasu ja mashi ciwon kai.

A tinanin mama ya miƙe ne zai yi wata magana a kan maganarta, sai ta ga ya dubi Smart, in a cool way sosai ya ce. "Ba zan iya zama a nan ba, ina son waje so silent like gida, nan ya mun jama'a dayawa". ALLAH sarki bai iya zama a cikin mutane ba, ko da yake shi da ya girma cikin ɗaki yaushe zai iya zama da mutanen da suka wuci biyu zuwa uku, ai ba zai iya ba. Cikin harshen turanci ya yi maganar.

Hakan yasa dik suka ji abin da ya faÉ—a. Wlh dik cikin parlon nan ba wanda bai so Big Bro ya cigaba da yin magana kada ya dakata ba, saboda yadda sexy voice É—insa take, ga natsuwa sosai.

Smart da dama ya yunkura zai yi wa mama magana kenan Big Bro ya katse shi ne ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Momma baki da lokacinsu a yanzu, please muje part ɗinki". Smart ya faɗa yana maido da kallonsa a kan Big Bro. "Muje part na mommarmu babu hayaniya". Ya faɗawa Big Bro hakan.

"Kai ni wajen da wuri". Cewar Big Bro. Shi dai king bai iya ce masu komai ba saboda rashin kwarin jiki ga jinya, yanzu baya son ɗaga murya. Hannu Big Bro ya miƙawa momma a kan ta zo su tafi dan ya ga ta miƙe. Ba musu ta yi gaggawar matsawa ta rike hannunsa. Dik cikin parlon babu wanda ya sake iya ɗaga ido ya kallesa har Smart ya yi gaba suka rufa mashi baya shi da momma.
Chapter 68 · 0% Book details