← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 130

Sashe 93

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

WAI KUN SAN DA CEWA AKKA NA DA ƊIYA MACE? KING NA DA KANWA, UNCLE JAHIZ AUTA YANA DA SISTER, AMMA TA GIRMI UNCLE JAHIZ, DAN SHI KAM SHI NE AUTA, BARI DAI KING YA FARKA, LABARI BATA KARE BA, HAR YA SAMU LAFIYA ZAI FAƊA MAKU INA KANWAR TASU TAKE, SHI KAƊAI SAI AKKA NE SUKA SAN IN DA TAKE! LABARI ZAI BIYO TA KANTA!. MASU KOKARIN DOLE SAI SUN HAƊA DANGANTAKAR SU SWEETIE AND KINGDOM OF POWER KU KWANTAR DA HANKALINKU, TIN A BAYA NA FAƊA MAKU BASU DA ALAƘA, WAI KU BAKU GAJIYA DA KARANTA LITTAFI A KAN FAMILY GUDA NE? HABA MANA, KULLUM SAI A RINƘA WANI CEWA A'A IYAYENSU ƳAN UWA NE DA SAURANSU, AIKIN KENAN, TO NI DAI NA GAJI ATO, DAN HAKA STARS ƊINA BASU DA ALAƘA TA JINI SAI DAI TA SOYAYYA, KU KWANTAR DA HANKALINKU, KULLUM BURINA IN KAWO SABON SALO LABARINA YA BANBANTA DA KOWA AMMA KU BAKWA ZAMA WAYS😌

One by one mutanen cikin parlon suka fara watsewa, da kyar Sareena ta iya juyawa ta fita, saboda yau ta ga yadda ake soyayya da kirsa a in da ta dace, ta ga macen da ta cika mace mai iya juya zuciyar namiji kamar Big Bro, dik Æ´anmatan king sun raina kansu yau wlh.

Heleena na komawa bedroom ɗinta ta fara tambayar momma a ina ake ɗaukar small meals bari ta ɗauko, kwatance momma ta yi mata, da sauri ta fito dan ta je ta ɗauko, to kun san family part da wani mahaukacin girma, a garin dawowa ta ɓata hanya, sai shiga nan take yi ta sake fita, ga ginin iri guda ne, ruɗewa ta yi tana neman hanya har ALLAH ya faɗo da ita wani ɗan madaidaicin parlo.

Ta sha madarar mamakin ganin su Sareena a wannan parlo suna hira, dik Æ´an matan king suna wajen, harda su Mahnoor da Mahreen, ko sallama bata yi masu ba ta afko ciki, tana nan cikin wannan É—an ikka shiga nasu, ta wani riko plate a hannu, daga shigowarta ta hau dalla masu harara tamkar zata cinyesu da ido. Aikuwa gidanta ta zo, dan kuwa harara suka fara dalla mata suma.

Harta Aneesa dake rike da waya Yah Rizwan yana ta tsokanarta ta Whatsapp, wai dik basu iya soyayya ba, su je Sweetie ta koya masu yadda ake kula da miji, to dama a kule da haushi take kan kalamansa, sai ga Heleene ta zo tana banka masu harara, me kuke tinanin zai faru? Ai suma harara tamkar idanunsu zai faÉ—i kasa suka shiga dalla mata har sai da ta É—an sha jinin jikinta, sai kuma ta kalli Sareena kallon tsab kafin ta ce.

"Ke zoki wuce ki kaini part na Rahilarh"........... Kun san mom Smart haka take kiran momma da sunanta watau Rahilarh, to shi ne ita ma Heleena dan tabbatar rashin kunya da rashin hankali take kiranta haka, kunga gara mom Smart ai tinda matar yayanta ne, momma kanwar mijinta ne, ita kuma Heleena fa? Hmmmmm wai a haka kuma take son Smart ya aureta, tab ai Heleena kadama ki bari ya ji ga sunan da kike kiran mommarsa, dan jikinki ne zai faÉ—a maki.

Ai suna jin ta faÉ—i haka suka wani bita da mugun kallon da sai da yasa ta ji kirjinta ya buga, wai ita nan zata gwada masu isa, bata san nan gidan isa da Izza ta zo ba. Sake pointing Sareena da hannu ta yi kafin ta ce. "I'm i not talking to you?!".

Ai yadda kuka san da wall Heleena take yi, suka yi banza da ita. Ranta ne ya ɓaci, ji take tamkar ta matsa ta kama Sareena tai mata mugun duka, amma kuma ita kanta tasan ba zata iya ba, dan ba karfine da su ba, dan haka sai ta ce bari ta kira ɗaya daga cikin escort da suka rakota zuwa kingdom ɗin, securitynta kenan, bari ta kisa ya zane mata su. Sai kuma ta tuna ai kingdom ɗin nan ba irin kuci ku bamun masarauta bace, ba kowani yuyu ma yake shigowa family part ba, dan sun hana securitynta ma shigowa, ita kaɗai ta shigo, Kingdom of power suna da wani irin bahagon dokoki da tsare-tsare, basu ɗaukar raini ko wasa, babu wanda ya isa ya shigo family part ba tare da izinin king ba, sai kuma izinin momma, ko bako ɗan gida ya yi dole sai king yasan waye shi kuma daga ina yake, ba haka suke ba su, akwai dokokin da dolen uban mutum ya bi, in ma baka bi ba jikinka ne zai faɗa maka, so su basa ɗaukar wargi, ita kanta Heleena ɗin sai da aka nema mata alfarmar shigowa family part, dan sai da momma ta roki King sannan.

Tina hakan ne yasa ta jefesu da harara ita ma, ji take tamkar ta je ta shake Sareena, wai ni kam na ce ba, anya kuwa Heleena bata san cewa Sareena abokiyar takararta bace kan Smart kuwa? Naga tin da ta zo ta tsani Sareena ne, kuma ba wanda ta rainawa wayau irinta, dik yadda aka yi tasan kishiyoyi suke, to ni dai zanga ya wasan nan zata kaya.

Sai hararar su take yi, suma kuma harararta suke yi, yo su da kansu da kansu ma basu bari ba suna hararar juna bare wata bare, su kansu basu shirya ba, ga Aneesa nan tin É—azun take faman harararsu dan Rizwan ya ce su koma su koyi soyayya, su Chuchu yau dik hararan juna ake ta faman yi.

Daidai lokacin Omaid ya shigo cikin parlon dan ya faɗawa Sareena ga plan da suka shiryawa Pretty wanda ba za'a taɓa gane su suka yi ba. Yana shigowa ya bi Heleena da wani irin kallo kafin ya ce. "Wannan mai kama da snooker stick ɗin kuma daga ina?".

Sareena na harararta ta amsa mashi da. "Wai part na momma take nema shi ne ta zo ta tasamu gaba zatai mana rashin kunya".......... Harara Omaid ya wurga mata kafin ya ce. "Yana da kyau ita ma a gyara mata zama, yanzu dai Aunty Sareena zo mu je akwai magana".

My people anya kuna ganin lafiyar su Omaid kuwa? Dik tsoron da zasu ji baya hanasu sake yin abin da suka yi niyya, sam babu ja da baya a lamarinsh! Anya kuwa haka kalau suke kuwa? Gaskiya da alamar tambaya a lamarinsu, ku duba kuga yadda suka shiga tashin hankali da tsoro a lokacin da Big Bro ya daki Bilal, har suka natsu, amma yanzu har sun sake komawa ruwa, kai akwai matsala fa!.

Miƙewa Sareena ta yi tabi bayansa tana hararar Heleena. Ita kuwa tsayawa ta yi shiru tana tinanin yadda zata yi, tin da dik sun ki kulata. Da dai ta gaji sai ta tausasa murya, ta dubi Mahnoor da cewa. "Please ki kaini part na Rahilarh". Taga Mahnoor ce kawai fuskanta ya nuna mai saukin kai a cikinsu, shi ne ta yi mata magana.

Ba musu Mahnoor ta miƙe tare da wucewa gaba tana faɗin ta zo su je. Da sauri ta rufa mata baya suka wuce, da harara su Aneesa suka bita tamkar idanun zasu faɗo kasa suna jan dogon tsaki.

After 10 minutes.

Heleena ce ta fito rike plate of small meals daga room É—inta, sannan ta nufi room É—in da momma ta ce mata shi ne na Smart, dan kewarsa take yi, tin da ta zo basu haÉ—u ba sai É—azun da ta gansa a parlo, tana san zuwa su ga juna.

Excuse ta yi tare da tura door ta shiga. Yanzu ya dawo daga hospital, an gyarawa Ronnie wajen, ya fito daga wanka É—aure da towel a waist É—insa, Pretty sarkin mulki tana kwance saman gado tana binsa da kallo.

Gabansa Heleena ta zo tare da miƙo mashi plate ɗin tana faɗin. "Good afternoon brother". Bai amsa gaisuwar ba, amma ya kai hannun zai ɗauki meat roll guda ɗaya daga cikin plate ɗin dan tsokana. Sai dai kuma me? Yana kai hannu zai ɗauka suka ga an buge plate ɗin gabaɗaya ya faɗi kasa ya zube.

A miliyan Heleena ta É—ago kanta, wani irin mugun kallo Pretty dake tsaye a gefe ta wurga mata kafin ta ce. "Yah Omerish wacece ita É—in?". Ta faÉ—a tana wani mugun É—aure fuska, irin babu wasa a tattare da ita É—in nan.

Ita kuma Heleena ruÉ—ani ta shiga, ta gagara tantance wacce ta rungumi Big Bro É—asun ne (Sweetie) ko kuma dai ba ita bace? Idan ita ce kenan maza biyu take tare dasu ko yaya? Kai kanta ya shiga duhu.

Sosai Smart ya ji wani irin daÉ—i, dama so yake ya gwadata ya ga tana kishinsa ko bata yi shiyasa zai ci abin Heleena, in baku manta ba ai baya cin dik abin da Heleena ta kawo masu tin suna Paris, dan haka sabida gwada Pretty ya so ci. Kun san maza na mugun son su ga ana kishinsu, wani musulmin daÉ—i suke ji.

Sabida ya kara gwada kishinta a kansa yasa ya ce. "Daga cikin family take". A hanzarce ta tari numfashinsa da cewa. "Kenan zaka iya aurenta? Akwai aure a tsakaninku?". Muryarta har rawa yake yi ta faÉ—a. Kai ya jinjina mata alamar e ba sister ta jini bace, dan haka zasu iya yin aure.

Ai wani irin fusata Pretty ta yi, cikin fushi tana ɗaure fuska ta kalli Heleena, da yatsa ta nunata, cikin harshen turanci ta ce. "Ke mai kama da allon mayu, sa idonki cikin nawa, ni ba sa'an irinku bane, bani da mutunci a kan mijina, tin wuri ki ɓace daga ɗakin nan tin kan raina ya ɓaci in karya wannan kafar taki mai kama da burugalin burga miya, kuma idan kika bari ko bisa kuskure idanunki ya sake kallon mijina sai na ƙwaƙwale maki shi, fita waje yanzu!!!". Tana huci ta faɗa.

DaÉ—i tamkar Smart ya zuba ruwa kasa ya lashe. Tsabar farinciki jawota jikinsa ya yi ya rungume yana jin zuciyarsa na wani irin sanyi, da hannu ya yi wa Heleena alamar ta wuce ta fita yana kara rungume yar tsanarsa.
Chapter 93 · 0% Book details