← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 130

Sashe 72

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Meyasa kika gujeni kwanaki dayawa?". Muryarsa ta ratsa dodan kunnenta. A miliyan ta É—ago kai, mamaki ne ya kamata, wai meyasa ta gujesa, lallaima bawan ALLAHN nan, to ita da shi waye ya guji É—an uwa? ALLAH mai iko.

Ganin ta kafesa da ido ne yasa ya É—an hura mata iska daga bakinsa. ÆŠan lumshe ido ta yi ta sake warosu a kansa.

"Kai ne fa ka gujemu". A shagwaɓe sosai ta faɗa, ɗan matseta a jikinsa ya yi tare da rankwafo da kansa a kanta. "Kada ki faɗawa momma ke ba matata bace". Kamar mai raɗa ya yi maganar.

"Amma kasan dik daren daɗewa zata san gaskiya ko? Kuma ai bama zai yiwu ba, dan a matsayina na matarka dole zan rinƙa kwana da kai a ɗakin nan a idanunsu, to ya zamu yi?". Cike da shakku ta yi maganar.

Uhm shi da ba addini ne da shi ba sai ya ce. "E to me laifi a ciki dan mun kwana a tare ɗin?. Ba zasu taɓa sani ba sai in kece kika faɗa masu"......... Tab yanzu ta kara tabbatarwa Big Bro bai san addinin musulunci ba.

Cikin natsuwa ta ce. "Haramune mace da namiji su zauna a É—aki É—aya haka in ba ma'aurata ba, addinina ya haramta hakan, dan haka ba zai yiwu ba"......... Yana kallon cikin idonta, ya yi shiru na Æ´an mintuna, har ta fidda ran zai sake yin magana sai ta ji ya ce. "Zaki kwana a saman sofa ni zan kwana a saman bed, ya yi maki?".

Shiru ta É—an yi kafin ta ce. "Dik da haka watarana zasu gane fa". Kai ya É—an girgiza mata. "Ba zasu gane ba, ba zamu jima a nan ba zamu koma, momma tana sonki, please kada kisa farincikin da take yi ya kau".

Kai ta ɗan jinjina mashi. "In Sha ALLAH farincikinta ba zai tsaya ba, zan yi abin da ya dace"....... Murya kamar yana a cikin maye ya ce. "Promise?". Kai ta jinjina alamar e kafin ta ce. "Zan yi alkawari, amma kai ma ka yi alkawarin ba zaka rinƙa taɓa mun jiki ba?".

Kai ya jinjina mata alamar ya yi alkawari babu wani abin da zai yi mata, kawai dai zasu shiga É—aki matsayin mata da miji a kingdom É—in wa idon kowa, amma da sun shiga sun rufe kofa kowa zai yi ta kansa babu ruwan kowa da kowa. MY PEOPLE'S ANYA WANNAN WASA ZATA YIWU KUWA? HMMM KOWA YANAI MASU KALLAN MATA DA MIJI FA, TAB AKWAI CASE, YANZU WASAN SABUWAR DUNIYA ZAI FARA!.

"Muje mu ci abinci to". Ta faÉ—a tana kallonsa.

Mai da kallonsa kan kayan abincin ya yi, sai yaga sun yi mashi local, shi da tsabar izza da kuɗi idan ya ci abinci a kayan abinci ba'a sake saka mashi abinci a ciki sai dai a rinƙa sanyawa kuyangu ko sojojin yakinsa a ciki, kullum cikin sabbin kayan zuba abinci yake cin abin, amma yanzu yake ganin wasu warmar wai a ciki zai ci abinci, to amma ya zai yi tin da momma ta zuba mashi? Ci yazama dole ai.

Kwace jikinta daga nasa ta yi ta nufi wajen cin abincin. Bayanta ya bi da kallo yana jin wani irin tsananin sha'awarta na fusgarsa, ji yake tamkar kawai ya kai kansa gareta, ya sallama mata kansa, amma ina ba zai yiwu ba, ya ma yi alkawarin zai daina taɓata, kunga dole in yana so ta cigaba da aminta da shi ta nunawa Kingdom ita matarsa ce to dole ya yi ƙoƙarin danne kansa.

Ya yi nisa cikin tinani ta yi mashi alama da hannu a kan ya zo mana. Ba musu ya karisa wajen, zama ya yi a saman carpet É—in, sai ya ji tamkar a kan kasa ya zauna, wai carpet É—in babu laushi, ba kamar na kingdom É—insa ba.

Zuba mashi abinci ta yi ta turo mashi gabansa, wani irin kallo ya bi abincin da shi, to shi ko shinkafa bai taɓa ci ba a rayuwarsa, yaga su basmati yau, sai ma suka yi mashi maka da tsutsa da kayan miya, cimansu ya sha banban nesa ba kusa ba. Amma yana jin yunwa, daurewa ya yi ya ɗauki spoon yana kokarin toshe hanci saboda kamshin girkin bata yi mashi ba.

Sam Sweetie bata lura da halin da yake ciki ba, ta ɗauki spoon tana ɗan jujjuya abincin ita ma, sam bai yi mata ba, amma saboda kada ya ga kamar ta walaƙanta mommarsu ta ce abincin bai yi mata bane yasa ta ce bari ta daure ta ci, bata san shi ma ɗin bai yi mashi ba.

Ɗebowa ta yi zata kai baki kenan ta ga ya miƙe da zafa yana toshe baki saboda aman da ta kubce mashi, da sauri ta miƙe tsaye ita ma. Ina tuni ya isa toilet, daga in da take tana jiyo wani irin kakarin amai da yake yi, hankalinta ne ya yi mugun tashi har bata san lokacin da ta afka cikin toilet ɗin ta bi bayansa ba. TO FAH!.

---------------------🔥

A daidai wannan lokacin shi kuma goyson yana tsaye a tsakiyar room na Mahreen yana kare mata kallo, ya zo bata labarin Big Bro É—insu ya bayyana, kun san idan kana son mutum ko wani irin abin farinciki ya sameka zaka yi haba-haban sanar da wanda kakeso, shi ita ma ya É—ebo farincikin ya zo sanar da ita. Amma ina bata bari ya sanar da ita abin da ya kawo shi ba fa hau zazzaga mashi masifar ya fita mata a É—aki, tana tsaye a gaban mirror tana ta kallon kanta, Chuchu ta yi mata make up, shi ne take karewa kanta kallo, sai faÉ—i take yi. "Mahreen wutar kyau, kyau iya kyau yarinya yar babanta, wannan kayan manyan kai ne, yar beautyn bappanta, kin fa yi kyau". Kamar wata zararriya ta tsaya tana yabon kai.

Tin da ya shigo ya tsareta da ido, sai zazzaga faÉ—a take yi tana ya fita amma sam baya jinta, hankalinsa na kan kyanta, ga doguwar rigar tata ta zauna a jikinta tsam, sai yake jin tamkar zai iya karisa tsawon rayuwarsa yana kallonta ba tare da gajiyawa ba.

"Ba zaka fita mun a É—aki ba sai na je na faÉ—awa Yah Jaish kana shiga harkata?". Cikin tsiwa ta faÉ—a. Gera guda ya É—aga mata kafin ya kwaikwayi yar muryarta ya ce. "Ni gaskiya ba zan fita ba har sai kin saurareni kin ji me na zo faÉ—a maki".

"Ni babu abin da zan saurara, kawai ka fita". "To zo ki fitar da ni idan kina da karfi". Kwafa ta yi a kufule ta ce. "Haka ka ce?"........... Gera guda ya É—aga mata alamar e. Fuuuuuu ta nufosa tana janye hannu riga sama ita a dole zata fitar da shi waje.

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
-------------------------------------------🔥♥️

ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥

Ko kaÉ—an bata ji shakkarsa ba tazo harda kara gyara hannun riga, sannan tasa hannun ya cakumo cikinsa, ta daddage wai zata É—aga shi sama ita ga mai karfi.

Ko motsa shi bata iya yi ba, shi kuwa yasa hannunsa ɗaya ya riko waist ɗinta ta wajen cikinta, sama ya ɗagata, saboda tsabar neman magana shi ma irin nasa da rashin son a zauna lafiya, ko da yake dama ya ce ba zai barta ba, ya rinƙa shiga gonarta kenan.

Daga in da yake ya yi jifa da ita sai saman bed ɗinta. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa kafin ya ce. "Jita ko karfin ɗaga hannuna ɗaya bata da shi, da wani idanunta a wajen, gata ba nauyi kamar kwali".

Yadda yake murmushi ita kanta ba zata so ya daina yi ba, dan wlh ba karamun kyau ya yi ba, ya haskaka ɗakin matuƙa, ga fararen hakwaransa tas suna ta kyalli tamkar babu abin da ya taɓa ratsa bakinsa ya wuce, dimples ɗinsa irin na yayansa Big Bro.

A fusace ta É—ago daga gadan, amma ganin yadda murmushinsa ta yi balain haskaka É—akin ne yasa ta É—an tsaya a saman mattress É—in tana satar kallon shi da wayau, dama ta taso ne da nufin ta sauko kasa ta kamashi da kokawa, ganin yana sakin cool murmushi yasa ta fake da ta tsaya tana huci tana harararsa sai kallan madarar kyan da ALLAH ya zuba mashi take yi.

Lokaci guda a ranta ta ji cewa in banda ma soyayya da babu ruwanta da kyau ko kuÉ—i ai ita kanta tasan guyson ya fita komai da komai, ya fita kyau, haske, kuÉ—i, komai ma, amma a haka yake ta binta yana rokon soyayya daga gareta, ALLAH mai iko kenan, ALLAH mai adalci sosai, ba ruwansa da karfin mulkinka sai ya sanya maka son almajira ma, dan kawai kowa ya ji shi mai daraja ne.

-------------------🔥
Chapter 72 · 0% Book details