← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 130

Sashe 109

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka ta fara yi hawaye sharɓa-sharɓa a kuncinta tana cigaba da girgiza kirjinsa tana kwala kiran sunansa. Yana son cewa ta bashi ruwa saboda wani irin azababben kishin da yake ji, makoshinsa tai balain ɗaukar zafi tamkar wuta ake hurawa a wajen, amma ya gagara ko yunkurin yin maganar.

A daidai wannan lokaci shi kuma Big Bro yana zaune saman sofa, momma na zaune a saman bed suna fuskantar juna, lokaci guda ya ji kirjinsa ta buga makoshinsa ta É—auki zafi sosai kamar yana son shan ruwan. Momma na yi mashi magana amma hankalinsa bayaa kanta, saboda ji yake yi tamkar a takure yake, tinawa da ya yi su identical ne yasa ya ce to ko dai Omerish yana cikin damuwa ne?.

ÆŠago kai ya yi ya kallon momma, a sanyayye sosai ya ce. "Ina Omerish ne momma?"........ "Ina ga yana barci, dan jiya bai yi barcin dare ba, nan ya zo muka yi hira, ina ga yana biyan barcin ne"...... "Shi ne ba'a kirani ba kuka yi hiran ku biyu".

Murmushi momma ta yi kafin ta ce. "Ai ka yi barci ne lokacin".......... Shiru ya É—an yi, shi dai a ransa yana jin wlh Smart baya lafiya, saboda zuciyar twins tana irin wannan bugawa ne kawai idan É—ayansu baya lafiya. ÆŠago kallonsa a kan momma ya yi, sai ya ga ta yi gaggawar cire idanunta daga kansa, mamaki ne ya kama shi, kenan in baya kallonta tana kallonsa, in kuma ya kalleta sai ta cire ido? Ikon ALLAH, wai meyasa suke tsoronsa ne? Ya jefi zuciyarsa da wannan tambayar.

"Momma zan je duba Omerish". Ya faɗa tare da yunkurawa zai miƙe ta katse shi da cewa. "Lafiya dai ko?"...... Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce. "Babu komai, ina kewarsa ne"........ Kun santa da ƙwaƙwalwa ita ma, sai ta zargi ba lafiya ba, dole akwai abin da yake ji a ransa ko kuma akwai abin da suke shiryawa shi da Smart ɗin.

Miƙewa ya yi, yana taka step biyu sai ga Pretty ta shigo da gudu tana kuka tana faɗin Yah Omerish ya mutu. Momma and Big Bro har suna rige-rigen tarota dan tambayar me yake faruwa?.

Tana kuka tamkar ranta zai fita ta ce. "Yah Omerish yana cin abinci kawai ya faÉ—i kasa yana amai sai kuma ya daina motsi"......... Ai tin bata kai karshen maganar ba Big Bro ya yi zafan yin waje tin da ya ji Smart É—in yana É—akinsa.

Da sauri momma ta rufa mashi baya rike da hannun Pretty É—in. A lokacin da suka isa É—akin Smart baya motsi. Da ace tin lokacin da ya fara murkusoson nan ta gudu ta sanar da su, kila su iya cetan rayuwarsa, amma a yanzu poison É—in da ya ci ya yi affecting abubuwa da dama nasa, ta yi damage na cikinsa, ba zai rayu ba in ma yana da sauran nunfashi a yanzu kenan. Poison ya ci a cikin abincin nasa........ DAGA INA AKA SAMU POISON A CIKIN ABINCIN DA MOMMA KAWAI KE GIRKA MASU? SABODA TSARO DA LAFIYARSU BABU WANDA YAKE KAI MASU ABINCI SAI MATANSU NA SUNNA DA SUKA YARDA DA SU, TO HOW COMES AKA SAMU POISON?. AKWAI KURA WLH.

A gabansa suka tsugunna, Big Bro ya kai hannu ya laƙaci kumfar dake bakin Smart, slowly ya juyo da kallonsa a kan Pretty dake ta faman kuka. "Kafin ya ci abinci bai ci komai ba?". Da sauri ta gyaɗa kai alamar e bai ci komai ba. Dawo da kallonsa a kan momma ya yi. "Poison ya ci, kuma ina ga daga cikin abincin nan ne, waye ya girka abincin?".

Zazzaro idanu momma ta yi kafin ta ce. "Omerish baya cin abincin kowa idan ba ni na girka mashi ba, dan haka nina girka abincin nan da hannuna, kuma babu wanda ya taɓa abincin nan har Omnish ta zo ta ɗauka mashi"........ Pretty na girgiza kai tana kuka ta ce. "Wlh nima har na kawo mashi abincin nan babu wanda ya taɓa shi, yadda na ɗauko daga ɗakin momma babu wanda ya buɗe abincin har na kawo mashi".

Kai tsaye Big Bro ya ce. "To kenan ke kika yi poisoning ɗinsa!!". Tashin hankali! Zazzaro mashi idanu ta yi tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa, wani irin ruɗani da ta shiga bata san lokacin da ta fara girgiza kai tana sake gyaɗa kai sama alamar e da a'a ba.

Miƙewa Big Bro ya yi ya cicciɓi Smart zuwa saman bed, hannu ya sanya a saitin zuciyarsa dan ya ji tana bugawa ko bata yi! Tsit ya ji babu wani motsi, gabaɗaya jikin Smart ta saki. Hankalin Big Bro idan ya kai miliyan to a yanzu ya tashi, har wani juya mashi ya ji kansa yana yi, da kyar ya iya cewa. "Me ya yi maki da zafi haka da har zaki yi poisoning ɗinsa?". Yadda ya yi magana sai da ya razana momma, bata taɓa jin murya mai firgitarwa da rikitarwa irin wannan ba, bata san in ransa ya ɓaci voice ɗinsa ma canzawa take yi ba.

Muryarta na rawa ta hau girgiza kai tana faɗin. "Wlh bani bane"....... With harsh voice sosai ya ce. "Idan bake bace wacece?!! Meyasa a lokacin da ya fara ciwon baki kiramu ba sai bayan ya mutu?!! Meyasa ke baki ci abinin ba bayan a tare kuke breakfast kullum?!! Karya kike yi, ke kika yi poisoning ɗinsa!! Ko kuma da haɗin bakinki aka yi!!". Ya faɗa tare da miƙewa cikin zafa yana pointining ɗinta da hannu.

Kuka mai sautin gaske ta fashe da shi kafin ta ce. "Wlh bani bace, fushi nike yi dashi shiyasa ban ci abinci da shi ba, dama ina son in ya gama ci ya fita ne sai nima in ci nawa, amma wlh bani bace.......". Bata karisar da maganar ba ta É—auke diff sakamakon...........

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
BAN SAMU DAMAR YIN EDITING BA SABODA BANI JIN DAƊIN JIKINA!!.👏🏻

Kuka mai sautin gaske ta fashe da shi kafin ta ce. "Wlh bani bace, fushi nike yi dashi shiyasa ban ci abinci da shi ba, dama ina son in ya gama ci ya fita ne sai nima in ci nawa, amma wlh bani bace.......". Bata karisar da maganar ba ta É—auke diff sakamakon ganinsa a gabanta da ta yi, har wani sama-sama ta ji numfashinta yana yi saboda razana.

"Meyayi maki da kika yi mashi wannan hukunci?". Ya faÉ—a fuskar nan a É—aure tamau. Gagara yin magana ta yi saboda tsoro da tashin hankali da ta shiga, ita damuwarta ma kawai shi ne su faÉ—a mata Smart É—inta yana raye ko yaya? Shi take yi wa kuka yanzu, bata san ina zata sanya rayuwarta ba idan ya mutu, ba zata iya jura ba!.

Ganin alamar yana son ɗaga hannu zai kai mata duka ne yasa Momma ta yi gaggawar matsawa ta shiga tsakaninsu, hannun nasa ta riko, muryarta a raunace cike da tashin hankali ta ce. "Gaskiya Omnish ba zata iya yin poisoning ɗin Omerish ba, dole dai akwai abin da ya saɓa, ko akwai wanda ya karɓi abincin lokacin da kika fito da shi?". Ta yi maganar tana juyo da kallonta a kan Pretty.

Kai ta shiga girgizawa. "Wlh momma babu wanda ya karɓi abincin nan, tin da na ɗaukosa har na zo babu wanda ya taɓa shi". YAU FA AKE YINTA.

Shiru momma ta ɗan yi tana tinanin, wlh ita ma tin da ta girka abincin nan ta kawo room ɗinta bata fita ba, kuma alamu sun nuna a iya abincin Smart aka sanya gubar ba a dikka abin da ta girka ba, da dikka ne to su Sweetie ma ba zasu tsira ba, dan tukunya ɗaya aka yi girki, zubawa kowa nasa kawai aka yi, a iya abincin Smart ɗin kawai aka sanya.......... Kansu ya ƙulle.

"Momma ku je waje". Big Bro ya faÉ—a da kyar, dan sam baya son buÉ—e bakinsa saboda wani irin É—aci dake ransa in ya buÉ—e baki za'a iya samun matsala!.

Jin yadda ya yi magana yasa momma bata sami kwarin gwiwar iya ce mashi a'a ba, dole ta ja hannun Pretty suka nufi waje, sai kuka Pretty take yi tamkar ranta zai fita. Shi kuma dawowa ya yi wajen Smart, saman bed É—in ya haye tare da matsawa dab da É—an uwan nasa, zuciyarsa na tafarfasa ya haÉ—e fuskokinsu waje guda. A hankali ya zuro doguwar tongue É—insa waje, sai ya kai hannunsa ya É—an matsa kumatun Smart, hakan ya bawa bakin nasa damar buÉ—ewa kaÉ—an.

Tongue É—insa ya zura cikin bakin Smart É—in, take idanunsa suka canza launi, da tongue É—insa ya yi amfani wajen buÉ—e hanyar makogwaran Smart, kunga ai ba idanunsa biyu ba, so dole hanyar makogwaronsa tana datse, sai ya yi amfani da tongue É—insa ya buÉ—e hanyar.

A hankali ya fara zubawa Smart yawunsa a cikin baki tana samun hanyar wucewa zuwa cikinsa, har lokacin huci yake yi. Kun san shi da yake master ne a magic, yawun bakinsa tana karya abubuwa dayawa ciki harda sihiri, yawun nasa zata sanya Smart ya yi aman poison É—in kaf, sai dai kuma ko ya tashi zai sha jinya, dan abin ya yi affecting É—insa sosai.

Ko da sunan wasa Big Bro baya taɓa tofar da yawunsa a waje, dan yasan me a cikinta, yanzu ma ba dan Smart bane bai ga dalilin da zai sanya ya bashi ba, saboda ba kowa yake samu ba, sai Sweetie mai facacity da ta lashe mashi zuciya. Yawunsa ba kamar na sauran mutane bane!.

-----------------------------🔥
Chapter 109 · 0% Book details