← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 130

Sashe 13

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙasa-ƙasa can ya ce. "Meyasa kika cike neman faɗa and baki da karfi ko na iya ɗaukar Omnish?"....... A tsorace sosai take da shi ta amsa da. "Saboda ina da kai da kuma Ronnie shiyasa bana damuwa zan nemi tsokana a dik in da nike so dan zaku tsaya mun tin da ban da karfi".

Ya ilahi ya lillahi wannan magana ta huda zuciyar Big Bro, like wow, wai saboda tana da shi da Ronnie, kenan ta saddakar su ne garkuwa a gareta? Ashe haka ta ɗaukesu da mahimmanci sosai? Wow. Ai gagara yin magana ya yi, saboda bai san me zai ce ba, an burge Big Bro a nan matuƙa.

Zame hannunta daga kan Cross ɗin ta yi, tana ƙoƙarin sake yin magana mirrorn bayansu ya ɗan yi kara, hakan yasa ya yi saurin kai kallonsa wajen. Like wow, Mommah ce bayyana a cikin mirror tana zaune saman bed ɗin King suna tattaunawa, bai taɓa zatan jujun tsafin nasa zasu iya ɗauko mashi ita ba, har ya fidda rai sai kuma gata ta bayyana.

Ai bai san time É—in da ya jawo Sweetie ta faÉ—a jikinsa ya samu damar ganin mirrorn da kyau ba. Ai daga ita har shi sai da suka É—auke wuta na wucin gadin, a gaggauce ya raba jikinsa da nata saboda wani irin shock da ya yi har tsakiyar kansa, hankalinsa a kan Mommah ya koma yanzu.

Da sauri ita ma ta juyar da kallonta izuwa kan mirrorn, lokaci guda ta zaro idanu waje, har voice É—inta yana sarkewa wajen cewa. "Big Bro wacece wannan kyakkyawar mata mai kama da kai É—in? Ka ganta kamar sis É—inka? Wlh tana da kyau sosai".

Kun san Mommah na da kyan jiki ba zaku taɓa zatan cewa ita ta haifesu ba, kun ji Sweetie ta ce sister ɗinsa.

Dawo da kallonsa kanta ya yi, in a cool way ya ce. "Are you serious tana kama dani?".

Kai ta shiga gyaÉ—a mashi kafin ta ce.............

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

Dawo da kallonsa kanta ya yi, in a cool way ya ce. "Are you serious tana kama dani?".

Kai ta shiga gyaÉ—a mashi kafin ta ce. "Kuna kama sosai, amma ta fika kyau ma fa, kalleta tamkar ita ta yi kanta, wannan daga gani tana da zuciya mai kyau duba da yacce lokaci guda ta shiga zuciyata kuma kalli yacce face É—inta yake kyalli alamar mutuniyar kirki ce". Ta kai karshen tana juyowa da kyau ta karewa Mommah kallo. (Kun san masu bin ALLAH da Manzonsa wlh har wani Musulmin kyalli zaku ga face É—insu yake yi suna wani walwali na imani, ga su da saurin shiga rai, ki daure ki zama ta kirki domin ki ribaci duniya da lahira, ba zan gaji da kwaÉ—aita maku zama na kirki ba, saboda ina son mu haÉ—e daku a aljanna, ina son ganinku cikin rahama)

Har cikin ransa ya ji wani irin Musulmin sanyi ta kara ratsa zuciyarsa yacce Sweetie ta faÉ—i kyawawan kalamai a kan Mommah, bai san dalilin da yasa ya ji Musulmin daÉ—i a kan hakan ba, kawai dai ya yi farinciki over to over.

Kun san aka ce jini ba wasa ba, jini ne kawai dake fusgar tsakanin Black Tiger da mommah, amma dai basa wani kama, ita dai Sweetie ganin kamar kawai ta yi, uwa ba wasa ba ai kun sani!.

Shiru wajen ya yi for almost 5 mins, suna sauraron hirar King da Mommah, do shi Black Tiger baya jin larabci, ba tsaginsa bane wannan, ita kuma Sweetie ai kun san da yaren da suke magana kenan a forest, dan haka tana jin dik abin da suke faÉ—e.

In a cool way sosai ya ce. "Kina jin abin da take faÉ—e ne?"........ Kai ta jinjina mashi alamar e idanunta a kan King dake bin Mommah da kallo, lokaci guda ta rikice, sai ta ga kamar da King da Mommah É—in ai dik kamanninsu É—aya, in baku manta ba Mommah ai Æ´ar uncle É—in King ne, dik jini É—aya ne, so ko ba kama ta fuska akwai ta jini da shi ne ma yafi rinjaye da sanyawa aga kama.

Binta da ido ya yi alamar yana jiran ta fassara mashi, amma bai yi magana ba, ta gane nufinsa sosai, dan haka sai ta ce. "Cewa ta yi daddyn Omerish tin da abin nan ya jagule har haka, just kawai ka fito ka faÉ—a mana dikkan abubuwan da suke faruwa, zamu yi maka uziri, sannan nasan Omerish zai fahimceka". Cikin harshen turanci ta fassara mashi.

King ne ya yi magana don baiwa Mommah amsa, nan ma dawo da kallonsa a kanta ya yi yana son ta fassara mashi. Cikin natsuwa ta ce. "In Sha ALLAH zan faÉ—a maku komai, yanzu ki kira mun Omerish idan kin fita, saboda ina son yin magana da shi, sannan ki haÉ—a mun kan Æ´aÆ´ana maza da mata dikka daren yau ina da zama da su, daga karshe dole mu nemo ta yacce aka yi É—an uwan Omerish ya bar hannunmu, wace kuyanga ce a lokacin take tare da Aleenarh?".

Shiru Mommah ta ɗan yi kafin ta ce. "In dai har ɗan cikina ne da gaske, to babu buƙatar mu nemo hanyar da zamu bi domin dawo da shi gida, da kansa zai dawo, yanzu ma ai ba mu muka kawosa nan ba, ALLAH ne ya kawo mana shi ya nuna mana yana raye, dan haka ina da yarda dubu bisa dubu a kan ALLAH! Na tabbata ba zai taɓa bani kunya ba! Domin dik wanda ya yarda da shi baya taɓa bashi kunya! Saboda haka ɗana zai kawo kansa gareni In Sha ALLAH!!".

Tin da Sweetie ta fara fassara mashi ya tsare ɗan bakinta da kallo, a ransa yake mamakin irin karfin hali da yarda da UBANGIJI da Mommah ta yi, lokaci guda a cikin ransa ya ce meyasa dik waɗan da suka yarda da ALLAH suke da confidence a kan komai ne?. NI KUWA INA DAGA GEFE NA BASHI AMSAR CEWA DIK DUNIYA ALLAH NE KAWAI ZAKA YARDA DA SHI BA ZAI TAƁA KUNYATAKA BA, SHI NE KAWAI ZAKA BAIWA AMANA YA RIKE MAKA HAR ILLAH MASHA ALLAH, SHI NE KAWAI ZAI BAKA YAU GOBE KA ROKA YA SAKE BAKA, JIBI MA KA ROKA YA BAKA YA KARA KARA MAKA, BAYA TAƁA GAJIYA DA TAIMAKA MAKA MUDDIN KA YARDA SHI KAƊAI ZAI BAKA, KUMA BAYA DA ROWA, GA SHI GAFURURRAHIM KUMA ALIMUL AZIM, SANNAN RAHMANURRAHIM, DAN HAKA MU DA MUKA YARDA DA ALLAH SHI KAƊAI NE DA CONFIDENCE ƊINMU MUKE KOMAI A KAN KOMAI BA TARE DA SHAYI KO DAR-DAR BA BARE SHAKKA BA!!!!!!.

Ya kalli yacce Sweetie take da karfin hali ne, bata da tsoro ko shakkar faɗar abin da ta yi niyya ko a gaban waye, kallo yacce ta kare da su Father's a church, karfin halinta yana burge zuciyar Big Bro, abin yana tsuma shi matuƙa, yanzu kuma ya ga Mommah ita ma da karfin hali wai ta yarda ta yi imanin zai kai kansa gareta, abin sai ya yi mashi wani iri, ga shi zuciyarsa ta gagara iya musa maganarta, yana jin kamar da gaske ɗin zai iya yarda suna da alaƙa da shi, ya gagara karyata zancen da zuciyarsa take yi na sune iyayensa. NI KUMA NA CE KAƊAN KA GANI DAGA KARFIN YARDA DA ALLAH, AI IDAN MUTUN YA YARDA DA ALLAH MAGANA IDAN YA YI MA MUTANE BASU ISA MUSA MASHI BA! SABODA ALLAH BA ZAI TAƁA BASHI KUNYA BA! DOLE A YARDA DA SHI! DAN HAKA KO KASO KO KAKI DOLE ZUCIYARKA ZAI YARDA DA MOMMAH CE MAHAIFIYARKA, TA RIGADA YA BAWA ALLAH WANNAN BATU!.

Tamkar mai raÉ—a haka ya ce. "Idan zan tambayeki me kike tinanin yake a tsakanina da waÉ—an nan mutane me zaki ce?". Ya faÉ—a yana mai da kallansa kan Mommah.

Shiru Sweetie ta É—an yi na Æ´an sakanni kafin ta ce. "If I guessed it right zan iya cewa wannan mutumin daddynka ne, and wannan mata kuma sister É—inka ce"......... "Your reason?". Ya faÉ—a game da É—an satar kallanta ta wutsiyar ido.

Nan ma shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Gaskiya wannan mutumin ya yi a matsayin daddynka, ina jin hakan a jikina duba da yacce fuskokinku yake, and wannan mata kuma kaga tana kama da shi, which means ƴarsa ce, kila yarsa babba ce sai kai second born, dik yacce aka yi dai kuna da alaƙa mai karfin gaske"

Tin da ta fara magana ya kurawa ɗan bakinta idanu, har cikin ransa yanzu ya ɗan gasgata maganganun su Mommah, da Sweetie ta yi magana yanzu ya shaida, but ya yi ƙoƙarin hana hakan tasiri a ransa, sai dai mother no be wasa oooo, uwa ta wuci nan, dan haka zuciyarsa ta fi karfinsa a wannan gaɓa da dole yasa ya fara ƙoƙarin bincikar gaskiya a kan babansa da ya renesa a nan.

Dawo da kallonsa a kan Sweetie dake ta faman kallon Mommah ya yi, dai'dai lokacin ita ma ta juyo da kallonta a kansa, kafe juna da wani lallausan Musulmin kallo mai kwantar da hankali suka yi ba tare da sun san sun yi hakan ba, wani irin kallo mai wuyar fassaruwa ya rinƙa binta da shi, while ita ma kallan da take mashi mai cike da fito da tsantsar abin dake a cikin zuciyarta zuwa kwayar idanunta.
Chapter 13 · 0% Book details