← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 130

Sashe 25

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tin daga kan yanayin tafiyarsa ta kara tabbatarwa da bashi bane, saboda Hoorain cikin tsananin jarumta yake tafiya, kuma a buɗe sosai yake, sannan kafafun Hoorain dikka basa taka kasa idan yana tafiya, wajen karshen kafarsa bata taɓa kasa in yana taku, bugu da kari tafiyar bahago daban yake, dan ya fi raja'a ta gefen hagun.

A gabanta ya matsa dab, tana tsaye bata motsa ba, sai dai daga ta ciki saura kaɗan ta saki fitsari a wando. Hannayensa ya kai cike da marmarinta zai riko nata hannayen ta ɗan yi saurin janyesu baya, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Kai my Hero, ka je ka yi Sallah ka dawo akwai wani abin da na tanada maka".

Sosai ya ji zafin yacce ya janye hannunta daga garesa, amma sai bai nuna hakan ba, ya makale murya haɗe da cewa. "A bani koda kiss ne sai in tafi". Kai ta shiga girgizawa kafin ta ce. "Bari ma in duba karfe nawa ne yanzu da kaki tafiya masallacin, nasan yanzu ma anyi sallah". Ta faɗa tare da wucewa wajen bed ɗinsu, wayar Rishma ta laluɓa a wajen da sunan zata duba time, jikinta ne ya fara kerma a lokacin da ta fara neman number sadauki Rishan a wayar, tana da basira sosai sai taki danna mashi kira da ta ga number, sako hawai ta hau rubuta mashi.

Uncle Rishan ka ce my Hero ya yi gaggawar barin dik abin da yake yi ya dawo gida yanzu akwai matsala. Shi ne abin da ta iya rubutawa a sakon, jikinta na kerma tana ƙoƙarin turawa kenan ta ji an kwace wayar, a zabure ta ɗago da kallonta a kansa, yana tsaye gabanta ya ɗaure fuska tamkar hadari, yanzu ya fahimci ta gane ba Hoorain bane shi, saboda yadda ya ga jikinta na kerma a yayin da ta rike wayar, shiyasa ya zargi ta ganesa, dan yasan in har bata gane ba babu dalilin da zai sa ta tsorata har jikinta ya hau kerma haka.

Pretending ta fara yi, tana kallonsa ta ce. "My Hero lafiya? Abu fa nike yi ka bari in gama sai mu yi magana". Cikin wata iriyar kakkausar murya ya ce. "Izuwa yanzu nasan kin gane ba shi bane".

A zabure ta ja baya da shi, take jikinta ya tsananta kerma. Shi kuwa cikin zafa ya yi kanta tare da kai mata wani irin damka a waist É—inta, ya janyota jikinsa da karfin tsiya. Ihu ta fara yi tana turesa tana kai mashi duka a jiki, sai dai ina karfi ba É—aya ba, ta fagara ko kwatanta kwace kanta. Da karfi ta É—agata ya yi jefa da ita a saman bed dake kusa da su.

Wani ihun ta sake kurmawa mai sauti take da yunƙurawa a miliyan ta diro ƙasan bed ɗin, da gudun gaske ta nufi kofar fita daga ɗakin, sai dai ina, magic eyes ɗinsa yasa ya datse kofar gam, tana zuwa ta hau bugu da karfi-karfi amma ina babu mai jinta, dan Rishma ma dai tana can tana Sallah a ɓangarenta.

Tana tsaka da buga kofar sai ji ta yi ya damki gashin kanta, da karfi ya jata izuwa gaban mirror É—akin, tsaidata ya yi a gaban mirror, cikin tsawa ya ce. "Ki natsu ki sa idanunki a kan mirror É—in nan".

A miliyan ta waro idanunta a kan mirror, take ta hango Hoorain and sadauki Rishan a cikin mota, suna zaune a gidan baya suna É—an hira jefi-jefi. Kara zaro idanu ta yi tana kallonsu, sai dai kuma wannan mummunar muryar tasa ce ta sake dakar dodan kunnuwanta da cewa. "Ko ki natsu ki bani haÉ—in kai a kan abin da nike so, ko kuma yanzun nan in saka wannan motar ta yi accident gabaÉ—ayansu su kone kurmus!!".

Jikinta ne ya kara tsananta kerma, take ta ji duniya na juya mata....... "Zaki bani abin da na zo nema ko kuwa in kashesu a gabanki kina gani?". Muryarsa ta sake karaÉ—e kunnuwanta ba tare da ta farfaÉ—o daga wancan magagi da ya jefata ba!.

"Me kake so daga gareni?". Cikin tsananin tashin hankali ta yi maganar, har muryarta na rawa.

Ko kunya bai ji ba ya ce. "Kanki, ke kawai nike so". DUM!!! DUM!!! DUM!!!. Haka ta ji kirjinta ya bada bugu, cikin sanyin murya ta ce. "Zan iya yin komai a kan my Hero". Da jin wannan kalamai Ude ya fara sakin murmushi, sai dai lokaci guda ta canza mashi murmushin izuwa bakinciki, domin kuwa cigaba ta yi da cewa.

"Zan iya yin komai a kan my Hero, amma ba wai hakan yana nufin zan iya yi har da saɓon ALLAH ba! Ko kan iyayena ba zan iya saɓawa ALLAH ba, dan haka ba zan aikata zina saboda cetan ransu ba, sannan ba zan iya bada kai'na da na yi ƙoƙarin killacewa na kare mutumcina tsawon shekaru domin in kawowa mijina mutumcina wa wani ba, dan haba bayan my Hero to wlh na gwammaci mutuwa da na bawa wani, kuma da kake maganar kashesu ai ba kai ka riƙe rayukansu ba, ALLAH da ya haliccesu shi kaɗai yasan ranar da zasu mutu, kai baka isa ka kashesu ba, idan kuma kana da ja da maganata ka kashesu ni ma ka haɗa da ni, dan wlh da na baiwa kare irinka kai'na gara na mutu mutuwa mafi tsanani da azaba!". Cike da confidence ɗinta na jinin Modarawa ta yi maganar, har cikin ranta da ta yarda ta yi zina da shi gwara ya kashe su Hoorain ɗin ya haɗa da ita, dan tasan ba shi ya rike rayukansu ba, idan ALLAH ya rubuta yau zasu mutu to ko ta yi zinar da shi sai fa sun mutu ɗin, dan haka babu batun bada kanta.

Kalamanta sun yi bala'in kona ransa, dan haka sai ya juyo da ita suna fuskantar juna, da tsannin karfin gaske ya dalla mata wani gigitaccen marin da sai da ta ji komai ya ɗauke mata diff, sannan ya yi jifa da ita saman gado, tana ƙoƙarin miƙewa ya damki kafafunta a in da ya janye kayan jikinta ya fata kiciniyar yagesu, ita kuwa da iya karfinta ta fara kiciniyar kare mutuncinta.

Sai dai ina, ya yage mata kayan gabaɗaya ya dire shi, ya rage daga ita sai wannan ɗan vest da take sanyawa a ciki da kuma kara mub pant. Ganin hakan yasa ta dakarkare da iya karfinta ta rarumo lamp ta buga mashi a kai wanda yasa ya ɗan ja baya da ita, da gudun gaske ta sake miƙewa ta diro kasan bed ɗin. Kai tsaye ta nufi toilet ta banko kofar ta murza key.

Sai dai kuma me? Yana zuwa duka ɗaya ya yi wa kofar toilet ɗin ta ruguje ƙasa, ai wani irin ihu mai sautin gaske ta saki, yau ta ga tashin hankalin da bata taɓa gani ba, ta shiga bala'i da ruɗani fiye da tinani. Da gudu ta yo waje ya biyo bayanta, rasa ina zata nufa ne yasa ta yanke shawarar da dai wannan tsinannen kafuri ya keta mata haddi gwara ta faɗa ta window kawai ta kashe kanta, ba tare da zurfin tinani ko tina cewa wanda ya kashe kansa wuta zai tafi ba, a lokacin tashin hankali ya zarce tinani a ranta, kawai ta buɗe window, bata ji bata gani ta afka ƙasa, ga shi suna sama can da nisa.

INNALILAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, UDE YA YI SANADIN AUTA. MY PEOPLE'S ME KUKE TINANIN ZAI FARU NE WAI? ME ZAI FARU IDAN HOORAIN YA DAWO YA TADDA GAWARTA TA FAÆŠO DAGA SAMA? KAI NI BARI IN JE BLACK WORLD KO ZA'A ÆŠAN SAMU SASSAUCI A CAN!.

----------------------🔥

BLACK WORLD 🔥

Wani irin kwalliya da Sweetie ta tsantsara bata taɓa yin irinsa ba, kuma dik Ronnie ya goya mata baya, shi ya tsaya kai da fata ya tsara mata yadda zata ƙasance, an shirya komai su kaɗai ake jira, shi ma Ronnie ya yi shiri cikin wannan white suit ɗin nasa, Pretty ta sanya ɗaya daga cikin kayan Sweetie, sun yi bala'in kyau tamkar ka sacesu ka gudu, jama'a sun hallara sun cika hall ɗin tab, robot sai rabon drinks a cikin manya-manyan tsadaddun glass cups suke yi. Abin ba'a magana.

Sai tashin fitinannen kamshi suke yi, cike da zumuÉ—i Sweetie ta ce tana zuwa bari ta riga kowa ganin kwalliyar Big Bro. Sai a lokacin ne Pretty ta ce. "Sweetie ina wancan mutumin ne na jiya?".

Kun san ita fa Pretty saboda tabbatar sakalci da shashanci ko sunan Smart bata sani ba. Ba tare da Sweetie ta amsa mata ba ta ce. "Ki jirani ina zuwa, bari in je". Bata jira amsarsu ba ta yi gaggawar wucewa waje. A ranta kawai tana tina irin yadda suka kasance daren jiya, sai take jin wani irin tsantsar farinciki na wuce misali.

Tana zuwa kai tsaye ta shige cikin room É—in nasa. Ya subhanallah, ai mutuwar tsaye a bakin kofar ta yi tana kallan cikin room É—in game da zaro idanu. Ba ta san lokacin da a fili ta furta. "Tsarki ya tabbata ga UBANGIJIN da ya yi wannan halitta".

Jin voice ɗinta yasa ya juyo, dama yana tsaye a tsakiyar ɗakin yana ƙoƙarin gyara hannun suit ɗin jikinsa, ya bawa kofar shigowa baya, my people's na ce wai kun san daga ina guyson ya gado ɗaukar wanka kuwa? Gaskiya Black Tiger karshe ne, kuma ga shi dik irin wankan da zai ɗauka sai kayan sun hau da jikinsa, sai ya yi wa kayan makurar kyau, shi fa shi yake yi wa kaya kyau ba su suke yi mashi kyau ba, tamkar wata cikin taurari, kun san idan wata yana waje gabaɗaya disashe hasken taurari yake yi, haka Black Tiger idan ya shiga waje.

Wlh ya yi fitina a cikin wanna kaya, sai dai da kallo É—aya zaka yi mashi kayan jikinsa a mace take, dik baya cikin mood mai kyau, kun san Ronnie ya katse mashi jin daÉ—i mafarkinsa, bai barci ya kai babban sashe ba.
Chapter 25 · 0% Book details