← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 144

Sashe 99

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’an jinkirtawa da maganan nasa yayi sakamakon wasu irin hawaye da kuma raunin da yaji yazo masa, domin kuwa baisan tayayane zasu fuskanci maganar tasa ba, yaya zasu d’auketa Allah Kad’ai masani, babban abun ji da tambayan kuma shine Maleek da k’addaran ta zama akansa ne.

Ahankali ya d’ago kansa ya kalli Maleek d’in wanda kansa ke k’asa, tsananin tausayinsa ne ya rufesa wanda har hakan yasa ya Kasa controlling kansa, harsaida wasu guntun hawaye suka sauk’a akan fuskarsa.

Cikin sanyin muryar dake bayyana zallan damuwarsa ya k’ira sunan Maleek d’in.

Maleek dake zaune kuwa jin yanayin yanda Abbou Jaheed d’in ya k’ira sunansa ne yasashi gane cewar Lallai akwae matsala.
Ahankali ya d’ago kansa ya kalli Mahaifinnasa.

Kai Abbou Jaheed ya d’an girgiza saboda girman abunda bakinsa ke kokarin fad’a, yasan cewa Lallai ba abu mai dad’ine zai fito daga bakinsa ba, amma to yaya zaiyi idan bai fad’i wannan matsalar a gaban kowa ba, meye amfanin b’oyewa? hakan zai zama kaman cutarwa ne.

Kansa ya d’an sunkuyar domin babu yanda za’a yi ya fuskanci d’annasa ya fad’a masa magana marar dad’i kaman wannan.

Cikin dauriya da kuma son ganar da Maleek d’in yace.

“Hakika Maleek nasan amatsayinka na Musulmi kayarda da k’addara mai kyau ko akasin haka, sannan kuma nasan kayi imani cewa Allah Yakan iya jarraba bawa takowanne siga, lallai tabbas kai kuma kalan naka Jarrabawar ahaka tazo, saidai nayi imani cewa amincewa da kuma yarda da hakan ba k’aramin karamci zai jawo maka awajen Ubangijin kaba, kayarda cewa komae Allah Ne Ya tsarashi!!�

Gaba d’aya falon shiru ya d’auka yayinda dukkaninsu suka zubawa Abbou Jaheed idanu.
Kowannensu buri yake yaji abunda Abboun Zai fad’a, amma banda Abbou Khareem dayasan komae akan zancen.

Kusan mintuna 5 aka share gaba d’aya ko ina ya d’auki shiru, rumtse idanu Abbou Jaheed yayi kana asanyaye yace.

“Kayi hak’uri Maleek asanadiyar accident d’in da ka samu Dr. ya shaidamin cewa kasa mu matsala amararka wanda hakan yasa ba zaka tab’a haihuwa ba!!!�

*22/2/2021*

*10:30 am*
2/24/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

#Life and Destiny

*Chapter 57*

Amatuk’ar Razane gaba d’aya mutanen dake cikin babban katafaren parlor’n suka d’ago kai dukansu suka kalli Abbou Jaheed.
Domin kuwa maganar da ta fito daga bakinsa ba k’aramin rugurguza musu k’wak’walwa tayi ba, har hakan yakai ga kowannensu ya shiga kokonton cewa kodae baiji abunda Abbou Jaheed d’in ya fad’a da kyau bane.
Abbou Khareem kuwa da yasan kwanan zancen kansa kawae ya sunkuyar tare da soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarsa.

Idanun Maleek wanda suka matuk’ar k’ank’ance lokaci d’aya kuma sukayi wani irin ja mai ban tsoro ya zubawa Abbou Jaheed d’in, yayinda kuma sannu ahankali kalaman da Abbou Jaheed d’in ya fad’a suka shiga yawo acikin brain d’insa filla filla, tamkar dae wanda aka bud’e aka watsasu.
Take kuwa wani irin matsanancin zufa ya shiga ketowa ta kowani sashi na jikinsa, b’angaren zuciyarsa kuwa bugawa take da k’arfin gaske tamkar zata faso kirjinsa ta fito waje.
Lallai hak’ik’a akaro na biyu kunnuwansa sunjiye masa magana mafi muni da kuma girma, maganan da tasa shi zama tamkar wani statue, maganar da ta tsayar da duk wani tunani da kuma gudun jininsa.

Ba kuma iya shi d’in kawae ba hatta Laylerh dake zaune ak’asa saida gaba d’aya ilahirin jikinta ya d’auki rawa, tare da shiga cikin wani k’aton tashin hankali, duk da kuwa tafara tunanin cewa kunnuwanta basu jiye mata komae adaidai ba.

Alhaji Farouk, Oum Ayush, Fou’ad harma da Najeeb wanda ke zaune ad’an nesa da Laylerh kad’an.
Kalmar.
“Innalillahi wa inna Ilaihirraju’un!!� Kawae suke furtawa, domin kuwa ba kad’anba maganan ta tada musu da hankali, wanda har hakan yasa suka kasa furta komae bayan salatin da sukeyi.

Abbou Jaheed kuwa akaron farko kenan bayan yayi maganan ya d’ago kansa ya kalli Maleek daya tsura masa jajayen idanunsa baya ko k’yaftawa.
Wani irin rauni da kuma matsanancin tausayin d’annasa ne ya cika masa zuciya, wanda kuma har ya kaisa ga kasa jurewa.
Ahankali ya tashi tsaye, cikin yanayin sanyi da kuma karyewar zuciyar daya samu kansa aciki ya k’araso inda d’ansa Maleek d’in ke zaune.
Inda su Abbou Khareem suka rakashi da ido.

Asanyaye ya zauna akan kujeran da Maleek d’in ke zaune, tare dasa hannunsa ahankali ya dafa kafad’an Maleek wanda zaman Abbou Jaheed d’in akusa dashi yasashi rumtse idanunsa.

“Kayi hak’uri Maleek Tabbas kowani bawa da irin yanda Allah Yake jarabtansa, babu kuma wanda ya isa ya tsallakewa k’addararsa, tabbas ka had’u da k’addarori masu girman gaske tun daga k’uruciyarka har zuwa yanzu, damuwa sunyiwa rayuwarka k’awanya, yayinda kuma rashin samun fata da muradi ke sake bibiyarka akoda yaushe, amma hakan ba shine ke nuna cewar baka da farinciki kwata kwata arayuwarka ba, sannan kuma bashi yake nuna cewa Allah Baya sonka ba.�
D’an numfasawa Abbou Jaheed d’in yayi tare da zaro wani farin handkerchief daga cikin aljihunsa ya share d’an guntun k’wallan daya cika idanunsa.
Still asanyaye Abbou Jaheed d’in yace.
“Tabbas nasan kasan cewa Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda bazai iyaba, Ina kuma fata da ka karb’i wannan jararrabawar Insha Allah watarana zakayi nasara, watarana lallai zakayi dariya Maleek, komai yakan faru sannan kuma yakan wuce har abada kaman bai tab’a faruwa ba, bakowa ke samun abunda yake soba, sannan kuma bakomai Allah ke baka dan kana tsananin soba, wani lokaci musanya maka yake, ya toshe wani ya kuma baka wani, hak’ik’a nasan zakaji k’unci da kuma ciwo acikin zuciyarka, amma hak’uri da fawwalawa Allah komae shi yafi, rashin haihuwa abune me tsananin ciwo da kuma k’unci, amma hakan Bawae yana nufin takura kai da yawan damuwa bane, Dan Allah Maleek kada kabar hakan ya zamo silar k’unci da kuma bak’inciki arayuwarka, ko ba aje ko inaba kayi dubi ga Abboun ka Khareem da kuma matarsa Oum Ayush, wanda tunda suke arayuwarsu basu tab’a haihuwa ba, sama da shekara 20 kenan yanzu amma kuma ahaka suke rayuwarsu, duk da cewar kuma sunajin ciwon abun acikin ransu amma hakan baisa sun tauye hakk’in farincikinsu ba, babu d’aya daga cikinsu daya daina murmushi ko dariya asanadiyar hakan, saboda sunyi imani cewa Allah Shike bayarwa shi kuma ke hanawa aduk lokacin da yaso, saboda haka kaima ka d’auki k’addararka kasa sanyi da salama acikin zuciyarka watarana Insha Allahu zakaga nasara da riban hakan.�
Again sake tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da d’an numfasawa ahankali ya d’ago kai ya kalli Alhaji Farouk da duk wani tashin hankali da kuma tausayin Maleek d’in ya bayyana k’arara akan fuskarsa.

Idanu Abbou Jaheed d’in ya d’an lumshe kana asanyaye yace.
“Kayi hak’uri dajin kalamaina adaidai wannan lokacin Alhaji Farouk, domin dama na gayyatokane dan kasan halin da ake ciki, domin koba komae kai ubane agaresa, sannan kuma matsayin suruki kake dashi agaresa, kaine mutumin da yake shirin basa auren kafun wannan mummunan k’addaran ta shigo rayuwarsa, K’warai nasan jin wannan maganan zaisa kaji babu dad’i acikin zuciyarka, sannan zai kuma iya sawa kasanja ra’ayi akan tunaninka na baya, duk da cewar kuwa lokaci ya k’arato sosai, amma kuma babu yanda muka iya, a irin wannan al’amarin ba ayin dole ba kuma acutarwa, saboda haka kana da y’ancin da zaka yanke ko wani irin hukuncine, zakuma ka iyayin shawara da iyalanka da kuma ita kanta yarinyar, domin abune me matuk’ar ciwo atauye mata hakk’inta mai girma irin wannan...�
Yanayin yanda Abbou Jaheed d’in ya k’are maganar cikin sanyin muryane yasa Alhaji Farouk yin shiru tare da sunkuyar da kansa k’asa, gumine kawae ke tsatstsafo masa saboda gaba d’aya ya samu kansa cikin tashin hankali.

Wasu irin hawaye masu matuk’ar zafi da kuma k’unane suka sauk’o daga cikin idanunta zuwa kan k’uncinta, saboda tsananin yawansu ne kuma yasa har suka soma sauk’a akan k’irjinta.
Wani irin matsanancin juyawa taji kanta nayi, yayinda gaba d’aya duk wani tunaninta ya tsaya cak.
Abu d’aya kawae brain d’inta ke nanata mata cewar.
“Yah M.Jay d’inta bazai tab’a haihuwa ba, k’wayoyin haihuwarsa sun samu matsala.�
Wannan tunanin kuwa shi yake k’ara mata jin jiri da kuma juyawar da kanta keyi.
Da k’yar ta iya motsa y’an k’ananan labb’anta, cikin kuma wani irin fusgan numfashi ta soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarta.
Domin ta shiga tashin hankali maitsanani.
Tambayar kanta take. “Shin wannan wacce irin k’addarace? wace irin jarrabawace haka mai tsananin zafi? tayaya Maleek zai iya jure duka way’annan k’uncin rayuwar? meyasa k’addara ke wasa da rayuwarsu? sai yaushene zasu samu nutsuwa da kuma farinciki arayuwarsu? yaushe k’addara zata barsu suyi dariya ita da d’an uwannata har hak’waransu su bayyana kowa ya gani?.�
“Lallai tabbas Laylerh babu wannan ranan, domin kuwa munanan k’addara sun riga sunyiwa rayuwarku k’awanya!�
Wani sashi na zuciyarta ya fad’a mata hakan.
Kanta ta d’an soma girgizawa ahankali, domin kuwa bazata iya jure abunda takeji acikin zuciyarta ba, Tabbas so take tayi kuka sosai, kuka irin wanda zai rage mata koda kaso d’aya daga cikin d’ari na k’uncin dake damun rayuwarta ne.
Ahankali ta had’e k’afafunta tare da cusa kanta atsakankanin cinyoyinta, batare da ta iya controling kanta da rauninta ba kuwa ta fashe da wani irin kuka mai tsananin tab’a zuciyar mai saurare.

Oum Ayush dake zaune akusa da Laylerh’n itama hawayene suka silalo daga cikin idanunta, natsananin tausayin Maleek da kuma su kansu ita da mijinta, domin kuwa tasan zafi da ciwon dake cikin rashin haihuwa, abune da iya juresa keda matuk’ar wahala, musamman ga Namiji matashi mai jini ajiki kamar Maleek, wanda ayanzune ya kamata ace rayuwarsa na tsaka dayi masa dad’i, amma kuma sab’anin hakan sai ya zama k’unci da damuwa ne akewaye dashi.

B’angaren Fou’ad kuwa tuni hawaye sun fito daga cikin idanunsa, dama shi akoda yaushe me raunine, Jin matsalar da abokinnasa ya samu ne kuma ya k’ara jaddada rauninsa, tausayin Maleek d’inne kuma ya cika zuciyarsa.

Najeeb kuwa hannayensa duka biyu yasa ya tallafi hab’arsa tare da aje idanunsa akan had’add’en carpet d’in dake malale atsakiyar d’akin, sosai jin matsalan da Maleek d’in ya samu ya sashi acikin shock, akaron farko kuma kenan da yaji tausayin Maleek d’in, tare dajin wani irin abu na musamman acikin zuciyarsa.
Chapter 99 · 0% Book details