← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 144

Sashe 25

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Note Editing*

*(am sorry na muku late update wallahi bani da charge ne, kuyi manage da wannan insha Allah Gobe da safe zan muku sabon update yanzu wayana saura 10 percent😪.)*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
Fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammad Sardauna Jaiz bank, Whatsapp number 07017879464.)*

*Chapter 13*

Hannu Abbou Jaheed yasa ya dafa kafaɗanta, cikin kulawa haɗi da muryarsa da tayi sanyi yaƙira sunanta, saboda kukan nata ya farayin yawa, wanda hakan kuma zai iya haifar mata da ciwon kai me tsanani.
Jin yanda Abbou yaƙira sunanta asanyaye ne yasa ta soma ƙoƙarin daidaita nutsuwarta, tare kuma da ƙoƙarin shanye kukan da takeyi ɗin, saidai duk yanda taso tsaida kukan nata hakan yaci tura, domin kuwa kukan ya riga da yaci ƙarfinta,wanda har hakan ke ƙoƙarin fallasa sirrin dake cikin zuciyarta.
sheshsheƙan kukan da take sakewa ne yasa Abbou Jaheed ɗin miƙo mata bottle water me sanyi, ayanda takejin ƙirjinta nayi mata ƙuna, yasa batajin zata iya ƙin amsan ruwan, hannunta dake rawa tasa ta karɓi goran ruwan, yayinda shi dakansa ya buɗe mata murfin goran, takai ruwan bakinta. Sosai ta shiga tuttulawa cikinta ruwa, har saida tasha fiye da rabin goran, ganin yawan shan ruwan zai iya kawo mata wani abu na daban, ko ma ta iya ƙwarewa ne yasa Abbou Jaheed ya karɓi bottle water'n daga hannunta. Ajiyar zuciya ta shiga sauƙewa akai akai yayinda takejin zuciyarta ta sakeyi mata nauyi, gaba ɗaya haka taji komai na duniyar ya daina yi mata daɗi, yayinda taji wani abu me nauyi ya tokare mata aƙirjinta, still ga kuma wani irin ciwon kai da takeji, wanda har ta kai ga tanajin kannata na sarawa, miƙewa tsaye tayi tare da lumshe kyawawan idanunta wanda sukayi jajur, suka kuma bayyanar da zallan abun dake cikin zuciyarta, wato haƙiƙanin gaskiyar da ita kanta batasan da cewar tana kwance acikin zuciyarta ba.
Kallonta Abbou Jaheed yayi cikin tausasa murya haÉ—i da tausayinta yace. "Ina zakije, bayan kuma bakici abinci ba?."
ÆŠan buÉ—e runannun idanunta da suka soma lumshewa tayi, cikin sanyi da kuma muryarta daya soma dashewa tace. "Bacci nakeji Abbou, zanje É—aki ne na kwanta."
ÆŠan jim yayi, kana cikin yarda da abun da tafaÉ—a É—in ya jinjina mata kai alaman "Taje ta kwanta."
Batajin zata iya sake ɗaga idanu ta kalli wani daga cikinsu, saboda haka asanyaye ta juya ta nufi hanyar sauƙa daga step na dining area'n.
Da kallo Abbou Jaheed ya bita yana mejin wani abu na yawo acikin ransa, hakanan yakejin kamar kukan da ta keyi, bana haka kawai bane yana ɗauke ne da ma'anoni guda biyu, wanda kuma yakasa fahimtar haƙiƙanin ma'anar hakan, saidai wata zuciyar tana nusar dashi cewar bawai tana kukane saboda batason zaɓin da yayi mata ba, tana kukane saboda al'amarin yazo mata abazata, kasancewar har yanzu ita yarinyace. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan yin shiru, kana ya daina cin abincin da yakeyi.
Aɗaya daga cikin ɓari na zuciyarsa sam bayajin cewa zaɓawa Laylerh miji da yayi, kawo nakasu ne acikin rayuwarta, domin yayi imani cewa Najeeb zai kula da Laylerh sosai. haka zalika bazai taɓa barinta tayi kukan maraici ba, saidai kuma ya rasa me yasa wata zuciyar tasa ke so da ƙoƙarin kawo masa wani tunani na daban adangane da hakan, wanda kuma ya tabbatar cewa tunanin hakan bazai amfanar dashi da komai ba, ganin da yayi damuwa na ƙoƙarin shiga zuciyarsa ne ya sashi share duk wani tunani ya cigaba da cin abincinsa, aransa yana me fatan hakan da yayi ya zamanto Alkhairi agaba ɗaya rayuwarsu.

Maleek.
Dake tafiya yana gauraya hanya, kamar yanda ya baro cikin falon baya iya ganin gabansa sosai, haka ma har yanzu dishi dishi yake gani a idanunsa, ahaka ya ƙaraso cikin tamfatsetsen bedroom ɗinsa wanda ke cike da kayan alfarma. Hannunsa dake rawa ya ɗaura akan handle ɗin ƙofar, tare da maida ita ya rufe, ahankali ya jingina bayansa da jikin ƙofar tare da rumtse jajayen idanunsa masu kama da garwashin wuta, zuciya da ƙirjinsa ne keyi masa wani irin zafi da suka, yayinda wani irin ɗaci ke mamaye maƙoshinsa, ƙwaƙwalwarsa ce ke ƙoƙarin zautar dashi, ta hanyar dawo masa da maganganun Laylerh'n cikin kunnensa. *"NA AMINCE"* wannan kalmar da ta faɗa tafi komai haukata tunaninsa,domin jin sauƙarta yayi acikin kunnensa tamkar diran aradu, kwata kwata bayajin zai iya jurewa, wani abu me kama da fargaba ne ke neman daƙushe tunaninsa, hakanne kuma ke sa zuciyarsa tsananta bugawa, har takai ga yana iya jin faɗuwar gaba da kuma wani yanayi na daban, sam bai saba da irin wannan yanayin da yakejin kansa aciki ba, wanda hakanne yasa bayajin zai iya jurewa.
Asanyaye ya buɗe idanunsa wanda suka sake runewa, yayinda kansa ke masa wani irin ciwo, irin wanda bai taɓa jiba, ahankali ya shiga taka ƙafafunsa da suke gab da kasa ɗaukar nauyinsa, saboda yanda gaba ɗaya jikinsa yayi weak, ƙarasawa gaban tsayayye kuma babban mirror'n dake manne agefen drawer'nsa yayi. Jajayen Idanunsa ya sauƙe akan madubin, wanda hakan yabashi daman kallon hoton bayyananniyar surar jikinsa, tun daga kan ƙafarsa har zuwa kansa, akaro na farko kenan daya taɓa zubawa kansa idanu ta cikin madubi, hakanan yaji gaba ɗaya zuciyarsa tayi rauni, wanda har hakan ya bayyana acikin idanunsa. "RAUNI!" Ya faɗa cikin wata irin murya, tare da rumtse idanunsa ƙam, domin itace kalmar daya fi tsana arayuwarsa, sanin cewa itace take ta wasa da zuciya haɗi da Ƙaddaransa.
Hannunsa dake adunƙule yasa ya bugi daidai saitin zuciyarsa, still cikin wata murya me ɗauke da wani irin amo dake son bayyana jajircewarsa yace. *"I am not a LOSER, and i will never be LOSER."*
Ɓuɗe idanunsa da suke a rumtse yayi tare da jingina bayansa da jikin bango, tabbas ayanzu shi kaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, duk da cewar yanajin zafi da raɗaɗi azuciyarsa, amma bayaso ya zamanto RAGO, aƙidarsa ce kuma fatansa ne, akullum yasan cewar shiba Rago bane, har yanzu kuwa yanaji ajikinsa cewa har abada bazai taɓa zama rago ba, duk da kuwa yasan cewar Ƙaddaransa nada rauni, amma hakan bazai sashi zama me kasawa ba, yanaji ajikinsa cewar kalmar LOSER bazata ci gaba da yawo acikin jininsu shida abokinsa SOORAJ ba, duk da kuwa cewar yasan SOORAJ yayi nasara na samun abun da yakeso, amma shi wata zuciyar bata gaya masa cewar zaiyi nasara.

Acan falo kuwa Najeeb da gaba ɗaya kukan Laylerh'n ya gama ɗaga masa hankali, ɗan jingina bayansa da jikin kujeran da yake kai yayi tare da lumshe idanunsa. Tabbas yasan cewa yana cikin farinciki ayau, domin samun Laylerh ba ƙaramar sa'a bace ga kowanni Ɗa Namiji, saidai kuma kukan dayaga tanayi ya matuƙar taɓa masa zuciya, duk kuwa da yanda ya zurfafa tunaninsa ya kasa tantance wa da kuma gano kukan nata na miyene, saboda zuciyarsa bata kawo masa cewar akan aurensa take wannan kukan ba, domin ya yarda cewa shi namiji ne da kowacce mace zatayi fatan samu, why Laylerh zatayi kuka akan maganar aurensa da ita?. Wani irin killer smile ya sake tare da ɗan soma jujjuya kujeran da yake kai, bayajin zai damu da koma meye, saboda yaji ajikinsa cewa Laylerh mallakinsa ce.
Momy kuwa da jin batun auren Laylerh da Najeeb, yasa ta aikin saƙawa da kuncewa acikin zuciyarta, samun mafita da tayi yasa ta saki murmushi me ɗauke da ma'anoni daban daban, cikin nuna kulawa da kuma son auren tace.
"Masha Allah Najeeb angon Laylerh, gaskiya wannan bikin na Æ´an gata ne, saboda haka ya kamata mu fara shiri tunda wuri, congratulation na ta yaka murna."
Murmushi Najeeb ɗin yayi tare da yin ƙasa da kansa, Abbou Jaheed da Alhaji Ahmad Rufae ma murmushin sukayi, domin sun riga da sunsan me suka shirya, Abbou Jaheed ne ya dubeta, cikin kulawa yace. "Karki damu very soon za'ayi biki Insha Allah, maybe ma nanda 3 to 4 weeks."
Cike da mamakin kusancin abun Momy taÉ—an zaro idanunta, wani abu kuma da ta tunane ya sata sakin murmushi. Tare da cewa. "Allah Ya kaimu."
"Ameen." suka faɗa atare daga haka kuma babu wanda yasake cewa komai acikinsu suka ci gaba da cin abinci, zuciyar Abbou Jaheed fari tas, domin gashi da yardar Allah Zai cika alƙawarin daya ɗaukarwa Amininsa, saidai kuma har yanzu idan ya tuna wani abu sai yanajin fargaba da kuma faɗuwar gaba na ziyartarsa, sanin cewa sharrin shaiɗan nada yawa ne ya sashi soma faɗin "A'uzubillahi!." acikin zuciyarsa, dan yasan da hakane kaɗai zai samu tsira daga abun da yakeji, wanda har yake zargin kansa da rashin aikata daidai.
Chapter 25 · 0% Book details