← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 144

Sashe 22

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ɗago kai Abbou yayi ya kalli Maleek ɗin, wanda har yanzu fuskarsa ke cikin tafin hanunsa.              
Kansa kawai ya girgiza, da kansa ya ɗauko ƙanƙara acikin fridge tare da  ɗaurawa Laylerh'n asaman ƙafarta inda indomie din ya ƙona ta.
Dubanta Abbou yayi cikin kulawa yace."Kije É—aki ki kwanta kinji, nasan zuwa anjima ciwon zai daina miki zafi."
Kanta ta jinjina tare da É—an jan sheshshekan kuka.
Mikewa tsaye tayi haɗe da ɗan ɗaga ƙafarta ta soma takawa ahankali, taku biyu kadai tayi ta tsaya da tafiyan tare da sakin yar siririyar kara, zafin da ta ji sosae ne yasata rumtse idanu, tare da cije laɓɓanta.       
Cikin zafi da kuma radadin da takeji tace "Abbu kafana zafi, bazan iya tafiya ba." Yanayin yanda tayi maganan tana me yarfa yan yatsun hannunta ne yasa Abbou jin tausayinta.
Kallon Maleek Abboun yayi cikin yanayin bada umarni  yace.
"M.J ka mata ka kaita É—aki please bari zan kira Dr."
Jin abun da Abbou'n ya fada ne yasashi saurin dago kansa.
Kai Abbu dake kallonsa ya jinjina masa tare da haÉ—e fuska.
Bottle watern dake aje a gabansa ya zubawa ido, yayinda zuciyarsa ta Shiga saka masa abubuwa da yawa.    Ajiyar zuciya ya sauke tare da dagowa ya kalli inda Laylerh ke tsaye, wanda tsawon one minute kenan da take tsaye ta kasa tafiya.
Kujeran da yake zaune akai ya ɗan baya tare da mikewa tsaye, ya nufi inda Laylerh'n ke tsaye, yayinda gaba ɗaya idanunta suka kaɗa sukayi ja.      Hannunsa ya ɗaura akan kafaɗarta, wanda hakan bisa dole ya tilasta mata juyowa, ɗan ranƙwafawa yayi     batare da tunani ko tsammani ba kawai taji ya ɗaga ta caɗak.     
wani irin abu me kama da shocking ne ya shiga yawo ajikinta.
Idanunta ta rumtse da ƙarfi, domin hakan ya zama wani baƙon yanayi  na musamman agareta, akaron farko kenan da ta samu kusanci dashi har haka, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya soma ratsa hancinta, tare da  cakuɗewa da numfashinta.      
Samun kanta ajikinsa da tayi, yasa bata da wani zaɓi daya wuce maƙale wuyansa da hannayenta, Cikin nutsuwa ya nufi hanyar da zai sadashi da ɗakinta,  daga gefe guda kuwa irin yanayin riƙon da yayi mata ne yasa tsikar jikinsa mimmiƙewa, lokaci ɗaya brain ɗinsa ta soma  ƙoƙarin juya  tunaninsa zuwa wani waje daban.  
Ƙarasowarsu bakin ƙofar ɗakin nata ne yasa shi tura ƙofar da ƙafarsa, wanda hakan yasa ƙofar  buɗewa da kanta.   
Yana kutsa kansa cikin ɗakin sassanyan ƙamshin cool perfumed ɗinta ne ya ratsa cikin hancinsa, hakanne ya sashi ɗan lumshe idanunsa,  shi mutum ne me tsananin son ƙamshi  wannan ne yasa hancinsa baya raina ƙanshi aduk inda yake.         Ƙarasowa cikin ɗakin yayi,  sai kuma alokacin ne ya kai dubansa kan kyakkyawar fuskarta.                
Wanda har yanzu idanunta alumshe suke, yayinda zara zaran eye lashes ɗinta ke jiƙe da danshin ruwan hawaye, dawo da kallonsa kan ƙananan  lips ɗinta yayi, wanda duk ta tattaune su da teeth ɗinta hakan yasa sukayi ja, take yaji wani irin abu na mamaye duk ilahirin jikinsa, wanda hakan ya sashi saurin ɗauke idanunsa akanta.
ƙarasawa kan ɗan madaidaicin gadon nata yayi, ahankali ya soma ƙoƙarin zareta daga jikinsa, tare da kwantar da ita akan gadon.   
Jin ya kwantar da ita akan gado ne yasa ta saurin juya masa baya tare da cusa kanta acikin pillow, tabbas da ace zai ga yanda ƙirji da zuciyarta ke bugawa sanadin ɗaukarta da yayi, to da bai ɗauketa a daddaɗan jikinsa kamar yanda yayi ayanzun ba.    
ÆŠan lumshe idanunsa yayi tare kuma da buÉ—esu alokaci guda.
Akaro na biyu kenan da tun dawowansa ya tsura mata idanunsa masu rikitata.      
Kallon dogon dunƙulallen gashin kanta wanda ya baje akan pillown da ta ɗaura kanta sanadin juya masa bayan da tayi yayi, ahankali ya soma yawo da idanunsa akanta, har zuwa kan hips ɗinta da suka sake cikowa, ƙasa yayi da kansa ahankali ya ɗan soma jan jikinsa baya, tare da zuba hannayensa acikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa. Abu ɗaya ne ke yawo acikin zuciyarsa, wanda akullum kuma ako da yaushe ke sukan zuciyarsa, wanda hakan kuwa shi ya haifar masa da rauni me girma acikin rayuwarsa, bayajin zai iya jure kallonta,domin yayi imani cewa itace raunin zuciya da kuma rayuwarsa, sannan kuma ya jima da sanin cewa itace  ƙaddara mafi girma agaresa, tabbas akwai wani abu dake kwance acikin ƙirjinsa, wanda yake azabtar da zuciyarsa akowacce rana.  Baisan meyasa yazama haka ba, baisan kuma dalilin dayasa raunin zuciyarsa ke ƙara fallasa kansa akowacce rana ba, baya fatan wani lokaci yazo masa da zai kasa jure abun da yake ji.
Kansa ya soma  girgizawa, sakamakon yanda yaji kasala na ƙoƙarin sauƙar masa, cikin sauri ya juya ya fice daga cikin ɗakin.                  
Jin alaman ficewarsa daga ɗakin ne yasa Laylerh dake kwance  buɗe idanunta, tare da juyowa tabi ƙofar ɗaƙin da kallo, wani irin sanyi ne ke ratsa duk jikinta, yayinda daddaɗan ƙamshinsa ya kama numfashinta.     Idanunta ta lumshe wanda hakan ya bawa hawayen dake cikin idanun nata daman gangarowa.    
Tabbas yau ranace ta musamman agareni, mutumin da nake gani acikin mafarkina ya bayyana,  "Ya. M.Jay" tafaɗa cikin tsananin shauƙin da takejin kanta aciki.
Sam bata taɓa kawo cewa M.JAY shine mamallakin waƴannan kyawawan idanun da take gani acikin mafarkinta ba.
Hannu tasa tare da dafe daidai saitin zuciyarta dake ta faman bugawa da ƙarfi.          
Tuno da yanayin da kuma zalla. kyawun eye balls dinsa da tayi ne,  yasa ta ƙanƙame jikinta waje ɗaya, pillown dake gefenta tayi rungume tare da ɗan sakin murmushi.    
"Jikin ka akwai daɗi ya M.Jay, haka ma ƙamshin ka komai naka akwai daɗi na tabbatar da hakan!."        Tafaɗi hakan cikin yanayin dake bayyana zallar abun dake zuciyarta, take taji ta nemi duk wani zafin da ƙafartata keyi mata ta rasa.          

Ɓangaren Maleek kuwa yana fita daga cikin ɗakin nata kai tsaye part ɗinsa ya wuce.    
Yana shiga cikin bedroom ya turo ƙofar dakin nasa ya rufe, tare da murzawa ƙofar key.
Ahankali ya ɗan jingina bayansa da jikin ƙofar, tare da lumshe gajiyayyun idanunsa.   
Bai tabbatar da abun da yakeji ba sai ayau ɗin, Lallai ne  akan Laylerh komai na musamman ne agareshi.  Buɗe idanunsa yayi haɗe da ƙarasowa cikin ɗakin, kan wata haɗaɗɗiyar kujera ya zauna tare da sanya hannu ya dafe kansa, still ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗan dafe ƙirjinsa.       Abubuwa da yawa ne ke yawo acikin tunaninsa, ahankali ya soma ɗan murza gold ring ɗin dake hannunsa,  daga gefe guda kuwa idanunsa ne suka kaɗa sukayi ja, tabbas tausayi da rauni sun riga da sunyi tasiri acikin rayuwarsa, wanda sanadin haka ako da yaushe yakanjin cewa ba akan daidai yake ba, ako da yaushe LAYLERH ce, kaman yanda jini ke gudana acikin jikinsa haka zanen ƙaddaranta ke bibiyan rayuwarsa.       Ƙaran wayarsa ne ya katsesa daga duniyar tunanin daya ke ƙoƙarin faɗawa.     
Kallon wayar tasa yayi, ganin sunan Abbou Jaheed  na yawo akan screen ɗin wayar ne ya sashi ɗagawa tare da kara wayar akan kunnensa.      
Abbou Jaheed dake zaune jin Maleek  ya ɗaga wayarne yasa shi cewa.   "Idan kayi sallan Isha kazo dinning area inason ganinka."       
"To."  ya amsa  cikin wata irin murya, dan lokaci ɗaya yaji ƙirjinsa na bugawa.    
Take Abbou Jaheed na gama jawabinsa ya kashe wayar.  
Jin Abboun ya katse ƙiran ne ya sashi aje tasa wayar shima, tare da miƙewa tsaye ya shige bathroom.         
Ruwa ya sakarwa kansa saboda hakanne kaɗai zai sama masa relief daga abun da yake ji a zuciyarsa.         

Najeeb..
tsawon mintuna 20 kenan da ya keta juyi akan makeken gadonsa, gaba ɗaya tunanin Laylerh ya hanawa ƙwaƙwalwarsa sukuni, wani irin hot feeling yakeji adangane da ita na ratsa duk ilahirin jikinsa, hakanne yasa yafara tunanin cewa abun daya ɗauka da wasa zai iya fin ƙarfin tunaninsa.   Jin ana ƙiran sallan Isha ne ya sashi miƙewa, ya shige  toilet tare da ɗauro alwala.  Yana fitowa kaitsaye ya wuce masallaci.   

7:30 pm  daidai Abbou Jaheed da Alhaji Ahamad Rufae suka shigo cikin gidan, yayinda Najeeb ke biye dasu abaya, ahaka har suka ƙaraso cikin falon.  Yayinda yau Momy da kanta ta shirya musu diner, bayan tasa Larai ta girka musu foods kala kala haɗi da drinks.       
Kujera Abbou Jaheed yaja ya zauna tare da duban  Larai dake ta aikin mopping tiles ɗin falon,  yace ta kira masa Laylerh. Cikin girmamawa kuwa  tace "To ranka shi dade."   Ahanzarce ta nufi ɗakin Laylerhn.     
Chapter 22 · 0% Book details