← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 144

Sashe 98

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Almost 20minute kenan yanzu da shigowarta cikin d’akin, amma gaba d’aya har yanzu ta kasa daidaita nutsuwarta, Sam batasan me yake damunta ba, amma saidai tayi amanna cewa moment d’inta dashi na d’azune duk ya rikita ta.
Domin kuwa har yanzu idan ta tuna da yanda lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa ya gogi nata fuskar saitaji tsikar jikinta ya tashi.
Idanunta dake bayyana zallan gajiya ta lumshe ahankali tare kuma da bud’esu alokaci guda, kana ta sauk’e wata irin sassanyar ajiyar zuciya, agogon bangon dake sak’ale acikin d’akin ta kalla.
8:30pm daidai da idanunta suka nuna matane yasata mik’ewa tsaye, tare da nufan toilet donyin wanka, saboda asonta sam bataso Najeeb ya dawo gidan ya sameta idanunta biyu.
Koda ta shiga cikin toilet d’in kayan dake jikinta ta rage tare da had’awa kanta ruwan wanka mai d’an d’umi a bathtube.
Sam bata wani b’ata lokaci awajen wankan nata ba, bayan ta gama wankanne kuma ta fito daga cikin toilet d’in jikinta sanye da bathrobe.
Ad’an hanzarce ta tsane ruwan dake jikinta, tare da k’arasawa gaban dressing mirror ta shafa wani body lotion dinta tare da turaren body spray maidad’in k’amshi.
Yanayin kuma yanda takejin kanta agajiyene yasa akasalance ta k’arasa gaban makeken drawer d’inta, wani sauk’akk’en doguwar rigar bacci mai kalan light blue ta saka ajikinta wanda gaba d’aya jikinsa ya kasance na net ne, sosai kuwa rigar ta amshi jikinta tare kuma da bayyana zallan kyawunta.
Koda ta kalli madubi kuwa ita kanta tasan cewa tayi kyau.
Hasken wutan daya cika d’akin ta rage tare da hayewa saman gado ta kwanta.
Mintuna kad’an da kwanciyarta kuwa bacci mai nauyi ya d’auketa, duk da cewar rabonta da tasa wani abu abakinta tun safe, amma haka ta gwammacewa kwana da yunwa.

Ahankali Najeeb ya turo k’ofar d’akin ya shigo, ganin kuma babu wadataccen haske acikin d’akinne yasashi k’arasawa jikin makunnin wutan ya kunna, take kuwa haske ya mamaye d’akin.
Yalwatan haske acikin d’akinne kuma yayi sanadiyar sauk’e idanunsa akanta.
Baccinta take cikin kwanciyar hankali yayinda ta dunk’ule duka hannayenta ak’irjinta.
Wani irin murmushine ya sub’uce masa sakamakon yanda yaga tayi masa matuk’ar kyau, ahankali ya k’arasa shigowa cikin d’akin, tare da ajiye ledodin dake hannunsa akan bedside.
Batare kuma daya yi abunda zai tashetaba ya shiga rage kayan jikinsa, saida ya cire komai sannan ya d’aura towel kaitsaye ya wuce bathroom.
Wanka kawae yayi batare kuma daya d’au wani dogon lokaci acikin bathroom d’inba ya fito duk gaba d’aya jikinsa d’auke da danshin ruwa.
Zama yayi na musamman a gaban dressing mirror ya kimtsa kansa, bayan ya gamane kuma ya zura wasu simple riga da wando wayanda basuda nauyi.
Haka ya nufo kan gadon yana ta zuba k’amshi.
Sanin kuma da yayi cewar Laylerh’n bataci abinci bane yasashi soma k’iran sunanta.
Acikin magagin bacci kuwa ta amsa masa batare da ta tashi zaune ba, ganin hakanne kuma yasashi d’agota ya zaunar da ita.
Hannunsa yasa ya shafa gefen fuskarta, cikin matsanancin so da kuma sha’awarta dake cinsa ko wacce rana yace.
“I’m sorry na tasheki ko, nasan bakici abinciba shiyasa, kici idan yaso saiki koma baccin.�
Fuska ta shagwab’e tare da karyar da wuyanta gefe, cikin yanayinta na bacci da kuma zallan shagwab’a tace.
“Nifa nak’oshi.�

Kansa ya d’an girgiza tare da jawo ledan daya shigo dashi babban robar vanilla ice cream din daya sayo mata ya bud’e tare da d’aura mata roban akan cinyarta.
Cikin kulawa yace.
“Naji kin k’oshi to amma kisha Ice cream.�
Jin ya ambaci ice cream ne yasa ta bud’e idanunta, ganin kuma da gaske Ice cream d’inne agabanta yasa ta d’an saki murmushi, batare da ta sake cewa komae ba kuwa ta d’auki robar ice cream d’in ta shiga sha tana wani lumshe idanunta masu yalwar lashes asamansu, sosae kuwa take enjoying shan ice cream d’innata.
Shikuwa Najeeb kwalin pizza’n da yayi ordering ya ciro tare da bud’ewa ya soma ci.
Time to time yake kallon Laylerh’n da zuwa yanzu Tasha kusan fiye da rabin roban ice cream d’in.
Kusan mintuna 20 ya d’auka yana cin abincin saidai kuma jin shiru babu motsin Laylerh’nne yasashi juyowa ya kalli b’angaren da take.

Cike da mamaki ya d’an zaro idanunsa sakamakon ganin da yayi cewa Laylerh’n har ta sake komawa bacci, ga hannunta kuwa rik’e da robar ice cream d’in da zuwa yanzu ya kusa zama ruwa dukansa.
Yanayin yanda take baccin azaune ne yasashi d’an sakin murmushi, asanyaye yace.
“I’m sorry kingaji sosae ko kuma nazo na tasheki.�
Hannunsa yasa ya dauke robar ice cream d’in tare da gyara mata kwanciyan da tayi.
Sauran pizza d’in dayaci ya d’auka yakai kitchine.
Bayan ya dawone kuma ya rage musu hasken wuta, had’e da hayewa saman gadon ya kwanta agefen Laylerh, tattausan blanket ya rufa musu ajikinsu, ahankali kuma ya lumshe idanunsa yana me shak’an daddad’an k’amshin dake fita ajikinta, duk da cewar yaud’in baiyi kusa da ita sosae ba, amma kuma hakan baihanashi jiyo sassanyan k’amshin dake fita ajikinta ba.

Hakika yana matuk’ar buk’atar ta, yana tsananin son yajita acikin jikinsa, yanason ya Santa acikakkiyar y’a mace, amma har yau yakasa samun daman hakan, saudayawa yakan tambayi kansa cewar.
“Shin meyasa har yau ya kasa kusantar Laylerh’n duk da cewar bataso?.�
Saidai bashi da amsar dayake bawa kansa, haka dai yabar abun acikin zuciyarsa.
Da tunani kala kala bacci b’arawo ya d’aukesa.

Washegari.

Tun tashinta yau d’in ta gyara komai nata, duk da cewar babu wani abu na part d’in nata dake da datti amma haka ta gyara komae.

Yayinda acikin zuciyarta kuwa Allah Allah Take Oum Ayush ta k’irata tace tazo suje asibiti, hakanne kuwa yasa tayi wanka ta kuma shirya kanta cikin riga da sket na atamfa wanda sukayi mata kyau sosae.
Saidai abunda batasani ba kuwa shine tuni har Oum Ayush ta bada breakfast ankai asibitin domin tunda sassafe Abbou Khareem da kuma Abbou Jaheed suka tafi asibitin kasancewar Dr.Mouhammad yace yau zai bawa Maleek d’in sallama.

B’angaren Najeeb kuwa yau da sassape ya tafi office kasancewar yana da wani aiki mai mahimmanci dazai gudanar, shiyasa koda Laylerh’n ta tashima bata sashi acikin idanunta ba, saidai yabar mata sak’on breakfast.

Ganin da tayi shiru Oum Ayush bata k’irata bane yasa kaitsaye ta wuce sashin Oum Ayush d’in, koda taje afalo ta samu Oum d’in.

Ganintane yasa Oum Ayush fad’ad’a murmushin dake kan fuskarta cikin kulawa tace.
“Laylerh yana ganki kodae su Maleek d’in sun isone?�

Kanta ta girgiza ahankali cikin sanyin murya tace.
“Aa amma Oum Ayush baza muje asibitin bane?�

“Eh ae zuwa asibiti ya k’are mana saboda anjima kad’an za’a sallamo Maleek d’in, Dr. yace babu wata damuwa kuma kinsan halin Maleek baicika son takuraba kinga kuma zama a asibiti koya yake akwae ta kura acikinsa.�

Kanta ta d’an rausayar gefe tare da neman waje ta zauna acikin falon, hakanan duk sai taji wani iri domin kuwa burinta ayanzu shine taga Maleek d’in.

Acan asibiti kuwa Dr. Mouhammad ne yashigo d’akin shida sauran wasu doctors suka sakeyiwa Maleek wasu gwaje gwaje bayan sun kammala gwaje gwajen nasune kuma suka rubuta masa irin magungunan da zaisha dama ta kardar sallamansa, duk da cewar akwae buk’atar yake zuwa duk bayan 1 weak suna duba lafiyar mararsa.

Godiya sosai su Abbou Jaheed sukayiwa doctors d’in, tare da d’aukan duk wani abubuwan da suka zo dashi suka kai mota.
Koda sukazo tafiya d’in kuwa har bakin mota Dr.Mouhammad ya rakosu sukayi sallama ta mutumci, tare da shaidawa Maleek cewar lallai yake zuwa suna dubashi.
Shidai kam da kai kawae yake amsawa Dr. d’in domin kuwa sam bayason yawan magana.

Koda suka kama hanyar dawowa gida jingina bayansa da jikin kujerar motar yayi tare da lumshe tsumammun idanunsa.
Bai bud’e idanun nasaba kuwa har saida suka iso compound d’in gidan nasu.

Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, wanda kuwa hakan yayi daidai da shigowar motar Alhaji Farouk cikin compound d’in gidan.
Da Mamaki Ya shiga kallon motar, yayinda Abbou Jaheed kuwa yaje ya taro abokinnasa cikin karramawa.

Juyawa Maleek d’in yayi danufin tafiya sashinsa, amma saidai jin Abbou Jaheed na cewa dukansu su wuce falonsa ne yasashi da katawa badon ransa ya soba kuma haka yabi bayan su Abbou Jahedd d’in.

Koda suka k’arasa falon Abbou Jaheed d’in mai yanayi da aljannar duniya, zama kowannensu yayi.
Nanfa Abbou Jaheed da kuma Alhaji Farouk suka shiga sabon gaisawa.

For the second time kenan dayaji gabansa na d’an fad’uwa, wanda kuma tun acikin asibiti yakejin hakan, baikuma san dalili ba, ahankali ya shiga addu’a da kuma fatan cewa koma meyene yazo masa cikin sauk’i.

Shigowar Oum Ayush da kuma Laylerh dake biye da ita abayane yasashi d’an lumshe idanunsa, domin kuwa duk da bai d’aga idanunsa ya kalleta ba amma k’amshinta ya isar masa.

Laylerh kuwa da k’irjinta keta faman dukan uku uku ahankali ta nemi waje anan k’asan sofa ta zauna, Sam batasan meyasa tunda Oum Ayush ta fad’a mata cewar Abbou Jaheed na nemansu ba, taji gabanta na fad’uwa domin kuwa tasan cewa Abbou Jaheed baya neman mutum haka kawae.
Ae kuwa zuciyarta bata k’ara tsinkewa ba saida taga Najeeb ya shigo cikin falon, hakanan taji wani irin tsoro ya lullub’eta, take kuwa zuciyarta ta raya mata cewa.
“Kodae Najeeb ne ya kawo k’aranta akan cewa bata basa hakk’insa�
Tabbas hakan zaiyiwu, amatuk’ar tsorace ta hade jikinta waje d’aya tare da sunkuyar da kanta da sauri.

Abbou Jaheed kuwa ganin dukansu sun ballara acikin falonne yasashi gyara zamansa tare da duban kowannensu, lokaci d’aya kuma yanayinsa ya sanja, ahankali cikin karyewar zuciya da kuma sanyin yanayi yace.

“Tabbas ban had’aku awajennan don maganan da zanyi ya zamo tashin hankali agareku ba, K’warai nasan cewa zakuji babu dad’i kamar yanda nima naji kuma har I yanzu nake kan ji.
Lallaine kuma Tabbas kamar yanda dukkaninku kukasani K’addara takan iya zuwawa bawa tako wanni siga, haka kuma Allah Yakan jarraba bawansa ta hanyar da duk yaso, da bara ko wayo kuma bazaisa ka kub’ucewa hakan ba.
Sannan kuma inason kowannenku yasan cewar zan fad’i maganan nan a gabansa ne saboda matsayi da kuma cancantar cewa ya kamata yasani, gaba d’ayanku duka k’ok’arin zama y’an Uwa muke, saboda haka nayi imani cewa matsalar d’aya daga cikinmu na mune dukan mu.�
Chapter 98 · 0% Book details