← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 144

Sashe 116

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin abunda bai wuce 15minutes ba kuwa saiga Aunty Zee d’in tazo, har bakin Mota Teemah ta raka Laylerh’n, saida taga tafiyarsu kuma kafun ta koma cikin makarantar dan a cewar ta zata shiga library’n makarantar tasu fad’an tab’a karatun exam d’in da zasuyi gobe, saboda goben ma two papers zasuyi.

B’angaren Laylerh’’n ma hakance takasance dan Koda suka koma gida karatu ta wuni yi, duk da yanda takejin soyayyarsa nayi mata suka acikin zuciyarta amma haka ta daure, musamman ma da ayanzu ta gano cewa idan babu tunaninsa acikin mind d’inta to babu abunda zata iya.

Koda dare yayi kuwa bata wani iya samun bacci sosae ba, karatu tayi sosai, Yayinda kuma kewarsa ke k’ara cika wani sashi na zuciyarta wanda har hakan yake sawa taji kamar tayi kuka.
Haka dai tayi ta abu d’aya har saida dare ya raba kafun ta iya samun bacci.

*Washegari*

Kamar dai yanda jiyan suka tafi school tare da Aleeya, haka ma yau, still saida aka sauk’eta kafun aka wuce da Aleeya.

Balaifi kuma exam d’in nasu na yau ya d’anyi musu sauk’i.
Paper biyu sukayi saidai yau ba kaman jiya ba sai 12 dukansu sukabar makarantar.

Daga wannan ranan kuwa koda yaushe ya zamana Laylerh’n tana cikin karatu, duk da kuwa tanajin matsanancin kewarsa acikin rai da zuciyarta amma haka take daurewa, aduk lokacin da tayi imagine d’insa kuwa haka takejin kaman zata shid’e.
Yayinda akullum hot feeling d’in da takeji akansa ke sake k’aruwa

**** *** ***

Tabbas adaidai irin wannan lokacin idan tace batajin dad’in zama agidan Aunty Zee tayi k’arya, domin suna bata kulawa maikyau, sannan kuma kullum sai tayi waya da Abbou Jaheed da kuma Oum Ayush, Yayinda Abbou Khareem ma ke k’ok’arin k’iranta.

Afannin mu’amala kuwa ita da Aleeya yanzu sun zama k’awaye sosae, aduk
lokacin da sukaje exam suka dawo sukan zauna su taya Aunty Zee aikace aikacen gida, hakan kuwa bak’aramin dad’i yakeyiwa Aunty Zee d’in ba, shi yasa ma yanzun bata shakkan saya musu komai na k’yale k’yale idan ta gani.
Babban abun da yake bawa Aunty Zee d’in mamaki kuwa shine, yanda har abada, Laylerh’n bata tab’a gajiyawa da kallon wani hoton Maleek dake cikin wayarta, domin da yawan lokuta Laylerh’n takan zauna tayi shiru, idan kuma tana kallon hoton Maleek d’in abune mawuyaci kaga babu k’walla acikin idanunta, wannan abun kuwa shiyasa Aunty Zee take mamakin irin tsananin soyayyar da Laylerh’n keyiwa Maleek.

Kamar yanda ranar yau ta kasance Friday, wanda ayau d’inne kuma zasu kammala WAEC examination d’insu.
Hakan yasa duk d’aliban dake zana waec zuciyarsu ke cike da farinciki, ga masu shirin zana neco exam kuwa hankalinsu ya tafi gaba.

Kasancewar kuma yau itace ranan k’arshe, shiyasa d’aliban suka b’ata lokaci mai tsawo basu fito a exam d’in ba, domin ba kad’an ba paper’n da ta kasance na Maths ta basu wahala.
Wanda hakan yasa sai k’arfe 11am suka fito.

Gaba d’aya compound d’in school d’innasu cike yake da d’alibai maza da mata, Yayinda kuma fiye da rabin students d’in suka b’ata uniform d’insu da zanen maka different colours.

Tabbas awannan lokacin zuciyar gaba d’aya d’aliban cike take da farinciki.

Saidai kuma ita acikin nata zuciyar banbanci ne da nasu, dake d’auke da wani irin yanayi.
Yanayin da akowacce rana yake gudana acikin jikinta kamar jini.
Tabbas ba zata iya fad’in sunan yanayin nata kaitsaye ba, domin akullum salo da zafinsa sanjawa yake, saboda yana hurting d’in zuciya da gangar jikinta sosae.
Duk da kuwa cewar yanayin ada bai zamo bak’o agareta ba, amma ayanzu tanajinsa wani daban.
Domin kuwa koda Idanunta ta lumshe saitaga nasa idanun acikin nata.
Tabbas kuma hakan shi ne ke k’ara haddasa mata matsanancin kewarsa.

Koda sau d’ayane kuwa tanason sake sanyashi acikin idanunta, Kamar dai yanda sau d’aya tak kawai ya bar mata wani azababben yanayin da har abada bazata tab’a iya mantawa dashi ba.
Yanayin daya zamo sanyi kuma Garkuwa agareta, kana kuma yanayin da tunda take aduniya bata tab’a sanin akwaesa ba.

Wani irin tashi tsikar jikinta ya shiga yi, haka ma y’an hairs d’in dake jikinta suka mimmik’e, lokaci d’aya sweet moment d’in ya shiga yawo acikin Brain d’inta, wanda hakan ya haifar mata da wani irin bugun zuciya.

Hakanan taji tamkar yazune abun ke faruwa.
Hannayenta duka biyu tasa ta k’ank’ame jikinta, tare kuma da lumshe idanunta, wanda suke dake dawo mata da ganin lokacin daya sauk’e lips d’insa akan nata, acikin yanayin sanyi kuma ya tura sweet tongue d’insa acikin bakinta.

Wayyo Allah Tayaya ma zata iya mantawa da wannan best moment d’in?
Lallai jure hakan abune mai wahala, domin tayi imani a zuciyarta cewa idan irin hakan ya sake faruwa, babu ko tantama zata iya rasa numfashinta, domin abune mai matuk’ar girma da daraja samun professional kiss daga wajen wanda zuciya da gaba d’aya gangar jiki keso.
Tabbas wani lokaci magana bata aika sak’o zuwa ga inda zuciya keso, domin wani lokaci magana a iya kunne kawae take tsaya wa, bata kaiwa izuwa gangar jiki, madadin hakan kuwa abu biyune kawae ke tasiri wa gangar jiki da kuma k’wak’walwa, wannan abu biyun kuma sune KISS and HUGGING.

Amatuk’ar kasalance ta bud’e idanunta dake lumshe, tare da zubawa wayarta dake ringing idanu.

Ganin kuma numbern da ake k’iranta dashi d’in ba na Nigeria bane yasa ta d’an tsurawa wayar idanu.

Saidai kuma ganin k’iran na shirin katsawa ne
Yasa tayi saurin d’aukan wayar tare da kara ta akan kunnenta.

Hakan kuwa yayi daidai da samun kanta da tayi cikin wani irin bugun zuciya, take kuma taji wani irin sanyi mai tsananin dad’i na ratsa duk ilahirin jikinta, irin dai sanyin da awajen mutum d’aya kawae take samunshi, Tabbas wannan yanayin shi ya sauk’ar mata da kasala, wanda har hakan yasa ta kasa cewa komae.

Daga can b’angaren kuwa sauk’an numfashinta acikin kunnuwansa ne , yasa shi lumshe idanunsa wanda sukayi jajur, tare dasa hannunsa ahankali ya dafe saman mararsa.
Cikin wani irin sabon yanayin daya samu kansa aciki kuwa ya d’an saki wani silent growing tare da bud’e gaba d’aya labb’an bakinsa.

*18/March/2021*

*6:32 pm*
3/19/21, 9:08 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Chapter 69*

Hak’ik’a shiru da kuma dad’in yanayin da ta samu kanta aciki ya masifar shagaltar da ita, wanda har hakan ya sata maida idanunta ta lumshe, kana ahankali ta cigaba da sauk’e wani irin breath, wanda ita kanta batasan tayaya akayi sautin numfashin nata ke tashi har haka ba, sassanyar iskar dake ci gaba da k’ara ratsa duk ilahirin jikinta ne, kuma yasa ahankali cikin yanayi mai kama da zallan shagwab’a ta bud’e y’an k’ananun jajayen labb’anta.
Da muryarta wanda ke fitar da shaking sound tace.
“Assalamu Alaekum!!�

Adaidai lokacin kuwa, yaji wani irin abu me kama da shocking ya ratsa duk ilahirin jikinsa, wanda hakan yasa take kwantattun gargasan dake jikinsa suka soma mimmik’ewa tsaye, haka ma tunaninsa ya tsaya cak, hakan ya faru ne kuma saboda sauk’an, da daddad’a da kuma kasallliyar muryarta a cikin kunnuwansa.

Ahankali ya fusgo numfashinsa dake k’ok’arin d’aukewa, tare kuma da saurin zare wayar daga kan kunnensa, batare kuma daya amsa sallaman nata, ko yace wani abu ba ya k’urawa gaban screen d’in wayar tasa idanu.

Hak’ik’a yanzu shi kad’ai yasan meyake ji acikin jikinsa, domin jin muryarta da yayi ya goge masa duk wani lissafi da nutsuwarsa, musamman yanayin yanda maganan nata ke d’auke da wani irin salo na daban, salo mai cike da kasala, da kuma bayyana abunda ke cikin zuciyarta, domin kasancewarsa ma’abocinta, ad’an jin muryar ta da yayi yanzu, har zuciyarsa ta fassara masa yanayin da Laylerh’n nasa ke ciki.

Wani irin abune yaji nayi masa yawo acikin zuciya da kuma gaba d’aya gangar jikinsa.
Duk kuma ga yanda yaso motsa harshe da kuma labb’an bakinsa abun yaci tura, atak’aice ma dai haka yakejin kamar an nannad’e masa tongue d’insa.
K’warae yanason bayyana abundake cikin zuciyarsa, ko da hakan zaisa ya d’anji sanyi.
Saidai kuma amma tayaya zai iya furta hakan?
Yau sama da 2weeks kenan da yakejin wani irin matsanancin kewarta na Adda ae zuciya da gangar jikinsa, duk da cewar tunda yazo USA d’in bai zauna ba, amma kome yake yi tana nan acikin zuciyarsa, da tunaninta yake kwana, haka kuma da matsanancin kewarta yake wuni.

Sau dayawan lokuta yakan tambayi kansa shin yaushe ne zasu ji dad’in rayuwa shida ita? yaushe ne munanan k’addara zasu daina bibiyar rayuwarsu? sai yaushe ne zai sake samun wannan daman da ya samu abaya?
Daman kusantarta akullum akuma koda yaushe, hakika ada yana sake tsammatawa kansa rayuwa da ita, ko da sau d’aya yana buk’atar sake shagwab’ata kamar yanda yayi abaya lokacin tana k’arama, yana buk’atar zama da ita, ta yadda jikinsa zai zame mata wajen bacci, sannan idan tayi kuka ya bata, finger d’insa ta tsotsa kamar yadda yakeyi mata abaya.

Tabbas yasani aduniya ita kad’ai ce macen da zata fuskanci al’amuransa, sannan ita kad’aice macen da zai iya fuskanta da koma wacce irin damuwarsa, duk da cewar babu wanda yasan hakan amma shi ya sani, k’warae yasani cewar Laylerh ce kad’ae zata san damuwa da kuma abunda ke cikin zuciyarsa koda bai furta mata ba, ita ce kawae zata jurewa al’amuransa, itace wacce har abada yasani baza ta tab’a gajiyawa dashi ba, domin yayi imani cewa zuciyarsa da nata abu d’aya ne.

Duk kuwa yanda yaso jurewa abunda yakeji ayanzu baya tab’a iyawa, domin acikin y’an kwanakin nan, zuciyarsa na yawan sak’a masa cewar bazai rayu da Laylerh ba, ba dan komae ba kuwa saidan lalura da kuma k’addarar da ta sameshi, domin yanaji ajikinsa cewa zama da ita ahaka tamkar cutar da rayuwar ta ne, duk da yasan Laylerh’n babu wata irin k’addararsa da bazata iya jib’anta ba.

Saidai kuma amma akwae cutarwa aciki, ita yarinya ce k’arama da babu abunda ta sani, zuciyarta da kuma tunanin ta basu san komae ba sai abu d’aya, wanda kuma kullum akansa ne kawae take rayuwa.
Chapter 116 · 0% Book details