← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 144

Sashe 42

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Da gudu ta faɗa jikinsa haɗe da rungumesa ƙam, cikin yanayin zallar shagwaɓa tace.  "Oyoyo Abbou na."   Murmushi jin dadi Abbou Kareem yayi, cikin jin daɗin ganinta yace.  "Oyoyo Laylerh nayi kewarki sosai."   Jin ya ambaci kewa ne yasata ɗagowa daga jikinsa asangarce tace. 
"To ba kune kuka ƙi zuwa ba.!"
Murmushi sukayi daga shi har Abbou Jaheed.
Kanta yaɗan shafa tare da haɗe hannuwansa biyu waje ɗaya, cike da ƙaunarta yace. 
"Tuba muke munsan munyi laifi, hakanne ma yasa muka taho da tsarabar jaka guda na chocolate"
Dariya tayi harsaida fararen haƙwaranta suka bayyana.  
Cikin jin dadi tace. "Wow thank you Abbou nah.!"
Murmushi sukayi dukansu zuciarsu cike da farinciki, saidai banda Momy wanda take murmushin nata abisa dole.
Sosai Laylerh tasake acikin iyayen nata, wanda zuwansu ya gusar mata da kaso 70 acikin 100 na damuwarta, suna tare har aka ƙira sallan Magriba, atare su Abbou Jaheed suka wuce masallaci, yayinda Oum Aysha kuwa suka wuce masauƙinsu ita da Laylerh, kasancewar part guda ake ware musu agidan idan sun zo Nigeria.

12:30 am.
Amatuƙar razane ta farka daga nannauyan baccin daya ɗauketa, lokaci ɗaya taji duk jikinta ya soma bari, hannayenta dake rawa tasa ta dafe daidai saitin zuciyarta dake bugawa da ƙarfi.
Yanayin yanda jikinta ke rawane yasata cije laɓɓanta, tare da rumtse idanunta ƙam, tabbas ta matuƙar tsorata da mafarkin da tayi akansa, ahankali taɗan soma jujjuya kanta da taji yayi mata nauyi sosae, sosai mafarkin da tayin ya ɗata mata hankali, ya kuma hautsuna duk wani tunaninta.
Yayinda wani irin tsoro me ɗauke da zallan fargaba ya lulluɓeta, batajin zata iya jurewa, domin zuciyarta ta karye sosai, tsoro takeji kada mafarkin nata ya zamanto gaskiya, hakan yasa ahankali ta zuro da ƙafafunta ƙasa tare da sauƙowa daga kan gadon.
Kallon agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin tayi, duk da cewar dare ya raba sosai bata tunanin akwae wani abu dazai hanata zuwa garesa.

(Gobe akwae update insha Allah, saboda ba'anan naso tsayawa ba, rashin time ne kawae.)

*Wednesday, 16 December.2020*
*12:28 pm*
1/19/21, 8:14 PM - Ummi Tandama: *Laylerh Maleek*

*Writting By*
fatymasardauna

*22*

Ahankali take tafiya, yayinda kuma zuciarta ke cike da tarin tsoro, domin kuwa babu wani abu dake motsi acikin gidan ko ina ya ɗau shiru, kasancewar awannan lokacin dayawan mutane sunyi nisa acikin baccinsu. 
Sam bata damu da duhun da ya mamaye falon ba, haka kaitsaye ta nufi ƙofar da zata sada ta da part ɗinsa.
Duk da cewar ayanzu zuciyarta ta fara kawo mata wani abu me kama da tsoro,  saidai sam batajin akwai abun da zai hanata zuwa garesa awannan daren, domin kuwa zuciyarta cike take da son ganinsa, saboda ba kaɗan ba mafarkin da tayi akansa ya ɗaga mata ahankali.
Ɗaura hannunta akan handle din kofar tayi tare da tura ƙofar ciki ahankali.
Sassanyan ƙamshi da kuma sanyin A/C ne suka daki kan fuskarta, wanda hakan ya tilasta mata lumshe kyawawan idanunta, tare kuma da buɗesu alokaci guda, ayanzu kam tafahimci cewa shi mutum ne me son ƙamshi, wannan yasa ako da yaushe ɗakin nasa baya rabo da ƙamshi.
Ahankali ta shiga ƙarewa falon nasa kallo, wanda komai dake cikinsa yake need babu alaman datti ko akasin hakan, duk da cewar babu yalwataccen haske acikin falon, dan blue light ne kaɗai ke kunne, amma hakan baisa ta daina ganin tsarin falon ba.
Gaba ɗaya zuciyarta ta riga da ta karye da tunaninsa, hakan yasa kaitsaye ta nufi ɗaya daga cikin ƙofar dake cikin falon, wanda kuma anan bedroom ɗinsa yake.
Bata ko tashi jin fargaba da matsanancin faɗuwar gaba ba, saida ta ƙarasa jikin ƙofar ɗakin nasa ta tsaya.
Ɗan lumshe idanunta tayi tana me sauraran yanda heart dinta ke beating, take wani irin tsoro ya lulluɓeta, abu biyune aranta wanda na farkon shike ƙara karya mata zuciya, domin kwata kwata batason ace mafarkin da tayi akansa ya tabbata, dan koda da second ɗaya ne batajin zata iya jurewa cutuwarsa, idanunta da suka cika da ƙwalla ta lumshe, lokaci ɗaya mafarkin da tayi ya shiga dawowa cikin kanta, wanda hakan yasa ta riƙe kannata da sauri, yayinda idanunta keyi mata imagine ɗinsa kwance acikin jini kamar yanda tagani amafarkin nata,  cikin sauri ta murɗa handle ɗin ƙofar, tare da tura ƙofar ciki take kuwa ƙofar ta buɗe.
Ahankali ta É—an tura kanta cikin É—akin, take kuwa taga duhu ya mamaye ganinta, kasancewar ko É—igon haske babu acikin É—akin.
Ganin duhun ne yasa ta jin wani irin faɗuwar gaba, tare kuma da tsinkewar zuciya, domin kuwa hakan alamace dake nuna mata cewar babu kowa acikin ɗakin, dan da akwae mutum to da dole zai bar haske komin ƙanƙantansa.
Kanta taɗan soma girgizawa cike da fargaban abun da zuciyarta ke ƙoƙarin raya mata,  bazata iya jurewa ba domin kuwa taji zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, duk kuwa da yanda zuciyarta ke sanar da ita cewar baya cikin ɗakin bata amince da hakan ba.
Ahankali ta soma ɗan bin jikin bangon ɗakin, tare da soma laluɓe ko zataji makunnin wuta.
Sanin da tayi cewar duka ɗakunan gidan makunnan wutansu kusa da ƙofa ake saka su ne yasa ta bin jikin bangon ƙofar ahankali.
Cikin sa'a kuwa taji ta É—aura hannunta akan makunnin wutan.
Idanunta ta rumtse da ƙarfi, sakamakon yanda zuciyarta ke cike da fargaba, haɗi da kuma tsoron abun da zata gani bayan ta kunna hasken, tabbas tana matuƙar jin tsoro, domin tasan acikin biyu dole ne ɗaya saiya faru, maybe kunna hasken da zatayi yasa mafarkinta tabbata, wata kila kuma akasin haka shine baya cikin ɗakin nasa.
ÆŠanjim tayi tare da sake rumtse idanunta, lallai tabbas tasan cewa acikin biyu za'ayi É—aya, zuciyarta cike da tsoro da kuma fargaba ta danna makunnin wutan É—akin, take kuwa gaba É—aya É—akin ya gauraye da haske.
Atsorace tasoma ɗan ware idanunta dake akulle, inda ta sauƙe ganinta akan haɗaɗɗen gadon dake cikin ɗakin,  gani da kuma nutsuwarta ne suka sauƙa akansa, inda yake kwance anan kan tsakiyar bed din yayi kwanciyar nan irin ta rub da ciki, yayinda kuma yake sanye yake da dogon wando ajikinsa, kasancewar bashi da riga ne yasa faffaɗar surar bayansa dake ɗauke da ƴan tsirarun tattoo ya bayyana.
Sauƙe idanunta akansa da tayi ne yasanya ta sakin wata ƙatuwar ajiyar zuciya, wanda ƙarfi da kuma sautinta ya bayyana, wani irin matsanancin farinciki ne ya shiga zuciyarta, yayinda takejin wani irin daddaɗan sanyi na ratsa har tafin ƙafarta, jingina bayanta da jikin bangon ɗakin tayi, tare da lumshe idanunta, wanda hakan yasa ahankali wasu sirararan hawaye suka silalo daga cikin idanunta.
"Alhamdulillah Allah!." tafaÉ—a cikin wata sassanyar murya dake bayyana zallan abun dake cikin zuciyarta.
Ahankali ta kuma buɗe kyawawan idanunta, tare da sauƙesu akansa, wani irin matsanancin farinciki takeji na ratsata, sanadin hakan kuwa yasa bugun zuciya da fitan numfashinta daidai ta.
Sauƙe idanunta akansa da ta yine yasata jin wani irin matsanancin shauƙinsa na bin jiki da jininta, ahankali cikin nutsuwa ta shiga takawa zuwa jikin gadon nasa.
Ayanayin yanda takejin zuciyarta ta tsumu da matsanancin shauƙinsa, batajin akwae wani abu na daban da zai kawar mata da tunaninsa.
Samun kanta da tayi abakin gadon nasa ne yasa ahankali ta zauna abakin gadon, still idanunta akansa yake, yayinda takejin wani irin matsanancin tausayinsa ya rufe mata zuciya, sanadin hakan ko yasa duk wani rauninta ya bayyana.
Idanunta wanda ke cike da ruwan hawaye ta sauƙe akan zanen tattoo ɗin dake bayansa, tsaida ganinta tayi akan wani zane da akayi masa me kaman butter flay, sosai zanen yayi mata kyau hakan yasa taji gaba ɗaya ta kwaɗaitu dason taɓa zanen.
Batare da tunanin komae ba ahankali ta kai hannunta dake rawa kan fatar bayansa, daidai inda zanen butter flay É—in yake.
Sauƙar hannunta akan fatar bayansa ne yasa tajin wani irin abu me ƙarfi ya shiga jikinta, yayinda lokaci ɗaya tsikar jikinta suka mimmiƙe, saidai kuma taushin skin ɗinsa da taji ya shigeta ne yasa ta kasa ɗauke hannunta daga jikin nasa.
Ahankali taɗan lumshe idanunta tare da sauƙe ajiyar zuciya.
Cikin muryar dake bayyana tsananin rauninta tace.  "Alhamdulillah Allah Nagode maka, da baka bari mafarkina ya zama gaskiya ba, Allah Na godema daka tsare shi ayanzu, Ya Allah Na Ina roƙonka daka tsareminshi ako da yaushe!."
Yanayin yanda takai ƙarshen maganan nata, cike da son bayyana abun dake cikin zuciyarta ne yasa wasu hawaye masu sanyi suka zubo daga cikin idanunta, take kuwa suka ɗiga akan fatar bayansa. Sauƙan hawayen nata akan fatarsa ne yasa taga gargasan jikinsa sun mimmiƙe, yayinda kowani ƙofar gashi dake jikinsa suka bubbuɗe.
"Ya Maleek.!!"  Akaron farko ta ƙira full sunansa, cikin wata irin kasallaliyar murya, tun bayan wani lokaci me tsawo daya shuɗe.
Sanin cewar bacci yake hakan yasa batasa aranta cewar zae amsa mata ba.
Jin bai amsa mata ba ne yasa ahankali ta soma wasa da ƴar yatsarta akan fatar bayansa, kana kuma cikin wani sabon  yanayi ta soma zagaye zanen tatto ɗin dake jikinsa.
Gaba É—aya ta shagala kan abun da takeyi masa din, wanda har hakan yasa ta soma sakin murmushi batare da ta sani ba.
Ahankali taɗan lumshe idanunta, yayinda takejin wani irin daddaɗan sanyi na ratsa ta, sassanyar ajiar zucia take sauƙewa tare kuma da shaƙan nunfashi me ɗauke da daddaɗan ƙamshin turarensa, wanda daɗinsa ke ƙara kashe mata jiki.
Akasalance ta soma yawo da yatsar hannun ta har zuwa tsakiyan bayansa.
Zubawa shining skin ɗinsa idanu tayi, dan har acikin ranta tana mamakin yanda skin ɗinsa keda kyau da kuma laushi, ganin yanda gargasan jikinsa ke mimmiƙewa da kuma tsikar jikinsa dake tashi ne yasa taji ƙirjinta ya buga, domin bata fata ace ya farka ya sameta haka, kuma akan gadonsa, sannan tana taɓa masa jiki batare da izininsa ba.
Kallon kanta tayi dan sai alokacinne ma ta tuna da rigan dake jikinta, wanda take na bacci ce kuma iyakanta guiwa, gashi gaba É—aya saman wuyar rigar net ne, wanda hakan yasa kusan gaba É—aya rabin breast É—inta suka bayyana kansu ta cikin net É—in.
Da sauri ta sanya hannu ta kare ƙirjinta, dan sai alokacin gaba ɗaya hankalinta ya dawo jikinta,  kasancewar kansa na facing ɗin door ne yasa ahankali taɗan ranƙwafo kansa, dan so take ta duba bacci yake ko kuwa idonsa biyu.
Ranƙwafowan da tayin ne kuwa yasa jikinta gogan nasa jikin, yayinda tausasan breast ɗinta suka gogi bayansa.
Ɗan leƙa fuskarsa tayi, ganin kyawawan idanunsa arufe ne ya sata sauƙe ajiyar zuciya,  idanu ta zubawa fuskar tasa tana kallon yanda zara zaran eye lashes dinsa suka kwanta lub aƙasan idanunsa, kana kuma ga eyebrow ɗinsa wanda suma suka kwanta lub, yayinda  gashin  nasa ya kasance baƙi siɗik dan har wani shining yake.
Ahankali ta sauƙo da idanunta zuwa kan dogon hancinsa, da kuma ɗan ƙaramin bakinsa, wanda ke ɗauke da jajayen laɓɓa masu sheƙi.
Ƙurawa lips ɗin nasa idanu tayi bata ko ƙyaftawa, domin ba ka ɗanba suka mata kyau, kana kuma sukayi matuƙar burgeta.
Hakanan taji wani irin abu na tsirga mata, lokaci ɗaya kuma taji wani irin abu na yawo acikin tafukan ƙafarta, hakanne ko ya tilasta mata lumshe ido tare da sakin numfashi, lokaci ɗaya taji duk jikinta yayi weak, yayinda kasala ya sauƙar mata.
Sake lumshe idanunta tayi akaro na barkatai cikin muryarta daya zama very silent tace.  "Kana da kyau Yah M.Jay, ban taɓa ganin wani irinka ba, your so so beautyful.!!" tafaɗi hakan tana me sake ninƙaya acikin wani sabon shauƙin da ta samu kanta.
Ƙaran bugawan agogon dake aje kan bedside din gadonne yasata bude idanunta da sauri ta kalli agogon 1:00 am daidai agogon ya nuna, ganin hakane yasa ta ɗan zaro idanunta waje dan gaba ɗaya ta shagala.
Cikin sauri ta matsa daga jikinsa tare da zuro da ƙafafunta ƙasa.
Tana sauƙa daga kan gadon nasa kuwa ta soma ƙoƙarin gyara rigar jikinta.
Ɗagowa tayi ta kallesa, ganin yanda yake fitar da numfashi ahankali ne yasata ɗan lumshe ido, cikin sanyi da kuma daɗin murya tace.   "Have a sweet dreama Yah M.Jay!."
Ahankali ta juya cikin takunta me É—auke da nutsuwa ta nufi hanyar fita daga É—akin.
Sam tama manta da batun kashe wuta haka tayi ficewarta.
Chapter 42 · 0% Book details