← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 144

Sashe 45

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Muje part É—ina saboda yau ya kamata afara miki gyaran amarya na musamman, da tunjia naso mu fara amma ganin ba lokaci yasa na bari sai yau."
Ayanda jikinta gaba É—aya yayi sanyi ne yasa ba musu tabi bayan Oum Ayush É—in.
Kaitsaye sashin Oum Ayush É—in suka nufa.
koda suka ƙarasa cikin falon, kallonta Oum Ayush tayi tare dayi mata nuni da ɗaya daga cikin kujerun falon,  gane abun da Oum Ayush ɗin ke nufi ne yasata zauna akan kujeran.
Ita kuwa Oum Ayush kaitsaye É—aki ta wuce.
Bata wani jima sosai ba ta fito hannunta ɗauke da wani ɗan ƙaramin towel, da kuma wani ɗan madaidaicin bowl wanda aka zuba wani abu me kaman kwaɓaɓɓen madara aciki.
Miƙa mata towel ɗin Oum Ayush tayi tare da cewa "Tashi kije ki cire kayanki."
"To" tace haɗe da karɓan towel din, kaitsaye ta wuce ɗakin Oum Ayush ɗin.
Cikin nutsuwa ta cire riga da sket É—in dake jikinta tare da É—aura towel É—in, wanda tsawonsa ya tsaya iyaka cinyarta.
Babban madubin dake kafe ajikin bangon ɗakin ta kalla, ganin yanda gaba ɗaya surar jikinta ya bayyana ne yasa duk taji kunya ya rufeta, saidai babu yanda zatayi dole ahaka ta bude ƙofar ta fita.
Anan kan wani darduma Oum Ayush ta zaunar da'ita tare da sawa ta miƙe ƙafafunta.
Cikin nutsuwa Oum Ayush ta shiga shafa mata wannan kwaɓaɓɓen abu me kaman madaran ajikinta, ƙamshi da kuma sanyin abunne ya sata lumshe idanunta, tare da ɗan jingina kanta da jikin kujera.
Cikin abun dabai wuce 20 minute ba kuwa Oum Ayush ta gama shafe mata duka abun ajikinta, wanda yasa gaba ɗaya falon ya cika da ƙamshi,  wani ruwa me kaman oil Oum Ayush ɗin ta shafa mata akan fuskarta.
Tsawon 30 minute ta É—auka zaune awajen, ganin abu ya bushe ne yasa Oum Ayush soma mummurza jikin Laylerh'n, É—an rumtse idanunta tayi saboda yanda Oum Ayush É—in ke murje mata fata yasa tana É—anjin zafi kaÉ—an.
Hannunta Oum Ayush ɗin ta kamo suka ƙarasa bedroom, kasancewar tuni ta haɗa mata ruwan ƙamshi ne yasa kaitsaye ta jata zuwa toilet.
Nuna mata bathrobe ɗin dake cike da wani brown ɗin ruwa me tsananin ƙamshi Oum ɗin tayi,  kana cikin kulawa tace. "Kishiga ki kwanta, kuma ki tabbatar kin buɗe jikinki yanda ruwan zai ratsaki da kyau, 30 minute zakiyi, idan time ya cika zan miki knocking door saiki fito."
Da to kawae ta amsawa Oum ɗin dan gaba ɗaya jikinta yayi luƙus.
Ganin Oum Ayush ɗin tafita daga cikin toilet ɗinne yasata zare towel din dake jikinta,  anutse ta ƙarasa jikin bathtube ɗin tare da shiga ciki ta kwanta.
Daddaɗan ɗumin ruwan da kuma ƙamshin daya ratsata ne yasata lumshe idanunta, tare kuma da sake nutsa jikinta cikin ruwan, ahankali ta shiga sauƙe ajiyar zuciya, yayinda kuma lokaci ɗaya taji wani irin daddaɗan bacci na neman ɗaukarta.
Kanta ta ɗaura akan saman bathtube ɗin, hakan yasa ko mintuna biyu ba ayi ba bacci ɓarawo ya ɗauketa.
Cikin baccin nata ne taji ana knocking ƙofar toilet ɗin.
Da sauri ta buÉ—e idanunta, sanin cewa Oum Ayush ne ke knocking É—in, yasa ta fitowa daga cikin bathtube É—in.
Wani sabon towel  ta ɗaura ajikinta.
Gama É—aura towel É—innata kuwa yayi daidai da shigowar Oum Ayush cikin toilet din.
Jin yanda lokaci ɗaya jikin Laylerh'n ya game da ƙamshi ne yasa Oum Ayush ɗin  sakin murmushi, hannun Laylerh'n ta kamo tare da buɗe tafukan hannun nata, ta fesa mata wani abu dake riƙe ahannunta me kaman turare, sanyin abun da kuma ƙamshinsa me masifar daɗi ne yasa Laylerh ta lumshe idanunta, lokaci ɗaya tunanin Ya M.Jay ɗin ya fado cikin brain ɗinta, domin tasan cewa  shine mutum me tsananin son ƙamshi, sanyin da taji aranta ne yasa ta saki murmushi.
Oum Ayush dake kallonta itama murmushin tayi cikin salon tsokana tace.
"Murmushin me kike kodae kin tuna da angon naki ne?."
Jin an ambaci angonta ne yasata shagwabe fuska tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, cikin yanayin shagwaɓan daya zame mata sabo tace.  "Ni wallahi ban tuna dashi ba."
Dariya maganar tata ta bawa Oum Ayush, saidai bata bari dariyar tata ta bayyana ba, madadin haka sai ta kamo hannun Laylerh'n suka fito daga cikin toilet É—in.
Tabbas har acikin ranta ta gano cewar  akwae wani abu da Laylerh ke ɓoyewa acikin zuciyarta, wanda kuma ita tasan ko meye ke cikin zuciyar Laylerh'n, domin ga mutum ne fahimta da kuma saurin nazarta,  kallo ɗaya kawai zaiyiwa cikin idanun Laylerh'n ya karanto duk wani abu dake kwance acikin zuciyarta, fahimtar hakan da tayi ne kuma yasa tun zuwansu jiya da taga Laylerh'n taji gaba ɗaya zuciyarta ta karye, saidai lokaci ya riga daya ƙure saboda  bata da yanda zatayi akan hakan,  amma  kuma abu ɗaya tasa aranta shine INDA RAI DA RABO, saboda babu wanda ya isa ya hana hukuncin Allah Faruwa, lallai ne kuma tilas abun daya tsara shi zai faru babu wanda ya isa ya hana, domin kuwa ƙaddara na iya sauyawa ako da yaushe.

Sake hannun Laylerh'n tayi tare da ƙarasawa Inda da ta ajiye burner wanda ta zuba masa turaren ƙamshi da game jiki acikinsa, kunna burner'n tayi tare dayiwa Laylerh alaman cewa ta zo ta tsugunna agaban burner'n, Laylerh da gaba ɗaya son ƙamshi ya shigeta, cikin hanzari tazo ta tsugunna agaban burner'n.
lulluɓeta Oum Ayush ɗin tayi da wani babban mayafi, wanda hakan yabawa turaren daman game gaba ɗaya jikinta.
15 minute ta É—auka turaren na bin jikinta, kafun Oum Ayush tace mata ta tashi hakanan.
Wani cup dake ɗauke da maganin da aka dama shi da madara Oum Ayush ɗin ta miƙo mata tare da cewa ta shanye sa tas.
Aɗan tsorace takai cup ɗin bakinta, dan duk atunaninta maganin zaiyi ɗaci, harshenta tasa taɗan lasa maganin, jin babu ɗaci ne yasaka ta sakin murmushi, kasancewarta gwanan shan zaƙi take ta shanye gaba ɗaya maganin, harda su sucking lips ɗinta.
Again wani magani me kaman zuma Oum Ayush ɗin ta miƙo mata, babu Musu kuwa ta karɓa ta shanye, tana shanyewa kuwa ta soma suɗe bakinta, saboda wanda tasha yanzun yafi na farkon zaƙi.
Ajiye cup É—in tayi tare da zama akan É—an madaidaicin bedside carbinet É—in dake cikin É—akin.
Wata doguwar riga marar nauyi Oum ayush ta miƙo mata tare da cewa tasa.
Babu musu kuwa ta amshi rigar tasa, wanda gaba ɗaya jikinta ke fitar da daddaɗan ƙamshin humra.
Hijab da kuma takalmi Oum Ayush din ta bata tasa, sannan itama ta shirya kanta, duban Laylerh'n tayi cikin kulawa tace. "Taso muje unguwa."
Jin cewar fita zasuyi ne yasata miƙewa cikin sauri ta bi bayan Oum Ayush wanda tuni tayi gaba.
Koda suka fito compound ɗin gidan, kaitsaye wajen da tarin motocin gidan ke fake suka nufa, wata baƙar benz Oum ayush ɗin tasa driver ya fito mata dashi, kasancewar da kanta takesonyin driving ne yasa ta buɗe murfin motar tare da shiga ɓangaren driver.
Ganin hakanne kuwa yasa Laylerh shiga gefen me zaman banza ta zauna.
Cikin ƙwarewa Oum Ayush ta murzawa motar key, yayinda me gadi ya wangale musu gate suka fice daga cikin gidan.

Kaitsaye wani babban saloon lounge suka nufa, wanda kuma wajene da bakowa ke zuwansa ba.
Koda suka ƙarasa cikin babban lounge ɗin amutumce aka tarbesu.
ÆŠaya daga cikin manyan ma aikatan wajen Oum Ayush ta samu, tare dayi mata bayani akan irin gyaran da takeso ayiwa Laylerh'n, saboda daga gobene za'a fara gudanar da events É—in bikinta, yayinda wasu event É—in kuwa sai bayan an É—aura auren ne za'ayi su.
Cikin girnamawa matar tace za ayi duk yanda oum Ayush din keso, za kuma suyiwa Layler'n gyara yanda ya kamata.
Ganin yanda Oum Ayush É—in ta zuba musu kuÉ—i sosai ne yasa nan take matar ta shiga gyara Laylerh.

Ita dai Laylerh kallonsu kawai take, yayinda aranta take mamakin gyaran da ake mata, wanda kuma tasan anayi mata hakanne dan zatayi aure, auren da har yanzu bataji ajikinta cewar
Eh dagaske za'a É—aura shi ko a'a ba.

*(Shin wa kuke tunanin cewa Laylerh zata aura acikin mazaje biyun nan? MALEEK ko NAJEEB? nasan dukan ku kun matsu dajin hakan, to koma dae wanene zai bayyana gobe a next page wajen ɗaurin aure. Lallai duk wanda yafi ƙuri'a kuma wanda yafi sa'a shi zaiyi wuf da ita😅 yaseen nagaji da typing hannuna zogi anan zan tsaya.🏃🏻‍♀�)*
1/19/21, 8:14 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp number 07017879464. )*

*(Hey guys wannan page ɗin na haɗa muku dana yau da kuma na gobe ne, so ku karanta rabi yau, sai gobe ku ƙarasa sauran😂, nidae na faɗa muku kada wata tace ban faɗa ba tam😆.)*

*Chapter 24*

Kusan awa ɗaya aka kwashe anayi mata gyaran gashin, wanda hakan yasa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci gashin nata yayi kyau, tare kuma da ƙara tsawo, yanayin yanda aka gyara kannata ne kuma yasa shining face ɗinta ƙara fitowa.
Kasancewar idan suka sake mata dogon gashin nata zai na taɓo tsakian bayanta ne, yasa koda suka kammala gyaran suka ɗaure mata gashin atsakiar kanta, tare da fesa mata wani turaren gashi me matuƙar ƙamshi.
Chapter 45 · 0% Book details