← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 144

Sashe 37

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunta ta ɗan lumshe, saboda kwata kwata bata taɓa tunanin cewa zai tambayeta game da tunanin da takeyi ɗin ba, mekenan zata ce masa? tace masa tunanin Ya M.jay ɗinta take, ko kuwa ta faɗa masa cewa tafara zargin kanta da cewar idan abun da takeji acikin zuciarta, shi ake ƙira So, to ta fara son Ya.M.jay.?
kanta taɗan girgiza, domin ita kanta bata yarda da cewar son Ya M.Jay din take ba, saboda kwata kwata ma batasan ya ake gane haƙiƙanin so na gaskiya ba.
Ganin tayi shiru ne yasa shi share maganar, saboda bayason matsa mata akan abun da take ɓoyewa acikin zuciyarta, kansa ya ɗan girgiza tare da sakin wani murmushi me ɗauke da ma'anoni daban daban, kana kuma cikin nutsuwa yaci gaba da tuƙinsa, yayinda kuma kusan rabin hankalinsa ya maidashi zuwa gareta.
Ganin tana hammane yasashi gane cewar bacci takeji, hakanne yasa shi ƙara gudun motar tasa, sai gashi kuwa cikin mintuna ƙalilan sun iso gida.
Laylerh da bacci ya soma ɗaukarta jin tsayuwar motar da kuma ƙaran horn ne yasa ta buɗe idanunta, ganin su a ƙofar gida ne yasata sauƙe ajiyar zuciya, domin dama duk jin kanta take atakure.
Ƙaran horn din motar nasu ne kuwa yasa maigadi tahowa cikin hanzari ya wangale musu gate din, anutse ya tura hancin motar nasa ciki, sai kuma da ya ƙarasa babban parking space ɗin gidan sannan ya daidaita parking ɗin motar.
ÆŠagowa yayi ya kalleta cikin sigar tsokana yace.
"Miss sleep wakeup mun iso gida."

Jin abun daya faɗane yasa ta ɗan sake ware idanunta, tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, cikin yanayin shagwaɓan da batasan tanayi ba tace. "Nifa ba bacci nakeyi ba." Murmushin daya bayyana fararen haƙwaransa yayi, cikin yin ƙasa da murya yace. "Really?."
Kai ta jinjina masa alaman ''Eh." Idanunsa ya ɗan lumshe saboda sosai yanayin shagwaɓan nata ya burgesa.

Ganin yanda ya zuba mata idone yasa ahankali ta soma ƙoƙarin buɗe murfin motar.
Akasalance yaƙira sunanta cikin wani irin murya, wanda jin amo da kuma sautin fitar muryar tasa ne yasata dakatawa, daga fitan da take ƙoƙarin yi tare da juyowa ta kalleshi.
Ganin ta juyo garesa ne yasa shi tura hannunsa acikin aljihun wandonsa, inda ya ciro wani haɗaɗɗen ɗan ƙaramin box me masifar kyau, irin dai box ɗinnan da ake sanya zobe ko sarƙa aciki, sosai aka ƙawata jikinsa, wanda kuma hakan alama ne dake nuna cewar zobe ko sarkan dake cikinsa me tsadane sosai, ahankali ya buɗe murfin box ɗin wanda hakan yabawa haɗaɗɗen diamond ring ɗin dake ciki daman bayyana, ring ne me kyaun gaske wanda aƙalla kuɗinsa zai iya kaiwa 500k, yanayin tsadan zoben da kuma kyaunsa ne, yasa yake wani irin shining, musamman ma duwatsun da akayi masa ado dashi, dan sunfi komai dake jikinsa ɗaukar hankali, ciro zoben daga ma'ajiyinsa yayi tare da ɗagowa ya kalleta, ganin ta zubawa zoben idanu ne yasa shi ɗan lumshe nasa idanun tare da sauƙe ajiyar zuciya, hannunsa ɗaya ya miƙa mata tare dayi mata alama akan tabashi hannunta.
Gane abun dayake nufi ne yasa tayi ƙasa da kanta, tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta, haka takejin kamar bazata iya sa hannunta acikin nasa ba.
Ganin tayi ƙasa da kanta ne yasa cikin wata irin kasallaliyar murya ya sake ƙiran sunanta.
Awannan karon kam bazata iya jurewa yanda amon muryarsa ke fita ba, gashi kuma duk ta ƙosa ta tafi, hakanne yasa ta miƙa masa hannun nata, kamar yanda ya buƙata.
Sauƙan lallausan fatar hannunta akan nasa ne, yayi sanadiyar miƙewar tsikar jikinsa, take yaji ƙofofin sadarwar tunaninsa sun tsaya, yayinda taushi da kuma laushin hannunta suka birkita masa tunani lokaci ɗaya suka kuma sauƙar masa da nannauyan kasala, idanunsa da suka ɗan soma marairaicewa ya zubawa kyawawan ƴan yatsun hannunta, wanda suke ɗauke da shining nails masu kyau, ahankali ya sauƙe ganinsa akan hafaɗɗen zoben dake sanye cikin ƙaramar ƴar yatsan hannunta wanda aka rubuta, *L.M* asamansa da manyan baƙi.
*L.M* ya maimaita kalman da aka rubuta ajikin zoben, wanda kuma haruffan da aka rubuta ɗinne suka ƙara ƙawata zoben, ƙurawa zoben idanu yayi, domin kuwa ya tabbatar cewa zoben ba gama gari bane, bakuma irin zoben nanne da ake zuwa super market asaya ba, zobe ne da idan mutum yanaso musamman ake haɗa masa a company, kuma ba ƙaramin kuɗi zoben ke dashi ba, musamman duba da irin yanayi da kuma tsarin zoben, wanda aƙalla kuɗinsa zai iya kaiwa 1.5 million. Ɗago shanyayyun idanunsa yayi, cikin sanyin murya yace.
"Waya saya miki wannan zoben?." Jin tambayar tasa ne yasa ta É—an É—ago ta kalleshi, sanin cewa bata da amsar da zata bashi shiyasa tayi shiru, domin azahirance itama batasan waya siya ko ya bata zoben ba, saboda itama kawai ganin ring É—in tayi ahannunta, wanda kuma har yau takasa ciresa daga yatsanta duk da kuwa cewar ayanzu ring É—in yaÉ—an matse hannunta.
Ganin tayi shiru ne yasashi sauƙe ajiyar zuciya, lokaci ɗaya yasoma ƙoƙarin yaƙi da mummunan tunanin dake son shiga zuciyarsa, ƴar yatsan hannunta na tsakiya ya kama, ahankali ya zura mata haɗaɗɗen zoben dake hannunsa.
"Happy Engagement!" yafaɗa adaidai lokacin da yagama zura mata zoben a yatsarta, wanda ya zauna ɗas kana ya kuma ƙarawa hannun nata kyau. "Engagement!." Ta maimaita kalmar acikin zuciyarta, dan kuwa hakanan taji kalmar tayi mata ban baraƙwai abakinta, gefe guda kuwa yanayin yanda ya riƙe hannunta ne yasa duk taji ta takura, ƙoƙarin janye hannuta daga cikin nasa tayi, saidai yanayin irin riƙon da yayi mata ne yasa bazata iya ƙwace hannun nata ba, har sai in dan kanshi ya sake mata, kwaɓe fuska tayi haɗe da ɗan karyar da wuyanta gefe, cikin muryarta dake ɗauke da zallan shagwaɓa tace. "Please ni zanje nayi bacci."
Sassauta riƙon hannun nata yayi, cikin kasalalliyar murya yace.
"Okay please ki kulamin da kanki sosai, sannan kiyi bacci me daɗi kinji, good night and sweet dreams my beautyful girl!." ya ƙare maganar yana me kissing ɗin soft hand skin ɗinta.
Cikin sauri ta janye hannunta tare da buɗe murfin motar ta fice, batare kuma da ta tsaya sauraran wani abu da zaice ba kaitsaye ta nufi ƙofar babban falon gidan.

Idanunsa da sukayi matuƙar ƙaɗawa kana sukayi ja ya rumtse, cikin wani irin zafin zuciya da kuma raɗaɗin daya keji ya dunƙule hannayensa tare da naushin glsss ɗin window'n, wanda hakan yasa gaba ɗaya glass ɗin amsawa, saidai kasancewar glass ɗin me ƙarfin gaskene yasa bai wani fashe wa sosai ba, akaro na farko kenan da tun tsayuwarsa awajen ya zame, inda ya zauna akan guiwowinsa, wanda kusan sama da 40 minute ya ɗauka a tsaye yana jiran dawowarsu, yanayin yanda yakejin ƙuna acikin ransa ne yasashi dafe ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa, komai kuwa daya faru atsakanin Laylerh da Najeeb din akan idanunsa, amatuƙar zafafe yakejin ƙirjinsa nayi masa suka, yayinda yakejin wani irin fushi ya cika zuciyarsa, haka yakeji kaman ya tashi yaje ya kakkarya Laylerh'n gida biyu, domin kuwa wani irin haushi da takaicin sune ya cika ƙirjinsa, babbar abun dayake sukan zuciyarsa kuwa shine, yanda yaga Laylerh'n ta miƙawa Najeeb hannunta, tabbas ganin da yayi musu yasa gaba ɗaya duniyar ta daina yi masa daɗi, yayinda baƙin ciki da ƙuna suka maye gurbin nutsuwarsa, bakomai yafi ƙona masa zuciya ba kuwa face kissing hannun Laylerh'n da yaga Najeeb ɗin yayi, wanda hakan ya zamanto tamkar sauƙan mashi ne akan ƙahon zuciyarsa, idanunsa ya kuma rumtsewa da ƙarfi, yayinda yakejin kansa na wani irin juyawa, sanadin hakanne kuwa yasa take memories din baya suka soma dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa, wanda hakan ya sashi ƙara birkicewa, kunnuwansa ne suka soma dawo masa da gunjin kukanta, inda yakejin siririyar muryarta dake cikin matsanancin neman taimako na dukan zuciya da kuma hautsuna masa ƙwaƙwalwa, ahankali yanayin daya wuce ya soma wanzuwa acikin idanunsa, hakan yasa shi jin tamkar alokacinne abun ke faruwa. Lokaci ɗaya gaba ɗaya jijiyoyin kansa suka amsa da wani irin azababben ciwo, yayinda kuma gashin jikinsa suka mimmiƙe, still kuka da sautin muryarta yakeji suna tashi acikin kunnuwan sa, wanda hakan yasa amatuƙar zauce ya soma buga kansa da jikin bango, kwata kwata bayason jin ihun nata dake ƙoƙarin mai dashi mahaukaci, kana kuma bayason ganin moment ɗin daya riga ya wuce acikin idanunsa.
Cikin 10 minute gaba ɗaya ya fita hayyacinsa tare da zaucewa, da ƙyar ya iya tashi ya ƙarasa gaban drawer'n da anan ciki yake ajiye cocaine ɗinsa, ɗeɓo cocaine ɗin yayi ya zuba akan tiles din dake malale ƙasan ɗakin, kwanciya yayi aƙasan wajen kana cikin yanayin zaucewa ya shiga shaƙan cocaine din azafafe, yanayin yanda yake zuƙanta kaman mahaukaci ne yasa take hankalinsa ya soma gushewa, sanadin hakanne kuma yasa duk wani tunani dake cikin ransa ya kau, lokaci ɗaya ya samu kansa cikin wata sabuwar duniya.
Ahankali ya buɗe idanunsa wanda suka rikiɗe suka sake yin ja, saman ɗakin nasa dayake ganin yana juya masa ya ƙurawa ido, saboda haka yake gani kamar ba acikin duniya yake ba, cikin abun da bai wuce 14 minute ba ya sake samun kansa cikin wata duniyar, wanda take kama da bacci, suma, da kuma fitar hankali. Idanunsa ne suka rufe yayinda gaba ɗaya jikinsa ya daina motsi.

Ɓangaren Laylerh kuwa koda ta ƙasara cikin falon, bata iske kowa ba hakan yasa kaitsaye ta wuce ɗakinta, kasancewar amatuƙar gajiye take hakan yasa doguwar rigar dake jikinta kawai ta cire, kana ta wuce toilet ta ɗauro alwala, baccine sosai ya cika idanunta hakan yasa tana fitowa daga toilet ɗin ta faɗa saman gadonta, cike da mayen bacci tayi addu'a, cikin abun da baiwuce mintuna 15 ba kuwa bacci ya ɗauketa.

Najeeb kuwa zuciyarsa cike da tarin tunani haɗi da saƙe saƙe kala kala ya wuce masauƙinsa, babu abun daya tsaya masa arai kamar kalmomi biyun da yagani ajikin zoben dake hannun Laylerh'n, gaba ɗaya zuciyarsa taƙi nutsuwa masa da hakan, baisan meyasa akaron farko yaji faɗuwar gaba ta ziyarcesa ba.
haka dai yayita juyi akan gadon, zuciyarsa cike da tunani kala kala bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

Washegari.
Chapter 37 · 0% Book details