Sashe 90
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ajiyar zuciya Dr.Mouhammad ya sauk’e tare da d’an gyara zamansa, cikin yanayin sanyi yace.
“Kayi hakuri Alhaji da irin tambayoyin da zan maka dole ce tasa hakan, shin Maleek yana da mata ne ko kuma y’ay’a?.�
K’irjin Abbou Jaheed ne ya buga, asakamakon jin tambayan da Dr.Mouhammad d’in yayi masa, lokaci d’aya yaji zuciyarsa ta karye yayinda kirjinsa ya shiga dukan uku uku, cikin sassanyar murya da kuma fargaban abunda kunnuwansa zasu sake jiye masa anan gaba yace.
“A’a ko d’aya bashi da mata kuma bashi da y’ay’a, hasalima shid’in bai tab’ayin aure ba, amma Dr. wani abune ya faru?.�
Idanu Dr.Mouhammad ya d’an lumshe, yayinda gaba d’aya jikinsa ya k’arayin sanyi, lokaci d’aya yaji wani irin matsanancin tausayin matashin saurayin da ko auren fari baiyi ba amma kuma ya had’u da babbar matsala.
“Doctor Mouhammad kaifa nake saurare, amma naga kayi shiru.�
Abbou Jaheed ya katsesa ta hanyar fad’in hakan.
Ajiyar zuciya ya k’ara sauk’ewa akaro na biyu, kana ahankali ya d’an gyara zamansa, cikin nutsuwa da kuma son kwantarwa da Abbou Jaheed d’in hankali ta yanda zai fahimcesa asanyaye yace.
“Kayi hak’uri da abunda zan fad’a maka Alhaji Jaheed, hakika kamar yanda kasani kowani bawa aduniya yana rayuwane da irin k’addara da kuma jarabawan da Allah Ya d’aura masa, mai kyau ko akasin haka, sannan kuma Allah Baya d’aurawa bawansa abunda bazai iya ba, tabbas Maleek ya had’u da k’addara wanda jurewa hakan Insha Allah Zai kaisa ga samun kyakkyawan sakamako awajen Ubangiji...� D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da d’ago kai ya kalli Abbou Jaheed daya zuba masa ido baya ko k’yaftawa.
Kansa ya sauk’e k’asa domin yasan abu ne me girma fad’awa Iyaye irin wannan gagarumin matsala musamman idan y’ay’ansu ne suka kasance sun samu kansu acikin irin matsalan.
D’an gyara zamansa yayi akaro na barkatai, cikin hikima irin tasu ta likitoti yace.
“Zan sake baka hak’uri Alhaji Jaheed, domin kuwa a bisa tsautsayin hatsarin da d’anka Maleek ya had’u dashi ya samu wata matsala, ya samu mummunan buguwa sosae akan mararsa wanda hakan yasa abinciken da mukayi mungano cewar D’ANKA MALEEK bazae tab’a haihuwa ba, bi ma’ana k’wayoyin haihuwarsa sun samu matsala ta yanda bazasu iya riki d’ewa su zama k’wayar halittan da zata Samar da y’a ko d’a ba...�
k’irji da kuma zuciyar Abbou Jaheed ne suka shiga bugawa akai akai, yayinda ya samu kansa cikin wani sabon matsanancin tashin hankalin da ya gigita tunaninsa, tabbas kalaman da suka fito daga bakin Dr.Mouhammad sun kusan tarwatsa masa zuciya, har saida yaji kansa na yi masa wani irin sarawa.
Lokaci d’aya gaba d’aya mood d’in Abbou Jaheed d’in ya sanja, yayinda idanunsa suka cika tab da k’wallan tausayin d’ansa.
Cikin wata irin sassanyar murya me d’auke da matsanancin tausayawa ya shiga furta kalamar.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un!!!�
Saboda yasan ita kad’aice kalmar da zata daidaita nutsuwarsa.
Ganin hakanne kuma yasa Dr.Mouhammad gyara zamansa, ahankali yace.
“Dan Allah Alhaji Jaheed kada ka tashi hankalinka, domin kuwa ba akan Maleek aka fara samun irin wannan matsalan ba, duk da cewa abune da baiyawaita ga maza ba, anfi samun irin way’annan case d’in ga mata, saidai kasani shi Maleek yasamu wannan matsalarne ta sanadiyar accident d’in daya samu, hak’ik’a Allah Yakan jarraba bawansa da k’addara kala kala, yayinda kuma wata k’addaran takanfin wata sauk’i, sannan ko acikin k’addarori Allah Yakan musanyawa bawa daga me tsananin had’ari izuwa me sauk’i, kamar dai yanda ya juyawa Maleek nasa, lallai na tsorata sosai alokacin da aka kawosa cikin asibitinnan musamman yanda naga kansa na fitar da jini, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar ya bugu sosae akannasa, wanda hakan yasa nafara tunanin cewa, ko ta sanadiyar hakan zai zamana cewa yayi losing memory d’insa, sai kuma da mukayi bincike sosai akansa nida abokan aikina sai muka gano cewar kokad’an kansa da kuma k’wak’walwarsa basu samu wani matsala ba, tabbas munyi farinciki da ganin hakan, domin kuwa abune me tsananin d’aga hankali ace mutum ya manta kowa da komai nasa, tayaya rayuwa zatayi masa dad’i? kwarai zai dawo kaman wani bak’on halittane acikin mutane, lallai nayarda cewa k’arfin ikon Ubangiji da kuma k’udurarsa ya wuce duk tunanin mai tunani, domin kuwa shine ya kawar wa Maleek da wannan matsalan, ya kuma jarrabesa da wata matsalan amararsa, wanda da ace yaso had’a Maleek d’in da mummunan k’addara tofa da ayanzu labari ya riga ya sanja salo, domin kuwa inda matsalan ya kasance akansa ne to fa komai zai iya faruwa ciki kuwa harda gushewar hankali ma’ana zai iya zama mahaukaci, amma da yake Allah baiso hakan ba sai ya had’ashi da wata tawayar, tabbas lokacin da nagano cewa Maleek yana d’auke da wannan matsalan na tausaya masa k’warai, duba da cewar ya kasance jarumin matashin Soja me jini ajika, amma saidai Allah Ne kad’ai yasan me yake nufi da faruwar hakan.�
Hannu Abbou Jaheed yasa asanyaye ya share hawayen da suka silalo daga Cikin idanunsa, wani irin matsanancin tausayin Maleek d’insa ne ya cika masa zuciya, wanda har hakan ya kaisa gajin kamar yayi ta rusa kuka, saidai kuma amatsayinsa na cikakken Musulmi ya zame masa dole d’aukan hak’uri da k’addara me kyau ko akasin haka.
Duk da kuwa bai tab’a kawo wa aransa cewar watarana wai d’ansa jininsa zai iya gamuwa da wannan mummunan k’addaran ba, saidai kuma duk da haka saidai ya godewa Allah da bai gama d’annasa da ciwon hauka ba, domin kuwa ciwon hauka yafi kowanne ciwo Muni.
Wani irin dogon numfashi me d’auke da karyewar zuciya yaja, asanyaye yace.
“Idan har na fahimci abunda kake fad’amin Dr.Mouhammad shine Maleek d’ina bazai tab’a haihuwa ba har abada, har ya koma ya ubangijinsa bazai ga d’ansa kuma jininsa ba, sannan kuma nima har abada bazan tab’a ganin Jika daga garesa ba, lallai tabbas Maleek ya had’u da babban k’addara wanda zatayi sanadiyar kasantuwarsa cikin k’unci, ba kuma zan iya jure hakan ba Dr. domin kuwa Ina matuk’ar son Maleek? dan haka wannan matsalar batasa bace shi kad’ai, wai ma shin tayaya xan fara fuskantar Maleek da wannan maganan tayaya????�
Ya k’are maganar muryarsa na d’an rawa da’alama kuka ne ke neman k’wace masa.
Kai Dr.Mouhammad ya girgiza cikin tausasa zance da kuma bada baki yace.
“Ayanzu Maleek Addu’ar samun sauk’i kawai yake buk’ata awajen baki d’ayan mu, domin kuwa hakan bawai yana nufin cewa har abada bazae tab’a warkewa bane, tabbas lalurar daya samu babbace, wanda da yawanta ba’a tab’a warkewa, amma kuma komai na Allah Ne shike sa cuta a lokacin da yaso, haka kuma shi ke sauk’ar da waraka alokacin da yaso, saboda haka mujira komai daga garesa, kar ka manta kuma cewa Alhaji Jaheed d’aukan k’addara yana d’aya daga cikin abunda yake k’ara inganta imanin mutum, saboda haka ka kwantar da hankalinka, sannan kuma inaso katuna cewa Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda yasan bazae iya d’aukansa ba.�
Wata irin nannauyar a ajiyar zuciya Abbou Jaheed ya sauk’e, tare dasa tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa dasu, tabbas wannan sabuwar matsalan da ta kunno musu tayi matuk’ar d’aga masa hankali da kuma gigita tunaninsa, babban abunda yake tsoro kuwa shine.
“Tayaya zai fara fad’awa Maleek wannan matsalan da ta sameshi? Yaya Maleek d’in zaiji? wani irin k’una da kuma zafin zuciya zai samu kansa aciki?.
Lallai Rayuwar Maleek acike take da tarin k’addarori, da fari yayi rashin mahaifiyarsa haka ya taso cikin kad’aici da kewa, bashi da y’a ko kuma k’anwar da suke uwa d’aya uba d’aya, ahakansa yake rayuwa har kawo yanzu, da adaidai wannan lokacinne yakamata ace yayi aure ya hayayyafa ta yanda y’ay’ansa za su zame masa abokan hira da kuma d’ebe kewa, amma kuma sai gashi rana d’aya Allah Ya sauk’ar masa da wannan k’addaran, sai yaushene Maleek Zaiyi farinciki arayuwarsa? Sai yaushe k’unci da kad’aicin da suke mamaye da rayuwarsa zasu yaye?�
Sam Abbou Jaheed d’in bashi da amsar tambayoyin, wanda hakan ya tilasta zubowar wasu y’an guntayen k’walla daga cikin idanunsa.
Ahankali ya mik’e daga zaunen da yake, cikin sanyin yanayi batare kuma daya ce da Dr.Mouhammad k’ala ba ya juya tare da nufar hanyar fita daga office d’in.
Dr.Mouhammad kuwa da idanu ya raka Abbou Jaheed d’in har ya gama ficewa daga cikin office d’in.
Wani irin matsanancin tausayin ahalinne ya kamasa, domin kuwa k’warai yasan cewa abune me matuk’ar ciwo da kuma tada hankali ace mutum Namiji ya samu irin wannan matsalan na rashin haihuwa, saidai kuma sanin da yayi cewa Maleek d’in bai rasa cikakken lafiyarsa ta zamowa d’a Namiji ba ne yasashi sauk’e ajiyar zuciya, domin yasan matsalar za tafi muni ne Idan akace Maleek d’in bazae iya biyawa Mace buk’atar taba, Alhamdulillahi kuma domin kuwa hakan bata faru ba, domin abincikensu sun gano cewa babu abunda ya samu manhood d’insa, zai iyayin sex da mace bama d’aya ko biyu ba, kuma ta samu cikakken gamsuwa, sannan kuma k’arfin sha’awarsa Yana nan bai ragu ba, saboda haka awannan fannin baida matsala kona d’igo ne kuwa.
Matsalar tasa dai guda d’aya ce, wato rashin haihuwa, wanda kuma ako da yaushe Allah Yakan iya sanja al’amura yanda yaso.