← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 144

Sashe 14

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Ahmad Rufa'e ne ya kalli Abbu cikin sakin fuska yace. "Tabbas Alhaji Jaheed nakusa samun suruka, masha Allah fatan dai baka manta da alƙwarin dake tsakanin mu ba."
Cikin son ƙarfafawa aminin nasa guiwa Abbu Jaheed yace. "Tayaya zan manta da alƙwari me girma irin wannan, hakan ma bazata faru ba, kuma Insha Allah ina meyi maka albishir da cewa kafun ka koma Polland zan cika maka wannan alƙawarin naka dana ɗauka, dan ni kaina nafiso ayi komai agabanka."
Murmushin jin daÉ—i Alhaji Ahmad yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah lallai zanji daÉ—in hakan kuwa."
Murmushi Abbu Jaheed yayi, sannan suka ci gaba da hirarsu.

Laylerh kuwa kaitsaye ɗakinta ta wuce, tana shiga ta turo ƙofar ɗakin nata tare da murza handle ɗin, school bag ɗin dake rataye akan kafaɗanta ta ajiye, tare da cire hijab ɗin dake jikinta.
Anan kan É—an madaidaicin gadonta ta zauna, tare da sakin ajiyar zuciya, ahankali ta É—an lumshe idanunta, wanda suka É—anyi ja saboda gajiya da kuma stress.
Kallon da Najeeb keyi mata me ɗauke da ma'anoni kala kala ne ya dawo cikin mind ɗinta, da sauri ta buɗe idanunta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, ashagwaɓe tace. "Ko waye shi ma oho, har da zaiyita wani kallona?." Ƙwafa tayi tare da soma ƙoƙarin watsar da tunaninsa acikin kanta, tashi tayi cikin nutsuwa ta soma ƙoƙarin cire uniform ɗin jikinta.
Koda ta kammala cire uniform É—in wani baby pink towel ta É—aura ajikinta wanda ko cinyoyinta basu kai ga rufewa ba, kaitsaye ta wuce toilet dan sosai takejin kanta na sarawa, tun safe kuwa takejin mararta aÉ—an É—aure, ruwan zafi ta haÉ—a dashi tayi wanka sannan ta É—auro alwala.
Koda ta fito daga cikin toilet ɗin, tsane jikinta tayi, tare da shafa wani body lotion ajikin ta, haka take bata dason yawan kwalliya, shi yasa ko powder bata shafa akan fuskarta ba, ƙarasawa gaban sif ɗin kayanta tayi tare da buɗewa, kayan cikin drawer'n ta zubawa ido kamar wacce ke na zartan wani abu, ɓangaren dogin rigunanta ta kalla, wanda kusan ma sune sukafi yawa acikin kayan nata, kasancewar tafison abayas, and kimono fiye da kowani kaya, wata blue ɗin abaya me adon manyan duwatsu wanda ke haɗe da ɗan gyalensa ta ciro, rigace me kyaun gaske dan ƙirar turkish abaya ce.
Anutse ta zura rigar ajikinta, baƙaramin kyau kuwa rigar tayi mata ba, dan ta bayyana ɗan madaidaicin shape ɗin jikinta wanda kullum ƙara fitowa yake, bama kamar hips ɗinta wanda suke ta ƙara faɗi da kuma buɗewa, wanda kuma hakan na da nasaba da girma da take ƙarawa ako wacce rana, dogon gashinta daya nannaɗe ta tubke waje ɗaya, tare da ɗaura vail ɗin abayan akanta, jin yanda mararta ke ƙara murɗawa ne yasa ta zauna akan bedside drawer, ahankali taɗan rumtse idanunta tare da ɗaura hannunta akan mararta, wanda asannu sannu ciwon ke ƙaruwa, abubuwa da yawa take saƙawa azuciyarta, daga gefe guda kuwa zuciyarta na neman gangarawa wani sashi ne na daban, wanda hakan ne ke ƙara jefa tunaninta cikin rauni, batason ko menene ke shirin faruwa da ita ba, saidai wani lokaci tunaninta yakan tafiya ne da kowani ƙwayan bugun zuciyarta.
Jin ciwon marar na sake nuƙurƙusanta ne yasa ta sake rumtse idanunta, tare da cije jajayen laɓɓanta, jin bazata iya jure zaman bane yasa ta tashi daga kan bedside ɗin, nan kan saman gadonta ta kwanta, tare da jawo blanket ta rufa ajikinta.

6:40 pm dai-dai.
Baƙar motarsa ƙiran Toyota Avalon, bugun 2020 ta danno kai cikin farfajiyar gidan, awannan karon baya tare da soldiers ɗinsa, hasalima shi da kansa yake driving motar.

Ganin motarsa ta kutso kai cikin gidan ne yasa soldiers din dake compound ɗin gidan shiga taitayinsu, inda duk suka ƙame awaje ɗaya.

Daga yanayin yanda yake tuƙin motar kaɗai zaka gane irin yanda yake cike da isa, kuma komai nasa yana yinsa ne acikin nutsuwa, kasancewarsa bashi da yawan hayani ya.
Atsakiyar compound É—in gidan yayi parking motar, wanda ya É—auki sama da 7 minute bai fito daga cikin motar ba.
Sanin yagama daidaita parking ɗin motar ne ya sashi ɗauke hannunsa akan steering motar, ɗan jingina bayansa da jikin kujeran motar yayi, tare da fesar da iska ta bakinsa, cute cat ɗinsa me kalan milk dake kwance akan kujeran ɓangaren me zaman banza ne tayi saurin hayewa jikinsa, ɗagota yayi tare da ɗan soma shafa gashin bayanta, yanason cutie ɗin nasa, wanda sanadin haka ne tayi matuƙar sabo dashi.
Madaranta ya ɗauko anutse ya soma bata abaki har sai da ta ƙoshi, gane ta ƙoshi ne yasa shi ɗaurata akan shoulder ɗinsa, anutse ya buɗe murfin motar ya fito.
Ganin fitowarsa daga cikin motar ne yasa soldiers É—insa soma sara masa, kasancewar haka suka sabayi masa ako da yaushe.
Abdul ne ya taho da sauri cikin takunsu na isassun maza wanda idan sunayi sai ƙasa ta amsa, da dukkan alama sun samu horo me tsanani awajen ogan nasu, dan duk wani soja dake cikin gidan daka kallesa, zaka san ba ragon namiji bane, da alama duka sojojin nasa horarru kuma ƙwararru ne, dan dukansu tsayayyu ne, kana kuma matasa masu jini ajika.
"Well come back Sir."
Abdul da ƙarasowarsa kenan yafaɗa cikin yanayin girmamawa.
Kansa ya jinjina alaman "Yauwa." Tare da É—an juyowa yayiwa Abbul É—in kallo me alamar magana, shiÉ—in ma Abdul kallonsa yayi, gane abun da kallon Ogan nasa ke nufi yasa cikin sauri yace.
"Yess Sir nayi mana takeaway É—in lunch harma dana dinner."

Jin haka yasa batare daya sake cewa komai ba, ya nufi babban ginin benen dake tsakiyar compound ɗin gidan, wanda kuma nanne zai sadashi da babban falon gidan har izuwa sashinsa da ƙofar shigansa ke cikin falon.
Ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar falon ya shiga, zuwa lokacin babu kowa acikin falon dansu Abbu sun tafi masallaci yin sallah'n Magriba da ta Isha, Larai ce kaɗai ke tsaye akan dining area tana shirya dinner, yayinda ta kusan cike saman babban table ɗin cin abincin, dan girke girken da akayi yau ɗin na musamman ne, an girka abinci kala daban daban sunkai 7 banda drinks ɗin sha da aka haɗa kala daban daban, wanda kuma hakan duk aikin Larai da sauran kukus ɗin gidan ne, dan aƙalla suna da kukus sunkai 5 agidan, amma duk da hakan baya hana Laylerh aikatuwa, dan watarana Momy hana kukus din komai take, tace Laylerh ce zatayi, to yaudai Allah Ya samawa Laylerh lafiya daga yin aikin gidan.

Kaitsaye ƙofar part ɗinsa ya nufa. Ƴan yatsun hannunsa yakai jikin wata na'ura dake jikin ƙofar tasa, na'urar na ɗaukan hoton ƴan yatsunsa ƙofar ta buɗe, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, yana shiga kuwa ƙofar da kanta ta kulle. Ƙarasawa tsakiyar falon yayi, tare da ɗaura hannunsa akan schoulder ɗinsa, kamo cutie ɗin nasa wanda ta fara bacci yayi, anan kan lallausan carpet ɗin dake malale atsakiyar falon ya ajiyeta, sannan ya nufi bedroom ɗinsa.
Yana shiga cikin ɗakin kuwa ya soma ƙoƙarin rage kayan jikinsa, rigar t-shirt na Calvin Clain Jeans ɗin dake jikinsa ya cire, aɗan ƙagauce ya cire takalmin sopport ɗin dake ƙafansa.
Zama yayi akan wata haÉ—aÉ—É—iyar cushion dake cikin É—akin.
Dan lumshe idanunsa yayi, yayinda ahankali yakejin kasala na sauƙar masa, jingina bayansa da jikin kujeran yayi, tare da sakin ajiyar zuciya, hakanan yau ɗin yakejin yanayinsa duk ba daɗi, hannunsa yasa ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake beating, wanda cikinta ke cike da fata haɗi da muradi da kuma burin samun abun da takeso, tabbas zuciyarsa cike take da muradi, wanda yayi imani cewa ƙaddara na kewaye da wannan muradin nasa, mafarkin da yayi adaren jiya ne yasoma dawowa cikin kansa filla filla, hakan kuwa shiya sanyashi buɗe idanunsa, tare da tashi tsaye kaitsaye ya nufi toilet, sam bayason maimaita tunanin mafarkin nasa because mafarkin kaman abune marar tushe awajensa. Ruwan shower me sanyi ya sakarwa kansa, ba tare da ya bari ruwan ya jima yana dukansa ba yayi wanka haɗe da ɗauro alwalan sallan Isha.
Koda ya fito daga wankan da wani farin towel ya tsane jikinsa, sama sama ya shafa men body lotion ajikinsa, wasu riga da wandon crazy jeans masu kyau yasaka, wanda suka sake bayyana hasken fatarsa, kasancewarsa mai son ƙamshi sosai, wannan yasa ako da yaushe baya barin jikinsa ba ƙamshi, hakan ne kuwa yasa koda bai shafa turare ba jikinsa ƙamshi yake.
Wata haɗaɗɗiyar lallausan darduma ya ɗauka haɗi da wayarsa wanda keta faman ringing ganin ƙiran bawani me mahimmanci bane yasashi ƙin ɗagawa, darduman na riƙe ahannunsa haka ya fito daga part ɗinsa ya nufi masallaci.

Ɓangaren Laylerh kuwa jin ciwon marar nata ya ɗan lafa ne yasa ta tashi tayi sallan magriba, koda ta sallame sallan bata tashi ba saida tayi sallan Isha, ɗan muskutawa gefe tayi tare da kwantar da kanta ajikin gado, azkar take amma gaba ɗaya tunani da hankalinta sun tafi zuwa wani waje daban, daga jiya zuwa yau wani irin fitinannen baƙon yanayi takesamun kanta aciki, babu wani minti da zai wuce batare da tayi tunaninsa ba, haka zalika ko wani bugun zuciyarta ɗaya da tunaninsa yake tafiya, haka takeji kaman ana zana mata tunaninsa acikin jininta, wani abu na musamman takeji akansa, wanda kuma hakanne kesawa taji zuciyarta na ƙoƙarin bayyanar da rauninta, batasani ba, bata kuma san meyasa tunaninsa ke sawa taji kaman tayi kuka ba, haka takeji ajikinta tanason kasancewa dashi, ayanzu ba abun da takeson shaƙa kaman ƙamshin sa, wani irin fitinannen feeling takeji akansa.
Samun kanta da tayi cikin shauƙin tunaninsa ne yasa ta sake matse jikinta waje ɗaya, tare da lumshe kyawawan idanunta.
Chapter 14 · 0% Book details