← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 144

Sashe 32

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren Laylerh kuwa tunda suka ɗauki hanyar dawowa gida bata buɗe idanunta da suke alumshe ba, ahankali kala kalan tunani ke cika zuciyarta, yayinda wani irin maganaɗisun son ganinsa ke yawo ajikinta. Jin tsayuwar motar tasu ne yasa ta gane cewar sun iso gida.
Ahankali ta buɗe idanunta tare da ɗaukan school bag ɗinta dake gefenta, anutse ta buɗe murfin motar ta fito, batare da ta tsaya sauraran komai ba kuwa ta nufi haɗaɗɗiyar ƙofar da zata sada ta da babban falon gidan, koda ta ƙarasa jikin ƙofar ahankali ta murɗa handle din ƙofar ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, babu kowa acikin falon sai tv plasma dake ta faman ɓaɓatu shi kaɗai.
Kasancewar agajiye take jin kanta yasa kaitsaye ta nufi hanyar da zai sadata da É—akinta.
Yanayin yanda ta sadda kanta ƙasa ne yasa sam bata ma lura dashi ba. Najeeb dake tsaye idanunsa yaɗan lumshe tare da sakin ajiyar zuciya, tsawon 10 minute kenan daya ɗauka atsaye yana jiran dawowarta.
Ganin zata wuce batare da ta ganshi bane yasashi kamo hannunta. Wanda hakan yasa ta juyo amatuƙar razane, tare kuma da ƙoƙarin fasa ihu saboda ta tsorata sosai, cikin sauri yasa hannunsa ya toshe mata baki, tare da ɗan soma girgiza mata kai, alaman kada tayi ihu.
Faɗawar idanunta cikin nasa ne yasata sauƙe wata ƙatuwar ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta, murmushin daya bayyana asalin kyawun fuskarsa yayi, cikin silently voice yace. "Matsoraciya kawai!." Jin yace mata matsoraciya ne yasata buɗe idanunta, tare kuma da daidaita nutsuwarta, cikin yanayin shagwaɓan daya zame mata jiki tace.
"To meyasa zaka tsoratani?."
"Saboda inason sanin wace irin mata zan aura!." YafaÉ—a yana me bin duk jikinta da idanu.
Jin da tayi ya ambaci aure ne yasa ta É—ago manya manyan idanunta ta kallesa.
Wani irin yaaarrr yaji ajikinsa sakamakon kallon da tayi masa, hakanne kuma yasashi kamo hannunta duka biyu ya riƙe ƙam acikin nasa, ahankali ya matso gab da ita wanda har hakan yasa numfashinsu gauraya dana juna. ahankali idanunsa suka ɗan fara lullumshewa, cikin muryarsa da ta sanja amo yace.
"INASONKI Laylerh, Inasonki sosai da sosai!!." Yanayin yanda ya ƙare maganar cikin wani irin tone ne yasata lumshe idanunta, wanda sanadin hakan yabasu daman sake kusanci da juna sosai, still kuma har yanzu hannayenta na cikin nasa.
Daga waje kuwa ahankali Maleek ya ɗaura hannunsa akan handle din ƙofar shigowa falon, kasancewar ƙofar ba akulle take bane yasa take ta buɗe, sako kansa cikin falon da yayi ne, ya sashi sauƙe idanunsa akansu.

*5/December/2020*
1/19/21, 8:12 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. Whatsapp number 07017879464.)*

*Chapter 17*

Mummunan ganin da idanunsa sukayi ne yasa lokaci ɗaya yaji wani irin abu me nauyi ya daki ƙirjinsa, wanda hakan ya tilastawa zuciyarsa bugawa da ƙarfi, idanunsa da suka zama jajaye ya rumtse tare kuma da dunƙule ƴan yatsun hannunsa, wani irin tafasa yakejin zuciyarsa nayi, ga kuma wani ɗaci da ya mamaye maƙoshinsa.

haƙiƙa wannan yanayin baƙone awajenta, irin wanda bata taɓa samun kanta acikinsa ba, tabbas a iyaka tsawon rayuwarta bata taɓa kusanci da wani namijin da ba muharraminta ba kamar yanda Najeeb ya tilasta mata yi ayau ɗin.
Yanayin yanda hucin numfashinsa ke dukan beauty face ɗinta ne yasa gaba ɗaya tsikar jikinta mimmiƙewa, ahankali ta ɗan soma jan jikinta baya, domin bazata iya jurewa kusancin nasu ba, wanda sanadin hakanne yasa taji jiri na ƙoƙarin ɗibanta.

Samun kansa cikin wata sabuwar duniya ta daban da yayi ne, yasa wani irin zazzafan shauƙi ya soma ɗibansa, sosai yanayin ya masa daɗi, kasancewar bai taɓa samun kusanci da ita har haka ba,
Jin da yayi tana ƙoƙarin nisanta kanta da shine yasa shi sake damƙe hannunta dake cikin nasa, cikin wani irin yanayin da yakejin kansa aciki yace.
"Please Laylerh faÉ—amin kina sona?"

Jin tambayan da yayi mata ne yasata buɗe tsumammun idanunta, tare da sauƙesu akansa, wani irin kallo takeyi masa wanda ke nuna kamar bata fahimci abun da yake faɗa ba, hasalima ayanayin da take ciki kamar bata gane komai.
Shi ɗinma idanunsa wanda suka juye izuwa kalan bacci ya zuba mata baya ko ƙiftawa,ahankali yakejin ƙaunarta na mamaye duk wani sassa na jikinsa.
kwata kwata batajin zata iya ci gaba da kallon cikin idanunsa, wanda yanayinsu ya riga da ya sauya, har takai ga tana hango wani abu na daban acikinsu, ahankali tayi ƙasa da kanta tare da ɗan lumshe idanunta, hakanan taji kirjinta na bugawa, yayinda wani irin abu me kama da fargaba haɗi da tsoro suka nemi mamaye dukkan sassan jikinta, sanyi da kuma iskan da taji na ratsa cikin tafin ƙafanta ne yasa zuciyarta fara yi mata wani tunani na daban.

Har zuwa yanzu idanunsa akulle suke, domin azahirance bayajin zai iya jurewa kallonsu a irin yanayin da suke ciki, har zuwa yanzu ƙuna da raɗaɗi yake ji acikin zuciyarsa, haka yakeji kamar ana caka masa mashi aƙirjinsa, haƙiƙa da ace yasan shigowarsa cikin falon zai gusar masa da ƴar nutsuwar da tayi masa saura, to tabbas da ya hana kansa ahigowa falon.
Idanunsa da sukayi jajur ya ware, yayinda tuni gashin jikinsa suka soma mimmiƙewa, lokaci ɗaya kuma fuskar sa tayi ja, kasancewar yaji tambayar da Najeeb din yayi mata ne, yasa zuciyarsa soma tafarfasa, domin jin amsar da Laylerh'n zata bashi daidai yake da hargitsewan tunani da ƙwaƙwalwansa.
Amatuƙar fusace ya saki handle ɗin ƙofar falon, wanda sanadin hakan yasa ƙofar falon rufewa da wani irin ƙarfi.
Jin ƙaran ƙofar ne yasa Laylerh da ta bawa ƙofar shigowa falon baya tayi saurin juyowa.
Ganin M.Jay dinne yasa zuciya da ƙirjinta yin wani irin tsalle kamar zasu faɗo ƙasa, cikin wani irin masifaffen tsoron daya shigeta tayi saurin janye hannunta daga cikin na Najeeb ɗin tare da ɗan matsawa gefe.

Ɗauke kansa yayi daga kallonsu tare da kawar da idanunsa da suka soma ganin dishi dishi zuwa wani waje na daban, cikin wani irin taku dake nuna zallan isa da taƙama irin na cikakkun soldiers, ya nufi hanyar part ɗinsa, sam bai yarda ya sake kallonsu ba, hasalima yi yayi kamar baisan dasu acikin falon ba.
Idanunta da sukayi raurau kana suka ciko da hawaye ta lumshe, ji tayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye, yayinda taji wani irin haushin kanta ya kamata, hakanan taji ajikinta cewa kamar bata aikata daidai ba. " Shin meyasa tabari Najeeb ya riƙeta? Meyasa?." tayiwa kanta tambayar da babu wani me amsa mata ita.
Najeeb wanda ya zura hannayensa cikin aljihun wandon jumper'n dake jikinsa ne ya sauƙe ajiyar zuciya tare da ɗan lumshe idanunsa, sahirtaccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa wanda har hakan yasa fararen haƙwaransa bayyana, idanunsa ya zubawa Laylerh'n wanda ta riga da ta basa baya.
Hannunsa ya ciro ahankali ya dafa shoulder ɗinta, cikin yin ƙasa da murya yace.
"Meyasa kika juyamin baya?."

Idanunta dake cike da tarin ƙwalla ta lumshe akaro na barkatai, kaman kuwa jira hawayen nata suke ta lumshe idanun nata, ahankali suka ɗan gangaro kan fuskarta, jin hawayen nata sun zubo ne yasa cikin sauri ta kai hannun ta share, tare da ɗan jan jikinta gefe, ahankali kuma ta soma ƙoƙarin zame hannunsa daga kan kafaɗanta, dan hakanan taji duk komai ya daina yi mata daɗi. Ganin yanda take ƙoƙarin zame jikinta ne yasa Najeeb sanya hannayensa duka biyu ya juyo da ita, suka zamana suna fuskantar juna.

Cikin sauri ta rufe idanunta dan kuwa kwata kwata batason sake haɗa idanu dashi, duk da kuwa kasancewar bata gama sanin menene ainihin haƙiƙan abun dake cikin zuciyarta ba, saidai batajin zata iya bari ya fuskanci rauninta, sanin da tayi cewa ayanzu babu komai acikin ƙwayoyin idanunta face rauni.
Sauƙe idanunsa akan zara zaran eye lashes ɗinta dake ɗauke da danshin hawaye yayi.
"Laylerh!!."
Yaƙira sunanta cikin wata irin murya me ratsa jiki da zuciya.
Sanyin muryan nasa da ya ratsa kunnuwanta ne yasa ta buɗe idanunta ahankali, saidai bata yarda ta sauƙe ganinta akansa ba. Kyakkyawan fuskanta da kuma kyawawan laɓɓanta yake kallo, ahankali yakejin wani irin shauƙi na sauƙar masa, hakanne kuma yasashi ɗan lumshe idanunsa tare da jan wani dogon numfashi, ahankali ya janye hannayensa dake kan kafaɗunta tare kuma da ɗan shafa gefen fuskarta, cikin wata irin silent voice me ɗauke da sassanyan amo yace.
"Ke kyakkyawace Laylerh, salon kyaun ki na daban ne, haka zalika duk wani sirrin kyau akwaishi atattare dake, please ki kulamin da kanki kinji, sannan kuma kimin kwalliya me kyau anjima zanzo zance wajenki, kamar yanda kowani saurayi yake zuwa wajen budurwarsa!."
Idanunsa ya lumshe tare kuma da buɗesu alokaci ɗaya, hancinta ya ɗan ja cikin kulawa yace. "Take care!." Raɓawa yayi ta gefenta ya wuce, wanda sanadin hakan yasa jikinsu gogan na juna.
Idanunta ta lumshe tare da jingina bayanta ajikin bango, sam ko É—aya kalamansa basu shigeta ba, hasalima kwata kwata bata fahimci inda kalaman nasa suka dosa ba, abu É—aya kawai tasani shine yanayin da taga M.Jay É—in aciki, domin yanayin nasa, ya nuna cewar akwai zallan damuwa atattare dashi.
Jin zuciyarta na ƙara raunana ne yasa ta jan ƙafafunta da takejin sun mata nauyi ta ƙarasa bakin ƙofar shiga ɗakinta, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige ciki.
Chapter 32 · 0% Book details