← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 144

Sashe 100

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yanayin yanda falon yayi shirune kuma yasa dukansu suke iya jiyo gunjin kukan Laylerh dake tashi k’asa k’asa, kasancewar ta b’oye kanta atsakankanun cinyoyinta.
Tabbas acikin irin wannan yanayin dukansu babu wani mai iya rarrashinta domin kowannensu da abunda yakeji acikin zuciyarsa.

Hannayensa dake adunk’ule kusan sama da mintuna 15 ya ware, ahankali kuwa ya shiga bud’e k’ank’antattun idanunsa da suka sake rikid’ewa, kana kuma suka bayyana abubuwa da yawa acikinsu.
Lallai tabbas ruwan hawayene kwance acikin idanunnasa wanda kuma har abada bayajin zai barsu su gangaro zuwa kan fuskarsa, hak’ik’a shikansa ayanzu bai isa fassarawa kansa gaskiyar abunda yakeji ba, domin kuwa abune da yake da tsananin girma da kuma ciwo.
Saidai kuma akan meyasa zai k’untatawa kansa? shin baiyarda da cewar Allah shike tsara komai bane? shine kuma ya tsara masa hakan, shiya tsara masa way’annan k’addarorin acikin rayuwarsa, yasani kuma cewa kin karb’an k’addararsa butulcewa ne, ba kuma ya fatan koda sau d’ayane na rayuwarsa ya butulcewa mahaliccinsa daya bashi ido biyu, kafafu biyu, ya bashi baki da hanci, Uwa uba rai da numfashi, wanda suke manya manyan rahamomi, idan bai gode akan wannan ba kuwa To bai cancanci yayi bak’inciki akan sabuwar k’addaran da tasameshi ba, saboda yayi imani aduniya idan Allah Zai hanaka komai ya baka rai,numfashi,lafiya, ji da gani, da kuma tafiya, to koya hanaka sauran abubuwa ba abun d’aga hankali bane, hakan ba kuma yana nufin cewa baya sonka bane, Tabbas shikam ya amincewa k’addararsa ya kuma yarda cewa zai rayu da ita, zai karb’eta hannu bibbiyu, ba kuma zai tab’a yiwa Allah K’orafi akan hakan ba.
Maida idanunsa yayi ya lumshesu ahankali, tare kuma da soma ambaton sunan Allah, saidai kuma har acikin zuciyarsa a yanzun babu abundake azabtar da ruhinsa kamar sautin kukan Laylerh da yakeji, wanda yake hautsuna duk wani tunaninsa, Sam ko kad’anne bayason kukannata, saboda yana matuk’ar tab’a masa zuciya.

Ganin kuma yanda Maleek d’in ke motsa labb’an bakinsa ne, yasa Abbou Jaheed dake gefensa tsura masa ido cike da matsanancin tausayawa, kasancewarsa kuma uba mahaifi agaresa yasa take ya fahimci cewar Maleek d’in yayi imani ya kuma amincewa sabuwar k’addaran da ta sameshi.
Hakanan Abbou Jaheed yaji zuciyarsa tayi wani irin sanyi, wanda har hakan ya bashi k’arfin guiwar dawo da kallonsa ga Laylerh dake kuka.
Cikin sanyin murya da kuma tausasawa yace.
“Najeeb kama hannun Laylerh kutafi can sashinku watak’ila zatayi shiru idan ka rarrasheta.�

Jin abunda Abbou Jaheed d’in ya fad’ane kuma yasa Najeeb mik’ewa anutse ya k’araso inda Laylerh’n ke zaune.
Cikin sanyin murya da kuma son lallab’ata yace.
“Please Laylerh stop crying ki tashi mutafi kinji, ai dama Maleek ne kuma ya dawo, sannan zai samu sauk’i Insha Allah.�
Ya k’are maganar yana me k’ok’arin kama shoulders d’inta ya mik’ar da ita tsaye.
Saidai kuma yanayin yanda tatafi suuu zata fad’ine yasashi saurin kamo hannunta, ahankali ya rab’a ta bayan Oum Ayush yana rik’e da hannun Laylerh suka nufi hanyar fita daga cikin falon.
Laylerh kuwa sam ta kasa koda d’aga idanunta ta kalli M.Jay d’inne, saboda wani irin tsananin tausayinsa da takeyi, wanda tayi imani sa kasa acikin idanunta ayanzu daidai yake da faruwar komae.
Haka dai Najeeb yaja hannunta batare kuma da tana cikin cikakkiyar nutsuwarta ba suka fice daga cikin falon, yayinda binsa kawai take don yana rik’e da ita, amma ko ganin gabanta batayi saboda yanda hawaye ke tururuwan fitowa daga cikin idanunta.

Fitan su Laylerh’n acikin falonne yasa Alhaji Farouk da gaba d’aya jikinsa yayi sanyi shima ya mik’e, asanyaye cikin kuma rauni ya kalli Abbou Jaheed.
D’an gyaran murya yayi tare da zura hannayensa acikin aljihun rigar jumper’n dake jikinsa.
Cikin yanayin maganan dayasan idan yayita su Abbou Jaheed d’in zasu gamsu yace.
“Zan wuce gida Alhaji Jaheed, domin wannan maganace da ta cancaci kowannensu ya sani, sannan kuma wannan k’addarar da ta sauk’a akan Maleek tana iya sauk’a akan kowa, babu wanda yafi k’arfinta, idan tanine kuma akan wannan bazae sa na fasa bawa Maleek auren Munnira kamar yanda nayi niya ba, domin kuwa koba komae Maleek matsayin d’a yake awajena, saidai kuma amma bazanyi gaban kaina ba, saboda a irin wannan yanayin yarinya da kuma mahaifiyarta suna da hakk’i, wanda ya kamata ace ambasu dama sun fad’i ra’ayinsu, matuk’ar sun amince da auren ahaka tofa Insha Allahu Za’ayisa babu fashi, domin haihuwa Allah Ne maikawowa aduk alokacin da yaso, domin koda likitotin duniya ne suka taru akan mutum suka kuma shaida cewar har abada bazae tab’a haihuwa ba, idan Allah Yasa yana da rabo, tofa komai daren dad’ewa sai Allah ya bashi.�

Kai Abbou Jaheed ya jinjina cike da gamsuwa yace.
“Insha Allah.�

Mik’ewa tsaye sukayi dukansu shida Abbou Khareem tare dayiwa Alhaji Farouk d’in godiya sosai, kana suka rufa masa baya donyi masa rakiya, hakan yasa falon yayi saura daga Maleek, sai Oum Ayush da kuma Fou’ad wanda yayi jigum.

Momy dake b’oye ajikin labule sama da yawan minutes d’in da suka kwashe suna magana, ganin su Abbou Jaheed zasu fitane yasa tayi saurin b’uya, tare kuma da sauk’e wata ajiyar zuciya mai k’arfi, yayinda takejin wani irin matsanancin farinciki na ratsa zuciya da gangar jikinta, lallai yau taji abunda yasata farinciki ba d’an kad’an ba.
Abbou Jaheed yak’i k’iranta saboda fushin da yakeyi da ita, tun jiya akan bataje ta duba Maleek a asibiti ba, amma kuma gashi hakan bai hanata sanin matsalar da Maleek d’in ya gamu da ita ba.
Wani irin murmushi tayi tare da lumshe idanunta cike dajin dad’i tace.

“Maleek ya samu matsala bazae tab’a haihuwa ba, shikenan ya zama fankon banza, Ya Allah Nagode ma da kakawomin cikar burina asauk’ak’e batare da nasha wahala ba, ayanzu Idan nakawar da Maleek da Laylerh shikenan babu wani mai iko da tarin dukiyar nan saini kad’ai, hak’ik’a duniya zatamin dad’i sosae!�
Tak’are maganar cikin matsanancin farincikin dake cin zuciyarta, gudun kuma kada su Abbou Jaheed d’in su dawo su isketa awajenne yasa cikin sauri ta juya ta nufi b’angaren ta, zuciyarta fara tas.

Acan cikin falon Abbou Jaheed d’in kuwa Oum Ayush ne tataso daga inda take zaune, asanyaye ta k’araso inda Maleek d’in ke zaune, wanda kuma har zuwa yanzu idanunsa alumshe suke, still kuma labb’an bakinsa suna d’an motsawa.
Matsanancin tausayinsa daya kamata ne yasa ta d’aura hannunta akan kafad’ansa.
“MALEEK!�
Ta k’ira sunansa cikin sanyin murya.

Jin muryar Oum Ayush d’in acikin kunnuwansa ne kuma yasashi d’an bud’e idanunsa, ahankali ya sauk’e ganinsa akan fuskarta, saidai kuma bai iya amsa mata ba, saidai idanu daya zuba mata kawae.

Hakanne kuwa yasa take idanunta suka cika da k’wallan tausayinsa, still kuma cikin murya mai rauni tace.

“Nasan mekakeji acikin zuciyarka Maleek, domin nima na d’and’ani wannan d’acin kuma har yanzu Ina kan d’and’ana, amma hak’uri da fawwalawa Allah yafi dukkan wani koke koke da k’unci, kayi hak’uri kaji Insha Allah Allah Yana tare dakai!!�
Ta k’are maganar cikin son k’arfafa masa guiwa yanda zaiji sanyi acikin zuciyarsa.

Kansa ya d’an jinjina, ga mamakinta kuma sai taga wani sihittaccen murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, cikin dauriya da kuma shanye damuwarsa yace.

“Na aminta cewa komae muk’addari ne daga Allah Oum Ayush.�
Maida idanunsa yayi ya lumshe tare da fesar da wani sassanyan numfashi.
Hakan kuwa shiyasa Oum Ayush ta kasa hak’uri bisa dole saida ta fashe da kuka.

Jin sautin kukan Oum Ayush d’inne kuma yasa shi saurin bud’e idanunsa, ahankali ya kamo hannayenta tare da girgiza mata kai, domin kuwa har cikin zuciyarsa yakejinta kamar mahaifiyarsa, ahankali ya d’an matso kusa da ita, cikin sanyi da kuma son samawa kansa nutsuwa ya d’aura kansa bisa cinyarta, tare da maida idanunsa ya lumshe.
Hakanne kuwa yasa Oum Ayush d’in tayi saurin tsaida kukanta, tare dasa hannunta ahankali ta shiga shafa tarin suman kansa, wanda yasha aski irin na turawa, wai ahakan an aske amma kuma kamar ba’a aske ba.

Idanu Fou’ad ya zuba musu yana mejin tsananin tausayinsu.

*Najeeb.*
Bud’e k’ofar d’akin yayi ahankali tare dajan hannunta suka shiga ciki, anan kan luntsumemen bed d’insu ya zaunar da ita, tare kuma da zama agefenta.
Ahankali ya kamo hannunta, cikin kuma sanyin murya me had’e da ban baki yace.
“Har abada kuka baya tab’a maganin damuwa Laylerh, kiyi hakuri ki daina kuka kinji!�

Kai ta shiga girgizawa tare da juyowa ahankai ta fuskancesa, cikin sheshshek’an kukannata ne kuma murya na shaking tace.

“Tayaya zan daina kuka Yah Najeeb? tayaya zuciyata zatayi sanyi? Wannan wacce irin k’addarace haka da take wasa da rayuwar d’an uwana? hak’ik’a nasan cewar ni yarinyace amma kuma hakan bashi zaisa na kasajin zafi akan duk wani abu daya samu Yah M.Jay ba, ya yakeji? meyakeji? shi kad’aine ya sani, amma kuma bashi kad’ai yakejin zafin ba, hardani zafin yana k’ona zuciyata!�
Tsagaitawa tayi tare da rumtse idanunta wanda suke fitar da zafafan k’walla.
Duk da kuwa tana da abun cewa amma hakanan taji bakinta yayi mata nauyi, bisa dole ta sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta.

Najeeb kuwa mik’ewa tsaye yayi tare da takawa ahankali ya k’arasa gaban dressing mirror tare da tsayawa ya k’urawa mirror d’in idanu yana me kallon kansa aciki, yayinda wani sashi na zuciyarsa ke ci gaba da sak’a masa abubuwa masu yawa, wanda batun yauba zuciyartasa take yawan sak’amasa hakan.
Wanda ayanzu yayi imani cewa acikin biyu za’a yi d’aya.
Chapter 100 · 0% Book details