← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 144

Sashe 135

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyowa tayi tad’an kalli Yah M.jay d’innata daya lumshe idanunsa, hakanan ta samu kanta da kasa d’auke idanunta akansa, domin duk da cewar akwae d’an k’arancin haske acikin d’akin, amma hakan bai hanata ganin kyau da kuma haskensa ba, shid’in kyakkyawa ne tabbas, sannan akowani yanayi yake kyawunsa baya b’uya.
Sam bata hango wata nakasa ko tawayayyar k’addara atattare dashi, domin ayanzu tasake gamsuwa cewar, lallai zata rayu dashi rayuwa kuma irin ta har abada, batare da fargaba ko kuma tsoron cewar zasu k’are rayuwarsu ahaka ba y’ay’a ba, komai Allah Ne ke tsarawa bawansa, rashi kuma bashi ke nuna cewar kazama kasashshe ba, haka zalika kuma rashi bashi ke nuna cewar, Allah Baya sonka ba, kowa da irin k’addararsa arayuwa, duk girman taka k’addarar kuwa idan zakayi dubi da wani, sai kafahimci cewa acikin munanan k’addarorin ma kai taka bata fiye muni ba, kuma asannu duk wani wanda yayi hak’uri ya kuma jure zaidace Insha Allah, abu mafi inganci akullum shine katsaya akan daidai, kada kuma kabari wata damuwa ta hanaka farinciki.

Ajikinsa yaji cewar Ayshnoor d’in na kallonsa, hakanne kuwa yasashi d’an bud’e idanunsa ahankali, take kuwa suka fad’a acikin nata idanun.

Murmushin daya sake bayyana kyawun fuskarsa yayi, tare da d’an ware hannayensa, cikin sanyin murya yace.
“Zo.�

Idanunta tad’an lumshe ahankali tare da sunkuyar da kanta k’asa, ahankali kuma ta mik’e tsaye, tare da soma taka k’afafunta dake d’an mata ciwo, ahaka harta k’araso inda yake zaune, durk’usa guiwowinta tayi ak’asa, tare da kama y’an yatsun hannunta ta shiga murzawa, cikin muryarta dake tafiya very slowly tace.

“Good morning Yah M.Jay!�

Hannayenta ya kamo tare da jawota jikinsa, ahankali ya had’e forehead d’insu, tare kuma da d’aura labb’ansa agefen bakinta.

“Morning!!!� Yafad’a yana me sakar mata wani irin sassanyan kissing, d’in daya haifar mata da tashin duk wani tsikar jikinta.
Hakanne kuwa ahankali ta lumshe Idanunta.

Shikuwa Maleek hannunsa yasa ya zare mata hijab d’in dake jikinta, tare da d’aura hannunsa akan zip d’in dake gaban rigar ta, cikin yanayin nutsuwa kuma ya zuge gaba d’aya zip d’in.
Ahankali ya d’ago idanunsa ya kalleta.
Cikin wata irin kasalalliyar murya yace.
“Daren jiya nayi hurting naki sosai ko? har yanzu kinajin zafi?�

Kanta tad’an jinjina masa alaman “Eh.�

Hannunta dake cikin nasa ya d’an murza, tare da fesar da iska ta bakinsa, still asanyaye yace.

“I’m sorry Ayshnoor nah, i promised you bazan sake hurting naki ba, ki yafewa Maleek kinji, bansan ya abun yake ba shiyasa, amma yanzu I know idan zanyi bazanyi sosai ba promise!!�

Ya k’are maganar yana me d’aura kansa akan shoulder d’inta, tare da shak’an daddad’an k’amshin daya kama fatar jikinta.
Saidai kuma ganin yanda duk tayi laushi ne, yasashi kwantar da ita akan gado, tare kuma da kwantawa shima ya jawota jikinsa.
Rigar dake jikinsa ya cire, had’e dajan blanket ya rufa musu.

Ahankali ta sake shigewa cikin jikinsa, saboda bakad’anba take matuk’ar son k’amshinsa, domin k’amshin yana bata nutsuwa sosai.
Cike da kasala kuma ta lumshe idanunta masu cike da bacci, alokacin da taji, sauk’an hannunsa akan bayanta yana shafata slowly, saboda dadin hakanne kuma yasa, cikin abunda bai wuce 10 minutes ba bacci ya d’auketa.

Almost 15minutes kenan yanzu da kwanciyarsu, amma ya kasa d’auke idanunsa daga kallon kyakkyawar fuskarta.
Wani irin yanayi na musamman yakeji akanta, hakika shikansa baisan cewar abunda yakeji akan Laylerh’n, ya zarce duk wani tunaninsa ba, sai ayanzu da tazama Halal d’insa.
Haka yakejinta acikin kowani jijiya da jinin jikinsa, Tabbas yayarda duk wani feeling d’inta da yakeji ada, ba feeling bane matuk’ar za’a had’ashi da wanda yakeji ayanzu.

Lallai kuma yayarda cewa itace cikon rayuwarsa, dole ne saida ita zaiyi rayuwa, Domin kuwa k’addara d’aya aka rubuta musu, wacce daga yanzu har abada zata ci gaba dayi musu yawo acikin jininsu, zuk’atansu guda ne, haka ma fata da burinsu duk abu d’ayane, K’AUNA’r junansu kuwa halittace dake rayuwa acikin jiki da zuk’atansu, har abada kuma wannan k’aunar ba zata tab’a gushewa ba.

Idanunsa da suka ciko da k’walla ya lumshe ahankali, tare da d’aura bakinsa atsakiyar forehead d’inta.
Yanayin yanda Laylerh’n ta sake cusa fuskarta acikin wuyansa ne kuma yasashi, soma sakin wani sassanyan numfashi ahaka har bacci ya d’aukesa.

9:30 am. Daidai vibrating d’in wayarsa dake aje akan bedside drawer ta tashe shi.
Zare jikinsa daga na Laylerh’n yayi ahankali, tare da sauk’a akan gadon kaitsaye ya wuce toilet.

Koda ya shiga cikin toilet d’in kuwa wanka yayi, bayan ya fito ne kuma ya sake kimtsa kansa cikin, wasu black T shirt and trouser.
Sosai kayan suka bayyana haske da kuma annurin dake jikin fatarsa, domin ayanzu kallo d’aya kawai zakayi masa, ka fuskanci wani sauyi da kuma nagarta dake yawo akan fuskarsa, lallai Tabbas yana cikin farinciki, domin abune da kowa ya sani cewar samun Laylerh yafiye masa komai.

Turarukansa na Oud ya shafa ajikinsa, tare kuma da d’aura babban agogo na company’n Gucci a hannunsa, cikin yanayin d’an hanzari ya saka wasu white sneaker shoe ak’afafunsa, bayan ya d’auki wayoyinsa da car key d’insa ne kuma, ya juyo ahankali ya k’araso inda Laylerh’n ke kwance tana bacci.
Ganin yanda take d’an had’a gumi ne, kuma yasashi yaye mata blanket d’in dake jikinta, tare da sunkuyowa ya sunbaci beautiful lips d’inta.

“I LOVE YOU Ayshnoor!!�
Yafad’a ahankali tare da gyara mata kwanciyarta.

Bayan ya k’ara mata gudun AC ne kuma, ya juya ya fice daga cikin d’akin, tare kuma da jawo mata k’ofar ya kulle.

Koda ya fito falon kuwa, kaitsaye stairs d’in da zai sauk’ar dashi k’asa ya nufa.

Bayan ya sauk’o falon k’asanne kuma ya tsaya yana k’arewa falon kallo, wanda shi kansa yasan bak’ananan millions su Abbou Jaheed suka kashe ba, wajen tsara had’uwa da kyawun faluka da kuma d’akunan gidan.

Sanin kuma da yayi cewar sam bayason b’ata lokacinsa ne yasashi nufar k’ofar waje, domin so yake yaje inda zashi har ya dawo ba tare da Laylerh’n tatashi daga baccin da takeyi ba.

Cikin takusan na nutsuwa ya gama fitowa daga cikin falon, inda ya samu kansa acikin babban compound d’in gidan.
Kaitsaye wajen motarsa wanda Abdoul ya kawosa da ita daren jiya ya nufa, yana zuwa kuwa ya sawa motar key ya bud’e tare da shiga cikinta ya zauna.
Kasancewar kuma su Abbou Jaheed sun turo masa maigadi ne, yasa tun kafunma ya tada motar, tuni maigadin ya wangale masa gate, atsanake ya cilla hancin motar tasa waje.

Kaitsaye kuma hospital ya nufa, koda ya isa cikin hospital din kuwa, direct Office d’in Dr.Mouhammad ya nufa, yana zuwa kuwa aka bashi izinin shiga.
Bayan kuma sun gaisa da Dr. d’inne Yayi masa bayanin cewar, yanaso ya rubutawa Laylerh magunguna ne saboda zazzab’in dake jikinta tun daren jiya.

Sarai Dr. Mouhammad d’in ya gane abunda ya faru, saidai kuma bai tambayi Maleek d’in dalilin dayasa baizo da Laylerh’n ba, sanin irin cases d’inne kuma yasashi rubutawa Maleek d’in magungunan da ya kamata ace Laylerh’n tasha, ba ita kad’ai ba kuma harda Maleek d’in, saboda shima har yanzu akwai d’an zazzab’i kad’an ajikinsa.
Gashi kuma tunda yayi sex d’in yakejin mararsa na rik’ewa, saidai kuma hakan bawani abun damuwa bane, domin hakan na faruwane ga wasu k’alilan daga cikin maza a lokacin da suka fara yin sex.

Bayan ya k’arbi card d’in magungunan ne kuma yayiwa, Dr. Mouhammad d’in godiya, kana sukayi sallama, koda ya baro office d’in Dr din anan cikin pharmacy na hospital d’in ya saya magungunan.

Bayan yafito daga hospital d’in kuwa kaitsaye hanyar gidansu ya nufa, Domin sosai yake da buk’atar ganin Oum Ayush musamman dan akwai wasu tambayoyin da yakeson yi mata, saboda abune da ke abayyane cewa, ita kad’ai ce zata iya bashi amsar tambayar da ke cikin zuciyarsa.

*(Sorry kuyi manage bani da enough charging ne, sannan Insha Allah kafun Ramadhan zan gama Laylerh Maleek, because ma pages d’in da suka rage basu da yawa.)*

*8:56 pm*
4/9/21, 6:43 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Note editing*

*Chapter 79*

Horn d’in motarsa ya danna adaidai lokacin daya iso gaban, tankamemen gate din gidannasu.

Cikin abunda bai wuce 4minute ba kuwa maigadi ya wangale masa gate d’in, anutse ya tura hancin motar tasa cikin gidan.

Saidai kuma sanin da yayi cewar bazae jima bane yasashi yin parking motar a tsakiyar compound din gidan, tare da bud’e murfin motar ya fito.

Cikin yanayin nutsuwa ya soma takawa, saidai bai wuce taku biyar yayi ba, ya tsaya tare da juyowa ya sauk’e idanunsa, akan part d’in da Laylerh da kuma Najeeb d’in sukayi rayuwa.
Idanunsa ya d’an lumshe ahankali, tare kuma da d’an cije jajayen labb’ansa, akaron farko kenan da yaji wani abu na rangwame acikin zuciyarsa.
D’auke kansa daga kallon part d’innasu yayi, lokaci d’aya kuma direct ya nufi b’angaren Oum Ayush.

Tsaye take agaban dinning table tana me harhad’a wasu had’add’un food flask acikin babban basket, k’aran knocking d’in falon da taji ne kuma yasa ta d’an dakatawa, tare da d’auko basket d’in ta rik’e ahannunta, dan a tunanin ta Abdoul ne, saboda tace masa yazo ya kaiwa su Laylerh’n kayan breakfast.

K’arasowa jikin k’ofar tayi tare dasa hannu ta bud’e k’ofar.

Idanu hud’u da sukayi da Maleek d’inne yasata dan bud’e baki, cikin kuma yanayin mamakin ganinsa tace.

“Maleek kaine da safe haka ina kabaromin Laylerh’n?�

Idanunsa ya d’an lumshe, batare kuma daya amsa mata tambayar da tayi masa d’inba, ya rab’a ta gefenta ya shige cikin falon.

Ganin hakan da tayi d’inne kuma yasata d’an tab’e baki, tare da maida kofar ta rufe, saboda dama tasan dole idan dai zasu had’u to sai ya nuna mata halinnasa na shariya, wanda kuma idan da sabo ta riga da ta saba da hakan.

“Good morning Oum Ayush.� Ya fad’a adaidai lokacin da ya k’arasa gaban, makeken fridge’n dake cikin falon, batare kuma daya jira amsawarta ba, ya bud’e murfin fridge’n ya d’auko bottle water maisanyi sosai.

Dawowa tsakiyar falon yayi tare da zama akan d’aya daga cikin kujerun falon, ahankali ya b’alle murfin bottle water’n, tare da d’aura goran abakinsa.
Only 8second kawai ya shanye rabin ruwan dake cikin goran, ahankali ya d’an janye kansa, tare da d’ago idanunsa ya kalli Oum Ayush da ta zuba masa ido.

Nuni yayi mata da goran ruwan, tare dayi mata alama akan ko zata sha.
Chapter 135 · 0% Book details