← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 144

Sashe 69

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ab’angaren Laylerh kuwa sama da awa d’aya ta kwashe zaune acikin falon tana kallon film d’in da Bollywood ke haskawa, jin bacci yacika idanunta ne yasata tashi asanyaye ta nufi part d’insu zuciyarta cike da fatan kada Allah Ya had’ata da Najeeb.
Bak’aramin dad’i kuwa taji ba alokacin da tashiga part d’innasu ta tarar da Najeeb d’in bayanan, hayewa saman gado tayi cikin abunda baiwuce mintuna kad’anba kuwa bacci ya d’auketa.
Bacci sosai tayi domin ba ita ta farka ba sai k’arfe 2:56 pm, ganin kuma irin lokacin da ta d’auka tana baccin ne, yasa ta shiga mamaki, dan bata tab’a bacci me nauyi irin haka ba, ahanzarce ta wuce toilet ta d’auro alwala koda tafito kuwa sallaya ta shumfud’a tare da hawa kai ta tada sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayanba saida ta sallame sallan la’asar, azkhar d’in yammaci tayi tare da mik’ewa tsaye ta soma rage kayan jikinta, bayan ta gama cire kayan nata ne kuma, ta wuce toilet wanka tayi tare da d’auro sabon alwala, koda ta fito ganin yamma tayi sosai ne yasa sama sama tashafa lotion ajikinta, powder da kuma lipstick wanda ya saje da kalan labb’anta ta shafa.
Ahanzarce ta k’arasa gaban sif d’in kayanta, kasancewar kuma bata fiye son kaya masu nauyi sosai bane yasa ta zaro d’aya daga cikin had’add’un dogin rigunan da Oum Ayush takawo mata tsarabarsu, duk da kuma kasancewar rigar nada d’an fad’i kad’an amma hakan bai hana had’add’iyar surar jikinta bayyana ba, yayinda kuma adon fararen duwatsun dake gaban rigar keta faman shining suna d’auke ido.
Anutse ta nad’a vail d’in rigar akanta kasancewar kuma vail d’in nada d’an girma kad’anne yasa ya sauk’o har kan k’irjinta, cool perfume ta shafa ajikinta tare da komawa kan gado ta zauna, d’an k’aramin handbag d’inta dake aje saman bedside ta jawo, wanda tun daren jiya da Oum Ayush ta ajiye mata shi bata sakebi takansa ba, zuge zip d’in jakan tayi, ganin kud’ad’e masu yawa acikin jakanne yasata d’an zaro idanunta, cike da yanayin mamaki kuwa ta sa hannu ta d’ebo kud’ad’en wanda bandir biyu na cikinsu suka kasance 2/2 hundred K, d’ayan bandir d’in kuma 100k ne.
D’an soma jujjya kud’ad’en tayi tare da sake lek’a cikin jakan ta zaro car key d’in da tagani aciki, sai kuma wayarta, maida kud’ad’en tayi tare dajan zip d’in jakan ta rufe, wayarta dake kashe ta kunna take kuwa sak’onnin Teemah suka fara shigowa, wanda dayawan sak’onnin kuma d’auke suke da zallan tsokana.
Share sak’onnin tayi batare da ta kulasuba ta somayin game dan shid’inne kad’ae zaihana k’wak’walwarta yin tunani marassa amfani.
Tana nan zaune kuwa har aka k’ira sallan magriba, sanin kuma da tayi cewar tana da alwala ne yasata shumfud’a sallaya ta tada sallah.
Tana nan zaune akan sallaya aka k’ira sallan Isha, bayan ta sallame sallan kuwa batawani tsaya yin dogon addu’aba ta mik’e tsaye saboda tun tashinta take jin cikinta na kukan yunwa.
Turare ta sake fesawa ajikinta tare da d’aukar wayarta tafice daga cikin d’akin, kaitsaye babban parlor’n gidan ta nufa, kasancewar tasan adaidai wannan lokacin ne sukeyin dinner.
Acan cikin falon kuwa zaune suke su dukansu ciki kuwa harda Maleek wanda ya maida gaba d’aya hankalinsa ga wayarsa dake rik’e ahannunsa.
Shigowarta cikin falonne kuma yasa Najeeb dake zaune ya d’ago kansa ya kalleta, hakan yafarune kuma saboda daddad’an k’amshinta da yaji ya ratsa cikin hancinsa.
Tabbas duk da cewar fushi yakeyi da’ita amma ganinta da yayi yanzun yasa shi jin zuciyarsa tayi masa sanyi, hakanan yaji ya nemi duk wani b’acin ransa ya rasa, kallon tsab yayi mata, tunawa kuma da abunda ke cikin zuciyarsa ne yasakashi sakin murmushi, domin alk’awari yayiwa kansa cewar ayau a kuma awannan daren babu abunda zai hanashi disvirgin d’inta.

Anutse ta k’araso dining table d’in, tare da d’agawa su Abbou Jaheed gaisuwa, saidai kuma wannan karon fuska asake Abbou Jaheed ya amsa mata.
Kujeran daya zamana shikad’aine awajen taja ta zauna, daidai lokacin kuwa idanunta suka Sauk’a akan Maleek wanda shigar jumper’n dake jikinsa tayi matuk’ar yimasa kyau.
Azahirance kuwa zaman nata, yayi daidai da mik’ewarsa tsaye, k’ok’arin barin dining area d’in yayi, domin matuk’ar Laylerh zata kasance akusa da Najeeb to bazae tab’a iya jurewa ba, saidai kuma k’iran sunansa da Abbou Jaheed yayi ne, yasashi tsayawa, batare kuma daya juyoba ya amsa k’iran Abbou Jaheed d’in.
Abbou Jaheed kuwa da ya tsaya dacin abincin da yakeyi, Sam baidamu darashin juyowan Maleek d’inba, cikin muryarsa da sam bata d’auke da alamar wasa yace.
“Kashirya gobe da safe za muje kaga matar dana zab’a maka, ma’ana wacce zaka aura, inason kasani kuma ba shawara bane umarni ne.�

*(Nasan dayawanku kunayiwa Abbou Jaheed kallon mutum meson kai, amma anan gaba kad’an zaku fahimci komae, then kada kuji haushi dan Abbou Jaheed yace zaiyiwa Maleek Aure, saboda saida wata hanyar k’addaran ake samun wani cikar burin, sannan kuma wata k’addara takan rikid’e tazamo alkhairi, please banaso kuyi saurin yanke hukunci domin bakusan wani future M.Jay da Laylerh kedashi agaba ba. Sannan ku k’ara hak’uri dani please danaso na bud’e WhatsApp dawani new sim saikuma naga abun bazaiyiwuba shiyasa na hak’ura har aka gyara wannan d’in.)*

*16/Jan/2021*
1/19/21, 9:09 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Chapter 39*

Tamkar sauk’an rugugin aradu haka su biyun sukaji sauk’an kalaman Abbou Jaheed d’in acikin kunnuwansu, wanda kuma ba iya su bama harta su Oum Ayush saida sukaji maganar Abbou Jaheed d’in tazo musu abazata.
“What!!!�
Ya fad’a cikin wata irin murya dake bayyana zallan tashin hankalinsa, tare da juyowa cikin sauri ya fuskanci Abbou Jaheed d’in, wanda jin kalaman da ya fad’a d’inne kuma yasa shi saurin juyowa tare da zazzaro idanunsa waje, cike kuma da rashin fahimtar inda kalaman Abbou Jaheed d’in suka dosa, cikin mauryarsa da tasanja amo lokaci guda ya maimaita kalmar ta. “Aure!!� abakinsa dan hakanan yajita wata iri, duba da irin yanda shigar Kalman cikin kunnuwansa ta haifar masa da matsanancin bugun zuciya, da kuma fad’uwar gaba.
Abbou Jaheed kuwa ganin yanayin tashin hankalin da Maleek d’in ya shiga ne yasashi d’aure fuskarsa tamau, batare kuma da alaman wasa ko wargi ba akan fuskartasa yace.
“Eh Aure zakayi kamar yanda kaji na fad’a, saboda bazan zuba maka idanu ka zauna haka ba, inaso kuma kasan cewa hakan umarnine ba wai shawara ba, na riga dana gama yanke hukunci, ba kuma zan tab’a sanjawa ba, saboda haka koda Yaushe yazamana kana cikin shiri, saboda ba neman amincewa ko yardarka nake da buk’ata ba, domin na baka dama amma kayi wasa dashi, atunaninka haka zanzuba maka ido, ina kallo kanayimin duk abunda kaga dama acikin gida? bayan kuma kasan cewar bazan tab’a lamuntar hakanba, sannan zab’i ya rage naka ko kaso ko karka so aurenka babu fashi, domin kai ba k’aramin yaro bane da za’a tsaya tambayar amincewarka ko akasin haka.�
Chapter 69 · 0% Book details