Sashe 119
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shin tayaya zata iya zab’an wata rayuwa?
Tayaya ma zata so nesanta kanta?
Ko kad’an batajin zata iya, domin aikata hakan tamkar cutar da kanta ne, yaya zatayi da Rauninsa dake damu da kuma sake cika zuciyarta akullum?
Wace macece zata karb’esa saboda Allah?
Koda sau d’aya tana son ganinta atare dashi.
Tabbas ayau zata fad’i duk wani abunda ke cikin zuciyarta, duk da kasancewar maganganun nata suna da nauyi sosai, amma Lallai ayau bazata iya dakatar da zuciyarta da akullum taje azabtuwa ba.
Zafafan hawayene suka sauk’a akan fuskarta, cikin kuma muryarta dake matsanancin rawa tace.....
“Yah Maleek Idan natafi wazai kula dashi? Kullum bayacin abinci, sannan koda yaushe haka yake tafiyar da rayuwarsa, babu farinciki acikinta, nakuma yi imani cewa har I yanzu baya cikin farinciki, saboda acikin zuciyata nakejin duk wani ciwo da kuma damuwarsa, waye zai basa farinciki? Koda sau daya ne kawai Abbou Jaheed inason ganin Yah M.Jay acikin farinciki, saboda haka na zab’i zama dashi fiye da kowa da komai, na sadaukar da duk wani farinciki na agaresa, bandamu Akan kowacce irin lalurarsa ba, abunda dai kawai nasani shine zan zauna dashi ahaka, zan rayu dashi, zan kuma jure duk wata damuwarsa, sannan kuma nayi imani cewa kowacce irin K’addara mai kyau ko akasinta Allah Shiya tsara mana!!!�
*21/3/2021*
3/23/21, 9:14 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Not editing*
*Chapter 71*
Idanu Abbou Jaheed ya zuba mata, Yayinda fuskarsa ke bayyana zalla da kuma tarin mamakin daya samu kansa aciki, sam koda wasa bai tab’a tunanin cewa akwai watarana da Laylerh’n zata zo gareshi da irin wannan maganan ba.
Wani irin raunin kuma daya lullub’e zuciyarsa ne yasa, take hawaye suka cika idanunsa.
Sam kwata kwata ma bayajin hakan zaiyiwu, tayaya zai d’auki Laylerh ya bawa Maleek dake d’auke da lalura? tayaya zai jefa rayuwar yarinya marainiya acikin k’addarar d’ansa?
Kansa ya d’an soma girgizawa, tare kuma da danne abunda ke cinsa acikin zuciyarsa, cikin wata irin muryar da takasa b’oye rauninsa yace.
“Hakan bazai yiwu ba Laylerh, abunda kike fad’a ayanzu wani abune da yake karkatacce, na kuma san ba komaine ke d’ibanki ba, illa k’uruciya da kuma raunin zuciya, tayaya kike son sa kanki acikin k’addarar Maleek? k’addarar da ta zame masa tamkar tabo acikin rayuwarsa, tayaya kike son tursasa zuciyarki akan auren Namijin da likitoti suka tabbatar da cewar bazai haihu ba, meyasa Laylerh? Meyasa kikeson kasancewa ahaka? Meyasa kikeson takurawa rayuwarki? Kada kice zaki rungumi k’addarar da bata zamo dolenki ba, domin kuwa ko ba komai ke MACE ce, dole kina da hope anan gaba, saboda haka zaifi kyau kitsarawa kanki rayuwar da zata zama cikinta akwai d’orewar farinciki...�
“Babu wani farinciki aduk wata rayuwar da babu sadaukarwa, sannan babu ingantacciyar farinciki ga wanda yasan kansa, matuk’ar har kullum zaiga d’an uwansa acikin damuwa, sai yaushe ne wanda yake cikin k’unci zaibar k’unci? Sai yaushe ne K’addarar sa zata yaye? Yaushe zai samu farinciki kamar yanda mafi yawan cin mutane ke samu? Wacece zata zauna dashi, ta sakashi murmushi, sannan kuma ta cire masa k’uncinsa? Wacece zata zauna dashi batare da ta cutar dashi ba? Saboda k’addarar da ta samesa kawai nefa, yasa aka janye maganar aurensa, bayan kuma kowa yasan cewa ba akansa aka fara halittar wannan k’addarar ba, sam banaso Abbou Jaheed, banason watarana Yah M.Jay yaji ajikinsa cewar shid’in mai yankakken farinciki ne, ba kuma nason ya fara Jin cewar shi mai nakasa ne, bana fatan wannan ranan, ranan da zaiji tamkar bashi da kowa, Tabbas bana fatan zuwanta, akullum akuma koda yaushe zanso ganin k’arfafawarsa, babu wanda yasan me yakeji, akoda yaushe shi kad’ai yake shanye duk wata damuwarsa, koda kuwa damuwar tasa takai girman da zata iya tar watsa zuciya!!!�
Idanunta dake tsiyayar da hawaye ta bud’e, wanda suka rikid’e suka zama jajur.
Gaba d’aya jikinta kuwa b’ari yake, wanda kuma hakan yasamo asaline saboda yanda wani irin azababben kuka me sauti keson k’wace mata.
A karon farko na gaba d’aya rayuwarta, da taji bazata tab’a iya b’oye abunda ke cikin zuciyarta ba, hasalima ganin Abbou Jaheed d’in take tamkar mahaifinta Abbou Mahmoud ne zaune agabanta.
Ahankali ta d’an matso kusa da Abbou Jaheed d’in, hannayensa duka biyu ta rik’o, cikin wani irin matsanancin kukan daya k’wace mata ta shiga girgiza masa kai, murya Amatuk’ar raunane tace.
“Dan Allah Abbou! Zan rayu dashi dakowacce irin k’addara koda kuwa tafi wanda ta sameshi ayanzu muni, zan zauna dashi koda ace shid’in Majanuni ne, lokuta da yawa danshi kawai nakeyin rayuwa, tun Ina k’arama shine yake kokarin zame min Garkuwa, ga kowanni d’an Adam jinin mahaifansa ne ke gudana acikin jikinsa, amma ni acikin jikina jinin Yah Maleek ne, shine komai nawa, shine wanda bayason yaga nayi kuka, shine kuma mutum na farko da yake fara bani abinci akowacce rana, shine wanda yake sanin kowacce irin damuwa ta, ba kuma zan tab’a mantawa da hakan ba har abada, domin abayan kowani bugun zuciya da numfashinsa al’amura nane, shine wanda ya fara koyamin yanda zanyi rayuwa, komai nasani aduniyar nan ta dalilinsa ne, tun Ina da shekaru 2 har izuwa 12 shi kawai nasani acikin rayuwata, har iyanzu ma shid’in kawai nasani....�
Wani irin kuka maitsanin sauti daya ci k’arfinta ne kuma yasa ta kasa k’arasa maganganun nata, kanta ta kifa da jikin kujera ta shiga rera wani irin kukan, dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarta.
Sannan kuma kukane dake nuna tsananin Rauninta akan Maleek, kukan da yayi matuk’ar tab’a zuciyar Abbou Jaheed.
Wanda har saida yayi sanadiyar hawayen dake kwance acikin idanunsa, suka gangaro kan fuskarsa.
Domin shikansa yayi imani acikin kalaman da Laylerh’n ta fad’a sam babu k’arya, ko waye zai sota bayan soyayyar da Maleek ya nuna mata ne, kasancewar abune da ke abayyane, duk wani wanda yasan su acan baya, to tabbas zai shaida cewar Maleek yamafi son Laylerh’n akan kansa.
Lallai ayau ya yarda cewa su duka biyun suna rayuwa ne akan abunda ko wannensu yake so, Muradi fata da kuma burinsu duk iri d’ayane, Laylerh ce fatan Maleek haka ma, Laylerh’n Maleek ne fatan ta.
Kuma Tabbas ita kad’aice macen da zata iya zama da Maleek d’in koda kuwa munin k’addararsa ta zarce misali, hak’ik’a ayanzu kam bashi da bakin dakatar da faruwar komai, domin ya riga ya fahimci abunda Allah Yayi ikonsa akai babu wanda ya isa hanawa.
Duk da cewar kuwa Auren Maleek d’in zai zama tamkar k’alubale ne agareta, Duk da cewar kuma ba shine mahaifinta ba, amma bazae tab’a so ace ta auri wani Namiji mai tawaya kamar Maleek d’in ba, zai so ace ta gina rayuwarta akan dogon tsauni ta yanda zata cimmawa nasarori da yawa.
Amma kuma k’addara ta riga fata, k’addarar soyayyar dake tsakaninta da Maleek, wanda girmanta ya zarce tunanin mai tunani.
Asanyaye yasa hannayensa ya share hawayen dake kwance akan fuskarsa, hannun Laylerh’n da har yanzu ke kuka ya kamo, cikin sanyin murya da kuma wata irin sabuwar k’aunarta da yaji ta sake shiga zuciyarsa yace.
“Kinason zama da Maleek duk da kinsan lalurar da yake d’auke da ita?.�
Kanta ta jinjina masa alaman “Eh.� Still kuma bata daina kukan da takeyi d’inba.
Tsananin tausayin tane ya lullub’e zuciyar Abbou Jaheed, musamman da yayi imani cewa, har abada bazai tab’a samun y’a irin Laylerh’n ba, komai na rayuwarta daban ne, Tabbas yasan cewar koda ace babu soyayya atsakanin LaylerhMaleek d’in, zata iya zama dashi tare da duk irin k’addarar da tazo mai.
Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciya.
Hannunsa yasa ahankali ya shafa kanta, cikin nuna tsananin kulawa agareta yace.
“Nagode miki Laylerh, nagode sosai da Allah Ubangiji Yabani ke, Allah Ya miki albarka, domin badan keba nasan abune mai wahala Maleek ya samu macen da zata zauna dashi, saidai kuma har yanzu inaji ajikina faruwar hakan tamkar cutar da kanki ne.�
Kanta tayi saurin girgizawa, tare da d’an motsa labb’an bakinta da takejin sunyi mata nauyi sosai.
Araunace tace.
“Babu cuta ko takurawa, Abbou Jaheed Yah M.Jay ne fa!!�
Takai k’arshen maganar nata cikin wata irin sangartacciyar murya, mai tafiya da sautin sheshshek’an kuka.
Idanu Abbou Jaheed ya tsura mata, Yayinda abayyane yake nazartar wani abu adangane da ita.
Adaidai lokacin kuwa Abbou Khareem da kuma Oum Ayush, wanda suke tsaye abakin k’ofar shigowa falon, almost 15mn ago suka kalli juna, gaba d’ayansu hawaye ne kwance acikin idanunsu, kasancewar sunji duk abunda Abbou Jaheed da kuma Laylerh’n suka tattauna.
Cikin jin dad’i da kuma k’arfafa guiwa suka k’arasa shigowa cikin falon.
Akusa da Abbou Jaheed Abbou Khareem ya zauna, Yayinda Oum Ayush kuwa ta kamo hannun Laylerh dake ta sakin sheshshek’an kuka, cikin kulawa tare da kuma son dakatar da kukan Laylerh’n tace.
“Kukan ya isa haka muje kici abinci.�
Kasancewar gaba d’aya jikinta asanyaye yake ne kuma, yasa bata musawa Oum Ayush d’in ba suka fice daga cikin falon.
Abbou Jaheed kuwa fuskantar Abbou Khareem yayi, cikin yanayin fahimtar juna suka shiga tattaunawa akan sabuwar magana da kuma al’amarin daya fuskantosu batare da sun shiryawa hakan ba.
Abbou Khareem ne ya gyara zamansa, tare da duban yayannasa fuska asake, cikin kuma son bawa d’an uwannasa k’warin guiwa yace.
“Naji duk abunda kuka tattauna da Laylerh, na kuma fahimci komai, saidai inaso ka goge kallon cutarwa da kakewa abun, domin Laylerh da Maleek abu d’aya ne, mun riga da munsan hakan tuntuni, kowanne yana rayuwa da soyayyar d’an uwansa acikin zuciyarsa, kaima kuma shaidane akan hakan, ko azaman da yayi a hospital ka shaida Son da yake mata, wallahi matuk’ar muka sakeyin wani ganganci zamu iya rasa su gaba d’aya, domin bawai yanzu ne suka fara son juna ba, kowannensu an haliccesa ne da soyayyar d’an uwansa acikin jini da tsokarsa, saboda haka amatsayina na Yayan Mahaifin Laylerh, na bawa Maleek auren ta, batare kuma da kokonto ko wani shakka ba, mun kuma amince da lalurar da ta sa mesa, domin munyi Imani cewa k’addarace dake iya sauk’a akan kowa, saboda haka afara shirye shiryen yin aurensu Insha Allah Next Saturday za’a d’aura musu aure.�