← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 144

Sashe 46

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Oum Ayush kuwa dake zaune ganin yanda gashin Laylerh'n yayi kyau sosae ne, yasa ta ƙara musu kuɗi. Sosae kuwa ma'aikatan shagon sukayi mata godia kafun suka baro saloon lounge ɗin.
Daga shagon saloon ɗin kuwa kaitsaye wani babban lounge na tailoring fashions styles suka nufa, aƙofar katafaren lounge ɗin Oum Ayush tayi parking motar tare da ɗagowa ta kai dubanta ga Laylerh wacce gaba ɗaya hankalinta ke ga motocin dake ta faman zirga zirga akan titi.
Cikin nutsuwa Oum Ayush É—in tace "Sarkin kalle kalle, fito muje ko."
Jin abun da Oum Ayush É—in tace ne, yasa ta yin murmushi tare da buÉ—e murfin motar ta fito.
Atare suka ƙarasa cikin babban lounge din wanda ke cike da tailors kala kala.
Ganinsu ne yasa Ogan shagon da kansa ya tarbesu cikin girmamawa, dan kamar yanda aka tarbesu a shagon saloon ɗin cikin mutum tawa haka ma aka karɓesu anan shagon ɗinkin, bayan sun gaisane kuma aka shiga jido kayayyakin da Oum Ayush ɗin ta bada ɗinki, saboda tun kafun zuwansu Oum Ayush ta yiwa shugaban lounge ɗin waya, wannan yasa tun kafun ƙarasowansu kayan nasu ya zama ready.
Ganin kuma kamar suna sauri ne yasa shugaban lounge É—in da kansa yasa aka kai musu kayan mota, godiya Oum Ayush ta mishi sannan suka baro lounge É—in.
daga tailoring lounge É—in direct gida suka nufo, yayinda tun ahanya gaba É—aya bacci ya cika idanun Laylerh.

Koda suka dawo gidan kuwa anan part É—in Oum Ayush ta zauna, kasancewar tafi jin dadin zama anan din fiye da ko ina.
Anan kan sofa ta zauna tare da ɗan jingina bayanta da jikin kujera, ahankali ta lumshe idanunta wanda suke cike da bacci, cikin abun da baiwuce mintuna goma ba kuwa baccin ya soma ƙoƙarin fusgarta, saidai kuma zuwan Oum Ayush da bowl ɗin dulka yasa dole ta buɗe idanunta.
Duk da kasancewar ta gaji sosai, saidai bazata iya musawa Oum Ayush dinba, haka ta zauna Oum Ayush É—in ta gurje mata gaba É—aya jikinta da dulka, saboda yanda tasha gurza kuwa har saida farar fatarta tayi ja.

Sama da awa ɗaya kwaɓaɓɓen dulkan ya ɗauka ajikinta, kafun daga bisani Oum Ayush ta sata taje tayi wanka, bayan tafito daga wankan ne kuma Oum Ayush ta sake bata wasu haɗaɗɗun magunguna, hannunta na rawa kuwa ta karɓi kofin maganin tare da kaiwa bakinta, saboda atunaninta maganin zai zamo me zaƙi kamar irin wanda aka bata afarko, saidai kuma ɗaura harshenta akan maganin da tayi ne, yasa tayi narai narai da ido, tare da taɓe bakinta, saboda haka taji ɗanɗanon maganin kwata kwata ba daɗi.
Ƙoƙarin furzar da maganin ta somayi, saidai ganin yanda Oum Ayush ke kallonta ne, yasa bisa dole ta shanye maganin badan taso ba.
Tana aje kofin maganin kuwa Oum Ayush ta sake turarata da wani turare me kamshin gaske, ita dai Laylerh sakin jiki kawae tayi, dan gaba É—aya ta gaji da shafe shafe da kuma murje murjen da Oum Ayush É—in ke mata.

Ahaka dai suka ƙare gaba ɗaya wunin na yau, yayinda Oum Ayush ta zage wajen gyara Laylerh'n sosai, wannan yasa acikin wuni ɗaya kacal taushin jiki da kuma ƙamshi suka matuƙar kama jikinta, koda dare yayi kuwa bayan ta idar da sallan Isha wani shafe shafen Oum Ayush ta sake yi mata, tare da bata wasu kalan magunguna na daban tasha, kasancewar agajiye take sosai ne yasa kafun ƙarfe 9 bacci ya ɗauketa, inda kuma anan sashin Oum Ayush ɗin ta kwana.

Dream!.
Lokaci ɗaya ya soma ƙoƙarin janye jikinsa daga nata, yayinda ahankali yake ɗan yin nesa da ita, tare da soma ƙoƙarin sakin hannunta dake cikin nasa.
Wani irin fitinannen yanayin da take gani acikin idanunsa ne, ya sata soma girgiza kainta, wanda hakan yasa hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa kan fuskarta, lokaci ɗaya kuma wani irin matsanancin kuka ya ƙwace mata, tabbas so take ta rungumesa ko zataji sanyi aranta, saidai yaƙi bata daman hakan, ganin cewar dagaske sakin hannunta dake cikin nasa zaiyi, yasa ta tsananta kukanta, kana cikin wata irin muryarta da bata fita da kyau tace.
"Kada ka sake hannuna Yah Maleek, dan Allah Kada kayi nesa dani! katsaya atare dani pleaseee...!!!"
Ta ƙare maganar cikin matsanancin kukan daya riga yaci ƙarfinta..
Sosae kukanta ke taɓa masa zucia, saidai kuma abun dayakeji aƙirjinsa ya wuce duk wani gaban kwantance.
Kansa ya shiga girgizawa haÉ—e dayi mata nuni da daidai saitin zuciyarsa, kana ahankali ya zare hannunsa dake cikin nata, tare da juya mata baya.
Ganin ya juya mata baya ne yasa cikin matsanancin kuka tatafi da gudu dan ta faɗa jikinsa, saidai kuma kafun ƙiftawar ido tuni ya ɓacewa ganinta, hakanne yasa ta sulale ƙasa tare da fashewa da wani irin kuka, cikin karyayyar muryarta ta ƙwala ƙiran sunansa da ƙarfi.
Yanayin yanda taƙira sunansa da babban murya ne, yasa sautin muryar ta ta bayyana afili.
Jin amo da kuma sautin muryar nata ne yasa ta dawowa daga cikin duniyar mafarkin da ta faÉ—a.
Ahankali ta soma buɗe idanunta wanda suka ɗan ƙanƙance saboda bacci.
Wani irin juyawa taji kanta nayi, yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri.
Jin sautin surutun mutane acikin gidanne yasa ta É—anyi shiru, domin tana son tabbatar da abun da kunnuwan nata ke jiye mata.
Jin da tayi cewar da gaske hayaniyan mutane ne ke tashi acikin gidan, bawai ƙarya kunnuwanta ke mata ba, yasa ahankali ta tashi zaune, tare da jingina bayanta da saman gadon da take kai.
Mafarkin da tayi akan Maleek ɗinne ya shiga dawowa cikin brain ɗinta filla filla, take kuwa taji ƙirjinta yayi mata nauyi, yayinda wani abu me kama da faɗuwar gaba ya shiga ziyartar duk wani kafar sadarwa na jikinta.
Yanayin yanda taji zuciyarta na bugawa ne yasa ta maeda idanunta ta lumshe.
Dai-dai lokacin kuwa Oum ayush ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.
Ganin Laylerhn azaune ne yasa ta sauƙe ajiar zucia haɗe da cewa. "Tun da kin tashi sai ki hanzarta yin wanka, dan masu lallen dana ƙira, sunzo tuntuni ke kawae suke jira."
Jin an ambaci masu lalle ne yasa ta kalli Oum Ayush É—in, cikin sassanyar muryar tace.
"Oum Ayush masu lalle kuma?."
Chapter 46 · 0% Book details