← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 144

Sashe 96

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“AYSHNOOR!!!.�
Ya k’ira sunanta da wata irin kasalalliyar muryarsa wacce da k’yar take iya fita, irin dai murya me d’auke da tsananin shauk’in dake bayyana yanayin da yakeji ajikinsa, yanayin kuma da bashi da misali, yanayin daya saka su fad’awa cikin wata irin sabuwar duniya ta daban, yanayin daya bayyana asali da kuma gaskiyar muradinsu.
Ahankali kuwa sauk’an muryarsa acikin kunnuwanta yasa gaba d’aya duk taji jikinta ya zama very weak, wani irin sassanyan yanayi ta samu kanta aciki wanda har ya kaita ga kasa jurewa, ahankali ta sake lumshe tsumammun idanunta, wanda suke cike da azabebbiyar soyayyarsa, ji takeyi kaman ta saka masa kuka, amma kuma zazzafan yanayin da tasamu kanta aciki yanzun ya kasa bata daman hakan, domin kuwa zuwa yanzu gaba d’aya zuciyarta ta riga da ta narke, sonsa da k’aunarsa ne kawai ke ruruwa acikin zuciya da kuma ganganar jikinta, amatuk’ar zauce kuma cikin wani irin yanayin dake fusganta ta daura hannunta dake rawa adaedae saitin kirjinsa wanda yake d’auke bandage, kanta ta d’an soma jujjuyawa cikin kuma muryarta dake shaking ta soma k’ok’arin harhad’a kalmar sunansa, saidai kuma amma duk yanda taso ga had’a kalmomin bakinta don su bada ma’ana abun yaci tura, hakan yasa ta rumtse idanunta tare da soma fitar da hucin numfashi ta bakinta.

Tabbas sauk’an dumin numfashinta akan wuyansa ne yasashi sakin wani irin numfashi, ahankali yasa d’aya daga cikin hannayensa ya jawota jikinsa.
Atare suka sauk’e wani irin k’akk’arfar ajiyar zuciyar, da yasa dukka zuk’atansu amsawa, batare kuma da sun hana rai da zuciyarsu abunda suke soba, still atare suka sake shigewa jikin juna, wanda kuma hakanne ya bawa gangar jikinsu daman kasancewa da juna.

Ahankali Fou’ad dake tsaye abakin k’ofar d’akin kusan mintuna 4 da suka wuce ya d’an lumshe idanunsa, cikin yanayin sand’a kuma ya juya tare da jawo k’ofar d’akin ya rufeta da sauri, batare da ya bari sun gansaba, duk da kuwa yasan cewar basa cikin hayyacin da zasu gansa d’in, domin yanayin daya gansu aciki bawae yanayine da kowa zai iya shigansa ba.

Ahankali ya jingina bayansa da jikin k’ofar d’akin, tare dasa hannu ya d’an dafe k’irjinsa dake bugawa da d’an k’arfi, wanda ba komae ne kuma ya jawo hakan ba, face ganin da yayiwa Laylerh Maleek d’in.
Mekenen idanuwansa suka gani? Wani irin zunubi me girma Laylerh da Maleek suke aikatawa haka? hak’ik’a tunda yake bai tab’a kawowa aransa cewa soyayyar da Maleek keyiwa Laylerh zai iyasawa idanunsa rufewa, har ya kasa banbance halak da kuma haram ba, wannan wani irin Zunubi ne haka? Tayaya Maleek da Laylerh zasu kasance a irin wannan yanayin bayan kasantuwar matsayin Matar wani?
Yayiwa kansa tambayar cikin yanayin mamaki da kuma al’ajabin abunda idanuwansa suka gane mai, lallai yau ya sake gamsarwa kansa cewar rayuwar Laylerh da Maleek cike take da k’addara.
“Da ace Najeeb ne kuma ya gansu ahaka fa?.�
Wani sashi na zuciyarsa ta jefo masa tambayar daya sashi, saurin fad’in kalman.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un.�
Domin kuwa yasan faruwar hakan ba k’aramin tashin hankali zai haifar ba, saboda abune mawuyaci ace Najeeb ya iya b’oye zargi da kuma b’acin ransa.
Lallai yasan cewa so makahone amma sam baiyi tunanin cewa soyayya zata rufewa Maleek idanu har haka ba.
Duk da cewar baisan me sukeji acikin gangar jiki da zuciyarsu ba, amma yanajin cewa hakan da sukayi sam baikamata ba.
Hannunsa yakai ahankali ya share gumin daya fito daga goshinsa, kana asanyaye yace.
“Insha Allah Komae yakusa zuwa k’arshe, domin kuwa acikin irin wannan al’amarin dole sai wani abu na daban ya faru.�
Sauk’ak’akk’iyar ajiyar zuciya yayi tare da k’arasawa ya zauna akan wani chair dake nan aje gefen d’akin.
Zamansa akan chair’n kuwa yayi daidai da hango Oum Ayush da yayi ta nufo sashin.
Cikin sauri had’i da tsoron kada Oum Ayush d’in taga abunda ke faruwa, ya mik’e tsaye tare da k’arasawa jikin k’ofar, da d’an k’arfi ya daki k’ofar d’akin wanda hakan yasa gaba d’aya ta wangale.
K’aran dukan k’ofannasa ne kuma yasa Laylerh da gaba d’aya jikinta ya soma narkewa acikin na Maleek d’in tayi saurin jan jikinta baya, tare da soma k’ok’arin k’wato numfashinta dake fusga da kuma barazanar d’aukewa.
Haka ma Maleek k’aran bud’e k’ofarne yasashi d’ago kansa da sauri, idanunsa wanda sukayi ja suka kuma k’ank’ance ya zubawa Fou’ad dake tsaye ajikin k’ofar wanda ya tamke fuska kamar anyi masa mutuwa.
Ganin Fou’ad d’inne yasashi lumshe idanunsa tare da kawar da kansa gefe.
Laylerh kuwa gaba d’aya jikintane ya d’auki rawa, yayinda ta kasa koda d’ago kai ta kalli Fou’ad d’in, hakanan taji wani irin matsanancin kunya ya kamata, tare kuma da fahimtar cewa sam bata aikata daidai ba.
Take kuwa taji wani irin abu maikama da fargaba ya daki zuciyarta.
Wanda hakan yasa asanyaye wasu sabin hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan k’uncinta.

Daidai lokacin kuwa Oum Ayush ta k’araso da d’an sauri musamman ganin k’ofar d’akin da tayi abud’ene ma yasa hankalinta ya d’an tashi.
Ganin Fou’ad da tayine kuma tsaye abakin k’ofar yasa ta d’an fad’ad’a murmushin dake kwance akan fuskarta, cike da kulawa tace.
“Fou’ad ashe har ka dawo? Yanzu Abbou Khareem yake cemin wae kaje sayayyan kayan fruits.�

Murmushi Fou’ad ya d’an k’ak’alo tare da d’an jinjina kansa.
“Yanzun nan dawowa na sai naga ashema M.Jay d’in ya farfad’o.�
Ya fad’i hakan yana me aje ledan fruits d’in dake hannunsa.

Baki Oum Ayush ta bud’e daniyar bashi amsa, saidai kuma ganin da tayiwa Laylerh tsaye agefen Maleek d’in sororo yasa tayi shiru, idanu ta zubawa Laylerh’n na d’an sakanni kafun daga bisani ta dawo da kallon ta ga kofin tea d’in dake aje akan gadon Maleek d’in, yayinda shikuwa ya juyawa cikin d’akin baya.
Cikin yanayin mamaki Oum Ayush tace.
“Laylerh baki bashi tea d’in ba ajiye masa akan gado kikayi?.�
Laylerh da kanta ke k’asa jin tambayar da Oum Ayush d’in tayi matane yasa tayi saurin girgiza kai, asanyaye cikin muryarta dako fita da kyau batayi tace.
“A’a na basa tea d’in amma yace ya k’oshi!�
Ta k’are maganan cikin hard’ewar murya.

Ajiyar zuciya Oum Ayush ta sauk’e tare da maida kallonta ga Maleek d’in, kaman zata ce masa wani abu kuma saita fasa, ahankali ta k’arasa jikin gadon nasa tare dasa hannu ta d’auki kofin tea d’in, da har yanzu zafinsa bai huce ba.
“Maleek.�
Ta k’ira sunansa cikin alaman rashin wasa.
Ahankali cikin kuma yanayin salon daya riga yabi jikinsa ya juyo da kansa, tare da zubawa Oum Ayush d’in mayun idanunsa.
B’ata fuska Oum Ayush d’in tayi tare da watsa masa harara, cikin kuma yanayin had’e fuska tace.
“Ka d’auki tea d’innan kasha tun kafun ranka ya b’aci.�
Yanayin yanda tayi maganan tana me mik’o masa kofin tea d’inne yasashi d’an lumshe idanunsa, tare kuma dasa hannu ya karb’i kofin tea d’in.
Domin kuwa har acikin zuciyarsa yasan bai isa hana kansa sha ko cin abunda Laylerh’n ta had’a da hannunta ba.
Ahankali kuwa yakai cup d’in bakinsa, cikin yanayin nutsuwa da kuma kasalan dake damunsa ya shiga sipping tea d’in, kasan cewar har yanzu baigama dawowa cikin nutsuwarsa ba.

Oum Ayush kuwa ganin ya fara shan tea d’inne yasa ta dawo da kallonta ga Laylerh wacce har yanzu kanta ke k’asa.
Fahimtar kuma da tayi cewar Laylerh’n bata cikin mood mai dad’ine yasa ta d’an tausasa murya asanyaye tace.
“Har yanzu hannun naki ne yake miki zafi?�
Sanin da ita Oum Ayush d’in take ne yasa ta d’an girgiza kanta, alaman “A.a.�
Batare da tajira abunda Oum Ayush d’in zata kuma cewa ba, ta juya cikin yanayin sanyi ta nufi k’ofar toilet d’in dake cikin d’akin.
Ganin haka yasa Oum Ayush girgiza kanta kawae tare da shumfud’a d’aya daga cikin sallayan da tazo dashi ta tada sallah, domin tun awaje ta d’auro alwalanta.

Laylerh kuwa tana shiga cikin toilet d’in ta kifa kanta da jikin bango tare dasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta dake bugawa da k’arfi, asanyaye tasa hannu ta share hawaye masu d’umin da suka zubo mata.
Sanin kuma da tayi cewar babu wadataccen lokacine yasa bata wani tsaya b’ata lokaci ba ta d’auro sabuwar alwala, had’e da gyara rufin mayafin dake jikinta.
Bud’e murfin kofar toilet d’in tayi ta fito.
Hakan kuwa yayi daidai da mik’ewa tsaye da yayi.
Da k’arfi ya rumtse idanunsa, tare dasa hannu ya dafe saman mararsa, wanda tsananin ciwon da yake masa yasa shi sakin wani numfashin azaba, saidai kuma kasancewarsa jarumin soldier yasa shi daurewa duk da kuwa zafin ciwon da yakeji.
Akaron farko kenan tun faruwar abun da ta d’ago idanunta ta kallesa, saidai kuma ko second biyu batayi tana kallonsa ba tayi saurin sadda kanta k’asa musamman da taga ya nufo inda take.
Saura kuwa baifi taku uku ya iso kusa da I taba tayi saurin matsawa gefe, hakanne kuma yabashi daman rab’awa ta gefenta ya bud’e k’ofar toilet d’in ya shige.
Jin shigarsa da tayi cikin toilet d’inne kuma yasa ta sauk’e wata b’oyayyar ajiyar zuciya, cikin sauri kuwa ta matsa daga wajen.
Tare da d’aukan d’ayan sallayan da yayi saura ta shumfud’a, cikin nutsuwa ta tada sallah.

Shikuwa Maleek koda ya shiga cikin toilet d’in, ahankali cikin kuma tafiyarta mai kama da d’ingishi ya k’arasa gaban wani d’an babban mirror dake lik’e saman sink.
Fuskarsa kawai ya kalla acikin mirror’n ya d’auke kai.
Hannunsa yakai ahankali ya b’alle aninin wandon dake jikinsa, wanda hakanne kuma ya bawa saman mararsa daman bayyana.
Idanunsa ya d’an lumshe tare dasa tafin hannunsa ya d’an shafa saman marar tasa wanda anan ne yakejin matsanancin ciwo.
Wani abu da yaji yana bin hannunsa ne kuma yasa shi saurin bud’e idanunsa tare da kai dubansa ga saman marar nasa.
Abunda ya ganine kuma yasa shi zaro idanunsa waje, yayinda take hankalinsa yayi wani irin mummunan tashi.

*(Manage please and please Insha Allah Gobe kafun na tafi skull zan baku update, nima dai na samu na gama littafinnan na huta kuma ku huta😨)*
2/23/21, 7:11 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Chapter 56*
Chapter 96 · 0% Book details