← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 144

Sashe 41

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙiran sunan nata ne yasata bude idanunta ahankali, kana cikin sanyin murya ta, amsa masa.
ÆŠan gyaran zamansa yayi tare da juyowa ya fuskanceta.
Tabbas so yake ta fahimci kalamansa, ayanzu so yake ta gane manufa da kuma hujjarsa, duk da cewar bayason bayyana mata irin faÉ—uwar gaban da yakeji.
Ahankali ya kamo hannunta ya riƙe acikin nasa,
cikin sanyin murya yace.
"Inasonki Laylerh, bansan da yaushe soyayyarki ta shigeni da yawa har haka ba, duk da kasancewar tun aganin farko da nayi miki naji ajikina cewa lallai zamu rayu tare, har yanzu kuwa inaji ajikina cewar lallai zaki rayu aƙarƙashin inuwata."
Ajiyar zuciya ya sauƙe, wanda yasa ya ɗan tsagaita da maganar, hannunta dake cikin nasa ya kuma riƙewa.
Cikin son gamsar da kansa haÉ—e da kawar da tunanin dake cikin zuciyarsa yace.
"Nasan cewa aurena dake haɗin Allah ne, amma daga wani ɓangare na zuciyata, ina yawanjin faɗuwar gaba, tare kuma da fargaba, inaji ajikina tamkar wani abu zaimin shamaƙi, wanda zai hana zuciyata samun nutsuwa, lallai ina hango wani ƙalubale wanda nasan zuciyata bazata iya jurewa ba, saboda haka nayiwa Abbou Jaheed magana ya kuma dawo da lokacin auren mu kusa, Insha Allah nanda sati 1 zaki zama mallakina tawa halak malak, matata ta har abada, dan hakan ne kaɗai zai gusar min da fargaban dake sukan zuciyata akowacce rana, ina da kishi Laylerh, kishi kuma matsanancin, saboda haka bana fata wani ya shigo cikin rayuwarki."

Wani irin dummm da taji acikin kunnenta ne yasa ta É—ago kai ta kalleshi.
"Nanda sati É—aya zaki zama mallakina, matata ta har abada.!"
Sune kalmomin da taji sun daki zuciya da kuma dodon kunnenta, haƙiƙa har yanzu takasa yarda da kuma tantancewar wai zata zamo mata ga Najeeb, saboda har yanzu bata samu wani ƙwaƙƙwaran gamsuwa azuciyarta dangane da hakan ba, bugun zuciya da shigar numfashinta duk batare dashi suke tafiya ba, haka zalika babu ko ɗigon dangar takarsa dake yawo acikin jininta, bazata ce tanasonshi ba, haka zalika kuma baza tace tana ƙinsa ba, tabbas ta yarda cewa koda ace shidin yana daga cikin littafin ƙaddaranta, to baikasance ababi me tasiri ba, domin zuciya da tunaninta kwata kwata ba'akansa suke ba.
Idanunta dake neman kawo ƙwalla ta lumshe tare da zare hannayenta dake cikin nasa, ahankali ta kawar da kanta gefe, dan karon farko kenan da taji wani abu me kama da ƙuna na yawo acikin ƙirjinta.

Najeeb kuwa ganin ta zare hannunta daga cikin nasa ne yasashi jin zuciyarsa tayi wani iri, the first time kenan daya fara tunanin cewa Soyayyar sa bata shiga zuciyar ta ba.
"Idan kuwa har dagaske ne babu soyayyar sa azuciyar Laylerh, to waye kenan take so?. " 
Yayiwa kansa tambayar da bashi da amsarta.
Saurin girgiza kansa yayi domin bashi da  lokacin da zaiyi wani dogon tunani, yanayin yanda yaga canjawar mood ɗinta lokaci ɗaya ne yasashi jin duk wani confidence ɗinsa na zama very low.
Ahankali ya tura hannayensa cikin aljihun wandonsa, bandir din fararen ƴan dubu dubu ɗauri biyu ya ciro daga cikin aljihun nasa, wanda aƙalla zasu kai 100k, kasancewar kowani bandir ɗaya na kudin 50k ne.
Sake kamo hannayenta yayi akaro na biyu, ya É—aura mata kuÉ—in akan tafukan hannunta.
Cikin muryarsa da tayi sanyi yace.  "Gashi kiyi amfani dasu, idan kuma kina da buƙatar ƙari ko wani abu na daban ki sanar dani."
Ɗan tsagaitawa da maganar tasa yayi, tare da sake sanya hannunsa acikin aljihun wandonsa, waya ƙiran iphone 11 ya ciro, tare da ɗaura mata wayar akan cinyarta, ahankali ya sanya hannayensa ya juyo da fuskarta, ɗan ranƙwafowa yayi, tare da kissing forehead ɗinta, cikin sanyin murya da haɗe da mood ɗinsa daya sanja lokaci ɗaya yace. 
"Please ki kulamin da kanki." 
Miƙewa tsaye yayi batare da ya sake duban yanayin fuskarta ba kaitsaye ya juya ya nufi hanyar fita daga cikin falon. da idanunta wanda suka ciko da ƙwalla ta bisa da kallo har ya fice daga cikin falon.
Maida idanun nata tayi ta lumshe tare da sauƙe wata irin ajiyar zuciya.
Duk yanda taso ga tsaida hawayen dake cikin idanunta kasawa tayi, dole saida suka sauƙa akan fuskarta.
Kuɗi da kuma wayar daya ajiye mata takalla,  hakanne yasa taji zuciyarta ta ƙara karyewa,  haƙiƙa so take tayi kuka sosai ko zataji sukunin abun dake addabar zuciyarta.
Kudi da kuma wayan daya bata ta É—auka asanyaye ta wuce É—akinta.
Tana shiga cikin É—akin nata kuwa anan kan gado ta zube tare da watsar da kudin harma da wayar.
Fashewa tayi da wani irin marayan kuka, kukan da ita kanta batasan dalilinsa ba, kukan da tarasa madogara da kuma dalilin yinsa, kana kuma kukan dake fallasa asiri dakuma sirrin zuciyarta, kukane me ɗauke da yanayin yarinta, damuwa, haɗe kuma da ƙunan zuciya.
Haka kuwa tasha kukanta ta ƙoshi har bacci ɓarawo ya ɗauketa, wanda kuma ko acikin baccin nata sheshsheƙan kuka ta dinga sakewa.

3:30 pm. Daidai jirginsu ya sauƙa anan cikin airport din Nnamdi azikwe international airport.
Abbou Jaheed dake tsaye ajikin motarsa hango ɗan uwan nasa wato Abbou Kareem da kuma matarsa Oum Aisha da yayine yasashi faɗaɗa fari'ar dake kwance akan fuskarsa, cikin matsanancin farinciki ya ƙarasa garesu.
Rungume Abbou Kareem din yayi cike da tsananin murna shima Abbou Kareem É—in ya rungeme É—an uwan nasa, domin kuwa yanzu kusan shakararsu 1 kenan basu haÉ—u ba, duk da kasancewar ma Abbou Jaheed É—in na kaiwa É—an uwan nasa ziyara lokaci zuwa lokaci.
Bayan sun gama murnar ganin junane cikin farinciki Abbou Jaheed ya dubi Oum Aysha dake ta faman sakin murmushi, dan zuciyarta acike take da nishaɗin zuwa ƙasarta da tayi.
A mutunce suka gaisa da Abbou Jaheed din.
Cikin farinciki Abbou Jaheed yace.  "Bayan lokaci mai tsawo da kuka ɗauka bakwa ƙasar yau gashi kun dawo saboda auren ƴarku."  Murmushi Oum Aysha tayi cikin zaƙuwa tace. 
"Ƙwarai kuwa, bana ma tunanin sake komawa wata ƙasar yanzu gaskia, dan ayanzu naji shauƙin ƙasata sosai, yayinda kuma na ƙosa naga tilon ƴata."
Murmushi Abbou Jaheed yayi cikin nuna jin daɗin zuwan nasu yace.  "Tabbas nasan Laylerh zatafi kowa farinciki da zuwanku, dan gaba ɗaya rayuwarta acike take da kewa, yanzu kuwa kunzo adaidai lokacin da tafi ko yaushe buƙatarku."
Murmushi sukayi su dukansu, kafun Abbou Jaheed ya musu jagora zuwa mota.
Kaitsaye suka kama hanyar unguwar ta Asokoro.

Koda suka iso gidan cikin kulawa Momy ta tarbesu, duk da kuwa har cikin zuciyarta bataso zuwan nasu ba, musamman ma zuwan Oum Aysha, saboda kwata kwata batason matar.
Anan cikin falon suka zauna, inda Momy tasa Larai ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye.
Basu wani ci abincin sosai ba Oum Aysha da idanunta suka matsu dason ganin Laylerh, ta ture plate ɗin abincin dake gabanta, tare da ɗago kai ta dubi Abbou Jaheed, cikin yanayin ƙosawa tace. 
"Nifa idanuna sun matsu dason ganin Laylerh, har yanzu kuma naji ta shiru, kodai bata nan ne?."
Murmushi Abbou Jaheed yayi tare dayi mata nuni da hanyar É—akin Laylerh'n, alaman cewa tana É—aki.

Gane abun da yake nufine yasata miƙewa tsaye kaitsaye ta nufi ɗakin Laylerh'n.
Ahankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Tana shiga kuwa idanunta suka sauƙa akan Laylerh'n dake kwance tana bacci, duk da cewar bacci take amma sai sakin sheshsheƙan kuka take, kana cikin sangartacciyar muryarta take ƙiran sunan Maleek.
Murmushi Oum Aysha tayi tare da É—an girgiza kanta, sam batayi mamakin jin da tayi Laylerh'n na ambatan sunan Maleek ba, domin abune da yake tilas, kuma hakan dama baikamata ya zama abun mamaki ba, dan kusan rabin jinin dake gudana ajikin Laylerh'n na Maleek ne, zuciya da kuma ruhinsu É—aya, haka ma tunaninsu É—aya. Sake sakin wani murmushi tayi domin
tabbas tana ƙaunar ɗiyar ƙanin mijin nata sosai, bawai kuma dan bata taɓa haihuwa bane yasa takeson laylerh'n ba, tana matuƙar kaunar Laylerh'n ne saboda maraicinta.
Ƙarasawa jikin gadon tayi ta zauna tare da sanya hannu taɗan dafa goshin Laylerh'n, cikin kulawa taƙira sunanta.
Kasancewar bata da nauyin bacci ne yasa ta jin sautin muryar Oum Ayshan acikin kunnuwanta, hakan yasa ahankali ta ɗan buɗe idanunta, cikin sa'a kuwa ta sauƙesu akan Oum Aysha.
Ganin kaman gizo idanun nata ke matane yasata tashi da sauri tare da ƙara ware idanunta.
Murmushi Oum Aysha tayi cikin kulawa tace.
"BuÉ—e idanunki da kyau Laylerh, niÉ—ince dai Oum Ayush É—inki bawata daban ba."
Cikin wani irin matsanancin farinciki tafaɗa jikin Oum Aysha'n tare da wani irin maƙalƙaleta, zuciyarta cike da tsananin farinciki tace.  
"Oyoyo Oum Ayush ɗina, oyoyo nayi kewarku sosai, meyasa kuka daina zuwa wajena keda Abbou Kareem?, meyasa kuka manta dani? bayan kuma kunsan zanyi kewarku sosae?." 
Tayiwa Oum Ayshan duka tambayoyin cike da zallan shagwaɓa.
Murmushi Oum Ayush ɗin tayi tare da ɗan soma shafa kan Laylerh'n, cikin kulawa tace.  "Am so sorry my daughter bamunki zuwa bane, kinsan yanayin aikin Abbou Kareem din naki babu zama shiasa bamu samu isashshen lokaci munzo ba, kiyi haƙuri ki yafe mana kinji!."
Murmushi tayi tare da ƙara shigewa jikin Oum Ayush din, cikin son bayyana farincikinta tace. "Naji dadi sosai Oum Ayush, naji dadin zuwanku ina Abbou Kareem ɗina?."
Murmushi Oum Ayush tayi tare da cewa. "Abbou Kareem dinki yana falo." 
Tana matuƙar son Ƴan uwan baban nata, domin kuwa suna iyaka ƙoƙarinsu wajen nuna mata ƙauna, hakama Oum Ayush data kasance mata ga yayan baban nata tana nuna mata soyayya sosae kamar uwar da ta haifeta.
Cikin yanayin zumudi ta sauƙa daga jikin Oum Ayush din, da sauri ta nufi falon zuciyarta cike da son ganin Abbou Kareem.
Chapter 41 · 0% Book details