← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 144

Sashe 62

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Najeeb kuwa ganin ta kwanta ɗin ne yasashi ɗan numfasawa tare da komawa kan wata haɗaɗɗiyar kujeran dake cikin ɗakin ya zauna, hannayensa yasa ya tallafi haɓansa, tare da tsurawa Laylerh'n dake kwance idanu, abubuwa da yawane ke yawo aransa dangane da ita, yayinda kuma har yanzu jarababben feelings ɗinta ya kasa sakeshi, saboda tsabar bala'ima har ji yake mararsa na murɗawa, shikansa baesan cewa ƙarfin sha'awar da yakeyiwa Laylerh'n takai haka ba sae yau, da yaga samu ya ga rashi nan take, abun da yake tambayar kansa ayanzu kuwa shine.
"Shin haka zai zauna da Laylerh'n batare da ya shayar da ita dadi, da kuma ɗanɗanon dake cikin aure ba?." Tabbas abun ya tsaya masa arai, saboda Allah Yasani amatuƙar buƙace yake da Laylerh'n, dan ko ada duk lokacin da ya kalleta, sai yaji wani irin hot feelings ɗinta na sukarsa, burinsa ako da yaushe shine ta zamo mallakinsa, tayanda zai kashe duk wani sha'awarta da yakeji, wanda akusan kullum take hanasa sukuni, amma kuma sai gashi ya kasa samun daman hakan.
Ahankali ya fesar da wani irin numfashi me zafi, tare da sa duka tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa, da kuma idanunsa wanda sukayi jajur.

Laylerh kuwa da tun É—azun take kallonsa, ganin ya rufe fuskarsa ne yasa ta lumshe idanunta, wanda suke fitar da hawaye.
Ƙaƙƙarfan numfashi taja, yayinda awani sashe na zuciyarta, takejin tausayin Najeeb ɗin ya lulluɓeta, domin duk da kasancewarta yarinya, hakan bai hanata sanin cewar ga kowanni Ango da Amarya ranar farkonsu, ranar farinciki ce agaresu ba, amma awajensu su ba hakan bane.
Sannan tambaya É—aya da ta fara yiwa kanta shi ne.
"Meyasa Ƙaddara ke wujijjiga rayuwarsu?."
Haƙiƙa dukansu suna buƙatar canjin rayuwa, ba itaba ba Maleek ba har ma Najeeb ɗin kansa, domin kwata kwata ita tasan bata dace dashi ba, dan ba irinta wanda zuciyarta tayi nisa acikin son wani ya kamata ya samu amatsayin mata ba, me ƙaunarsa ya kamata ya samu.
ÆŠanjim tayi kana kuma acikin ranta take faÉ—in.
Inama da ace kowa zai gane cewa Maleek shine zaɓin zuciyarta, mafarkinta, da kuma muradinta, inama da ace agogon ƙaddaranta zai juya ta hanyar kusanta ta da MALEEK, saboda shine ya kasance mafarkinta akullum.
Babban abun dake damunta kuwa shine, tayaya zata fara koyawa zuciyarta zama batare da shi ba? Tayaya zata koyawa kanta soyayyar Najeeb, wanda acikin kaso ɗari na zuciyarta, batajinsa acikin kashi biyar, kana tausayi da kuma feeling ɗin da takeji akan Maleek sam batajinsa akan Najeeb, ƙwarai tasan akwae banbanci atsakaninsu.
Idan tace banbanci kuma, to tana nufin tazara me nisa.

*6/January/2021*
1/19/21, 8:28 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for that, if you know you did'nt pay, please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. Whatsapp number 07017879464.)*

*(Note Edit)*

*Chapter 35*

Ajiyar zuciya ta kuma sauƙe akaro na barkatae, tare da sake matse jikinta waje ɗaya, haƙiƙa awani ɓangare na sashin zuciyarta tausayin Najeeb ɗinne yayi kwance, wanda har hakan yasa takejin kamar akwai wani abu na rashin kyautawa da tayi masa, saidai kuma bata da wani zaɓi wanda ya wuce ta ƙyalesa, duk da kuwa ta lura da cewar yana cikin damuwa.
Ahankali kuma cikin yanayin sanyi takae hannu ta share hawayen dake tsiyaya ta gefen fuskarta, jin brain ɗinta na ƙoƙarin tuna mata kalaman da Oum Ayush ta faɗa mata ne yasa ahankali takai hannayenta ta toshe kunnuwanta, saboda tuna maganganun Oum Ayush ɗin zai ci gaba da sawa taji kaman bata aekata daedae ba, wannan yasa ta soma ƙoƙarin nutsar da kanta yanda bacci zai ɗauketa, kasancewar tun ɗazu takejin baccin, amma kwata kwata rashin samun gamsashshiyar nutsuwa ya hanata.

Najeeb, Kusan mintuna 15 ya ɗauka yana zaune akan kujeran, yayinda kuma har yanzu tafukan hannunsa ke kan fuskarsa, tunani daban daban ne ke yawo acikin ƙwaƙwalwarsa,yayinda wani tunanin yake kasancewa me daɗi, wani kuma akasin haka.
Ahankali ya fesar da wani numfashi me zafi ta bakinsa, haɗe da janye hannayensa dake kan fuskarsa, wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauƙe, kana ya kuma sauƙe ganinsa akan Laylerh'n.
Kallon agogon dake maƙale aɗakin yayi.
Ƙarfe ɗaya 1:00 am dai dai ya gani, aransa da kuma zuciyarsa yace. "Sabuwar ƙaddara da kuma sabuwar rayuwa."
Sake dawo da kallonsa ga inda Laylerh'n ke kwance yayi, wanda zuwa yanzu yasan ta riga da tayi bacci, sannna kuma har yanzu sosae yakejin feelings ɗinta na ratsashi, musamman ma idan ya tuna da yanda ɗazun ya sauƙe lips ɗinsa akan soft skin ɗinta, me tsananin taushi da ƙamshi, haka yakejin tsikar jikinsa na zubawa, gefe guda kuwa ga mararsa dake ta faman murɗawa, saidai kuma sanin kansane babu yanda zaiyi dole haka zaiyi haƙuri ya ƙyaleta, saboda baisan me zai faru anan gaba, idan ya sake taɓata ba.
Ahankali ya miƙe tsaye daga zaunen da yake, cikin yanayin dake bayyana cewar gaba ɗaya jikinsa ya gamayin sanyi, ya ƙarasa gaban gadon da Laylerh'n ke kwance.
Ɗan sunkuyawa yayi ya leƙa fuskar Laylerh'n wanda ke ɗauke da danshin hawaye.
Murmushin daya ɗan bayyana ɓoyyayen dimples dinsa yayi, ahankali yakai hannunsa kan fuskarta, tare dasa ƴar yatsarsa ya lakato hawayen dake maƙale agefen idanunta.
"Wataƙila kuka baya bata wahala." Yafaɗi hakan azuciyarsa yana me shafa gefen fuskarta, wanda sili silin dogon gashinta suka kwanta awajen.
Jawo blanket É—in yayi ya rufa mata da kyau, tare da zagayawa ahankali ya hau kan gadon, gudun kuma kada ya tasheta abaccin da takeyi É—inne yasa shi yin komansa ahankali, inda yaja blanket É—in shima ya rufe rabin jikinsa, yanayin yanda ya kwanta É—inne yasa yana iya kallon bayanta, da kuma dogon gashinta da ya watse akan pillow.
Idanunsa wanda sukayi ja ya lumshe tare da shaƙan wani sassanyan numfashi, me ɗauke da fitinannen ƙamshin dake fita ajikin Laylerh'n, jin ƙamshin na ratsa hancinsa ne yasashi buɗe idanunsa ya tsurawa bayanta ido, take kuwa yaji wani irin sabon sha'awarta na sake shiga jikinsa, yayinda yake jin kamar ya juyo da ita ya haɗe bakinsu waje ɗaya, ko hakan zaisa yaji sassauci na daga abun da yakeji.
Ahankali yaɗan matso da jikinsa kusa da ita, saidai kuma hakan baisa ya zama suna kusanci da juna ba, saboda tsakaninsu akwae ɗan tazara kaɗan, alokacin da ƙamshin nata ya ci gaba da shiga hancinsa kuwa, lumshe idanunsa yayi tare da sakin wani irin numfashi me kama da nishi, asanyaye yasa hannunsa ya dafe mararsa da yakejin tanayi masa ciwo, haƙiƙa shi kansa baisan cewa ƙarfin sha'awan Laylerh'n da yakeyi yakai haka ba sae yau, dayake ganinta gashi gata, aɗaki ɗaya, kuma agado ɗaya, saidai kuma babu yanda za'ayi ya kawar da duk wata damuwar da ta dameshi ayau ɗin, duba da irin halin da Laylerh'n ke ciki, idan kuma har bazai tauyawa mata ayau ɗin ba, to haƙiƙa baicika masoyin gaskiya ba, duk da kuwa cewar yana matuƙar buƙatarta, akuma yanda yakejin kansa ayanzu, nutsuwa kawae yakeson samu daga gareta, tabbas da ace taɓata bazai zamo masa wani sabon case ba, to daya shiga jikinta yayi romancing ɗinta ko zaiji nutsuwar da zata sa ya iyayin bacci, saboda Allah Ma ya gani amatuƙar matse yake, ayanzu kuwa sosae yake buƙatar mace akusa dashi.
Sake dafe mararsa yayi da ƙarfi, saboda yanda yaji ta murɗa masa, tare kuma da rumtse idanunsa, ahankali ya sake matso da jikinsa kusa da Laylerh'n, tare da cusa fuskarsa acikin bajajjen gashin kanta dake fitar da ƙamshi, kasancewar turarukan gashi na musamman Oum Ayush ke bata tana shafawa.
Ahankali ya sake gyara kwanciyarsa, tare da ƙara kusanta gansa da ita, saidai kuma duk da haka baiyi yunƙurin taɓa jikinta ba, saboda yasan abu kiris ne zai iya tada ta daga baccin da takeyi.
Idanunsa ya lumshe, tare da sake dafe mararsa, ahankali yake fitar da wani irin numfashi, domin tabbas awannan lokacin shi kaÉ—ai yasan me yakeji.
Duk abun da yakeyi ɗin tanajinsa, saboda dama baccin nata bawae yayi wani nisa bane, tun hawansa kan gadon kuwa ta ɗan buɗe idanunta, saidai kasancewar bataso yagane cewar ta farka ɗinne yasa ta maeda idanunta ta rufe, tare da ƙinyin kyakykyawan motsi, duk da cewar kuwa hawansa kan gadon yasa taji faɗuwar gaba, saedae bisa dole ta daurewa duk wani fargaba da tsoronta, dan tayi imani awannan karon idan wancan mood ɗin ya dawo mata babu wani me cetonta,, jin kuma yanda ya matso bayanta ne yasa ta, soma ambaton sunan Allah acikin rae da zuciyarta, tare dayin fatan Allah Yasa bacci yakuma sake ɗaukarta, cikin ikon Allah kuwa ko 5 minute ba'ayi bacci me ɗan ƙarfi ya ɗauketa.
Ɓangaren Najeeb ɗinma dae rufe idanunsa yayi, tare da yiwa kansa fatan bacci, saboda ya tabbatar cewa nan da mintuna kaɗan idan bacci bae ɗaukesa ba komae zai iya faruwa, domin feelings ɗin nasa ƙara hawa yake, wanda kuma zuwa nanda ƴan mintuna kaɗan yasan bazae taɓa iya control ɗin kansa ba.
Jin kuma yanda sautin numfashin Laylerh'n ke fita ne ya sashi gane cewar baccinta ya ɗan soma nisa, wannan dalilin ya sashi sake matsowa jikinta, wanda kuma hakanne ya bashi daman jin feelings ɗin nasa naɗan sauƙa, take kuwa bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Chapter 62 · 0% Book details