← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 144

Sashe 23

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Laylerh dake kwance tayi hugging pillow,yayinda zuciyarta tayi nisa cikin tunanin Maleek wanda hakan yasa ita kaɗai take ta sakin murmushi.   Jin ana knocking ƙofar ɗakin tane yasa ta miƙewa, ahankali take ɗan taka kafarta wanda tuni ta ware ta daina yi mata zafi sosai.  Ƙarasawa jikin ƙofar tayi tare da buɗewa.        
Ganin Larai tsaye abakin ƙofarne yasata sakin murmushi, cikin son bawa Larai'n girmanta tace.  "Inna Larai ki shigo mana."  
Murmushi Larai tayi tare da cewa.  "Aa ai bama sai na shigo ba, dama Alhaji ne yace na ƙirawoki."   murmushi Laylerh tayi tare da cewa to gani nan zuwa.    
Komawa cikin ɗakin tayi, kaitsaye drawer ɗinta ta buɗe wani farin ɗan ƙaramin mayafi ta ɗauka tare da yane kanta dashi, cikin nutsuwa ta nufi falon dan amsa ƙiran da Abboun ke mata.       
Tana shigowa cikin falon tayi ido huɗu da Najeeb wanda dama tun zamansa awajen jiran fitowarta yake.     Kasa tayi da kanta tare da ƙarasowa dining area ɗin.
Kujera taja ta zauna, cikin salon shagwaɓan da sometimes bata sanin tanayi tace "Abbou gani."   Murmushi Abbou yayi sannan cikin kulawa yace.   
"Ya ƙafan naki ta daina zafi ko?."    kai ta gyaɗa masa alaman.    "Eh."      Kanta yaɗan shafa cikin tausayi haɗi da ƙaunarta yace.  "Good girl tashi kiyi seving ɗinmu to."      Murmushi ita ɗinma tayi, wanda har acikin ranta tanajin daɗin kulawan da Abbou Jaheed ke bata, tabbas tarasa uwa uba amma Abbou na iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin batayi kukan maraici ba.
Cikin nutsuwa ta soma ƙoƙarin seving ɗinsu.  Daidai lokacin M.Jay ya shigo cikin falon.  Ɗan Lumshe idanunta tayi tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin turarensa da ya kawowa hancinta ziyara,  jin motsin ƙarasowansa dining area dinne yasa tajin wani irin sanyi na ratsa jikinta, take ta kwaɗaitu da son ɗaura idanunta akansa.   Jan kujera tayi ta zauna tare da ɗan satan kallon gefen da yake, sosai yayi kyau cikin shigar white shirt, da kuma white trouser ɗin dake jikinsa.     
Maida kanta ƙasa tayi tare da jawo plate ɗin abincinta gabanta, kasancewar yunwa takeji sosai yasanya bata jira komai ba ta fara cin abincin.     
Maleek kuwa tun isowarsa wajen bai ɗaga kai ya kalli kowannen su ba, wani haɗaɗɗen cup ya ɗauka tare da haɗawa kansa tea, komawa yayi ya zauna ahankali ya ke ɗan sipping tea ɗin yayinda rabin nutsuwarsa ke kan wayar dake hannun sa.       
Ɗagowa Abbou Jaheed dake cin abinci yayi ya dubi kowannensu.   
Tsaida cin abincin nasa yayi tare dayin ɗan gyaran murya.  
Cikin kulawa haɗi da nuna musu amfanin abun da yakeson faɗa yace.  "Tabbas duk wani buri da kuma fatan uba nagari shine farinciki da kuma samun nasaran Ƴaƴansa."  Ɗan jim yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallon Laylerh dake cin abinci yayi cikin kulawa haɗi da tsananin tausayinta yaƙira sunanta.      "LAYLERH!."        
akaron farko kenan da taji ƙiran sunanta da Abbou'n yayi ya tsinkar mata da zuciya, tsaida cin abincin nata tayi tare da ɗago kai ta kalli Abou'n.      
Hannunta ya kamo cikin kulawa yace.   "Laylerh ke ƴata ce da nakejin soyayyarki acikin raina, duk da nasan cewar banine na haifeki ba,amma koda sau ɗaya ban taɓa kallonki amatsayin wacce ba jinina ba, haka zalika ako da yaushe matsayin Uba nake agareki, kuma nasan ina da haƙƙin da zanyi miki zaɓi  na gari arayuwa, nayi imani cewa kamar yanda bazan iya cutar da yayanki Maleek ba haka kema bazan iya cutar dake ba, tabbas kina da matsayi me girma awajena Laylerh,  wanda hakan yasa na yanke wani hukunci  batare da nayi shawara da kowa ba, fatana da kuma burina ako da yaushe shine ki karɓi zaɓin da nayi miki hannu bibbiyu!."   Ɗan numfasawa yayi tare da sake riƙe hannunta ƙam, idanunsa ne suka ciko da ƙwalla, saboda lokaci ɗaya yaji Rasuwar ƙaninsa Abbou Mahmoud ya dawo masa sabuwa, dan tabbas da ace yana nan ayau shine zaiyiwa Laylerh'n haka.      
Ganin Hawaye a idanun Abboun ne yasa Laylerh zaro idanunta, cikin tsananin mamaki haɗi da kaɗuwa ta soma girgiza kai, cikin muryarta dake ckracking tace.  "Please Abbou dan Allah, Ka umarceni akan komai bazan taɓa saɓa maka ba, please Abbou dan Allah karka bari hawaye sufita daga cikin idanunka saboda ni!."   tayi maganar ƙwalla na saukowa daga cikin idanunta.       
Ganin hawaye akan fuskarta ne yasa Abbou shima ya girgiza kai, cikin sassanyar murya yace.  "Kada ki sake barin hawaye su fita daga cikin idanunki Laylerh, burina ako da yaushe shine nafaranta miki, har abada ina fatan hakan da nayi bazai zamo cutarwa agareki ba."    tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da ɗan gyara zamansa cikeda  kulawa yace.  
"Nasan ke ƴace me biyayya agareni ako da yaushe, kamar kuma yanda yake alhakin kowani Uba ne ya zaɓawa ƴarsa miji nagari, nayi ƙoƙarin kamanta hakan, dan na zaɓa miki NAJEEB amatsayin mijin da zaki Aura.!!!."

*(Hmmm chab chakwakiya kenan Abbou ya zaɓawa Laylerh Miji, lallai akwai gurmi.)*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 0002214625 Abubakar muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp Number 07017879464.*

*Chapter 12*
Chapter 23 · 0% Book details