← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 144

Sashe 79

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wayarsa k’irar Samsung wanda ke aje bisa saman wani had’add’en table ne ke ta faman kuwa, da’alama dae k’iran wayannasa ake babu k’akk’autawa.
Ahankali ya d’ago kansa daga durk’uson da yake, wanda hakanne kuma ya bani daman kallon idanunsa wanda sukayi jajur, kallo d’aya kawai zakayi masa ka fuskanci cewa d’auke yake da damuwa me tarin yawa.
Kasancewar yanzu kusan sama da 40min kenan da ya d’auka zaune awajen, yayinda ya duk’ar da kansa k’asa.
Hakanan yakejin gaba d’aya duniyar batayi masa dad’i, yayinda ajikinsa yakejin sauyin yanaji, wanda hakan ke yawan haifar masa da fad’uwar gaba, saboda yanda yakejin wani abu na daban na neman haukata tunaninsa, yayinda yakeji ajikinsa cewar wani abu na daban na shirin tunkaro rayuwarsa.
Daga gefe guda na zuciyarsa kuwa tunani da kuma k’aunar Laylerh ne ke hura masa wuta, wanda har hakan yasa yakejin kamar zuciyar tasa zata buga.
D’ago kansa yayi tare da jingina bayansa ajikin had’add’iyar kujeran da yake kai, wanda ke cikin katafaren office d’insa.
Hannunsa yakai kan wayarsa dake ta faman tsuwa, batare kuma da ya duba wanda ke k’irannasa ba ya kashe wayar tasa gaba d’aya.
Idanunsa wanda sukayi ja sosai ya lumshe, tare da fesar da wani irin zazzafan numfashi.
Ahankali aka turo k’ofar office d’innasa aka shigo.
Fou’ad wanda shine ya shigo cikin office d’in ganin yanda M.Jay d’in ke zaune ya rumtse idanunsa ne yasa shi d’an tsayawa tare da kafesa da idanu.
Ganin da yayi kuma kaman Maleek d’in baisan da zuwansa bane, ya sashi sauk’e wata irin ajiyar zuciya, ahankali kuma ya shiga takowa zuwa tsakiyan office d’in.
D’aya daga cikin kujerun da aka tana da musamman dan zaman bak’i ya ja ya zauna, har zuwa lokacin kuwa Maleek bai bud’e idanunsa ya kalli Fou’ad d’in ba, duk da kuwa cewar ya ji shigowansa, k’amshin turaren D&G kuma da yaji ya shiga hancinsa ne ya sashi gane cewa Fou’ad d’inne ya shigo, saboda aduk mutanen dayasan zasu iya shigo masa office kai tsaye, Fou’ad ne kad’ai ya fiye amfani da turaren na kamfanin Dolce & Gabbana.
“Captain.�
Fou’ad ya k’ira sunansa cikin d’an d’aga murya ta yanda zai jisa da kyau, saboda atunaninsa Maleek d’in yayi nisa ne acikin tunanin da yakeyi shiyasa baiji shigowarsa ba.
“M.Jay.�
Fou’ad ya sake k’iran sunansa akaro na biyu, tare da d’ansa hannu ya buga table d’in dake gaban Maleek d’in.
“What?.�
Maleek d’in ya fad’a cikin cushewar murya, domin sam baiyi farinciki da zuwan Fou’ad d’in ba, because yasan zuwan Fou’ad d’in babu abunda zae k’ara masa sae yawan tension.
Fou’ad d’in kuwa jin abunda Maleek d’in ya fad’a ne yasa shi, d’age kafad’ansa cikin yanayin mamaki yace.
“Dama kenan kanajina amma kashareni kayi kaman baka ji ba? anyway duk ma ba wannan ba, Ashe har babban abu me girma zai taso maka amma ka kasa fad’amin, atunani na dai baka da wani aboki aduniyarnan sama dani, meyasa ka b’oyemin hakan?.�
Idanunsa wanda ke alumshe ya bud’e kana ahankali ya sauk’e su akan Fou’ad d’in dake zaune facing d’insa.
Hannunsa yasa ya d’an shafi gefen fuskarsa, inda lafiyayyen sajen daya k’arawa fuskartasa kyau ke kwance lub.
“Me na b’oye ma?� Ya fad’a cikin muryarsa dake bayyana zallan miskilancinsa, wanda kuma da alama yau miskilancinnasa ne ya motsa fiye dana kullum.
“Abubuwa da yawa ciki kuwa harda maganan aurenka da Munnira y’ar gidan Alhaji Farouk, na tabbatar da ace Abbou Jaheed bai k’irani ya fad’amin akan mufara shirye shirye da wuri ba da bazaka tab’a fad’amin ba, why Maleek meyasa kake shashantar da duk wani abu naka me mahimmanci ne?�
Cewar Fou’ad da ya tsaresa da idanu.
“Abu me mahimmanci? meye shi? Aure shine abu me mahimmanci? Hmmm.�
Idanunsa ya d’an lumshe tare dasa teeth d’insa ya ciji jajayen labb’ansa, cikin wata irin murya dake bayyana gaskiya da kuma zallan abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“Ba yanzu ba ko agaba bana tunanin akwae wani abu me mahimmanci’n da zai sake tunkarar rayuwata, duk way’annan abubuwan sun isa Fou’ad nagaji da komai, ba kuma nason komai da kowa banason wata mace ta rab’eni domin ban tsarawa kaina rayuwa da wata ba, impact ma babu zanen k’addara da sunan wata mace daban acikin jinina, so please leave me alone banason sake jin wani zance na daban akan wata!!� Yanayin yanda ya k’are maganar yana me dunk’ule hannayensa ne yasa Fou’ad sakin murmushi.
Cike da takaicin halin da M.Jay d’in ya jefa kansa aciki yace.
“Da kyau komae ka tsarawa rayuwarka daidai ne awajenka, bakason sake jin wani zance na daban akan wata, amma kana son sake jin wani zance akan matar da take mallakin wani, kana kuma da lokacin da zaka b’ata sama da awanni kana tunaninta, koda sau d’aya ne kuma baka tab’a tunanin yawan zunubin da kake kwasawa kanka bako? Good Maleek bazan hanaka gudanar da rayuwarka daidai da irin yanda kakeso ba, amma kasani amatsayina na abokinka dole ne na fad’a ma gaskiyar abunda ke akwae, koda kuwa hakan zaisa kaji ba dad’i, nasan cewa kanason Laylerh so kuma matsananci, amma cire ta acikin zuciyarka shine abu me sauk’i, domin tariga ta haramta agareka karka manta ita fa ayanzu matar wani ce, kuma......”�
“Enough is enough Fou’ad, banason jin komae, domin babu wani abu da zaka fad’a wanda zaiyi tasiri acikin rai da zuciyata, saboda ba kasan menene SO ba, Fou’ad nayi imani cewa koda da second d’aya ne bakasan hak’ik’anin abunda nakeji acikin zuciyata ba, soyayyar zuciya kawae kasani bakasan ta jini ba, bakasan komae ba Fou’ad, ba kuma zaka tab’a sani ba, saboda nasan babu wani wanda za’a k’ara halitta masa matsanancin so azuciyarsa kaman yanda aka halittamin na Laylerh acikin jiki da jinina, ka tashi kaje Fou’ad banason ganinka please!!�
Yafad’i hakan cikin wata irin raunannan zuciya, wanda kuma salo da yanayin maganar tasa ta matuk’ar bayyana rauninsa, saboda hakan kuwa harsaida yasa hannu ya dafe daedae saitin zuciyarsa.
Fou’ad kam kasa koda motsa k’afarsa yayi saidai idanu kawae daya zubawa Maleek d’in.
K’warai yana mamakin irin sonda Maleek keyiwa Laylerh, soyayyar da har rana me kaman ta yau yakasa furta mata, soyayyar da yakeyinta da gaba d’aya rayuwarsa, tabbas shikam baya fatan Allah Ya d’aura masa k’addaran so me tsananin zafi irin ta Maleek, domin kuwa rashin samun abunda kake so d’in ba k’aramin nakasar maka da rayuwa zaiyi ba.
“Maleek!!!�
Fou’ad ya k’ira sunansa da wata irin sassanyar murya.
Bai d’ago kansa ba haka kuma bai amsawa Fou’ad d’inba, domin kwata kwata bayason jin kalaman Fou’ad d’inma acikin kunnuwansa, saboda yasan ba abunda Fou’ad d’in zai iya cemasa face ya cire son Laylerh azuciyarsa.
Soyayyar Laylerh azuciyarsa kuwa abune da har abada bazae tab’a fita ba, domin ayanzu soyayyar tata ce kad’ai ke rik’e dashi, rashinta rasa rayuwarsa ne gaba d’aya.
Fou’ad kuwa ko kad’an baidamu da rashin amsawan Maleek d’in ba, domin yasan halin Maleek d’in sometimes ma baicika yawan son adameshi da magana ba, saboda kamar yanda yake bazai yiba haka ma bayaso amasa.
Saidai kuma ayanzu tunanin da zuciyarsa tayi masa ya sashi d’anjin sanyi acikin ransa, domin yana ganin cewar idan Maleek d’in yayi aure komae zaizo da sauk’i, duk dama dae yasan cewa abune me wahala Maleek d’in ya iya jure kallon Munnira amatsayin mata, amma yasan yau da gobe k’addara zata sa ya k’arbi Munniran dan dolensa, ko ba komae kuma zata d’an rage masa zafi.
Tabbas zuwan sa wajen Maleek d’in da yayi yanzu ya sashi fahimtar cewa Maleek bazae tab’a shigowa ayi sha’anin bikin auren tare dashi ba.
Wannan yasa shi yanke hukuncin cewa shi da kansa zai tsara duk wani abunda ya dace har zuwa lokacin bikin, zai kuma gayyaci iya mutanen daya sani, duk da cewar yasan zai buk’aci me tayasa, amma zaiyi iya nasa k’ok’arin shima, saboda daga shi sae SOORAJ ne Maleek d’in ya aminta dasu, saidai daga Maleek d’in har SOORAJ jirgi d’aya ne ya d’ebosu, afannin halayya kamar uwa d’aya uba d’aya suke, domin koda sun had’u kowannensu zai iya sha re 40 minute baice da d’an uwansa k’alaba, sunan kuma waisu manyan abokai, amma kuma magana wahala take basu, wannan yasa bazae ma nemi SOORAJ d’inba shikad’ai zai tsara komae.
Ahankali ya mik’e tsaye daga zaunen da yake, kallon Maleek d’in da har yanzu ke dafe da daidai saitin zuciyarsa yayi, kamar kuma zai ce dashi wani abu, amma sae ya fasa tare dajan bakinsa yayi shiru, kaitsaye kamar yanda Maleek d’in ya buk’ata ya fice daga cikin office d’in da yake kamar wani hamshak’in falo, anzuba masa komae da komae na burgewa.
Chapter 79 · 0% Book details