← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 144

Sashe 2

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin yanda ta ƙare maganan tana ɗan rawar da idanunta ne yasa ƴan guntun ƙwallan da suka maƙale acikin idanunta suka samu daman gangarowa.
Daidai lokacin kuwa wata motar taxi tazo wucewa, da sauri ta sanya hannu tana taran taxi É—in, cikin sa'a kuwa ya tsaya.
Tana faÉ—a masa inda zai kaita, batare da tajira me zaice ba ta buÉ—e motar ta shiga, yayinda me taxi É—in yaja motar sukayi gaba.
Jakan dake goye abayanta ta ɗaura akan cinyarta, zage zip ɗin jakan nata tayi, ahankali ta sanya hannu acikin aljihun jakan ta zaro 1k wanda shine iya kuɗin da ya rage mata,  bayan shi kuwa bata da ko sisi.
Ɗan jingina bayanta tayi da jikin kujeran motar, ahankali ta sauƙe ajiyar zuciya me nauyi, tabbas idan naira dubu ɗayan nan ta ƙare batasan ya zatayi ba, dole ne ta fara takawa da ƙafa.
Ahankali taÉ—an lumshe kyawawan idanunta.
Tunani ne kwance acikin zuciyarta har suka iso bakin katafaren school É—in nasu batare da ta sani ba.
Jin taxi ɗin ya tsaya ne yasa ta buɗe idanunta, ganin sun iso bakin gate ɗin makarantar ne yasata fitowa daga cikin taxi ɗin bayan ta miƙa wa me taxi ɗin, 1k ya bata canji.
Ganin gate É—in makarantar tasu a rufe ne yasa taji gabanta yaÉ—an faÉ—i, dan tabbas tasan cewa tayi latti.
Ahankali ta ƙarasa jikin gate ɗin tare da ɗan  ƙwanƙwasawa.
Ɗaya daga cikin securities ɗin dake gadin gate ɗinne ya buɗe ƴar ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin,   ganinta ya sashi zuba mata ido, tare da ɗaure fuskarsa, duk da cewa shi sabo ne awajen amma  tabbas ya shaida fuskarta saboda tana yawan zuwa late, cikin gurɓatacciyar hausan sa da bai gama iyawa ba yace. 
"Yarinya ki koma gida dan kinyi latti, kin san kuma bazan barki ki shiga ba, saboda yin hakan saɓawa aiki na ne." 
Idanunta da suka ɗan ciko da ƙwalla ta ɗago ta kalleshi, cikin sassanyar murya tace.
"Dan Allah kada ka hanani shiga, wallahi ban samu bus da wuri bane, please insha Allah zanna kiyayewa."    Kai ya girgiza  mata, tare da maida ƙofan ya soma ƙoƙarin rufewa, dan yasan idan har ya barta tashigo, muddin aka ganta akwai matsala, dan dokane na makarantar duk ɗalibin da baizoba har aka rufe gate to fa ko yazo saidai ya koma gida, idan kuwa aka kama ɗaya daga cikin  masu gadi da laifin buɗewa wani ɗalibi ko ɗaliba ƙofa to zai karɓi punishment me ƙarfi.

Saurin riƙe ƙofar tayi cikin yanayin roƙo tace.  
"Dan Allah Kamin alfarma koda sauÉ—aya ne, na yau kawai kabarni na shiga, 9 daidai muna da test kuma idan banyi ba zai iya kawomin nakasu please."

Kallon yanda idanunta suka ciko da ƙwalla gate man ɗin yayi,  hakanan yaji wani abu adangane da ita,  duk da cewa shi ba musulmi bane, amma yakanji wani irin nauyi aransa idan aka haɗasa da ALLAH.
Ɗan jinjina kansa yayi, cikin gurɓatacciyar hausan sa yace. 
"Zan barki ki wuce, amma ki kula kada wasu su ga shigowarki, saboda idan aka kamaki nima hakan zai shafeni."  
Dasauri ta jinjina kanta, cikin jin daÉ—i tace.
"Nagode sosai."  da sauri ta shige cikin makarantar, shi kuma ya maida ƙofar ya rufe.

Cikin hanzari take tafiya, har kafafunta suna harÉ—ewa, tsoro ne fal zuciyarta, addu'a take tayi Allah Yasa kada aganta.
Cikin ikon Allah kuwa har ta kawo bakin class É—insu bata taradda malami ko É—aya awaje ba, duka suna cikin aji suna gudanar da lectures, haka ma securities É—in da suke kula da makarantar basu taho ta wajen da take ba.
Ɗan leƙa ajin nasu tayi ta window, gabanta ne ya faɗi ganin tuni Maths teacher ɗin da zaiyi musu text ya shiga, har ya fara rubuta musu questions akan  board.
Jikinta ne ya soma rawa, dan sarai tasan  Teacher David baida mutunci ko kaɗan, yanzu sai yace bazata shiga ba.
Ɗan danne siraran laɓɓanta masu kalan pink tayi, ahankali ta ƙaraso bakin ƙofar ajin nasu ta tsaya.
Ƙarasowanta kuwa yayi daidai da ɗago da kansa, yakai duba zuwa bakin ƙofar.
Ganinta ya sashi ƙanƙance ƙananan idanunsa, cikin halin baƙin hali yace.
"you, from where?".
Yatsun hannunta ta soma ɗan murzawa, samun kanta tayi da kasa cewa komai, dan tasan sa kamar maye yake, daka masa ƙarya zai gane.
Kallonta yayi naɗan wasu daƙiƙu, wani yawu ya haɗiya tare da cewa.  "Oya come in."  
Jin haka yasa taji wani sanyi aranta, ƙarasowa cikin class ɗin tayi, hakan yasa idanun gaba ɗaya ƴan ajin ya dawo kanta, ɗan satan kallonta Teacher David yayi, can ƙasan maƙoshi yace.  
"Oya Go and sit down."  ai kuwa kamar jira take da sauri, ta nufi wani benci wanda bakowa akansa ta zauna.
Da sauri ta buÉ—e jakanta ta ciro paper da abun rubutu, sunanta ta rubuta ajikin papern sannan ta zubawa white board É—in nasu ido, cikin ranta take karanta questions É—in dake rubuce akan allon.
Daga  bayanta yaji anja hijab ɗinta ta ƙasa ,ƙin juyawa tayi dan tasan Teemah ce kaɗai zata mata haka.

Ɗan cije lips kyakkyawar matashiyar budurwan da ake ƙira da suna Teemah tayi, cike da takaicin rashin juyowan na LAYLERH,  ƙasa ƙasa tace.
"Wallahi Laylerh ke Æ´ar air ce, kina sane da cewar ban iya maths ba, me makon ki zauna akusa dani shine zakije ki zauna awani sit daban ko hmmm."
Ƙwafa tayi tare da hararan teacher david ƙasa ƙasa, cikin ranta tace.   "Banza tsohon maye, sai shegen son bada assigment da test, saikace an faɗa masa kowa ke gane darasin aljanu irin nasu, zaka gane wallahi kai da kunnuwan ƙwarangwal zan zana maka, sai injera maka sufuli aƙasansu."   Murmushi tayi tare da soma rubatawa takardan nata zero zero.

Laylerh kam da gangan taƙi juyowa, dan tasan da ta juyo Teemah bazata barta ba, sai tayi duk yanda tayi teacher David ya ƙwace musu takardan su.
Idanunta taɗan lumshe ahankali bayan tagama karanta questions ɗin, wani tunani ne yasoma shigowa ƙwaƙwalwarta, ahankali yanayinta ke sauyawa, zuciyarta ne ta fara bugawa da ƙarfi, yayinda numfashinta yasoma ƙoƙarin hautsunewa,  hannunta tasanya inda ta ƙanƙame jikinta, tare da sake rumtse idanunta,  gaba ɗaya jikinta ne ya ɗauki ɓari, wani irin zufa ne ya shiga keto mata.
Sannu ahankali  hoton haɗaɗɗun cikin idanunsa masu masifar kyau suka soma yawo acikin idanunta, laɓɓan bakinta ne suka soma rawa.
So take ta faÉ—i abun dake rai da kuma zuciyarta, kalma É—aya tak, ita takeson furtawa ako da yaushe, amma har yanzu takasa samun dama.
Tabbas tanason sa ni, tanason sanin wanene mamallakin wannan kyawawan idanun masu kyau da burgewa, meyasa yake shigowa cikin tunaninta akoda yaushe? batasan shi ba, batasan a ina zata ganshi ba, abu ɗaya kawai take iya fahimta amatsayinta na matashiyar budurwa, wanda ayanzune take ƙoƙarin mallakan hankalin kanta, wannan abu shine BUGUN ZUCIYA, tana da yaƙinin cewa lokuta da dama bada tunaninta take aiki ba, sannan kuma bugun zuciyarta na tafiya ne da abu guda.
Farinciki, ko akasinsa, tsoro, ko fargaba, rauni da kuma tarin ƙaddara, tayaya zata iya ɗaukan hakan, bata fatan zuciyarta ta tarwatse akan wannan dalilin.

(Kubiyoni, dan wannan labarin ba irin sauran bane, wannan daban yake da kowanne, kuyi comment da kuma votting  ɗina kamar yanda kuka saba, har ma fiye da haka, dan ta hakane kaɗai zan iya gane cewa lallai kuna enjoying labarina yanda ya kamata, sannan kuma karku manta ina alfahari daku akullum akuma koda yaushe, sannan ina neman Alfarma awajenku gaduk wani ko wata da ya karanta fejin nan, dan Allah kuyiwa YAYANA addu'a, akan  ALLAH yabasa lafiya😭. Then masoyana kuyi haƙuri da jinkirin dana samu na rashin kawo muku sabon labari da wuri, nagode sosai da nuna ƙaunarku agareni.🙏🏻)

      
       *Vote*
*and comment*

            

             *fatymasardauna*
1/19/21, 8:09 PM - Ummi Tandama: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*LAYLERH MALEEK*

*Writting by*
Phatymasardauna

*Wattpad*
@fatymasardauna

#Generalfiction

*Chapter 2*

Tunaninta ne ke neman juyewa, tamkar yanda taji duniyar na juya mata, idanunta ta kuma rumtsewa da ƙarfi, ƙoƙarin furta wani abu take amma takasa, saidai laɓɓanta dake motsawa ahankali, sannu ahankali bugun zuciya da fitan numfashinta suka soma daidaita, kyawawan idanun ne suka soma ƙauracewa ganinta, hakan yasa ta soma sakin ajiyar zuciya, idanunta ta buɗe
asanyaye ta maida hankalinta ga takardan dake gabanta, duka questions ɗin da aka rubuta, babu wanda batasan answer'n saba, saboda tayi karatu sosai akan test ɗin, hakan ne yasa cikin mintuna ƙalilan ta gama amsa tambayoyin.

Teemah dake ta faman rubuta masa shirme acikin paper'n ne ta kuma jawo Hijab ɗinta, cikin ƙasa da murya tace. "Laylerh wai bazaki juyo bane, kinataji ina miki magana tun ɗazu."
Laylerh kam bata juyo ba, yima tayi kaman bataji Teemah'n ba, tasan Teemah sarai Æ´ar rigima ce, yanzu tana juyowa kuma shikenan bazata saketa ba har sai tasa malami ya gansu, maybe ace ma suje suyi kneel down awaje.

Ganin Laylerh bata juyo bane yasa Teemah ta saki ƙwafa, abayyane tace "Wallahi zanyi maganinki Laylerh."

Mumurmushi kawai Laylerh tayi, tasan halin mutumiyar tata sarai, fitinanniya ce, karatun ma bawai ya wani damunta bane.

Mintuna 30 kacal teacher David yace suyi submit, nan yasoma bi line by line yana amsan papers É—insu.

Yana ƙarasowa kan Laylerh ya miƙa mata hannu alaman ta bashi paper'n nata, miƙo masa tayi kaman yanda ya buƙata, saidai batare da ta yi aune ba taji ya shafo hannunta, da sauri ta ɗago idanunta ta kalleshi, gani tayi ya wani irin lumshe mata ido, harda lashe laɓɓansa.
Da sauri ta janye hannunta, jin tacire hannunta daga nasa ne yasa shi wucewa sit ɗin Teemah, idanunsa da suka soma sanja kala ya watsawa Teemah harda ƙarin harara, cikin faɗa faɗa yace.
"Ke bani takardanki."
Miƙa masa takardan tayi, yana amsa ya juya ya tafi.
Har yakai bakin ƙofar fita daga cikin ajin ya juyo cikin kakkausar murya yace.
"LAYLERH MAHMOUD GWANI, by 10:00 am kizo office É—ina kisameni." Baijirayi me zata ceba ya fice daga cikin ajin.
Chapter 2 · 0% Book details