Sashe 9
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Abbu wanda ya kammala cin abincin sa ne ya É—aura idanunsa akan wayan Maleek, wanda ke aje nan kan saman table É—in, sauÆ™e idanunsa akan wayan kuwa, yayi daidai da soma Æ™iran wayar da akayi, kallon Laylerh da ke goge bakinta da tissue Abbu yayi, cikin kulawa yace. Â
"Laylerh É—auki wayarsa ki bisa da shi."
Jin maganan da Abbun ya faɗa ne, yasa lokaci ɗaya ta fara tari batare da ta shiryawa hakan ba, da sauri ta ɗauki ruwa tasha, tare da soma mutsustsuka idanunta, kallon da Abbu yayi mata ne yasa asanyaye ta ɗauki wayar tasa dake ta faman ringing.
MiÆ™ewa tsaye tayi tare da barin dining area'n, koda ta Æ™arasa cikin falon kaitsaye ta doshi Æ™ofar da zata sada ta da sashin sa. Â
Hakanan takejin ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, gaba ɗaya jikinta rawa yake, ahanakali ta ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar, tare da murɗawa ta tura ƙofar ciki, asanyaye taɗan kutsa kai cikin falon,  takun farko ta jefa ƙafanta akan wani lallausan carpet me taushin gaske, ga kuma wani irin daddaɗan sanyi me tafiya da ƙamshi daya daki kan fuskarta, ɗan lumshe idanunta tayi, tare da maida ƙofar ta rufe, idanunta ta baza wajen ƙarewa falon nasa kallo, komai na cikin falon atsare yake, da dukkan alama mamallakin falon bayason yawan tarkace, domin daga yanayin tsarin falon nasa zaka fahimci haka, inda aka zuba wasu haɗaɗɗun cushions masu kyaun gaske atsakiyar falon, sai kuma royal blue nd milk curtains da aka saka ajikin kowacce ƙofa da window dake cikin falon, kasancewar kujerun falon nada kalan royal blue shiyasa curtains ɗinma suka kasance royal blue nd milk, gefe guda kuwa wani jibgegen tv plasma ne, wanda aka ɗaurasa akan wani glass table me kyaun gaske, gefe da gefensa kuma wasu fararen flowers ne masu kyau, kallon haɗaɗɗen turkish carfet ɗin dake malale atsakiyan falon tayi, wanda shima kalan royal blue da milk ne, tsarin falon yayi kyau sosai, ahankali ta shiga takawa har ta ƙaraso tsakiyan falon, ganin bakowa afalon ne yasa ta ɗan ciji lips ɗinta, idanunta ta sauƙe akan wata haɗaɗɗiyar ƙofa dake cikin falon, wanda da dukkan alama kuma ƙofar bedroom ne.
Kallon wayartasa dake riƙe ahanunta tana ta faman ringing tayi.
Rasa yanda zatayi yasa ahankali ta ƙarasa jikin ƙofar zuciyarta cike da tsoro, ɗan murɗa handle ɗin ƙofar tayi, take kuwa ƙofar ta buɗe, kasancewar dama ba arufeta da kyau ba.
Ganin ƙofar ta buɗe ne yasa ta ɗan zaro danunta waje, sam batayi tunanin ƙofar abuɗe take ba shiyasa ta tura, atsorace batare da ta ƙarasa shiga cikin ɗakin ba, da ƴar siririyar muryarta tayi sallama.
Saidai shiru haka taji, ba ko motsin mutum bare tasa ran za'a amsa mata, sake kwaÉ—a wani sallaman tayi, still babu amsa.
Jin shiru ne yasa tayi tunanin cewa ko baya cikin ɗakin, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙarasa shigowa cikin ɗakin.
Wani daddaɗan ƙamshin da ya daki hancinta ne, yasa ta kuma lumshe idanunta tare da jan wani dogon numfashi, tashin farko kenan da taji tana masifar son ƙamshin, dan ko tantama baza tayi ba, wannan ƙamshin shine ƙamshin da taji yana fita ajikinsa.
Ɗan buɗe idanunta tayi ahankali, inda ta sauƙe su akansa.
Zaune yake agaban dressing mirror yayinda ya bawa ƙofar shigowa ɗakin baya, sanye yake da white trouser yayinda ya cire rigar jikinsa ya ajiyeta agefe, yanayin yanda ya juya baya ne yasa gaba ɗaya surar bayansa ta bayyana, wasu ƙananan hairs ne kwance lub akan white skin ɗinsa, yayinda fatar tasa ke wani irin shining, yanayin yanda ya juya baya ya kuma duƙar da kansa ƙasa shiya sanya ba'a iya ganin me yakeyi, kuma shima ba lallai yasan anshigo ɗakin ba.
Idanunta masu kyau ta zubawa fatar bayansa bata ko ƙiftawa, bakomai ya ɗau hankalinta ba kuwa face wani ɗan zanen tattoo wanda akayisa kaman rubutu dake manne a tsakiyan bayansa.
Ahankali taɗan lumshe idanunta, tare da budesu alokaci guda, gaba ɗaya ta shagala da kallon zanen dake kwance abayansa, hakanan taji shauƙin taɓa zanen na fusgarta, cikin nutsuwa ta soma takawa zuwa inda yake, wanda har zuwa yanzu bai ɗago kansa ba, baikuma yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba, da'alama dai baisan da shigowanta cikin ɗakin nasa ba.
Taku huɗu kacal ya rage mata ta ƙarasa garesa, ƙiran wayansa da aka kumayi ya katseta, wani sabon tsoro ne ya lulluɓeta dan gaba ɗaya tamanta me ya kawota ɗakin nasa,
Ɗagowa tayi ta kallesa, still har yanzu baiɗago kansa ba, murza ƴan yatsun hannunta ta soma yi ahankali dan batasan ta ina zata fara yi masa magana ba.
Akaro na barkatai kenan daya closing very beautyful eyes ɗinsa, ahankali ya ɗan juyo da kansa, batare daya ɗago ya kalleta ba, ya miƙo mata hannunsa alaman ta bashi wayan.
Kamar dama jira take da sauri kuwa ta saka masa wayar atafin hannunsa, saidai tasha mamaki ƙwarai dan batayi tunanin yasan da zuwanta ɗakin ba.
Ɗan satan kallon sa tayi, saidai bata iya hango full face ɗinsa, dan bawai ya juyo gareta bane, amma tana iya ganin rabin fuskarsa, da kuma gefen kumatu'nsa wanda ƙawataccen sajen dake wajen ya kwanta lub gwanin ban sha'awa.
Juyawa tayi cikin sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin, wajen sauri kuwa har ƙafafunta na harɗewa.
Tana fita daga cikin ɗakin ta saki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ɗan kallon cikin falon nasa tayi, sannan da sauri ta fice.
Koda ta fito daga sashin nasa, bata samu kowa anasu part É—in ba, dan haka kai tsaye É—akinta ta wuce.
MALEEK kuwa yana amsan wayar, picking call ɗin yayi tare da kara wayar akan kunnensa, har wanda ke kan wayan yagama bayanin da zaiyi baice ƙala ba, yana gama jin bayanin da akeyi masa acikin wayar ya kashe ƙiran tare da cilla wayartasa kan bed, ahankali ya ɗago da kansa tare da lumshe tsumammun idanunsa, numfashi yaɗan fesar sannan ya miƙe tsaye daga zaunen da yake.
Tsadadden wrist watch É—in dake É—aure ahannunsa ya duba. Â
9:15 pm daidai, cikin takunsa na isa, da kuma yanayin da ya saba ya Æ™arasa jikin haÉ—aÉ—É—en gadonsa, hannunsa yakai jikin bango, inda ya kashe hasken wutan É—akin, bedside lamp Ya kunna, wanda yake bada blue nd pink light, hayewa saman gadon yayi tare da lumshe idanunsa, gaba É—aya jin kansa yake agajiye. Â
LAYLERH.
Sake sakin wata sabuwar ajiyar zuciya tayi akaro na barkatai, ahankali ta matse pillown dake hannunta tare da lumshe idanunta.
"Yana da Kyau!." tafaɗa abayyane batare da ta sani ba, naked skin ɗin bayansa da kuma kwantaccen sajen da ta gani agefen fuskarsa ne keta yiwa idanunta gizo.
Sannu ahankali wani baƙon tunani ke shiga yana ratsa cikin ƙwaƙwalwarta, wanda asanadinsa ne zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi, saurin sanya hannayenta duka biyu tayi ta toshe kunnenta tare da rumtse idanunta.
Ahankali ta shiga ambatan sunan Allah, dan sosai zuciyarta ke bugawa, wani abu ne keyi mata yawo acikin kai da zuciyarta, take wani irin masifaffen kewar iyayenta ya rufeta, duk da kasancewar bata gama sanin daɗinsu agareta ba, alokacin da ta rasasu, amma tabbas ayanzu tana da buƙatarsu acikin rayuwarta, idanunta da suke alumshe ne suka ciko da ƙwalla, ahankali ta soma sakin shashsheƙan kuka.
Tabbas har yanzu ita yarinyace, sannan kuma tana da buƙatar me rarrashinta alokacin da take kuka, rayuwarta cike take da kewa, akwai abubuwa da yawa wanda hankali da tunaninta bazasu iya ɗauka ba, haƙiƙa bakomai zata iya jurewa ba amatsayinta na mace me ƙananan shekaru, gaba ɗaya rayuwarta fata ce da kuma gurbi, wanda batasan yaushe ne zasu cika ba.
Cusa kanta acikin pillow tayi tana me ci gaba da sakin shashsheƙan kuka ahaka har bacci ɓarawo ya ɗauketa.