← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 144

Sashe 93

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ci gaba da ruri wayan Abbou Jaheed d’in tayi, yayinda ya k’urawa screen d’in wayar idanu, zuciyarsa cike da fargaban abunda zai biyo baya nan da y’an kwanaki kad’an.
Ganin kuma da yayi wayar tasa ta kusa tsinkewa ne yasashi d’aga wayar tare da karata akan kunnensa, gudun kuma kada yawan maganansa yayi yawa acikin wayarne yasashi tashi tsaye ya fice daga cikin d’akin, don amsa wayar tasa awaje.
Abbou Khareem kuwa da har yanzu tausayi, da kuma aljabin daya shigesa najin matsalan Maleek da yayi baisake saba, maida kallonsa yayi ga Maleek d’in, tare dasa hannu ya tallafi hab’arsa.
Tausayin Maleek d’inne tsantsa ya cika masa zuciya, domin kuwa shi kansa yasan ya zafi da rad’ad’i had’i da ciwon rashin haihuwa yake, yasan abune me tsananin ciwo da k’unci, abune dake sa zuciyar mutum koda yaushe ta zamana cikin rauni, saidai kuma babu wanda ya isa gujewa k’addararsa, domin kuwa abunda Allah Ya tsara tabbataccene sai ya faru ko min jimawa.
Y’an guntun k’wallan da suka zuba masa yasa hannu ya share, tare da maida kansa jikin kujera, ahankali kuma cikin sanyin murya yace.
“Yah Allah Ina rok’onka da kabawa Maleek ikon cin wannan jarrabawa mai tsananin k’una da ciwo daya sameshi, Allah kasa ya d’auki k’addararsa da hannu bibbiyu, domin kuwa kafi kowa sanin abunda ka shirya.�
D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da soma ambaton sunan Allah dan samawa kai nutsuwa.
Baiwani jima ahaka ba kuwa Abbou Jaheed ya dawo cikin d’akin bayan ya gama amsa wayar.
Kallon d’an uwansa yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Alhaji Farouk ne ya k’ira nakuma shaida masa cewa Maleek ya samu accident, yanzu haka Insha Allah yace suna zuwa shida iyalansa.�
Kai Abbou Khareem ya jinjina tare da cewa.
“Allah Ya kawosu lafiya.�
Daganan kuwa shiru sukayi babu wanda ya sake cewa d’an uwansa wani abu.

Acan gida kuwa duk yanda Laylerh taso samarwa kanta nutsuwa ta kasa, abubuwa da yawane ke faman ci da azalzalan zuciyarta wanda hakan yasa taji bazata iya jurewa kwanciyar da takeyi d’in ba.
Ahankali ta yaye blanket d’in da Najeeb d’in ya rufa mata, tare da zuro da k’afafunta k’asa, yanzun kam Alhamdulillahi domin kuwa ciwon kan da takeji d’in ya d’an lafa mata, duk da kuwa cewar kannata baidaina ciwo duka ba, amma baya mata ciwo sosai kaman na d’azu da takejinsa kaman zai rabe biyu.
Hannunta tasa abayanta ta k’arasa zuge zip d’in rigar dake jikin nata, tare kuma da zare rigar gaba d’aya daga jikinta.
Hakanan taji tanason yin wanka, saboda tana da yak’inin cewa yin wankan zai taimaka mata ta d’anji kuzari ajikinta.
Doguwar rigar da ta cire d’in ta d’auka tare da jefata acikin dustbin d’in wanki, cikin tafiyarta me d’auke da sanyi ta k’arasa gaban makeken drawer’n dake cikin d’akin, anutse ta bud’e murfin drawer’n inda ta ciro wani mini pink towel sabo k’al ta d’aura ajikinta.
Brush da kuma Maclean d’inta dake aje akan mirror ta d’auka, kai tsaye kuwa ta wuce toilet.
Kasancewar kuma akwai komai da komai na kayan wanka acikin toilet d’inne yasa tana shiga ta zare towel d’in dake jikinta, d’aya daga cikin showercap d’in dake jere akan wani abu na glass dake cikin toilet d’in ta d’auka tare da suturce gashin kanta dashi, tayi hakanne kuma saboda sam bataso yau d’in ruwa ya tab’a kanta, saboda ana busa sanyi sosae.
Ruwa me d’an d’umi ta had’awa kanta acikin had’add’en bathtub d’in wankan nasu me yanayi da jikin kakkauran glass.
Ahankali ta shiga cikin babban bathtub d’in ta kwanta, tare da nutsa duk jikinta acikin ruwan, wanda dad’i da kuma d’uminsa yasa ta lumshe idanunta ahankali.
Take kuwa kaman jira idanunnata suke ta rufesu, kyakkyawar fuskarsa ce ta soma yi mata gizo, wanda hakan yasa bisa dole ta karyar da wuyanta gefe, cikin muryarta da tayi sanyi kana take fidda rauni sosae tace.
“Banason ka tafi ka barni, domin kai bawai iya duniyata bane kawae, gaba d’aya rayuwata ce kai, bana fatan ciwo da kuma k’unci su d’ore acikin rayuwarka Yah Maleek!!!�
Ahankali wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro kan kumatunta, yayinda kuma lokaci d’aya ta sakejin matsanancin tausayin kanta da kuma na Maleek d’in ya cika mata zuciya.
Asanyaye cikin rashin kuzari tayi wankan, koda ta fito daga cikin bathtub d’in kuwa alwala tayi domin taga yamma ya d’an soma rufawa sosai.
Fitowarta daga cikin toilet d’in kuwa yayi daidai da bugawan agogon dake nuna cewa daidai lokacin k’arfe biyar tayi.
K’arasawa gaban dressing mirror d’inta tayi tare da d’aukan wani towel ta tsane ruwan jikinta.
Body lotion na Nevea me dad’in k’amshi ta shafa ajikinta, batare kuma da tunanin shafa powder ko kuma yin kwalliya ba ta k’arasa gaban sif d’in kayanta.
Wani riga da sket d’in Australia’n lace me kalan blue da golden ya ciro, wanda akayi masa simple style d’in pencil sket da kuma riga fitted wanda iyakanta cinyarta.
Koda ta sanya kayan kuwa sosae sukayi mata kyau, musamman ma rigar da ta zauna ajikinta, tamkar ma ajikinta aka d’inka rigan.
Dogon gashinta ta nannad’e da ribbom, tare da d’auko wani siririn Australia’n vail ta yafa ajikinta, wanda ya tsaya daga wuyanta zuwa cinyoyinta, kasancewar kuma d’an kwalin kayannata babbane yasa ta d’aurashi akanta irin d’aurin nan da ake parking d’insa a tsakiyar kai, sosai kuwa d’aurin ya sake fito da kyaun da tayi, wani cool parfume me dad’in k’amshi ta fesa, batare kuma da ta sake kallon madubi ba ta zura wasu new designer half cover shoe ak’afanta kai tsaye ta fice daga cikin d’akin.
Direct sashin Oum Ayush ta nufa koda ta k’arasa part d’in Oum Ayush d’in kuwa ta samu harta kammala had’a abincin da zasu kai asibitin, yayinda Fou’ad kuwa tuni ma ya koma asibitin.
Ganin Laylerh’n ne kuma yasa Oum Ayush d’auko mayafinta, domin dama itama already ta shirya don komawa asibitin.
D’aya daga cikin basket d’in da food flask d’in abincin ke ciki Laylerh’n ta d’auka, yayinda Oum Ayush kuma ta d’auki sauran.
Kusan atare suka fito daga cikin sashin na Oum Ayush d’in tana me tambayanta.
“Ya ciwon kannata?.�
“Da sauk’i.� Ta bawa Oum Ayush d’in amsa adaidai lokacin da suka iso bakin motar Oum Ayush d’in.
Kamar dae yanda suka tafi d’azu haka yanzun ma Oum Ayush da kanta tayi driving.
Tunda suka d’auki hanyar asibitin kuwa Laylerh keta faman sak’awa da kuncewa, yayinda acikin zuciyarta take fata da kuma burin idan taje ta samu Maleek d’in ya farfad’o, domin kuwa tasan akasin hakan zai k’ara sata acikin wani sabuwar fargaba da kuma fad’uwar gaba.
Isowarsu cikin asibitin kuwa yayi daidai da isowar Alhaji Farouk da kuma Ilayansa wato Hajiya Buzuwa da kuma Munnira wanda take matsayin amarya, duk da kuwa cewar asibiti suka zo amma fuskarnan tata ayalwace take da meckup yayinda kuma kallo d’aya kawae zakayi mata ka fahimci cewa, cike take da yauk’i.
Kasancewar kuma motarsu ce agaba yasa sam basu lura da ta su Laylerh’n ba, suna gama daidaita parking kuwa suka fito direct suka nufi cikin asibitin.
Su kuwa su Laylerh sam basu ma lura dasu ba, domin saida su Munnira’n suka wuce kafun su Laylerh suka fito daga cikin motar ita da Oum Ayush.
Hannayensu d’auke da basket suka nufi sashin da aka kwantar da Maleek d’in.
Daf da zasu haura steps d’in da zai sadasu da d’akin Maleek d’inne kuma bisa tsautsayi Laylerh tayi missing d’aya daga cikin steps d’in take kuwa tatafi su ta fad’i k’asa.
Wanda hakan yayi sanadiyar zubewar gaba d’aya kayan dake hannunta, fad’uwan da tayinne kuma yasa ta saki wani irin k’ara, saboda ta d’an bugu kad’an ahannunta.
Adaidai lokacin kuwa zuciyar da bugawanta ke tafiya slowly tayi wani irin harbawa, har saida gangar jikin mamallakin zuciyar nan ta samu motsawa.

*(Bani da enough charge shiyasa na muku wannan kud’an rage lokaci kafun gobe Idan Allah Ya kaimu.
Shin me kuke tunani akan Maleek? Idan Alhaji Farouk yaji matsala da kuma lalurarsa zai bashi auren yarsa? koma me Insha Allah Zakujishi a page d’in gobe.)*

*9:10 pm*
2/19/21, 9:36 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

*Chapter 54*
Chapter 93 · 0% Book details