Sashe 89
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Saurin juyawa Abbou Jaheed yayi da k’arfi ya rumtse idanunsa wanda suke cike tab da k’walla, k’wallar kuma dake d’auke da abubuwa da yawa, wani irin karaya da rauni zuciyarsa tayi, wanda hakan yasa dole yasa hannu ya dafe zuciyartasa, saidai kuma duk yanda yaso hana hawayen dake cikin idanun nasa fitowa, abun yaci tura, dole haka yanaji yana gani wasu hawaye suka ziraro masa.
Awajen Abbou Khareem ma kuwa hakan take domin shima tuni idanunsa sun cika da k’wallan tausayin y’ay’annasu.
Fou’ad kam dama shi mai raunine sosae akan abokinnasa, sanin kuma abundake cikin zuciyar Laylerh da Maleek d’inne da kuma yanda Laylerh’n ke kukane yasashi sanya hannu ya kama kansa, domin kwata kwata bashi da ikon hana idanunsa kuka ayau, watarana abanza ma haka yake kuka, bare yau da abun kukan ya samu, shi Soja ne amma yasan yana da raunin zuciya sosai.
Najeeb.
Tayaya zai iya d’auke idanunsa daga kallon Laylerh’n, hak’ik’a duk da cewar kukan da Laylerh’n keyi yana matuk’ar tab’a masa zuciya, amma hakanan ya samu kansa da kasa janye idanunsa daga gareta, duk da kuwa cewar idanun nasa sun kad’a sunyi jajur tamkar wanda aka watsawa borkono, k’warai a yanzun shi kad’ai yasan meyakeji acikin zuciyarsa, wanda ayanzu bazai tab’a iya fassarawa kansa ma’anan hakan ba.
Ahankali cikin son tausasa harshe da kuma bawa Laylerh’n baki, Oum Ayush ta k’arasa zuwa gareta, hannunta tasa ta dafa kafad’an Laylerh’n, cikin muryarta da ke cike da tsananin tausayin su asanyaye ta k’ira sunan Laylerh’n, wanda har yanzu bata daina kukan da takeyi ba.
“Laylerh!!�
Oum Ayush ta sake kiran sunanta akaro na uku, hade dasa hannunta ta jawo Laylerh’n jikinta.
Jin da tayi kuma Oum Ayush din ta rik’e ta ne yasa Cikin sheshshek’an kuka ta d’aura kanta akan kafad’an Oum Ayush d’in, k’ok’arin fad’in wani abu takeson yi amma ta kasa, saboda tuni kuka ya riga da yaci k’arfinta.
Ahankali Oum Ayush ta soma kokarin zare hannun Maleek d’in daga rik’on da Laylerh’n tayi masa.
Cikin sa’a kuwa ta samu Laylerh’n ta saki hannun Maleek d’in.
“Muje ki huta kinji, ya isa haka ki daina wannan kukan, ai Maleek d’in ba mutuwa yayi ba, yana da rai kuma zai bud’e idanunsa Insha Allah.�
Oum Ayush ta fad’i hakan cikin tausasa murya tare dajan Laylerh’n anutse ta zaunar da ita akan wani kujera dake d’an gefe da gadon da Maleek d’in ke kwance kana itama ta zauna a gefen Laylerh’n, hakanne kuwa yasa ahankali Laylerh dake ta faman sakin sheshshek’an kukanta da har yanzu ya kasa tsayawa ta d’aura kanta akan cinyar Oum Ayush d’in. Saidai kuma karfin kukan nata ya d’an ragu ba kaman d’azu ba da gaba d’aya sautinsa ya cika d’akin.
Haka gaba d’aya d’akin ya d’auki shiru, ba abunda ke tashi acikinsa sai fitan numfashi da kuma amon gunjin kukanta.
Hakika gaba d’ayansu duk acikin wani irin yanayi suke musamman ma Abbou Jaheed da zuciyarsa ta riga da tafi na kowa rauni awajen, bakuma iya rauni kawai ba, wani abune na daban ayanzun ke damun zuciyarsa akan Laylerh da Maleek d’in.
Ahankali Dr.Mouhammad ya turo kofar dakin ya shigo, bakinsa dauke da sallama, wanda hakanne kuma yasa duk hankalinsu ya koma kansa.
Ganin irin kallon da sukeyi masa ne kuma yasa shi d’an fad’ad’a murmushi akan fuskarsa sab’anin da da yanayin fuskartasa ke d’auke da damuwa.
“Ya naga duk kuna kallona kodai ya Far fad’one?�
Dr.Mouhammad d’in ya fad’i haka cikin raha da kuma d’an sakin fuska.
Kusan kowannensu ajiyar zuciya ya sauk’e, asanyaye Abbou Khareem yace.
“Aa har yanzu dai bai farfad’o ba, fatan mu dai shine Allah Yasa ya farfad’o d’in.�
“Karka damu Insha Allah Zai farfad’o, wannan matarsa ce?.� again Dr. Mouhammad ya tambaya adaidai lokacin da ya d’aura idanunsa akan kyakkyawar matashiyar budurwar dake sakin kananan sheshshek’a wato Laylerh kenan.
Tabbas tambayar tasa tazo musu awani irin siga, hakan yasa suka d’anyi shiru, saida aka d’an d’au sakanni kafun Abbou Jaheed ya numfasa, asanyaye yace. “Aa k’anwarsa ce.�
Wata irin gagarumar ajiyar zuciya Dr.Mouhammad ya sauk’e tare da sake kallon Laylerh’n da kyau, sosai kuma amsan da Abbou Jaheed d’in ya basa ya sashi samun gamsuwa, tare dajin wani sanyi aransa, domin kuwa da ace kyakkyawar yarinyar da yake gani d’in ta kasance matar Maleek d’inne dakuwa akwai matsala sosae, domin asonsa zaifi son jin cewa Maleek d’inma bashi da mata, domin kuwa sabuwar matsalan daya fuskanta ta sanadiyar accident d’in da yayi bak’aramin ci baya zata kawo garesu ba.
Ahankali ya kawar da kansa daga kallon Laylerh’n, tare da k’arasawa gaban gadon da Maleek d’in ke kwance, ruwan allura da kuma sirinjin alluran dake hannunsa ya had’a, anutse ya so kawa Maleek d’in alluran akan damtsen hannunsa, wanda jijiyoyinsa suka fito sukayi rad’au akai.
Bayan ya gama yi masa alluran ne kuma ya juyo ya kalli Abbou Jaheed.
Kasancewar kuma yasan cewa Abbou Jaheed d’in babban mutum ne da sunansa ya zagaye wajeje da dama, saboda kud’i da kuma halin k’irkinsa hakan yasa cikin basa girma yace.
“Alhaji Jaheed Gwani idan babu damuwa ko zaka iya biyoni office d’ina?�
Jin abunda Dr.Mouhammad d’in ya fad’a ne kuma yasa Abbou Jaheed jinjina kae ahankali yace.
“Ba damuwa Doctor muje.�
Kai Dr.Mouhammad ya jinjina kafun ya wuce gaba, Abbou Jaheed kuwa ya bisa abaya, domin Jin cikakkiyar rahoto akan d’ansa Maleek.
*(Afuwan bansamu daman turowa da wuri ba wallahi two days ba anutse nake ba shiyasa, duk typing d’in rabi da rabi atsaye nake kareshi, amma Insha Allah Zanyi k’ok’ari na gobe yafi nayau yawa.)*
*Friday12/2/2021*
*11:33 am*
2/13/21, 9:39 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Not Editing*
*Chapter 51*
Fitan su Abbou Jaheed da kuma Dr. Mouhammad daga cikin d’akinne yasa Najeeb da gaba d’aya yaji duk tsayuwar da yake ta isheshi ya juya tare da kama hanya ya fice daga cikin d’akin, Laylerh kuwa da zuwa yanzu kukan nata ya tsagaita sosai, sake kwantar da kanta akan cinyar Oum Ayush tayi tare da lumshe idanunta, saboda kukan da tayi d’inne kuma yasa lokaci d’aya cikin abunda bai wuce 15 minutes ba bacci me nauyin gaske ya d’auketa, duk da cewar kuma bacci take, amma hakan bai hanata sakin wani gunjin kuka acikin baccin nata ba, yayinda daga gefe guda kuwa ajiyar zuciya kawai take ta sauk’ewa akai akai.
B’angaren Abbou Jaheed kuwa direct office d’in Dr.Mouhammad suka nufa, suna shiga cikin office d’in kuwa Dr. Mouhammad d’in yayiwa Abbou Jaheed nuni da wata kujeran da musamman aka ajiye ta dan zaman bak’i na musamman.
Zama Abbou Jaheed yayi, tare da d’ago kansa ya kafe Dr.Mouhammad da idanu, wanda ya zauna akan permanent sit d’insa na Office.
Ahankali ya bud’e wasu files dake gabansa ya shiga dubawa, ak’alla kuma wasu y’an mintuna ya d’auka yana duba files d’in, saida ya kammala sannan ya d’anyi rubutu acikin kowannensu, d’ago kansa yayi ya kalli Abbou Jaheed da har yanzu baidaina kallonsa ba.
Shiru yayi tare da d’an sunkuyar da kansa, domin kuwa zuciyarsa cike take da fargaba da kuma halin da Abbou Jaheed d’in zai samu kansa aciki matuk’ar ya sanar dashi hak’ik’anin gaskiyar abunda ya faru da d’ansa, saidai kuma yasan dole babu yanda zaiyi, wanda ya wuce ya fad’awa Abbou Jaheed d’in komai, domin babu wani bawa aduniya daya wuce wa samun irin wannan k’addaran.
“Kai nake saurare Dr. Mouhammad amma kuma har yanzu naji baka ce komae ba, kodai akwai wata matsala babba daya samu Maleek ne wanda bakason fad’a miji?.�
Abbou Jaheed ya fad’i hakan cikin yanayi na d’an damuwa, domin daga yanda yaga yanayin Dr.Mouhammad d’in yasan baiwuce ace masa akwai wata gagarumar matsala.